Author : Nanah Kanwar Soja Category : Romantic Hausa Novels
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
Horror Short Story
PART 1 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9/1/2026
starting posting on 4/2/2026
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
PART 1
“Sakina! ke tashi a wannan baccin na tabbata baki yi sallar Asuba ba! Shegen baccin nan asara ne 'karfe takwas na safe fa! kuma kin san yau graduation ɗin Afra ne, dole ki je!”
Muryar Momma ta fado min kamar tsawa.
A hankali na mirza ido, na yi hamma mai nauyi, zuciyata na jin kasala kamar an ɗaura min dutse na ɗaga murya cikin kasala ina cewa:
“A’uzubillahi… wai da gaske ƙarfe takwas yayi? bare na tashi nayi ramukan sallah nan… amma wallahi Momma, banason zuwa wannan graduation ɗin kawai dole ne, ba yadda na iya.”
Ta tsaya tana kallo na na ƴan dakiku, sannan ta girgiza kai cike da ɓacin rai “Sakina wai bazaki fito ba ko?”
Na tashi zaune a kan gado, zuciyata na nauyi fiye da jiki. A daidai lokacin nan Momma ta juya ta cire hijab ɗinta, alamun ta gama shirin fita.
“Momma gani fa, na gama sallah. Zuwa ƙarfe goma sha ɗaya zan shirya na je graduation ɗin,” ta faɗa da murya mai laushi amma mai ƙarfi.
“To na ji,” Momma ta ce. “Amma kafin nan zo ki sayo min nama can Gadar Lado.”
“To Momma,” na amsa, duk da cewa zuciyata bata so.
Sakina yarinya ce cikakkiya, mai shekaru ashirin da huɗu a rayuwarta su uku aka haifa a gidan su — maza biyu da ita ce ta uku. Ta yi primary da secondary har ta kammala Diploma, daga nan ta fara Degree wanda za ta yi graduation ɗinta a shekara mai zuwa.
Afra ƙanwarta ce, suka haɗa uba ɗaya. Ita kaɗai ce ƙanwarta ta jini. Afra tana zaune a gidan su tun bayan mutuwar mahaifiyarta. Yanzu haka ta kammala secondary school, kuma yau, 9/1/2026, ita ce ranar graduation ɗinta — ranar Juma’a.
Ranar da ya kamata ta kasance ranar farin ciki amma zuciyar Sakina tana mata wani irin nauyi da ba ta iya fassarawa ba.
Tun daga farkawa, akwai wani abu a ranta da ke mata ƙaiƙayi wani irin tsoro mara suna. kamar zuciyarta na mata gargaɗi — amma ba ta san me ba.
Ta tsaya a bakin ƙofa, ta kalli sararin sama, iska mai sanyi ta buge ta, ta ja numfashi a hankali ta ce a ranta:
“Me yasa zuciyata ke bugawa haka yau…?”
Ba ta san cewa wannan graduation ɗin
ba zai zama kamar sauran graduation ba, ba ta san cewa
wani abu mai duhu yana jiran su ba …
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION TA FARA… 💀☠️
LIKE FOR MORE TYPING
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 2 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9/1/2026
starting posting on 4/2/2026
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
TITLE: BEYOND THE RED CEREMONY
Na fito daga gida sanye da doguwar riga, jikinta ya yi dai-dai da ni, ba matse ba kuma ba sake ba. Na rufe da mayafi orange, na saka flat shoe kasancewar bana iya sa high heel Tsayina matsakaici ne, jikina ma haka ba zan ce ni kyakkyawa sosai ba, amma Allah ya bani hallita da kwarjini — irin wadda ba ta hayaniya, amma tana ja hankalin mai kallo.
A takaice, ni middle ce a kyawun mata, da na isa wajen taron, sai na tsaya cak.
Dandazon mutane!
Abin mamaki, wajen ya kasu gida biyu.
A ɓangare ɗaya, an cika da poster na Ali Nuhu, babban jarumin Kannywood, suna masa kirari da King.
A ɗayan ɓangaren, kuma Adam Zango ne a jiki kowa yasan sa da farar jini, kwalliya, magoya baya suna ta ihu.
Kowanne rumfa na da nasa hayaniya. Ana ta muhawara mai zafi:
“Ali Nuhu ne Sarki!”
“A’a! Adam Zango ne jarumi na gaskiya shine sarki!”
Na yi murmushi kaɗan ni dai ina sanye da facemask, saboda matsalar numfashi ta — asthma na tsaya a rumfar Adam Zango, ba wai don komai ba, sai don naga nan yafi cunkoso da nama me kyau .
Hayaniya na ƙara ƙarfi, maganganu na kaɗawa. Cikin haka, na ji an dafa kafad’ata daga baya.
“Ke baiwar Allah! ba mu yarda dake ba fa. Kin rufe fuska, ga leader a hannunki, kina team na Ali Nuhu Amman kinzo rumfar Adam Zango !”
Na juya a hankali, na yi murmushi a bayan facemask ɗina, na ce cikin murya mai ɗan sarƙewa saboda numfashi:
“Wallahi bana iya buɗe fuska yanzu, safiya ce kuma iska tana da haɗari a gare ni. Kuma a ganina, Adam Zango da Ali Nuhu duk ɗaya ne. ku dai kuke wannan haukar. Idan za ku binciki tarihinsu, zaku gane cewa suna haɗe — jiya da yau. Zango ya taba ɗaukar Ali a labarinsa, haka ma Sarki Ali yana ɗaukar Zango. Don haka ban san me zai faru a feature ba… amma na san haɗin gwiwa ne.”
Wasu matasa suka fara ihu daga waje.
Hayaniya ta tsaya cak.
Sai muka ga napep yana chusa kansa cikin wani gida — ba birki!
Gidan ya girgiza!
Nan take aka watse, ana ta ihu da firgici.
Ni kuwa ban tsaya ba nabi ta lungu-lungu na dawo gidanmu.
Gida ne mai matsakaicin hali — ba mu talakawa ba, ba mu masu kuɗi sosai ba muna ci, muna sha, muna sutura, muna makaranta. Alhamdulillah.
“Yaya Nabil ina kwana,” na faɗa ina wucewa.
Sai ya kira ni da murya mai ƙarfi:
“Sakina! ki shirya da wuri fa gaba ɗaya zamu fita, ke kaɗai kike bata mana lokaci!”
Na wuce ina murmushi a raina. Graduation kamar dole ne sai an je kai na na ɗan ciwo saboda bana samun kitson ya kamata nayi stretching kafin shiri.
Na shirya cikin red lace, ɗinkin pencil da tattara a ƙasa na yi adon pinch, na rataya mayafi launin pinch, na saka flat shoe. Wallahi na yi kyau — tubarakallah na fesa turare, amma har yanzu Yaya Nabil yana jirana da masifa.
Da misalin 11:30, napep ya sauke mu a makarantar.
Yau ne rana ta biyu da na taka kafata a HAYBIL PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL, KANO — babbar makaranta ce, day and boarding. Class suna da yawa, bishiyoyi sun cika ko’ina, musamman bayan makarantar da aka ƙawata da salo na musamman.
Sai zuciyata ta buga.
Komai ja da baƙi ne — red and black an 'kawata wajen graduation cikin salo mai burgewa.
Amma…
ban san dalilin da yasa zuciyata ta tsinke ba.
wani irin sanyi ya ratsa ni, na ji kamar wannan ba graduation na al’ada ba ne.
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION NA KARA KUSA… 💀☠️
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 3 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9/1/2026
starting posting on 4/2/2026
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
TITLE: BEYOND THE RED CEREMONY
“Ga ƙanin Baban mu can… ki je ki gaida su ni kuma zan wuce ɓangaren maza.”
Yaya Nabil ya faɗa cikin gaggawa, bai jira jin amsata ba ya juya ya ɓace cikin taron mutane.
Na tsaya na kalli inda ya nufa.
Hayaniya ce ko’ina.
Ihu, dariya, magana suna gauraye kamar amo a cikin rami ban son cunkoso, ban son hayaniya — zuciyata ba ta da daɗi tun safe.
A hankali na sulale, na fake ta gefe wasu sun gan ni, wasu ba su gan ni ba. Ban damu ba. Gaisuwa ce kawai bana buƙata, amma yau ma baki na yana min nauyi.
Na shiga wani class na zauna.
A nan na hango Habiba da Ummul ƙawayena tun secondary school suna zaune suna hira a hankali.
“Assalamu alaikum,” na faɗa cikin murya mai rauni suka amsa, amma idonsu ya tsaya a kaina kamar suna nazari.
“Ke kuwa yau ba kya kamar da,” Habiba ta faɗa tana lanƙwashe fuska.
“Tun shigowar ki nake kallo, kamar wacce aka bi da abu.”
Na tabe baki.
“Ehh… kaina ne kawai,” na ce, duk da na san ba kai ba ne kaɗai.
Ban gama rufe baki ba, sai aka ambaci sunan ƙanwata a speaker “AFRAH ABDULRAHMAN…” Amo ya ɗauke dakin.
Na miƙe da sauri, zuciyata na bugawa da ƙarfi. Na fito waje na ɗaga wayata — Tecno Spark 8 na fara ɗaukar video da hoto guda ɗaya kacal.
Da na kalli screen…
hannuna ya sanyi Afrah ce amma ba Afrah da na sani ba Idonta sun fito waje.
Jini yana zuba daga gefen idanunta kamar hawaye yana tsiyaya da guda gudan sa suna sauka akan leɓɓenbta bakin ta a buɗe yake faɗi kamar bakin mayya na saki numfashi da ƙarfi.
“Ba gaskiya ba ne…” Na goge ido na, na sake kallo komai ya koma normal.
Afrah na murmushi, tana daga takardar graduation na sauke ajiyar zuciya.
“Wannan tsoron nawa zai kashe ni,” na furta a raina.
“Ya Allah, kada ka bar na fara ganin abin da ba ya wanzuwa.” Na koma class amma jikina ya fara rawar sanyi Fitsari ya takura min na miƙe cikin gaggawa na nufi toilet.
Da na shiga, na rufe ƙofa lace na ya dame ni, sai naja zip kafin na zauna akan toilet na gama fitsari.
Na juya na buɗe bidet, ruwa ya fesa sai na ga ja, ba ruwa ba Jini ne.
mai kauri ɗumi a kan hannuna.
Na yi ihu — ihu mai tsage kunne.
Hasken toilet ɗin ya fara rawa ya yi rauni…
sai ya kashe cak naji wani Irrin kururuwa dariya daga nesa ba dariyar mutum ba.
Dariya ce mai raɗaɗi, mai kaɗa zuciya toilet ya fara girgiza kamar ana girgiza kabari.
Naja zip ɗina da sauri ina rawar jiki. Na miƙe cikin firgici — wayata ta zame ta faɗi ƙasa.
Screen ɗin ta haske.
Amma ba home screen ba abin da ya bayyana daga cikin wayar
ya sa idona ya juya.
HOTONA NE.
Sakina Ina tsaye sanye da rigar graduation ja Idona na zubar da jini bakin na buɗe kamar na Afrah a rubuce da ja a ƙasa “KIN SHIGA.
BA ZA KI FITA BA.”
Na ji ƙasa ta ɗauke ta lafta ne da ƙasa kai na ya bugu a take na sake wani Irrin ihu mai giggittacen ƙara da wani fitsarin da bashi da linzamin na faɗi a sume.
Abu na ƙarshe da na ji shi ne
ƙarar gashi yana ja a ƙasa kamar ana jan gawar mutum.
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 4 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9/1/2026
starting posting on 4/2/2026
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ، فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَسَّسُوا.👌🏿
Ku nisanci zato domin zato shi ne mafi ƙaryar magana🤐 kuma kada ku yi leƙen asiri ko binciken abin da wasu suke aikatawa✍🏾
PART 4
THE SCREAM BEHIND THE MIRROR
Na buɗe ido a hankali kamar wanda aka dawo da ita daga kabari kai na yana sara, zuciya ta na bugawa kamar zata faso kirji na , naji ƙanshin jini da wani wari irin na tsohon ɗaki da aka rufe shekaru masu tarin yawa dasuka gabata , na fara mirza ido nan nan hasken toilet ɗin ya dawo normal, komai ya yi shiru… amma shiru mai ban tsoro.
Na taɓa gashin kaina, ɗan ƙwalin da ya faɗi yana nan manne da jini. Hannuna na rawa. A hankali na miƙe na ɗauki wayata daga ƙasa. Screen ɗin ya fashe, amma abin da ya fi tsorata ni shi ne hoton da ya tsaya a jiki.
Afrah ce…
amma ba Afrah da na sani ba Idon ta baki-baki, bakinta cike da jini, an rubuta da ja a ƙasan hoton “KE CE TA GABA.”
Na saki ihu mai ƙarfi.
“Waiyooo Mama na ”
Na jefa wayar, ta bugi bango ta sake dawowa. ta tsaya chakk tana shillo a sama tana wani zubar da wani abu baƙi tamkar ruwan batir A madubi na ga wani inuwar mace a bayana. Doguwar gashi, sanye da rigar graduation ja… rigar tana diga jini ƙasa-ƙasa a hankali ta ɗaga kanta.
Fuskar ta… tawa ce.
“Ba ni bane!” na faɗa ina ja da baya har na bugi ƙofar toilet tayi murmushi, murmushin da bai da rai, ta fara zare idon ta masu kama da walwawalin rana babu ɗigon baƙi bare na kira shi da cikakkun ' ido
“Kin fara gani Sakina…” ta ce da murya mai sanyi kamar iska daga sanyayyar hontoro mai ratsa sassan jikin ya daskare
“Wannan graduation ba ta rayayyu kaɗai bace.” ta ɓacce ɓattt haske ya kashe cak.
Na ji ƙarar takalmi yana matsowa kusa da ni…
tak… tak… tak… sai wata murya ta buga ƙofar toilet da ƙarfi.
“Sakina! Lafiyar ki kuwa?” muryar Habiba ce komai ya ɓace haske ya dawo na buɗe ƙofa da sauri na faɗa jikin Habiba ina kuka kamar mahaukaciya.
“Ke lafiya kuwa?” ta tambaya cike da tsoro.
na kalli madubi karo na ƙarshe rubutu ja ya bayyana a jiki
**PARTY YA FARA.
A take rungumar ta ta yi sanyi… sanyi irin na dutse na buɗe ido a hankali abin da na gani ya kulle min numfashi Habiba ba Habiba ba ce.
Haƙoranta sun zalzallo, wasu suna rataye, wasu sun faɗi harshe ya fito tsawo, baki-baki kamar an ƙone shi Idonta guda ɗaya ya ɓace—ɗaya tilo yana tsaye a tsakiyar goshinta, yana kallo kai tsaye cikin raina.
Jini na malala daga hancinta, yana digo kan rigata.
Ta buɗe baki , ta ɓabaki da dariya.
Dariyar ba ta kama da ta mutum ba—ta yi zurfi, ta yi sanyi, ta yi kama da amo daga ƙasa a hankali ta ɗaga yatsa ta nuna ni “Keee…”
muryar ta ta fito kamar an goga ƙashi da ƙasa.
Na saki ihu.
A take, bench ɗin class suka fara rawa.
Allunan tebur suna karkarwa kamar suna numfashi.
Fanka ya yi ihu ya ɓalle daga sama—ya faɗo ƙasa da ƙarfi, yana juyawa yana watsar da iska mai sanyin ƙanƙara sai dariya ta cika class ɗin.
Ba dariyar ɗalibai ba dariyar da ba ta da jiki.
Ƙofofi suka rufe da kansu—bam! tagogi suka yi ƙara suna girgiza.
Haske ya yi walƙiya—ya kashe—ya dawo.
A duk inda na juya, fuska ɗaya nake gani:
fuskar graduation ja… fuskar mutuwa.
Habiba—ko abin da ya mallake ta—ta matsa kusa da kunnuwana ta raɗa:
“An fara wanda ya ga jini, ba ya tsira.”
Class ɗin ya giggice.
Ihu, kuka, gudu—amma babu hanyar fita.
Ni kuma na tsaya a tsakiyar wannan hauka…
hannuna na rawa…
zuciyata na bugawa da kalmar guda ɗaya:
MOMMY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️🤌
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 5 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9/1/2026
starting posting on 4/2/2026
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ، فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَسَّسُوا.👌🏿
Ku nisanci zato domin zato shi ne mafi ƙaryar magana🤐 kuma kada ku yi leƙen asiri ko binciken abin da wasu suke aikatawa✍🏾
BA UPDATE RANAR LAHADI
PART 5
THE SCREAM BEHIND THE MIRROR