Author : Nanah Kanwar Soja Category : Romantic Hausa Novels
ZAN CHIGABA DA SALON BAYAR DA LABARIN SABODA YANZU SAKINA BAZATA IYA CHIGABA DA BAKU LABARIN ABINDA YA FARU......
Ta ji ciwo mai tsanani a hannunta.
Ta kalli—jini yana zuba, yana gangarowa ya jiƙa ƙasan class. Gashinta ya faɗi kan kafafunta, yana manne da jini. Duk jikinta na rawa.
Wani ƙarar gargadi ya daki kunnenta—kamar karar ƙararrawar da ke fitowa daga zurfin ƙasa. Ba ta san daga ina ba, amma zuciyarta ta tabbatar mata: lokaci na ƙarewa.
Ta miƙe da ƙyar, tana ja da ƙafa, tana nema hanyar tsira cikin firgice.
Class ɗin ya zama duhu ƙirin—babu haske, babu amo—sai bugun zuciyarta da numfashi mai yankewa.
Sai wayarta ta yi walƙiya.
Haske ya cika class ɗin na ɗan lokaci. Ta leƙo ta haska bango, ƙofa, kujeru—duk sun yi kama da fuskoki masu kallonta. Ta juya hasken a hankali, tana neman ƙofa Sai ta ga rubutu yana fitowa a iska, ja kamar jini, yana zubowa kamar yana digo:
ONE HOUR LEFT
TILL THE GRADUATION END…
FOREVER
Zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci.
“FOREVER?” ta raɗa, muryarta ta karye.
Hasken wayar ya soma rawar jiki. Allon ya yi sanyi kamar kankara. A bayan rubutun, inuwa ta motsa—ta kusanto.
Ta ji wani abu ya shafi kafarta.
Ba ta kalli ƙasa ba.
Ta san idan ta kalla—ba za ta ƙara tashi ba.
Ta ja numfashi da ƙarfi, ta tattara ƙarfin da ya rage mata, ta yi niyyar gudu—ko da zai kashe ta.
A bayan ta, wata murya ta busa kamar iska daga kabari “Sa’a ɗaya ko ki fita
ko ki zama ɓangare na bikin.”
…Hasken wayar ya yi walƙiya sau biyu, sannan ya fara dusashewa kamar fitilar da ake kashewa a kabari.
Ta fara gudu.
Matakanta suna buga ƙasa da amo mai kaifi—tak… tak… tak…—amma duk lokacin da ta matsa, class ɗin yana tsawaita. Ƙofar da ta gani a nesa tana ƙara ja da baya kamar tana tserewa daga gare ta.
Numfashinta ya rikice. Kirjinta na ƙonewa. Jini yana zuba daga hannunta yana barin layi ja a bayan ta.
Sai kujeru suka fara motsi.
Ba ta tsaya ba. Ba ta duba baya ba.
Kujeru suka ja da ƙasa suna toshe hanya, tebura suka karkata suna fadowa kamar ana shirya fage. Wata dariya ta tashi daga ko’ina—ba murya ɗaya ba, dariyoyi da yawa, masu sanyi, masu ƙwanƙwasa ƙashi.
“Ku zauna…” “Bikin bai ƙare ba…” “Jini bai isa ba…”
Ta buga jiki da bango. Ta juya hasken wayarta madubi ne a bangon. Ta hango kanta a ciki… amma ba ita kaɗai ba.
A bayanta—su ne. Dalibai cikin rigunan graduation ja da baƙi, idanuwansu sun ɓace, baki cike da jini, suna tsaye cikin tsari kamar hoton da aka ɗora.
Wata ta matsa gaba—fuska irin Afrah—amma idonta ba a inda ya dace ba, idon ta ɗaya a saman ƙoshin ta kuma ba hanci a fuskar ta sai ƙaton baki mai girman gaske
“Ke ce ta ƙarshe,” ta ce cikin murya mai taɓa kunne. “Bayan ki… bikin zai cika.”
Sakina ta saki ihu, ta juya ta gudu—ƙofar ta bayyana a ƙarshe. Ta tura—ta buɗe da ƙarfi.
Ta faɗo waje.
Haske hayaniya kiɗa dariya
Graduation na gudana kamar babu abin da ya faru.
Ta kalli hannunta—jini ya ɓace. Ta kalli kafarta—gashi babu. Ta kalli mutane—suna murmushi, suna daukar hoto.
Sai wayarta ta sake walƙiya a hannunta.
Saƙo ɗaya ya bayyana 30 MINUTES LEFT.
DON’T TURN AROUND.
Ta tsaya cak.
A bayan ta— dariyar da ta sani ta buga kunnenta.
Ta san idan ta juya— babu dawowa.
Sakina ta hango su huɗu—samari uku da mace ɗaya—sun ratsa bayan makaranta. Ba su tsaya, ba sa magana, kamar suna tafiya a cikin duniya ta daban, duniya da ba kowa zai iya gani ba. Ko wanne mataki su ke ɗauka, ƙasa tana girgiza kamar suna jan ƙasa da kafafunsu.
Ta tsaya cak. Ko da take ganin sauran mutane suna harkar su—iyaye suna ɗaukar hoto, yara suna wasa, malamai suna dariya—ba su lura da su ba. Amma zuciyarta ta gane wani abu ba daidai ba ne.
Da sauri ta juya hanyar gate, zuciyarta na bugawa, numfashi ya yi sauri. Burinta ɗaya: fita daga wannan makarantar kafin ya yi ƙyama.
Amma kafin ta kai ƙafa uku—wani ƙarar ƙarfi ya shiga kunnenta, kamar ƙaƙƙarfar murya daga ƙasa mai zurfi. Ta tsaya, zuciyarta na bugawa har zata fashe. Ta juya a hankali—abinda ta gani ya sa jini ya tsaya a jiki.
Su huɗun nan sun tsaya—amma ba kamar jikin mutum ba. Matar ɗaya ta fara narke kamar dutse mai narkewa, fuskarta ta zame, idonta ya rataya, bakinta ya buɗe fiye da kima. Samarin ukun kuma—sun canza siffa:
ɗaya ya juya kansa digiri 180
na biyu hannuwansa sun tsawaita har suka taɓa ƙasa
na uku ya ɗaga kai ya kalli Sakina kai tsaye da ido ɗaya a goshinsa
A lokaci guda, duk suna da murya guda ɗaya mai sanyi “Ba za ki fita ba… sai an cika adadi.”
Sakina ta ja da baya cikin firgice. Ta juya da gudu—amma gate na gaba yana fara rufe kanta a hankali, kamar wani abu yana jan ta.
Ta danna gudu, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Kafin ta kai ƙofar—hannun wani ya fito daga ƙasa ya cafke ƙafarta.
Ta faɗi da ƙarfi, ta saki ihu—amma babu sauti da ya fita wayarta ta faɗo, ta yi walƙiya: allon ya nuna sabon rubutu mai ja, mai ɗauke da jini kamar yana digo:
15 MINUTES LEFT.
ONE WILL REPLACE YOU.
Ta ɗaga kai a hankali—su huɗun nan sun ɓace. Amma ƙasan bishiyar nan, takalmin graduation ja yana nan—sabon, amma daidai nata.
Zuciyarta ta tsaya cak tsoro ya mamaye ta ..
Makarantar ta zama fanko ƙirin babu ihu babu dariya babu motsin numfashi sai iska da gigginniyar kaɗawar bishiyoyi.
Kamar an tsotse dukkan rayuwa daga cikin harabar, an bar bango da inuwa kawai.
Sakina tana gudu ba tare da sanin inda za ta dosa ba ƙafafunta na rawar tsoro, numfashinta yana yankewa kamar ana tsinka shi da wuƙa. Duk bugun zuciyarta yana ƙara mata rauni, kamar zuciyar za ta tsinke daga kirjinta.
Tana waiwaya baya—amma babu wanda take gani Sai dai… tana jin ana binta tamkar rundunar sojojin yaƙi , sautin sahun su na mata dukkan bugu a dodon kunnen ta sai wani sauti yake bayarwa wanda zai iya tauna ta jinta da motsin ta..
Nan take ta hango wani office a gefe ƙofar a buɗe take kaɗan, tana karkarwa a hankali kamar tana numfashi.
“Nan zan tsira…” ta faɗa a ranta.
Ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta shiga, ta rufe ta da sauri, ta jingina bayanta da ita. Ta zube ƙasa a hankali, tana sauke numfashi da ƙyar. Hannuwanta na rawa, idanuwanta cike da hawaye shiru.
Sai wani motsi daga cikin ɗakin.
Ta ɗaga kai a hankali—jikinta yana sanyi kamar an watsa mata ruwa daga kabari a can, kusa da tebur wata mata ce tsaye.
Sanye da tsohuwar riga ja.
Rigarta ta yi duhu, kamar an jiƙa ta da jini da lokaci ya ƙi busarwa a hannunta—jariri Jaririn bai motsi ba bai yi kuka ba.
Bai numfasa ba.
Matar tana kallon Sakina—amma ba da idanu biyu ba.
Ido ɗaya ne kawai ke kallonta, ɗayan ya ɓoye cikin duhu kamar bai taɓa wanzuwa ba.
Sakina ta ji sanyi mai kaifi ya ratsa jikinta, ya tsaya a ƙashin bayanta ya daskare.
Ba zato ba tsammani, matar ta ɗaga kanta…
ta yi murmushi Murmushi mara rai.
Sai ta fara yin wani abu da jaririn…
wani abu da zuciya ta ƙi karɓa, baki kuma ya ƙi furtawa saboda tsananin firgita , Sakina ta saki ihu mai tsaga kunne, da wani fitsarin da bashi da linzami takai idon ta ƙasa a maimakon taga fitsari sai taga jini ne kifita na bin ƙafafunta
Ta juya da gudu zuwa ƙofa—ta buge ta, ta rufe, ta jingina jikinta da ita, tana kuka, numfashi na fita da wahala.
“Ba ni gani ba… ba ni gani ba…” tana faɗa wa kanta ,tana numfashi mai ɗaukewa da wani nauyin jiki.
Da ƙarfi ake buga ƙofar Amman ta daskare ta kasa ko motsi , nan take matar ta bayyana a gabanta Ba ta buɗe ƙofa ba.
Ba ta shigo ba ta tsaya kusa da Sakina.
Sakina ta ji ana shakar numfashinta.
Da murya mai sanyi kamar ƙasa bayan rami, matar ta ce:
“Sakina…”
Jikinta ya daskare.
Matar ta matsa kusa, ta miƙa jaririn gaba—fuskar jaririn a ɓoye, amma shiru ya fi ihu tsoro Ta raɗa mata:
“Za ki ciyar da shi.”
“Ke ce za ki ba shi madara.”
Sakina ta girgiza kai, hawaye na zuba.
“A’a… don Allah… ba ni…”
Matar ta yi dariya—dariya mara amo, amma ta girgiza zuciya.
“Lokaci yana ƙarewa.” “Ɗaya daga cikinmu dole ya cika gurbi.”
ta ɓacce ɓatt hasken wayar hannun ta ya dawo sai wayar Sakina ta yi walƙiya a duhu.
Rubutu ja ya bayyana a screen:
10 MINUTES LEFT.
MOTHER OR SACRIFICE Sakina ta rufe idanu.
Ta san wannan ba mafarki ba ne.
Ta san—idan ta tsaya nan,
ba za ta fita da sunan Sakina ba.
Ta fara gudu Kafafunta na rawa, numfashinta yana yankewa Sai ihu ya tashi.
Ihun jarirai—ba a gani a fili ba, amma muryoyinsu suna zagaye ta, suna shiga kunnenta, suna caka mata zuciya hannunta ya yi sanyi.
Wani abu mara rai
ya kama ƙafarta, kasusuwa ta kiji a ƙafar tana duba ƙasa taga ƙwarangwal na jariri ya buɗe baki yana cewa " zaki ban madarar ke nasha yunwa nakiji" nan tasa hannu a saman ƙirjin ta ta dungule gunɗaya tana girgiza bakin ta ya bushe ba ruwa ga ɗan banzan ƙishi nan da nan aka dafa. ta tabaya aka miƙa mita gorar ruwa bataga kowa ba yana leloo a sama bataye tunanin komai ba saboda bala'en kishi da ta tsinci kanta a ciki , tana budewa ta sa bakin ta nan taji kauri da wari a take furzar sai jini ta kama amai kamar zata amayo da kayan cikin ta tana ihu tana kururuwa ,, dariya mai amo aka ƙifta dashi wanda yasa ta zabura ya cigaba da gudu tana neman hanyar fitta
Duk inda ta ja ƙafa—suna binta.
“ALLAH NA!… INAI!” ta saki ihu ta juyo—babu kowa babu mutum Sai dai ihun jariran…
suna ƙara kusantowa.
Sakina ta ci gaba da tserewa, amma duk gudun da take yi—
kamar tana gudu ne zuwa cikin su, ba daga gare su ba.
Tsayawa yaye chakk ta so chigaba da gudu aman ko yatsa ta sun kasa motsawa domin an makireta ta kasa sarrafa komai nata
“WELCOME BACK TO THE GRADUATION HALL.”
Sakina ta tsaya cak ta ɗaga kai , abin ta hango yasa ta zube a sume ......
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 7 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9 /2 /2026
starting posting on 4/2/2026
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕
✨ Ramadan na kusata! ✨🌙
Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka.
🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara.
🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu.
Ramadan Kareem! 🌙💫
₦
Harabar makarantar da take ciki ta canz bango ya tsufa cikin daƙiƙu, haske ya dusashe, ƙasa ta fara bayyana da layukan graduation stage da ta taɓa gani a hotuna… amma a wancan lokaci an cika su da farin ciki yanzu ba farin ciki.
Gaba ɗaya ɗakin ya zama hall ɗin kammala karatu kujeru suna nan, amma babu mutane. A kan stage—jarirai uku suna kwance, shiru, idanuwansu a buɗe.
Sai murya ta fito daga speaker, murya ɗaya da ta san ta taɓa ji a baya
murya da aka ambata a GUGUWAR GRADUATION:
“Ba a kammala kowa ba… sai an biya farashi.”
Sakina ta ja da baya a jikin bangon baya, wani rubutu ya fara bayyana da jini:
“CLASS OF THE DAMNED.”
Nan take, matar riga ja ta bayyana a kan stage—amma yanzu ba ita kaɗai ba ce. A bayanta, inuwa-inuwa suna tashi, kowacce tana ɗauke da jariri.
Matar ta yi murmushi, ta ce: “Kin tsira daga jarrabawa.” “Amma graduation… ba kowa ke wucewa ba.”
Ihun jarirai ya koma kamar sautin applause—clap… clap… clap… amma da kuka a ciki.
Wayar ta sake walƙiya:
MAKE YOUR CHOICE.
BECOME A MOTHER.
OR
BECOME A MEMORY.
Sakina ta kalli hannuwanta—sun fara dusashewa kamar hoto da ake gogewa. Sunanta ya bayyana a screen, sai haruffa suka fara gogewa ɗaya bayan ɗaya:
S A K I N A
Ta saki ihu: “BAN YARDA BA!”
Muryar ta amsa daga ko’ina: “Kowa ya ce haka.”
Matar riga ja ta miƙa jariri ɗaya—yanzu jaririn yana motsi. Ya buɗe baki, amma abin da ya fito ba kuka ba ne…
“WELCOME TO GUGUWAR GRADUATION.”
Haske ya kashe.
Sai sautin ƙarshe—sautin hula ta graduation tana faɗowa ƙasa.
Sakina ta ci gaba da gudu, zuciyarta na bugawa kamar zata tsage. Kowa da kowa a makarantar ya ɓace, dukkan wuri ya zama duhu mai ɗanɗano na tsoro. Sai ga wani abu ya fado daga sama—ta yi tsammani ruwan sama ne, amma ya ɗauki siffar ruwa mai ja ja kamar jini, ya fara zuba a kanta.
Jikin ta ya yi sanyi, kamar kankara na yawo a cikin ƙashi. Ruwan jini ya manne da fuskarta, ya shiga gashinta, ya manne da tufafinta, har numfashinta ya ɗan tsawaita, zuciyarta na bugawa cikin tsananin firgice.
Ta tsaya cak, idonta ya buɗe sosai, sai ta ga cewa duk da gudu da ta yi, duhun class da office da ta tsere sun koma a gabanta. Kowane kusurwa, kowane bango, duk yana motsawa kamar yana kallonta, kamar suna jiran ta kammala minti ɗaya kawai.
Sakina ta miƙe hannayenta da ƙarfi, tana neman hanyar fita, amma ƙafafunta sun kasa tafiya kamar suna manne da ƙasa. Wani ƙararrawa mai sanyi ya busa cikin kunne:
“Ba za ki tsira ba… har sai kin tsaya… har sai kin zama ɓangare na abin da ke nan.”
Ta saki ihu mai tsanani, amma kowa da kowa ya ɓace—duhu da ruwan jini kawai suka tsaya a kanta. Ta fara juyawa cikin tsoro mai tsanani, ido nata ya haɗu da inuwa mai lankwasawa daga sama.
Ruwan jini ya ci gaba da sauka, amma yanzu yana murmurewa kamar yana rera murya, yana busa kamar numfashin wani mutum da aka rufe a cikin kabari. Zuciyarta ta tsaya cak—ta fara fahimtar cewa wannan ba mafarki bane, wannan gaskiya ne, kuma tsoron da take ji yanzu yana ci gaba da matsowa a cikin ƙashin kanta.
Sakina ta hango ruwan jini yana zuba kamar sama ta buɗe, ta yi ƙoƙarin tserewa amma ƙafafunta sun tsaya, kamar wani ƙarfin da ba ta iya kawarwa. Ta yi ihu, sai zuciyarta ta daina bugawa na ɗan lokaci—ta suma a cikin firgice.
.
Ta farka a cikin sanyin firgice, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Ko’ina duhu ne, amma idanunta sun fara gane wasu inuwa masu motsi a zagaye da ita. Murya babu, sai wani kukan cikin zuciya, da jijjiga mai sanyi a ƙashi.
wani wuri mai duhu da tsoro fiye da tunani. Halittu marasa rai da baƙaƙen inuwa suna zagaye da ita. Fuskar su babu rai, idanunsu suna kallonta kai tsaye, muryoyinsu suna ƙara ihu cikin zurfin zuciya—kamar karar jini da kukan mutanen da aka manta da su shekaru.
Ta yi ƙoƙarin motsi, sai ta gane hannuwanta da ƙafafunta an ɗaure da wani abu mai sanyi da mai kaifi, yana manne da fata da nama. Ta fara leloo, ta ɗaga kai, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Duk wuri na zagaye da inuwa masu murmushi mara rai, suna kallonta da dariya mai sanyi kamar suna jin daɗin tsoronta
Hannunta da ƙafafunta an ɗaure da igiyoyi masu tauri, kamar sun fito daga cikin kabari. Ta leko sama, wasu halittu ne—dogaye, fuskarsu ba ta ɗanɗana, idanu sun yi ja kamar harshen wuta, gashin su mai tsabta, amma duk da haka jikinsu yana kama da kayan sanyi da jini.
“Me suke so da ni?” ta yi ƙoƙarin cewa, amma muryarta ta fashe, ta koma hawayen tsoro kawai.
Duk lokacin da ta motsa ƙafarta, ɗan jijjiga ya shiga igiyar da ke ɗaure ta, yana sa ta jin ciwo mai tsanani. Halittun sun tsaya a zagaye, suna kallonta, ba sa motsi, amma zuciyarta ta gane: kowanne daga cikinsu na jiran wani abu.
Sai ta lura wani ruwan sanyi ya fara zuba a kanta. Ta ɗan girgiza kai, zata ce ruwa ne, amma daga ƙasa ya fito… ruwan ja, kamar jini mai tauri, yana wanke jikinta, yana shiga cikin igiyar hannunta, yana sanya ta jin kamar tana nutsewa a cikin wani kabari mai rai.
Ta yi ƙoƙarin ihu, amma babu muryarta. Sai zuciyarta ta tsaya, ta ji kankanin jijjiga a ƙashi, gashin kanta ya tsaya, hannunta na rawa, ƙafafunta ba za su iya ɗaukar nauyi ba. Ta leƙo sama, inuwa sunyi wani motsi mai tsanani—suka ɗan juyo kamar suna murmushi… ba murmushi na rai ba, murmushi na kabari.
Daga gefen ta, ɗaya daga cikin halittun ya matso kusa da ita, hannunsa ya taɓa fuskar ta, sanyi kamar kankara, zuciyarta ta tsaya cik. Wannan shi ne lokacin da ta fahimci: ba zata tsira daga nan ba idan ba ta yi wani abu ba amma me za ta iya yi?
Lokacin na ƙarewa… kuma kowace numfashi na iya zama na ƙarshe.
COMMENTS SECTION GROUP
https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️
🩸 Storm of Graduation 🩸
Horror Short Story
PART 8 / 10
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
Writer of Dr Sadeeq
This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️
9 /2 /2026
starting posting on 4/2/2026
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*