Author : Nanah Kanwar Soja Category : Romantic Hausa Novels
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
✨ Ramadan na kusata! ✨🌙
Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka.
🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara.
🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu.
Ramadan Kareem! 🌙💫
Wani gajeriyar ƙato ya matso kusa da Sakina, jikinsa ya yi ƙarfi kamar ƙarfe mai dumi a cikin duhu. Hannunsa ya manna akan kafadar ta, yana matsa da ƙarfi, kuma murya mai ƙarfi ta fita daga bakinsa:
“Dole ki zaɓa… lokacin na ƙurewa ya kusa.”
Sakina ta ƙoƙarin motsa bakin ta, ta yi niyyar magana ko ihu, amma babu komai da ya fita—ba ta iya furta kalma ɗaya ba. Ta ji kamar harshenta ya matse, kamar wani abu ya ɗaure muryarta da igiya maras gani.
Ta tsaya a hankali, idonta na fadawa, zuciyarta ta tsaya cak. Duk motsi ko numfashi yana cike da jin tsoro mai ƙarfi—kamar kowanne abu a cikin class ɗin nan yana kallonta, yana jira ta yi kuskure.
Kurma ta zama, Sakina ta ji kanta a tsaye kamar wata mayya a cikin duhu. Amma duk da haka, zuciyarta na bugawa, tana neman mafita. Ta gane cewa kowanne ɗan tsokaci daga ƙato nan na iya zama ƙarshe—lokaci ya kurewa, kuma wannan ba ɗabi’a ce kawai ba, wannan gaskiya ne mai tsananin firgici.
Duhu ya matso mata, inuwa sun yi yawa, suna zagaye da ita kamar wani zobe na kabari. Kowanne daga cikin halittun nan suna kallonta da ido mai wuta, ba su yi murmushi ba, amma kowane kallo na sa jikinta ya ji sanyi da ƙarfi.
> Duk duniya ta tsaya cak a firgice, kuma Sakina ta fahimci: idan ba ta zaɓi ba… za ta zama ɗaya daga cikin su—har abada.
Sakina ta tsaya tsaye, jikinta na rawa kamar ganyen da iska ke girgiza. Halittun nan da ke zagaye da ita sun matso kusa, kowanne kallo na ɗauke da sanyi mai kaifi da tsananin fushi da rashin rai. Duk motsi na ta yi kamar ƙanƙanta a hannunsu—kamar babu wanda zai iya tsira.
Wani ɗayan ƙaton ya matso gaba ɗaya, fuskarsa ta rufe da inuwa, hannunsa ya ja Sakina kusa da shi. Murya mai ƙarfi ta fita:
“Zaɓi, Sakina… ko ki tsaya… har abada!”
Idanunta sun cika da tsoro, amma ta san cewa idan ta tsaya, ba za ta sake tashi ba. Ta tattara ƙarfin zuciya ɗaya kaɗai da ta rage, ta fara ja da ƙafa cikin ƙoƙari. Kowanne ƙoƙarin ta yana jawo su ƙato nan da nan, suna motsi da sauri kamar iska mai ƙarfi.
Sai wani ƙato ya shiga tsakanin ta da hanyar fita, gashin kansa ya rufe haske na karshe daga wajen kofar. Sakina ta ji zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Ta yi ihu… amma wannan karon, muryarta ta canza—kurma ce kawai ta rage, babu wani amo.
A nan ta fara fahimtar gaskiyar wannan wuri:
ba makaranta ce, ba duniya ba… wannan wani labari ne mai rai, inda lokaci ya tsaya, kuma kowanne lokaci na batawa rai yana nufin ƙarshe.
Jinin da ya dinga ruwa a cikin class ɗin nan ya fara motsi kamar yana neman ta. Yana zuba a ƙafafunta, ya manne da kafafunta, yana sa ta ji kamar tana nutsewa cikin ruwan ja mai sanyi. Kowanne mataki na ta ja su ƙato nan, suna ƙara matsa mata, murmushi a fuskarsu babu rai.
Ta yi ƙoƙarin kallon ƙasa… sai ta ga rubutu a bango yana haskakawa da ja 5 MINT LEFT… FOREVER…
Idanunta sun ɗaure a rubutun. Ta ji jikinta ya tsaya, zuciyarta ta bugi ƙasa da ƙarfi, kuma numfashinta ya tsaya cak. Duk motsi ko ihu yanzu babu abin da zai iya fitar da ita daga wannan wuri—komai natsuwa ko ƙarfin zuciya.
Sakina ta fahimci: ko da ta yi ƙoƙarin tsira, wannan graduation ba zata taɓa ƙarewa ba. Lokaci da wuri sun haɗu don ɗaure ta cikin wannan duhu… har abada.
INA MAFITA ???
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 8 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9 /2 /2026
starting posting on 4/2/2026
SECOND TO THE LAST PAGE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
✨ Ramadan na kusata! ✨🌙
Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka.
🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara.
🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu.
Ramadan Kareem! 🌙💫
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
PART 9 / 10
BY NARNAH KANWAR SOJA
Sakina ta tsaya a tsakiyar duhu, idanunta na bugawa kamar za su fita. Ta ji muryoyin nan suna zagaye da ita, suna magana amma ba ta gane su ba. Sun ce: “Zaɓi… zaɓi yanzu…”
Ta rasa fahimta. Menene zaɓi? Me suke nufi? Ta dinga ja da ƙafa cikin firgice. Halittun nan sun kwance a gabanta, duk motsi da su ke yi yana ƙara sa ta ji tsoro da fargaba.
Ta fara gudu. Duk inda ta ratsa, ganye da bishiyoyi sun yi kama da bakin ruwa mai sanyi, suna murɗe kafafunta. Ana jin sautin tsaye da faɗa, amma ba ta iya gane ko daga ina suke fitowa. Kowanne mataki yana ƙara raba ta da duniyar da ta sani.
Azaba ta fara tashi a zuciyarta. Ta ji kamar tana nutsewa cikin duhu mai nauyi, wani nauyi mai ƙarfi da ba za a iya tsayawa ba. Hasken ja da fari yana motsawa, yana sa class ɗin, toilet ɗin, bishiyoyin… komai ya zama kama da mafarki mai ban tsoro da gaskiya.
Ta yi ƙoƙarin tunawa: wannan ba graduation bane da ta sani… wannan GUGUWAR GRADUATION ce.
Duk abin da ya kawo ta nan… bai da kyau. Fargaba ta mamaye zuciyarta, tana jin numfashi yana yankewa. Ta ji ƙamshi irin na jini, tsotsa na halittu, da murmushi mara rai suna zagaye da ita.
Ta ratsa cikin bishiyoyi, kowanne reshe yana kama da hannu mai neman ta ɗaure. Kowanne ciyawa da ƙasa suna sauti kamar ana kira da ita zuwa wurin da ba za ta iya tsira ba. Duk ƙoƙarin ta na gudu yana ƙara sa halittun nan su matsa kusa da ita, suna kallonta kamar abun wasa da rai.
Sakina ta rike kanta, zuciyarta na bugawa, idanunta na kallon duhu…
ta fara gane: idan ta rasa ƙarfin zuciya yanzu, wannan GUGUWAR GRADUATION za ta ɗaure ta har abada.
Sakina ta fara jin tsoron da bai taɓa ji ba. Lokaci ya yi ƙanƙanta: 5 minutes left…
Ta yi ƙoƙarin gudu, amma duk mataki na sa halittun nan su yi ƙarin matsa kusa da ita. Kowane reshe, kowanne ciyawa, kowanne ƙasa… suna kamar hannu ne masu neman ta ɗaure.
Sai kawai, daga cikin duhu mai tsanani, wata muryar sanyi ta busa kai tsaye:
“Zo… kar ki ɓuya… lokaci yayi…”
Sakina ta tsorata sosai, zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci, sannan wani ƙarin ƙarfi ya ja ta ƙasa.
Ta ji ƙafafunta na rasa ƙasa, kamar an ja ta cikin wani rami mai zurfi. Ramin yana sanyi, yana ɗaukar ta cikin duhu mai zurfi da wari na jini da ƙamshi mai ƙunci.
Ta yi ihu, ta yi ƙoƙarin ɗaga kai… amma babu komai. Ramin ya zama azabtarwa, bango da ƙasa suna motsi kamar suna rufe ta daga kowanne gefe. Kowanne numfashi da ta ɗauka yana cike da muryoyin ban tsoro, wasu suna kiran ta, wasu suna dariya da ƙarfi.
Zuciyarta ta ƙara bugawa da tsanani. Idonta ya tsaya, yana ganin babu hanyar tsira, babu hanya ta fitowa. Kowanne sauti yana matsawa, yana cika zuciyarta da firgice da tashin hankali “ 2 MINNT LEFT… FOREVER…”
Ramin ya yi kama da sabon duniya… duniya ce da ba ta san ta wanzu ba, kuma Sakina ta fara fahimtar cewa wannan GUGUWAR GRADUATION ba ta da dawowa.
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 10 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9 /2 /2026
starting posting on 4/2/2026
THE LAST PAGE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
✨ Ramadan na kusata! ✨🌙
Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka.
🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara.
🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu.
Ramadan Kareem! 🌙💫
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
FINAL PAGE
Kamar yadda nagayyamu ku labarin bashi da tsawo nayisa ne a bisa wani dalili kuma ina fatan ya ƙayyatar daki sako ne me muhimmanci wanda ya faru ne da gaske wacce ta bani domin in mayar dashi a labari sai dai na gyara inda ya kamata wasu abubuwan kuma bazai faɗu a zahiri ba Muna fatan Allah yasa mu shiga wanan wata mai albarka lafiya da kwanciyar hankali, Allah yasa mu fara lafiya mu gama lafiya , Allah ya sadamu da alkaire cikin ta , Allah ya karɓi ibbadunmu Ameen ya rabbil izzati.
A duk lokacin da Ramadan ya shigo idan muna da time a koyaushe muna program na wasa ƙwaƙwalwa a addini in Sha Allah kamar ko yaushe zamu gabatar idan Allah ya bamu daman hawa online.....
Afuwan Afuwan Afuwan, ga wanda nayi Wa laifi cikin sani ko rashin sani a sanadin rubbutu ina neman gafarar ku Saduwar Alkaire sai mun haɗu bayan sallah in Sha Allah da littafin AFNAN .......
&&&&&&
Sakina ta faɗa cikin ramin, zuciyarta na bugawa da tsanani. Ko da ta yi ƙoƙarin miƙewa, duhu ya lullube ta gaba ɗaya. Sai haske ya fito daga wani gefen rami…
Ta ɗan haska ido, zuciyarta ta tsaya cak.
Gaba ɗaya, a cikin wannan rami mai girma, ta hango mutane da yawa a rataye. Jikin su yana zamewa, fuskar su cike da tsoro da azaba. Wasu suna motsi kaɗan, wasu kuwa babu rai… amma duk sun kasance a cikin wani hali mai ban tsoro.
Sai kuma ta ji raƙumin ihu mai tsananin firgice, mai sa ƙashi su rawa, mai girgiza ramin daga ciki zuwa waje. Ihu ne da zai sa mai karatu ya ji tsoro mai ƙarfi, zuciya ta tsaya, ido ya ƙasa, numfashi ya yanke.
“AAAAHHHHHHHH!!!”
Ihu ne da ya karye zuciya, ya haɗu da muryoyin waɗanda aka rataye. Wani murya mai sanyi ta busa a kunne:
“Zaɓi… ko zama kamar su…”
Sakina ta girgiza, ta rufe idonta, amma duk da haka hotunan mutanen da aka rataye sun ci gaba da bayyana a cikin duhu. Kowanne murmushi da ihu yana cika zuciyarta da firgice da tashin hankali.
Zuciyarta ta ce: “Ba… ba zan zauna kamar su ba… dole in tsira… dole in fita…”
Amma ramin ya yi kama da gidan mafarki, kowane gefe na tattare da duhu, jini yana zubowa daga bango, kuma muryoyin ban tsoro suna zagaye da ita daga kowanne bangare.
Sakina ta ɗan ja numfashi, ta fara neman hanya, amma duhu ya hana ta ganin komai, sai kawai mutanen da aka rataye da ihu mai ban tsoro…
Ihun ya balle mata makogwaro.
Ihu ɗaya tak. Amma komai ya girgiza — ƙasa ta motsa, bango ya yi rawa, inuwa ta tsawaita. Kan mutanen da aka rataye suka fara juyowa a lokaci guda, idanuwansu a buɗe, bakinsu a buɗe kamar suna son magana amma babu murya.
Sai haske ya fado daga sama.
Ja… mai kauri.
A iska ta ga rubutu yana walƙiya kamar bugun zuciya:
5 SECONDS REMAIN
Da kafin ta yi tunanin tserewa— aka ɗaga ta sama.Ba hannaye ta ji ba. Ba igiya ba. Kamar iska ce ta ɗaga ta.
Kafafunta sun bar ƙasa. Hannuwanta sun daskare. Numfashinta ya yanke.
Sai ta ji sanyi a wuyanta wani kakkakaifan zarton wuƙa mai sheƙi da walkiya
Ba ta ga wanda ya riƙe ta ba. Amma ta ji ƙarfin hannun a bayanta. Murya mai amo ta sauko daga sama, ba kusa ba, ba nesa ba:
“Lokaci ya ƙare.”
Zuciyarta ta daki ƙarfi. Hawaye suka taru amma ba su zubo ba. Ta so ta yi motsi—
ta kasa.
Ta so ta yi ihu—
ba murya A ranta kawai take ihu:
“Don Allah… kar ku kashe ni.”
Bakinta ya motsa. Kalmomin sun fito ba tare da sauti ba. Lips ɗinta na rawa, jikinta na karkarwa.
Sai rubutun ya sake walƙiya:
3…
Wuƙar ta matso kusa da fata. Ta ji sanyi ya ratsa jiki.
2…
Dukkan hotunan ranar graduation suka shigo mata lokaci ɗaya— dariya, tufafi ja, fanka, hayaniya.
Ta gane a wannan sakan:
“Wannan ba graduation ba ne… hukunci ne.”
1…
Bakinta ya motsa karo na ƙarshe:
“Ya Allah ka taimake ne na tuba ASTA'GFURRULLAH INNALLILAHI WAI'NA ILLAIHIN RAJIOU'N ALLAHUMA AJIRNI FI MUSSIBATI ”
Sai komai ya tsaya .. ana marin ta a kan fuskar ta ana cewa Sakina ! ke tashi kiye sallah '''''''
Sakina ta farke, tana gumi, zuciyarta na bugawa, tana ihu, tana cewa "Mommyyy! Mommyyy! Na ji tsoron… na ji tsoron sosai!" ta a zare idano tana bin ɗakin ta da kallo dayan bayan ɗaya ta daga kanta da hannun ta tana duba ko taji rauni ashe duk mafarki ne...
Ta tashi daga bacci, dakin Bachi ya shiru, babu ƙwarin wuƙa, babu halittu, babu jini. Amma tsoron ya zauna a zuciyarta — har sai da ta ga ƙananan zubin gumi a goshi da hannunta da ke tunatar da mafarkin.
Ita kawai ta yi murmushi, ta ce:
"Alhamdulillah… mafarki ne kawai… Amma… ya kasance da kamar da gaske sosai!"
Mommy tace, “Sai ke tashi, ki shirya, kiye sallah asuba mu tafi graduation na Afrah kina nan kina bachin asarar sai mun makara .”
Sai ta diro Sakina a kan gado, tana cewa, “Wallahi Mommy, bazan je ba, zanyi sallah kuma wallahi daga yau na daina makara zan tashi da asuba "…
Sakina ta juya ta tsaya kan gado, zuciyarta na bugawa cikin tsoro da ƙarfi. Ta ɗan ja numfashi, ta miƙe fuska da darewarta, tana cewa, “Wallahi Mommy… bazan je ba , !” tafe ta ta barta Domin chigaba da shirin ta
Amma kafin ta yi wani motsi, wani inuwa mai tsawo ya bayyana a gefe na ɗakin. Fuskar sa bata bayyana ba, amma muryar sa ta busa cikin sanyi:
“Wallahi… wannan graduation ba ta gama ba…”
Sakina ta tsaya cak, zuciyarta na tsorata sosai, hannunta na rawa. Idanunta sun buɗe sosai, tana ganin duhu yana zagaye ta, kuma wani abu a hankali yana matso kusa da ita.
Sai kuma ta ji wani abu ya busa cikin kunnenta, kamar iska mai ɗaci:
“FOREVER…”
A wannan lokaci, ta gane cewa ba mafarki ba ne. Wannan graduation… wannan GUGUWAR GRADUATION tunda ya fara mata gizo saboda tsananin firgita da tsoro da taki ciki tana faruwa a gaskiya
FINAL ......
NARNAH ƘANWAR SOJA
08101235739
MU HAƊU A LITTAFI NA GABA BAYAN SALLAH IN SHA ALLAH
AFNAN
KAR KU MANTA AKWAI HIJJAB'S NA MANYA DA NA YARA FOR UR EID .....