Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
AURENA
Da dai sauransu,
SURBAJO RETURN CIGABAN SURBAJO YANZU 100 NE DAGA YAU ZUWA KWANA BAKWAI MESO YA TURO KUƊINSA,KAR KU BARI ABAKU LABARI*
*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*A TURO SHAIDAR BIYA TANAN 07044600044*
*Free book*
*15*
Yana ji yana gani tasa kai tayi wucewarta ƙarƙashin rakiyar ɗaya daga cikin yaran saurayinta.
Ayan bin bayanta yayi da kallo cike da danasanin saninta da yayi.
"ku ɗaukemin wannan ɗan iskan kuje dashi ɗakin matattu"cewar saurayin na junaiha.
Ɗaukarshi akayi zuwa ɗakin daa ka kira ɗakin matattu,koda ya shiga in banda wari ba abinda ke tashi acikin ɗakin.
Dubansa yakai atsanake cikin ɗakin wasu mazane su biyu ciki se yarinya ɗaya wacce shekarunta bazasu gaza sha huɗu ba.
Guri ya samu ya zauna yana binsu da kallo,suma kallonshi sukayi ba wanda yace komai sede kallon.
********
Junaiha kamar yadda saurayinta ya koyar da ita hakan tayi,ayko sosai mutane suka tausaya mata.
Nanfa aka ɗaukota zuwa Kano,tana ta rusa kuka,lokacin da mahaifiyarta taganta ta kuma samu labarin abinda ya faru sosai ta firgita
inda tace"kuje asibiti a duba lafiyarki sannan aje gurin ƴan sanda akai report.
Ayko haka akayi,duk gwajin daya dace likita ya mata,sede abinda bata tsammataba watakan aduba aga ko anmata fyaɗe sosai taji tsoron hakan dan duk abinda take aykatawa iyayenta basu sani ba,
Koda result ya fito na cewa an kwanta da ita kuka tasa,inda mahaifiyarta itama kukan take tare da sauram ƴam uwanta.
gIda suka dawo zuciyarsu ba daɗi,yayanta ne ya takura da tambaya,seta faɗi yadda akayi buɗar bakinta se cewa tayi.
"Tun kan tsautsayin ya faru damu a hanya ayan ya kaini gidansa inda acan ne ya yaudareni ya kwanta dani"ta faɗi cikin matsanancin kuka.
Kaurewa gurin yayi da salati inda hajiya tace"Au dama mayaudarine bamu xani ba ayko Allah ya isa tsakaninmu dashi ya cucemu,da Allah zesa ya dawo duniya wallahi kotuce zata rabamu"ta ƙarasa maganar tana kuka.
Haka kowa yay ta tofa albarkacin bakinsa na ɓatanci ga ayan gamuda tausayawa junaiha sabida yarinyat kirkice.
******
Nasir jin ɗan uwansa kwana biyu be samunsa a wayane yasa ya taso da kansa zuwa gidan nasa,sede labarin daya samu gun megadinsa wai an kasheshi ba ƙaramin ɗaga hankalinsa yayiba.
Da ike sun taɓa zuwa gun junaiha tare da ayan hakanne yasa yaja mota zuwa gidansu.
Inda da ƙyar iyayenta suka amince aka barta taimasa bayani harda bashi tabbaci agabanta aka kasheshi aka ba karnuka gawar.
Yanke jiki nasir yayi ya faɗi agurin yana kuka,"yaya me yakaika kaduna bayan ka barota,wayyo ɗan uwana"haka nasir yay ta kuka da ƙyar aka rarrashe shi yayi shuru,ya miƙe jikinshi na ɓari ya faɗa mota.
Allah ne kawai yakaishi ƙauyensu lafiya,dan ko gabanshi be gani lokacin dayake tuƙin
Iyayenshi na ganinsa suka san ba lafiya ba,ayko be ɓoye musu ba ya faɗa musu abinda ya samu ayan ɗin.
Tashin hankali baa sa maka rana,ba wanda labarin mutuwar ayan ɗin bata girgizashi.
Haka akai masa sallar gawa ba tare da gawar ba,sannan aka fara xaman makoki.
Iyayensa sunyi tawakkali,basu tsaya wani bincikeba tunda ga ganau ba jiyau ba ta faɗa musu.
********
Kwanan ayan biyar a wannan ɗakin inda duk sauran biyun maza an kashesu agabansa shida wannan yarinya wacce firgici ke sawa ta ɓoye kanta abayansa tana ihu
Abinci se sun ga dama suke basu inda ayan da ya fara ci yakeji ya ƙoshi se yaba yarinyar,dan yana tausayin kansa amma yafi tausayawa yarinyar,dan ƙarama kamarta yadace ace tana gida gaban iyayenta.
Cikin daren ranar aka fara ruwa kamar da bakin ƙwarya,inda suke dama kusa da kogine,suna jiyo ƙugin ruwa,inda ɗakin da suke ciki rufinsa ya ɗaga ruwan zubowa kawai yake yana jiƙasu
Gasu a ɗaure suke jikin sarƙa guda shida yarinyar,yana kallon yadda take rawar sanyi amma ya gaza taimaka mata da komai.
Kamar saukar aradu ruwan yayo ambaliya cikun ɗakin ya rusa ɗakin dama na kwano ne,da wani mahaukacin gudu ya kaɗa su cikin kogin.
Wayyo Ayan da ƙarfin hali ƙoƙarin ya taimaki yarinyar yake amma ruwan yafi ƙarfinshi haka ruwan ya dinga garasu tun yana jiyo ihunta har ya dena ji,shima tun yana jin har ya sume.
Ruwan seda yayi tafiya dasu me nisan gaske sannan ya watsar dasu bakin gaɓa.
Suna tare sabida sarƙar da aka ƙullesu tare.
Wani ɗan ƙauyene inda aka watsar dasun dan haka ana xuwa bakin kogin ɗibar ruwa.
Rukunin wasu mata ne suka zo ɗibar ruwan suka gansu,ayko nan fa suka shiga duba fuskokinsu,ay suna duba fuskar yarinyar suka koma suna ihun"jamaa kuzo ga ƴar gidan megari data ɓace a bakin kogi"
ƙaramin garine cikin ƙanƙanin lokaci me gari ya iso da tawagarsa dan yarinyar watanni biyu kenan da ɓacewarta,sunzo ɗibar ruwa da ƙawayenta,ruwa ya jata to anata nema baa gantaba segashi yau ruwa ya dawo da ita
Surbajo for life.
[6/14, 10:22 PM] ZAHRA SURBAJO: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAZINATA NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*littafin surbajo return yadawo normal price ɗinshi 500 Kar akuma turo 100 in ka turo kayi sadaka,kar akuma turo naira ɗari kar akuma turo naira ɗari,yau 14-06-2023 in ka turo kayi sadaka*
*16*
Kurar shanu aka kawo aka kwashesu xuwa cikin gari.
Masu maganin gargajiyane suka rufu akansu har Allah ya taimaka suka dawo hayyacinsu
Abinci aka basu suka ci sannan sukai wanka,shide ayan tunda ya fito wankan ya kwanta ya fara bacci cikin natsuwa, dan ya wahala.
Bashi ya tashi a baccinba se washe gari,wanka yayi ya rama sallah sannan yaci abinci aka kaishi gun me gari.
Cikin sakin fuska megari ya tarbeshi yana bashi gurin zama.bayan sun gaisa ne yace"bakunanmu ɗauke da tarin tambayoyi,amma kana bacci ita kuma fatima bata sanar damu komai ba tade ce da ruwa yakaita wata gaɓar ta farka tana neman hanya ta haɗu da wasu mutane suka saceta aketa gana mata azaba tare daku harde ruwa ya sake kawoku nan"
"eh to ni ba tare mukaje gurinba,ni yaudarata akayi aka kaini"daga haka ya kwashe komai ya sanar dasu.
Sosai suka tausaya masa, inda kowa ke tsinewa junaiha.
Ƙauyen jallo sunan ƙauyen,kauyene me cike da mutane manoma wanda basa gajiya da noma,shiyasa basa rasa abinda zasuci.
Akwai ƙarancin wayewa da ilimi tattare da mazauna garin shiyasa kallo ɗaya zaka musu ka fahimci hakan.
Sosai suke karrama Ayan hakanne yasa yayi zamansa cikinsu ya ɗan huta dan beson abinda xe sake haɗashi da wata mace kuma.
*******
Junaiha ta samu labarin mutuwar saurayinta acikin wannan ruwa da akayi daga bakin ɗaya daga cikin yaransa wanda ya tsira da ƙyar
Taji mutuwar sosai dan kuka tayishi kamar itama zata mutum,bata ma tsaya tambayat su ayan ba dan tasan ya jima da kasheshi.
Bayan watanni uku da faruwar lamarin ciki ya bayyana ajikin junaiha,
Mahaifiyarta da ƴanuwanta basu tsaya tunanin komaiba sukace na marigayi ayan ne..
Tasan cikin na saurayintane to amma yanzu be raye batasan ya zatayi da iyayenta da cikinba hakanne yasa koda akace na Ayan ne bata musa ba.
Number nasir suka karɓa agurinta suka kirashi,inda suka buƙaci ya basu address ɗin garinsu
Beyi wani tunaniba ya basu,dan shima ya kwana biyu acan yana kwantar da hankalin iyayensu tun bayan rasuwar ayan.
Junaiha da iyayenta sun isa daɓaro cikin ɓacin rai dan da ƙyar suka amince da a zauna ayi magana ta fahimta.
"ayan ya yaudareta da cewa ze kawota gurinku ku gaisa ya mata ciki,dan alhakinta ne ma ya kamashi yasa ya gamu da ajalinsa dan haka mude bazamu yarda ba"cewar yayan junaiha rai aɓace.
Salatine ya kaure agurin kana kuka ya biyo baya"bayin Allah ɗana ba fasiƙi bane taya zewa ƴarku haka dan Allah karku ɓatamin gawar ɗa don Allah." cewar me unguwa yana zubar da ƙwalla.
Nasir ne ya amshi zancan muryarshi na rawa yace"koda ace yayi abaya yaya ya tuba yabar saɓon ubangiji,dan haka kiji tsoron Allah tunda har yasoki da aure baze miki haka ba junaiha"
''wallahi shine nasir in bashi bane ay bazan masa ƙazafi ba"cewar junaiha cikin matsanancin kuka.
"Yanzu ya kukeso ay muku don Allah arufe maganar,tunda shide ya riga daya mutu,"cewar nasir.
"au nasiru nufinka ka amince ɗan uwanka fasiƙine kenan,to wlh vazata saɓuba ni ban amince ba kuma bazan amince ba"cewar mahaifiyarsu tana hawaye.
"mama don Allah kudena jainja,dasu abarsu zuwa ta haihu,se agwada jinina dana yaron,tunda jininmu komai iri ɗayane da yaya,gashin kan yaya ko nasan agidansa bazaa rasa ba,tunda shikaɗai ne ke rayuwa cikinsa"
Jikin junaiha ne yayi sanyi jin abinda nasir ya faɗi amma se ta maze tayi kamar bata tsorata ba.
"eh mun amince da hakan dan ƴarmu kowa ya shedeta bata ƙarya,amma kamin ta haihun dole a ɗauki nauyinta har zuwa lokacin"cewar yayanta
"mun amince mude don Allah kuyi shuru kar zancan ya fasu"cewar nasir.
Kuɗi masu yawa aka basu sannan suka tafi,nasir ya koma bayan ya rakasu .
Gun iyayenshi ya koma dan ya kwantar musu da hankali yace"koda kukaji na amshi ciki ay bawai dan yayan yayi bane,kawai dan kar su ɓata masa gawa,shine yasa amma yanxu in ta haihu ay zaa gwada kuma inada yaƙinin ba nashi bane,amma kamin lokacin dole semunyi haƙuri munbi duk abinda sukeso."
Haka de yay ta rarrashinsu har suka sakko suka ci gaba da nemawa ayan rahamar Allah.
Surbajo for life.
[6/15, 1:54 PM] ZAHRA SURBAJO: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAZINATA NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*Surbajo beauty luxury,duniyar gyaran fata,muna siyar da skin care product masu kyau da maana,wanda zasu gyareki ki dawo yarinya,kama daga cire ƙurajen fuska dana jiki,wanda mai ya ɓata musu jiki,masu son nasa fari,da masu son fito da aynihin fatarsu,to ku garzayo surbajo beauty luxury dan magance matsalarku da kuɗi ƙalilan,07044600044*
*littafin surbajo return yadawo normal price ɗinshi 500 Kar akuma turo 100 in ka turo kayi sadaka,kar akuma turo naira ɗari kar akuma turo naira ɗari,yau 14-06-2023 in ka turo kayi sadaka*
*17*
Ayan zamansa a garin ya samu shaƙuwa sosai tsakaninsa da fatima,koyaushe tana tare dashi,xuwa yanzu in ka ganshi bazaka taɓa cewa yasan birni ba bare har ace ya fita ƙasar waje.
Ya karɓi rayuwar ƙauye da hannu biyu,ba tare da ya nuna ƙyamarsu ba.
A duk sanda yake tare da fatima tana sashi nishaɗi,dan yarinyar akwai wawta wacce kesawa cikinshi ciwo sabida dariya.
Yauma kamar kullum sun fita shida ita vayan gari suna hirarsu,can fatima tace."Ɗan birni wai ka taɓa hawa jirgin sama kuwa?"ta faɗi tana ƙureshi da ido.
Murmushi yayi yace"na taɓa hawa mana ya akayi?"
Gyara zama tayi tace "wai hi jirgin in aka hau hi,ana bacci"?ta faɗi tana murmushi
"meze hana bacci anayi mana sosai ma kuwa"
"To ay abinda ke ban mamaki,in ka hau yanzu kamar ni meyin kahin dare to yazanyi in inaso inyi kahin,ni hine damuwata"ta faɗi tana ɗan tagumi.
Dariyace ta kama ayan seda yayi me isar sa sannan yace yana riƙe ciki"seki shiga banɗakinsu kiyi"
"Jar uba yo ni mi ze kaini higa jirgi in tahi tsaye,tabɗijan,ay ka ganni.lahira kaini ankayi"ta faɗi tana riƙe baki gamida zare ido.
Sosai ayan yake darawa da ƙyar yace"to me ze faru dan kin miƙe,?"
"Ay in na miƙe kace ubana goma,yo to kana ganinfa yadda yake higewa sama to in miƙe in hangi saman da kyau kenan aa,sabida masu gadin saman ma se suce ni bani da kunya kowa a zaune ni na miƙe"
Hawayene suka fara zubowa ayan sabida dariya.
Haka taci gaba da bashi dariya har laasar sannan suka wuce gonar megari dan su ɗan tayashi ayki duk da de shi ayan ba iyawa yayi sosai ba.
"ranka ya daɗe yaron nan fa naga ka saki jiki dashi da ƴar wajenka karfa aje ya cutar da ita fitar da suke yi bayan gari tunda de mu ay ba saninshi mukayiba."cewar malam ado ɗaya daga cikin mazauna garin.
"watakan malan ado zancanka gaskiya ne sede ni na masa kyakkyawan zato insha Allahu nasan ba abinda xe faru yarone me hankali wlh"cewar megari.
So tari ansha kawo munafuncin ayan cewa ya goya fatima ko ya riƙe mata hannu wanda shi ayan kallon ƙaramar yarinya sosai yake mata,shiyasa yake mata hakan,amma su ba haka suka tsammata ba.
********
Cikin juhaina kullum ƙara girma yake nasir na kulawa da ita,ba tare daya gajiba gamida adduar Allah ya jiƙan ɗan uwansa.
Ko kaɗann be gamsu da cewa cikin ɗan uwansa bane amma yasan ko ba jima ko ba daɗe gaskiya zata bayyana.
********
Yau ayan ya tashi da som zuwa gida dan yana yawan mafarkin yan uwanshi,hakanne yasa ya sanar da me gari,.
Gashi fatima bata da lafiya kwana biyu tana fama da kumburin ciki,wanda ya takuramata cikin ya kumbura,se kuka take,ya rasa ya zeyi gashi ba kayan ayki bare ya dubata.
Haka akaita jiƙa mata magani tana sha tana amai.
Koda yazo mata sallama kuka tasa masa da ƙyar ta saki hannunsa shima seda ya mata alƙawarin ze dawo.
Me gari ya vashi kuɗin guzuri sannan aka rakashi tasha,inda ahanya ya sayi face mask sabida idon sani sannan akaci gaba da tafiya.
Bayan tafiyarshi ne aka kwashi fatima zuwa asibitin cikin gari dan nema take ta fita hayyacinta,sabida ciwon
Koda suka je asibiti awon farko likita ya tabvatar musu da cewa fatima ƴar kimanin shekaru sha huɗu na ɗauke da ciki har tsawon watanni bakwai batare da kowa yasani ba,dan yanzun haka naƙuda take.
Tashin hankali baa sa maka rana,me gari najin haka ya yanke jiki ya faɗi agurin,
Sauran mata ko kuka suka sa,musamman da likitan yace cs zaaymata tayi ƙanƙanta da haihuwa
Surbajo for life.
[6/16, 9:59 AM] ZAHRA SURBAJO: .🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAZINATA NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*Surbajo beauty luxury,duniyar gyaran fata,muna siyar da skin care product masu kyau da maana,wanda zasu gyareki ki dawo yarinya,kama daga cire ƙurajen fuska dana jiki,wanda mai ya ɓata musu jiki,masu son nasa fari,da masu son fito da aynihin fatarsu,to ku garzayo surbajo beauty luxury dan magance matsalarku da kuɗi ƙalilan,07044600044*
*littafin surbajo return yadawo normal price ɗinshi 500 Kar akuma turo 100 in ka turo kayi sadaka,kar akuma turo naira ɗari kar akuma turo naira ɗari,yau 14-06-2023 in ka turo kayi sadaka*
*18*,
Ayan ya isa garinsu lafiya batare daya haɗu da kowacce irin matsalaba.
Koda ya shiga gidansu anyi saa shima nasir yazo ga mamakinsa ba wanda ya firgita da ganinsa sunde miƙe suna binshi da ido
Nasir ne yayi ƙarfin halin cewa "yaya ayan dama kana raye"?
Hawayene suka zubo a idonsa yace,"nasir ina raye ba mutuwa nayiba.
Nasir dame unguwane suka ƙarasa gurinshi suka rungumeshi,duka suna matse kwalla dan suna tsananin kaunarsa.
Mahaifiyarshi ko murmushi take haɗe da hawaye,har seda yazo gareta suka rungume juna
Bayan sun natsane megari yace"Ayan baka mutuba to taya ka rayu vayan mu ance mana ka mutu?"
"Abba na gamu da sharrin mace ne,wlh ban mutuba"daga haka ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar dasu.
"amma ko lallai junaiha takai makira kuma muguwa azzaluma"cewar nasir cikin fushi
Suko iyayensa kasa magana sukayi dan mamakin abun zuwacan megari ya ce"to shi kuma cikin jikinta kasan dashi?"
"Cikin jikinwa kuma Abba?"ayan ya tambaya a firgice
"Junaiha mana sunzo nan da iyayenta sunce kaine ka yaudareta ka mata ciki yanzu haka kulawa da ita da lafiyarta na hannuna"cewar nasir
Murmushin takaici ayan yayi ya sunkuyar da kai ƙasa yace a hankali"Allah hukuncinka ne wannan nasani Allah ka yafemin"ya faɗi yana hawaye,sannan yaci gaba da cewa.
"hannun junaiha ban taɓa riƙewaba wallahi bare akaiga na mata ciki,amma tunda kun cimma matsaya inaso ku bari zuwa ta haihun suzo."
"ay kamata yayi mu haɗata da hukuma tunda tana haɗa kai da ƴan kudnapping"cewat nasir.
"ka barta nacema nasir"cewar ayan.
Nanfa sukai ta tattauna matsalar, har suka cimma matsaya.
Ayan a garinsu yaci gaba da rayuwarsa ba tare daya koma cikin gariba.
Gurin aykinshi nasir yaje ya musu bayanin komai da kuma dalilin ɓoye kanshi yanzu da yake,kuma sun gamsu sun bashi dama.
Ayan koda yaushe tunanin fatima da jikinta na faɗo masa,yana son zuwa ya ganota, gashi garin nasu ba service bare ya kira yaji.
Kullum da damuwar hakan yake yini yake kwana.dan yarinyar na bashi tausayi.
*********
A can ƙauyen su fatima ko,gari ya ɗauka ayan ɗan birni yawa fatima ciki ya gudu.
Me gari ko tun daga wannan rana daya yanke jiki ya faɗi ba sauƙi se na Allah wanda a Ƙarshede mutuwa yayi.
Kukan baƙin ciki ba wanda iyalinshi basuyi ba sabida nutumin kirkine.
Fatima anyi nasarar yimata operation ta haifi ɗanta namiji,sede akwai buƙatar ta zauna a asibiti sabida yaron beda ƙwari.
Babban ɗan megarine yazo asibitin bayan sun dawo daga binneshi cikin fushi.
Fatima dake kwance ita kaɗai a ɗakin ta ɗago ta dubeshi.
"dama gurin haihuwarki uwarki ta mutu,to gashi shima ubanmu baƙin cikin ki ya kasheshi,wallahi daganan kiyi wani gurin in kuma kikq sake muka ƙara ganinki kema se mun kasheki wlh"be jira jin me zatace ba,yasa kai yayi tafiyarsa
Fatima jikinta har karkarwa yake jin ance xaa kasheta,haka ta diro daga gadon tanufi ƙofar fita har takai ta dawo ta kwashi yaronta dake cikin tulin tsumma.
Ficewa tayi daga asibitin hankalinta tashe dama ita kaɗaice aka haifa agidan namanta ta rasu,matar megari ba sonta take ba dama har ƴaƴanta,megarinne kawai yake sonta se ɗan uwansa dake burni.
Ɗinkin jikinta satinsa uku ga ɗa da baason iska ta sameshi haka take takawa a hankali har tayi nisa da garinsu,dan tunda ɓarayi suka saceta take tsoron mutuwa.
*ME BUƘATAR ATALLATA MASA HAJARSA A SAMAN WANNAN LITTAFI YA MIN MAGANA A FARASHI ME SAUƘI*
Surbajo for life.
[6/17, 12:36 AM] ZAHRA SURBAJO: .🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAZINATA NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*Surbajo beauty luxury,duniyar gyaran fata,muna siyar da skin care product masu kyau da maana,wanda zasu gyareki ki dawo yarinya,kama daga cire ƙurajen fuska dana jiki,wanda mai ya ɓata musu jiki,masu son nasa fari,da masu son fito da aynihin fatarsu,to ku garzayo surbajo beauty luxury dan magance matsalarku da kuɗi ƙalilan,07044600044*
*littafin surbajo return yadawo normal price ɗinshi 500 Kar akuma turo 100 in ka turo kayi sadaka,kar akuma turo naira ɗari kar akuma turo naira ɗari,yau 14-06-2023 in ka turo kayi sadaka*
*19*,
Fatima yawo ta dinga a gari,har de Allah ya kaita garin kaduna,
A ƙarƙashin gadar kawo take rayuwa,dan jamaa da dama ɗauka suke mahaukaciyace,duba da yadda take wari saboda jinin haihuwa da take zubarwa.
Ɗan hannunta ko tuni ya jima da mutuwa amma bata saniba,inbanda wari ba abinda yake, shiyasa ko ina ta gifta ake korarta.
Yauma ta tashi cike da jin yunwa,dan haka ko gabanta bata kallo ta faɗo titi ayko jinta tayi tayi sama ta taɓo gadar ta dawo ƙasa tim.
Ƙarar taka burkin da akayine yasa jamaar gurin waigawa,mahaukaciya aka bige.haka kowa ke cewa.
Itako me jan motar da mahaukacin gudu ta fito sanye da kayanta na aykin asibiti,Ba kowa bace face saudat ɗin ayan.
Agigice tayi kan fatima tana jijjigawa,ganin bata numfashine yasa ta nemi taimakon mutane,tasata amota,duk da warin da take be dami saudat ba seda ta kaita asibitinsu.
Likitansine yashiga dubata,inda cikin saa ta farfaɗo amma an mata allurar bacci, dayasa ta kasa buɗe ido.
Likitan bayan ya