TANTABARA COMPLETE BOOK BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 36.7K words

faɗi a ruɗe.

Da sauri suka fito doctor bala yace"wa muka gani a hanyar?"

Hawayene ya fara fitowa a idonta,tace"naje kitchen kan infito nasamu fanan batanan,shine maigadi yace a mota akazo aka ɗauketa"


dafe kai mahboob yayi yace "jikina ya bani hakan na iya faruwa,to amma wannan duk ba abun tada hankali bane matuƙar ƴan uwantane suka ɗauketa,matsalar itace in wanine daban yasaceta fa?"ya faɗi cikin yanayi na dauriyar daya gaza ɓoye tsananin damuwar dayake ciki.

"Tayi wayane kan ta fito?"doctor bala ya tambayi aisha.

"Eh ta amshi wayata ta kira wani ɗan uwanta,har tana bashi address ɗin gidannan,to bansan guduwa takeson yiba yasa na bata"ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta.

Doctor bala rufe Aisha yayi da faɗa inda
mahboob ya tsaidashi da cewa "doctor ta tara sani da Allah ne da zata san manufar fanan,?bata saniba kaga ko ay bata da laifi,abunde da zakiyi shine ki bamu number data kira ɗin."

Jikinta na ɓari ta koma ta ɗauko wayarta ta nemo number,ga mamakinta fanan ta goge kiran da tayi.


Dafe kai mahboob yayi jiri na ƙoƙarin ɗaukarshi,
Ya dafe bango da sauri.

Doctor bala shima yaji ba daɗi kan hakan data faru,shuru dukansu sukayi kamin doctor bala yaje"muje computer room ay akwai cctv ata wajen get se muga wanda ya ɗauketa kaga in amotane ma har number motar zamu iya samu."


Ayko da sauri mahboob ya wartsake yabi doctor bala zuwa cikin ɗakin computer ɗin.




muje zuwa.

*07044600044*
[8/16, 11:08] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*




*16*


.......Tun daga isowar kabeer ƙofar gidan da fitar fanan da rungume juna da barin ƙofar gidan da sukayi va wanda cctv ɗin bata ɗaukaba.

A hankali mahboob yasa hannu yayi zooming fuskar kabeer yana kallonshi yayi murmushi yana sauke ajiyar zuciya me nauyi yace"case closed doctor ɗan uwantane ya ɗauketa,ka duba da kyau zaka ga kamanninsu"

"Nima naga hakan mahboob to yanzu meye abunyi tunda munsan tana tare da ƴan uwanta?"

"Doctor number motar zamu ɗauka musa abinciko mana adireshinta,tanan ne zan iya kaiwa ga fanan"cewar mahboob yana murmushi.

gyara zama doctor bala yayi sannan yace"mahboob for now you have to relax kaje kasamu mummy kuyi solving issue ɗinku kaida ita,inka gama da wannan seka fara nemo fanan."

"doctor nifa fanan ɗinnan wallahi sonta nake da duk zuciyata bana samun natsuwa wallahi matuƙar bata tare dani,"mahboob ya faɗi,

Dariya bala yayi sannan ya dafoshi yace"haba mahboob bafa yau muke tare ba,duk wani halinka ba wanda ban saniba,ay tun ranar da kazo zaay mata wankannan a hospital ka kamu da sonta,shiyasa na baka shawarar kula da lafiyarta dan zata amfaneka"

Murmushi yayi yace"toko kaga ay batun relax ma ay betaso ba"

"Hakane amma de kafara da issue ɗin mahaifiyarka first."

Daga haka suka shiga tsara yadda zasu ɓullowa lamarin mummy.

********

Fanan duk abinda tasani bayan dawowa hayyacinta ta sanar da ƴanuwanta,sosai suka yabawa mahboob inda aunty habiba tace"ayko baa kyautaba in har baa nemeshiba fanan,tunda ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarki."

Murmushin ƙarfin hali fanan tayi tace" mahaifiyarshi sananniyace a ƙasarnan haka mahaifinshi,haɗuwa ta da ita a farko ta nuna bata son na raɓi ɗanta,kan hakanema tasa akamo mata shi shikuma ya zauna tare dani a gidan abokinshi,na baroshine dan ya samu damar shiryawa da mahaifiyarshi" ta faɗi hawaye na biyo idonta.

Shuru sukayi ba wanda ya kuma magana.

Fanan tana jin daɗin rayuwa cikin soyayyar ƴan uwanta,shiyasa duk damuwarta taji takau.

*******

"Mummy kiyi haƙuri ki yafe min,yarinyarnan fa bata da kowa garinnan shiyasa na bita dan in tabbatar dataje gida lfy"cewar mahboob lokacin da yaje ga mummy.

Cikin tsananin fushi tace"mahboob me kuma yay saura,meye yay saura wanda baka ɓataminba.,kujerar mataimakin shugaban ƙasa da zaa bani kasa ƴan jamiyya sun faara tunanin tureni,kujerar minista da nake kai itama ana kai suka ta koina kan asaukeni,gaba ɗaya ka shafamin baƙin fenti kan abinda banjiba banganiba"

"Mummy komai me gyaruwane aduk abinda kika lissafa insha Allahu zaa gyara"

Tsabar takaici batasan lokacin data ɗaukeshi da mari ba.
Tace tana nunashi da yatsa"kaban kunya mahboob,to waima in vanda abunka talaka har abun ataimakeshine ajashi ajiki,?talaka kajine tsakaninka dasu kabasu hatsi,dan inka raɓesu koya seka raɓo masifar dake tattare dasu."


"mummy dukanmu kayan Allah ne,beyi wani dan beson waniba,kuma niimar da muke ciki ba rawa mukai ya bamuba dan haka rayuwa ƴar sannuce mummy"yana kaiwa nan be jira me zata ce ba yasa kai ya bar mata falon zuwa nashi sashin.

Mummy ta gama ɓata masa rai dan shi bega abunƙi a gun mutum ɗan uwanka ba,da zatai ta zangawa fuskarsa mari daga taimako.


Ko kaɗan halayen mahaifiyarshi basui masa ba,dan tsanarta da talauci abun na masa zafi

Fridge ya buɗe ya ɗauko kwalbar giyarsa da kuɗinta yatasamma milyan guda,ya ɓalle hancinta ya kwankwaɗe.


Yana gama sha ya bi lafiyar gadonsa ya kwanta yana tunanin yadda ze haɗu da fannan ɗinshi.


.Bayan watanni biyu da faruwar komai,yanzu akwai daidaito tsakanin mahboob da mummy dan abun ya ɗan rage trending a social media.

"mahboob batun auranku da nadiya,ya kamata ace yanzune zaayishi kaga andinke bakin surutun abunda ya faru"cewar mummy tana murmyshi.


"well,but mummy nafa sha faɗa miki nadiya ba test ɗina bace meyasa mummy kikeso dole sena aureta?"ya faɗi cikin damuwa.

"sabida mahaifinta shine ɗan takarar shugaban ƙasa wanda shi ya zaɓeni amazaunin assista ɗinsa. wannan shine kawai dan abun alfaharine ace ɗana ne ke auran nadiya.."

"A gaskiya mummy ni banasonta, sabida ni banason mace me kyau sosai"


Dan tsananin mamaki mummy batasan lokacin data tuntsire da dariya ba dan abun dariya ya bata,saida tayi me isarta sannan tace"ayko ban taɓa ji ba bazaa kuma fara daga kanka ba kowanne namiji kyau yake so bama maza ba har matan ma suna son kyau,inde wannan shine dalikinka to ka shirya sati me zuwa auranka da nadiya ko kanaso ko baka so,amma se in har zaka ci gaba da kirana da sunan uwa gareka ina amsawa"tana kaiwa nan ta miƙe tabar falon.
.
Mahboob riƙe kanshi dake juya masa yayi,mummy ta ɓata masa komai wanda besan lokacin daze gyara ba.yana son fanan gashi ta cuso masa damuwa wai nadiya.

Duk yadda yaso daya daure seda hawaye suka zubo a idonsa.dan yama rasa mafita dan yasan mummy kaifi ɗayace bata amai ta lashe.

Nadiya lokacin da batun auranta da mahboob ya sameta ba ƙaramin daɗi tajiba dan dama abinda ya faru tsakaninshi da fanan ya tsoratata dan ta hango tsantsar so da ƙaunar fanan a idon mahboob lokacin da yakewa mutane warning akan jifanta.

Amma yanzu ta samu natsuwa tunda,itade ze aura at last.

Nan fa ta shiga faɗawa ƙawayenta aka shiga shiri,aranar suka fitar da anko ko ina se posting ake da hashtag,#mahnad2023

Mahboob dake gida lokacin da yay arba da edited pics ɗinshi da nadiya anata save d date abun ba ƙaramin zafi yay masa ba.

..Haka kiran waya seda ya gaji da ɗagawa na jamaar dake kira dansu ji gaskiyar magana.

.Ganin bazaa barshi bane yasa ya ɗora akan whatsapp status ɗinshi da cewa "Allah ya kawo mu,save d date."

Ay angudu baa tsiraba nanma ƴan congratulation sika kunno kai suma.


Be samu kansa ba seda ya kashe wayar gaba ɗayanta.

Ranar seda yasha kwalba biyar ta giya,dan yakauda damuwar komai aransa.


Da ike manyan giya yakesha shiyasa ko bugar dashi vasayi sede sui masa aykin da yakeso.






muje zuwa.

*07044600044*
[8/17, 09:49] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*




*17*


.......Tun daga wannan lokaci mummy ta shiga hidimar gadan gadan wanda shi da ake abun dominsa ko ajikinshi.

Abokansa ne ma suka zauna meeting kan abinda zaayi na hidimar bikin shiko ajikinshi,dan giyar da ya mayar ruwan sha ta ɗauke masa damuwar komai.

A na saura kwana biyu biki nadiya ta kirashi awaya,ba tare da damuwar komai ba ya ɗaga.

"baby wai dan Allah wanne irin aurene zamuyi kaƙi kazo mu tsara event komai saidai abokanka su kirani"ta faɗi a shagwaɓe.

"to base ki godewa Allah ba ma inada abokan da suke tsaye kan hidimar"ya bata amsa.

"to amma ay yadda kakeyi kamar auran dole zaay maka hakan zesa aymin dariya cikin friends,kai kofa a social media baka taɓa sawa ba inbanda status na whatsapp."

"Look nadiya,aurena dake fa zaɓin iyayene,nidake ban taɓa cewa ina sonki ba,dan haka duk abinda kikeso aymiki a bikinnan ki kira wacce ta haɗa auran nasan zata miki"ya faɗi aɗan faɗace dan ta fara kaishi bango.

"bangane haɗin iyayeba,ay kai da kanka ka amsa kana sona harda min alƙawarin aure da zaran ka dawo, dan haka auren soyayya de zakace"ta bashi amsa cike da ƙwarim guiwarta.

"yaushe na taɓa faɗa miki duk wannan abunda kika lissafa ɗun,da yaushe mukayi haka dake"?

."Kana italy mukayi dakai a whatsapp,in kuma kana musu ka hau whatsapp ɗin ay se in turama."

Kashe wayar yayi yana juyata ahannunshi yana juya maganganun nadiya aransa.

Hawa kan whatsapp ɗin nashi yayi nakan wayar,bega saƙon komaiba,tunawa da yayi yayi blocking ɗinta a wannan whatsapp ɗinne yasa ya ɗauko ɗayar wayar daya taɓa ba fanan ya hau whatsapp ɗin.

Shi abunma dariya ya bashi ganin yadda nadiya keta zubo kalamun soyayya fanan na mayar mata azuwan shine,

Ya fahimci da fanan sukai chatting ɗinne sakamakon betaɓa ba kowa wayarba se ita,kuma tunda ta bashi be ba kowaba.

Call history ya shiga,inda yaga number da ta kira a ranar,da sauri ya ɗauki number a ɗayar wayarshi,ya kira,ayko jikinshi har ɓari yake yanaso yaji ko waye.


Daga can kabeer ya ɗaga kiran bakinshi ɗauke da sallama.

Natsuwa mahboob yayi sannan yace "hello Abdul ya abuja"yayi hakane dan ya gano koma waye kuma daga ina.

Ayko kabeer ba tare da damuwar komai ba yace"ba shi bane kabeer ne wannan daga kaduna waye?"

"yes"mahboob ya faɗi a hankali dan tarkon nasa ya kamu.cigaba yayi da cewa.

"Au yi haƙuri don Allah,sunana hysam daga zaria,yaya dama numberka aka bani lokacin dana gwadawa abokina ƙanwarka ina sonta,to Allah da ikonsa se na kasa gane wacce numberce."ya faɗi a ladabce.

Allah sarki kabeer jiyayi wani farinciki ya kamashi,jin masoyin fanan dan haka da sauri yace"yaushe ka fara ganin ƙanwar tawa bawan Allah?"

"A tv naganta shine ni kuma naji duniya ba wacce nakeso sama da ita,in ka bani dama zanzo gida na gabatar da kaina"

Hawayen farincikine suka biyo fuskar kabeer dan yanzu shekarum fanan talatin kuma ba aure,dole ya shiga farinciki.

"To in kasamu lokacin kazo gida muyi magana dan wasu maganganun sede in kazo ɗin,nagode sosai"cewar kabeer cikin farinciki

"kaban address ina nan zuwa gobe insha Allahu"cewar mahboob shima cike da farincikin ze gana da fanan cikin ruwan sanyi.


Kabeer ba tare da damuwar komai ba ya bashi full address ɗin gidansu.

Sallama sukai ya ajiye wayar ransa fess.

Kabeer yana gama wayar ya ƙwalawa fanan kira,dama yazo cin abincin rana ne ayko tana zywa ta durƙusa yace

"fanan haskaki agidan tv ya janyo alkhairi,tunda gashi wani ya ganki yana so,"

Da sauri ta ɗago ta dubeshi tace"yaya ni kima yakeso waye shi ɗin?"


"Haisam sunanshi ɗan zaria ne,kuma gobe yace zezo nan gurina"

Shuru tayi batace komai ba, dan ita bata da abin cewa tunda ta lura ɗan uwannata yana murna da hakan.

"fanan girma kike akwai buƙatar kema kiyi aure ki haifu,dan kiga naki ƴaƴan wannan buri shine na iyayenmu akanki amma in kina ganin bakiso abar maganar"

"A a yaya duk abinda kace shi zanyi kawai de inaso ne in yazo kar ka ɓoye masa komai gameda ni in ya amince dani a hakan fine,in kuma be aminceba kaga ay shikenan."

"kinyi tunani me kyau fanan kuma hakan zaayi insha Allahu Allah de ya zaɓa miki miji nagari"


"Aminn yaya"ta faɗi a sanyaye dan gani take adduar kamar bata dace da ita ba.

muje zuwa.

*07044600044*
[8/18, 18:09] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*




*18*


.......Ranar mahboob bacci ɓarawone ya ɗaukeshi,dan gani yake garin kamar baze wayeba,dan ya ƙosa yaje ga fanan.

Koda gari ya waye,da wuri ya kimtsa ya fice daga gida ba tare da sanin mummy ba, dan yasan zata hanashi tunda yaune zaayi dinner bikin nashi.

Saida yakai zaria,ya tura mata test cewa yayi tafiya.ayko yana shiga yay saurin kashe wayarshi gaba ɗaya dan yasan zata kirashi.

Ilai kuwa,mummy na gama karantawa ta fara kiranshi kamar kububuwa,dan ba ƙaramin ɓata mata rai yayiba,dan dinner ɗin ta manyace har shugaban ƙasa ze halarta da gomnoni,amma shine ya mata haka.

Kasa zama tayi tarasa yadda zaayi ta sameshi awaya,haka ta dinga safa tana marwa dan ta fabimci ya shiryo tozartata ataron jamaane.

Haka suka hawo private jet daga kano zuwa abuja inda zaay dinner ba tare da ango ba inda abokansa se kiranshi suke bata shiga gashi ba wanda yasan inda yaje.

Itako fanan tun safe tabar gidan yayan nata ta tafi gidan aunty habiba dan bazata bari masoyin nata su gana ba,har sai yaji labarinta tukunna in ya amince se su gana.

Mahboob ya isa lafiya,gidansu fanan,koda kabeer ya tarboshi,sosai yayi mamakin ganinshi,dan be zaci shi vane dan sosai yasanshi.

Jiki asanyaye kabeer ya shiga motar mahboob suka ƙarasa gidan,suna zuwa ya masa masauki asit room ɗin gidan nashi.

Ruwa da abinci ya gabatar masa batare daya sa ran zeciba ga mamakinsa sosai yaci abincin yasha ruwa

Bayan sunje masallaci sun dawo ne,kabeer yace"kayi haƙuri bisa ɗauko fanan da nayi na gudo da ita,tace tanaso ka samu daidaito da mahaifiyarkane yasa ta hana anemeka."

Murmushi mahboob yayi dake nuna tsantsar farinciki da yake ciki,yace"yayanmu konine hakan zanyi,damuwata alokacin bansan hannunwa ta faɗa ba,amma tunda na ganka a cctv camera nasan kai ɗan uwantane."ya faɗi yana murmushi.

Murmushi kabeer yayi yace"hakane amma ranka ya daɗe ay da kace kainema baka tsaya ɓoyewaba ay kana da ƙimar da zamu saurareka koda bakace kana son fanan ba"

"Batun son fanan da gaske nake,kuma har zuciyata auranta nakeson yin inhar kun amince min"cewar mahboob ba tare da damuwar komaiba.

"bakasan baƙin littafin dake rubuce da labarin fanan ba,wanda nasan inkasanshi vazaka ƙara koda minti guda zaune tare daniba"cewar kabeer asanyaye

Shuru mahboob yayi yana juya maganar kamin yace"duk yadda yakai da baƙi insha Allahu Zan wankeshi insake rubutashi a farar takarda,inba damuwa kasanar dani koma menene."ya faɗi cike da ƙwarin guiwa.

Cikin jin nauyin abinda bakinshi ze furta kabeer yace"Fanan ba cikakkiyar budurwa bace duk da baa taɓa ɗaura mata aureba,"

Da sauri mahboob ya runtse idonshi yana karanto duk addu'ar datazo bakinshi.sakamakon jikinshi dake kakkarwa.

Kabeer cigaba yayi da cewa"saurayinta ne ya yaudareta da soyayyar da take masa yasa ta amince dashi"daga haka ya kwashe komai daya faru gameda video ɗin tsiraicinta,ya faɗa masa


Gashin jikinshine suka fito idanunshi suka kaɗa sukai ja jikinshi se ɓari yake kamar mejin zazzaɓi,ya jima awannan yanayin kamin ya samu natsuwa,dan kabeer kanshi ya tsorata da ganin halin daya shiga.

A hankali yace"kana da number wayar fahad ɗin?"

"Eh inada ita,muma abinda ya hana mu nemeshi yanzu yayi ƙarfine ta yadda bazamu iya dashi ba"

Murmushin takaici mahboob yayi yace"badamuwa kaban numbershi,ya haɗu da daidai shi yanzu"

Karanto mishi numbar yayi yasa awayarsa yayi saving.sannan yacewa kabeer.

"koda ace fanan ta ɗauki sanaar blue film sanaa da saninta ake ɗaukarta ake yaɗawa,wallahi ni ina sonta ahaka matuƙar tana sona,dan haka yaya kamar yadda nace sunana haisam kabarshi ahaka agurinta,karka faɗa mata nine,kawai de zanbaka kuɗi kasiya mata waya ayau ka turomin numbarta,dan Allah kar fanan tasan nine mahboob nazo da kaina"ya ƙarasa maganar cikin magiya.

"babu damuwa insha Allahu bazan sanar da ita ba,kadena roƙona"cewar kabeer yana murmushi.


Kuɗi ya tura masa ta acct sannan yay masa sallama yatafi ba tare daya buƙaci ganin fanan ɗinba.


Yana baro gidan su fanan da misalin ƙarfe biyu na rana dinner ɗinshi kuma a abuja ne zaayi yasan duk inda momy kenan tanacan rana faɗa,dan haka hanyar abuja ya kama,inda ya saki motar sosai akan titi dan ya isa da wuri.
.
Ya isa abuja lafiya,lokacin mummy da ƙawayenta sun fito zasu tafi gurin dinner ɗin,an shirya faisal ƙaninsa yaje amazaunin angon tunda suna kama....

Ganinshi tayi kwatsam yana shigowa,gidan,ayko tai kanshi kamar zata rufeshi da duka,dariya yay mata yace"mummy tunda nazo va shikenanba"

Daga haka ciki ya shiga ya yi wanka ya kimtsa,kamin ta fito tuni su doctor bala sunzo ɗaukarsa,dan mummy ta sanar dasu ya dawo.

..Rankayawa sukai zuwa gun dinner ɗin inda amarya da tawagarta kecan bakin ƙofar hall ɗin suna jiranshi

muje zuwa.

*07044600044*
[8/21, 07:03] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TANTABARA*
_(uwar alƙawari)_
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*




*19*


.......Amarya nadiya lokacin dataga mahboob da kanshi a wajan ji tayi kamar ta suma dan daɗi dan ta cirec rai da zuwan nashi segashi yazo.

Hakafa ta dinga manne masa yana basarwa,jamaa se hotuna ake ɗauka sabida big wedding ne,kowa se update yake saki a media.

Basu tashi taron ba se misalin sha ɗaya na dare,sannan suka taho tare da nadiya zasu kaita gida sannan su wuce.

Doctor bala da Aisha matarshi nr a gaban motar shike driving,se bayan motar angone da amaryarsa.

Sun fara tafiya nadiya ta kamo hannun mahboob tace a shagwaɓe"babe wai ina kajene mummy ta kira tace bakanan faisal ne ze wakilceka?"

murmushi yayi yace"Gidan iyayen budurwata mana wacce nakeson aurowa"ya faɗi yana kallon idonta.

Dariya tayi me sauti ta kauda kanta gefe tace"ay sede ko in kunje lahira kwayi acan,amma ay matarka nan gidan duniya ay nice,"ta faɗi tana fari da ido.

Dariyace ta ƙwacewa doctor bala,dan yasan in har mahboob be auro fanan va ta mutune ko kuma shi ɗin ya mutu.

"Au dake zan ƙari rayuwar tawa ta duniya kaf wai nufinki?"ya faɗi yana kallon idonta.

Murmushi tayi gamida fari da ido tace"haka yake baby nice kawai kuma na wadatar"


Dariya yayi bece mata komai ba har suka kawota gida,sauka tayi sukai mata sallama suka wuce.

A hanya doctor bala yacewa mahboob"aboki nifa tunda akace bakanan nayi zaton guduwa kayi,amma dana tuno fanan kawai zuciyata ta bani gunta katafi"

"Doctor bala to taya kake zaton zan iya zama ba fanan acikun rayuwata,ita natafi gani kuma na dace da hakan"daga haka ya kwashe komai ya faɗawa balan amma banda batun blue film ɗinta,dan yasa wannan amatsayin sirrin rayuwarsune"

"Amma maza kuna shaaninku wallahi,yanzufa gobe zaa kawoma amarya kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa amma ka duba kaga wai labarin budurwa kuma kukeyi"cewar Aisha matar bala.

Dariya suka sa mata bala yace yana shafo cinyarta"nima na kusa darzo tawa budurwar "doke masa hannu tayi tace"nima kuma in darzata dakyau a gidana"


Haka suka kawo mahboob gida suma suka wuce nasu cikin raha dajin daɗi.

Mahboob yana shiga gida ɗakinsa ya wuce,wanka ya farayi sannan yayi sallah,kan ya idar mummy tasa ankawo masa abinci me rai da lafiya,

Yana idarwa yaɗan ci abinci ya kora da mutuniyar ƙaramar kwalba,dan beson damuwa ko kaɗan.

Yana kammalawane,ya haye gadonshi ya zaro wayarshi,number fahad ya nemo,sannan ya kirashi da wani tsohon layinsa da ba wanda yasanshi dashi,dan doctor

5 / 13