DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   37 / 39

108K to 111K   out of 116.4K words

sai na fahimci ba ya kan layin kana na saduda.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta ina dafe ƙirjina da yake buga wa fiye da kima a kimiyyance. Jikina a sanyaye na je ɗakin Anty Sawwama na sanar da ita zuwan su Saifullah, ita kan ta sai da ta tambaye ni ko lafiya na ce da ita ni ma ban sani ba. Haka na gudanar da aikin da ya kallafa a kaina cikin sanyin jiki da rashin kuzari.
Ina zaune a ɗaki na ji sallamarsu a tsakar gida na leƙo ta taga na ga tare suke da Yaya Alhassan da kuma Umar da suka yi musu jagoranci har zuwa cikin gidan suka shigo falo suka zauna, Anty Sawwama ta fito suka gaisa kana Umar ya zo ya ƙira ni na fito na gaishe su, ganinsa tare da Muhammad Taufik ya sanya jikin ƙara sanya tamkar kazar da aka gauraya a cikin ruwan gishiri, na je musu ruwan sha na ajiye a gabansu zan koma ciki Yaya Alhassan ya ce na dawo na zauna haka na yi na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraron yadda ƙirjina yake bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawan disko.

"To kamar yadda na riga na sanar da kai tun a waje wannan shi ne dalilin zuwanmu, don na ga ya dace ku san abin da yake faruwa. Sannan aminina Sultan ya buƙaci ya zo don ya gabatar da godiyansa a gare ku a madadin dukkan ahalinsu".
Saifullah ya yi zancen a dunƙule da ya sanya kan Anty Sawwama kullewa, take Saif ya warware musu duk yadda muka yi da shi akan wannan memory card ɗin akan kowa. Anty Sawwama ta cika da mamaki don a ta yi zaton hakan ba, Yaya Alhassan ma duk da Saif ya riga da ya sanar da shi zancen tun kafin su shigo ciki sai da ya cika da mamaki ainun.

A wannan karon Muhammad Taufik ne ya karɓe zancen cikin faɗin"tabbas sa'ilin da na saurari wannan sautin muryar ba zan iya fasalta tashin hankalin da na shiga ba, duk dauriya da juriya irin zuciyar na miji sai da na ji hawaye sun zubo daga idanuna na kasa fassara kaina da har sai da hankali na gushe daga gare ni. Saifullah shi ya kasance a tare da ni a cikin wannan yanayin mai tsauri ba zan taɓa mance wa da shi a cikin tarihin rayuwata, cikin hikima da fasaha muka tunkari Sheik da zancen kuma cikin ruwan sanyi ya amsa cewar duk abin da muka ji haka ne, kuma tun daga ranar da lamarin ya faru shi kansa ya yi nadama mai tsananin gaske, tun daga lokacin ya kasance cikin zulumi, fargaba da kuma jiran fitan sautin muryar a duniya sai dai kuma shuru lamarin da ya karya masa zuciya ke nan. Tsoronsa ɗaya kar asirinsa ya tuno a idon duniya kar kima da darajarsa ta gushe a idanun jama'an da suke yi masa kallon tamkar waliyi a gare su, haƙiƙa manyan mutanen da ya sani da tarin ƴan siyasan da yake mu'amala da su za su yi ɓatan dabo, don babu wanda zai so ya lalata tafiyar siyasansa sa boda ƙoƙarin kare masa martaban sunansa. Tabbas ya aikata laifin da ya yi ikirari sai dai yanzu ya yi nadama matuƙa don na hangi hakan a cikin idanunsa, Malam ya yi nadama matuƙa don har sai da ya yi ƙwalla kuma ya nema gafara a bisa samar da ni ta hanyar da ba ta dace ba, ya tara dukan iyayensa ya sanar da su abin da yake faru ya kuma roƙi yafiya da gafaransu. Tabbas ba mu san inda za mu sanya kanmu ba idan maganan nan ya watso a duniya, ba mu san wani hali Malam zai shiga ciki ba, na zo ne musamman na yi miki godiya a bisa madadin dukkan ahalin Sheikh Dawood akan killace wannan sirrin da kika yi kika kuma ɗamka sa a hannun da ya dace har ya iso gare shi a cikin sigar da ya dace".

Tun da ya soma maganar nake kuka marar sauti har ina ƙoƙarin shiɗewa, sai da Anty Sawwama ta riƙo hannuna tana murzawa a hankali cikin sigar lallashi da kwantar mini da hankali.
Muryarta a shaƙe sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni na soma magana a hankali, sautina ba ya fita yadda ya kamata.

"Yaya Alhassan ka yi haƙuri na kasa bin umarninka, na kasa yi maka biyayya wallahi zuciyata ce take azalzala ta yayin da ni kuma na gaza jure wa har sai da na biye mata. Ban aikata hakan don na nuna maka ba ka isa da ni ba, ban aikata hakan don nuna maka cewa ba ka kai ka kafa mini umarni na bi ba. Yaya Alhassan na tuba na you nadama na gurfana a gabanka ina neman afuwa da yafiyarka".
Falon ya yi tsif babu abin da ake ki face sautin kukana.

Cikin taushin murya Yaya Alhassan ya soma cewa"Amatullah ba ki yi min komai hasalima kin yi tunanin da ni kaina ban yi shi, wallahi na ji daɗin abin da kika yi na kuma cika da alfaharin kasancewarki ƴan uwa a gare ni. Kin yi wani babban lamarina da ya dace a yaba miki kuma a jinjina miki".
"Ƙwarai don tabbas kin zamo silar wanzar da haske a cikin rayuwata kin haska min hanyar da zan yi tafiya ba tare da ɗan jagora ba. Ba zan da wani baki zan yi miki godiya Amatullah". Muhammad Taukif ya yi zancen cikin sanyin murya harrufan har suna harɗe wa waje guda.

"Ba na buƙatar godiya don na yi hakan ne domin Allah ba don a gode mini ba". Na yi zancen cikin ƙarfin tare da tashi na koma cikin ɗaki ina shiga na zubo akan katifa ina ci gaba da kukan, na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina ya toshe. Lokacin Anty Sawwama ta shigo cikin ɗakin ta din ga lallashina da ba ni baƙi.

"Tashi ki je falo ki same su don ke suke jira". Ta yi zancen ta na goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana, kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na fito kamar yadda ta umarce ni.
Kaina a ƙasa na fito falon bakina ɗauke da siririn sallama na ƙariso na zauna a ƙasa, shuru-shuru cikin mu babu wanda ya yi magana kafin can Muhammad Taufik ya yi kawar da shurun.

"Ni dai kam ba zan iya daina yi miki godiya ba, kuma ina so na ƙara tabbatar miki da cewar abokina yana yi miki ingantacciyar soyayya ina ji a jikina shi ne mijin da ya dace da ke, don haka ina fata da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku".
Ban iya amsa wa da baki ba sai a cikin zuciyata na amsa. Har ya tashi ya fita daga cikin falon yana tsokalan Saifullah ban ɗago kaina ba.

"Amatullah". Na tsinkayo muryar Saifullah a kunnuwana, ban amsa ba illa ɗaga kai da na yi ina kallon sa ido cikin ido a karon farko a cikin rayuwata. Kamar an buɗe fanfo na ji hawaye suna zuba daga idanuna.
Da ƙyar na buɗe bakina na yi magana"ina ta jir ƙiranka shuru idan na ƙira kuma ba ya tafiya, ka san girman tashin hankalin da na shiga kuwa?".

"Ban sani ba sai dai yanzu ki sanar da ni". Babu shiri na watsa masa harara da wutsiyar idona ina goge hawayen idona.
"Afuwan ranki ya daɗe na san na aikata gagarumin laifi. Tashin hankalin ganin Sultan cikin halin da ya shiga shi ya hana ni kunna wayata, Sultan ya shiga tashin hankalin da ko maƙiyinsa ne sai ya tausaya masa har ma ya zubar masa da hawaye, don har kwanciya ya yi a gadon asibiti ya shafe kwanaki uku ba tare da ya san inda kansa yake ba. Wannan tashin hankalin shi ya hana ni samun lokacin wayata balle har na ƙira ki, amma yanzu na kawo kaina a yi min ko wani irin hukuncin da ya dace da ni". Ban iya cewa da shi komai ba illa kukan da na ci gaba da yi, ban yi aune ba na gan shi zaune a gabana dan da ni ina ɗago kai muka haɗa ido da shi.

"Don Allah ki daina wannan kukan idan ba so kike yi ni ma na fara hawayen ba". Yadda ya furta zancen ya sanya jikina gabaɗaya sanyaya tabbas yadda na ga idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ga jijiyoyin kansa sun fito sun yi ɓaro-ɓaro a saman goshinsa hawayen ma idan ya yi ba zan yi mamakina.
Ba don na daina jin zafin da nake ji a cikin ƙirjina ba na kai hannu na goge hawaye fuskana, ya furzo mini iska daga bakinsa a fuskana da har sai da na lumshe idanuna.
"Yauwa ko ke fa, to yanzu an yafe min ne ko kuma?".

"Ai daman babu abin da ka yi".

"Ni dai ki ce kin yafe min sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa".
"To shi kenan na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaga".

"Amin ya Allah".

Daga haka na yi shuru har sai zuwa lokacin da ya ce"to yanzu kuma me ye ya rage?". Na ɗage masa ido ɗaya alamar rashin fahimta da hakan ya sanya sa faɗin"ko sai na tuna miki alƙawarin da kika yi kafin ku fuskanci idan maganan tawa ta dosa?".
Numfashi mai nauyi na sauƙe kafin na sama zarafin cewa"na ba ka dama Saifullah ka turo iyayenka gidanmu, don su nema maka aurena". A kunyace na ƙare zancen ina rufe fuskana da tafukan hannayena.

"Alhamdulillah".

Ya furta yana yin sujudul shukur ga Ubangiji, ya ɗago ya ɗaga hannayensa sama yana addu'a cikin tsananin farin ciki.
"Allah na gode maka bisa wannan damar da ka ba ni. Ina roƙonka ka ba ni ikon killace soyayyarta a cikin zuciyata ba tare da na haɗa ta da wata ɗiya mace ba, Allah ka ba ni ikon riƙe ta bisa amana na kuma inganta rayuwarta ta hanyar da ta dace. Ka hana ni yi mata kishiya har abada". Ganin na yi shuru ban amsa ko ɗaya daga cikin addu'o'insan ba ya sanya faɗin"ba ki amsa ba ke nan?".

"Na amsa a cikin zuciyata".

"To ki amsa da bakinki na ji". Na taɓe fuska ina faɗin"na amsa a cikin zuciyata fa".
"Na amsa a cikin zuciyata fa". Ya yi zancen cikin kwaikwayon muryata da salon yadda na yi zancen, sunkuyar da kaina ƙasa na yi sa boda kunyar da ya lulluɓe ni.
"Wai kunya kike ji? Uhmm! To yanzu idan kin shiga ciki ki sanar da su cewar iyayena za su zo jibi in sha Allah".

Babu shiri na ɗago kaina"da sauri haka?"? Ya ɗage mini giransa ɗaya"to me ye za a jira". Ya ƙare zancen yana sunkuyo da kansa daidai saitin fuskana. Babu shiri na tashi na yi ciki da sauri sa boda kunyan da ya gama ba ni. Ɗakina na nufa na zauna na tsawon awanni ji nake yi saƙayau duk wani damuwana ya hau, zuciyata ta yi fes yayin da raina ya yi tas, haka na wuni cikin karshashi da ƙwarin gwiwan da ya zagaye jikina da yamma muka yi waya da Amira na sanar da ita komai ta taya ni murna matuƙa, ita ta hanyar ni shawaran na ƙira Anty Zulaihatu na sanar da ita zancen zuwan iyayen Saifullah jibi na yi na'am da shawaranta. Mu na gama waya da ita na ƙira Anty Zulaihatu na irge masa komai, Baiwar Allah har da kaddara kafin ta shiga rero mini ruwan addu'a ta kuma shaida mini a ranar za ta ƙira Anty Sawwama da Yaya Alhassan ta shaida musu zancen.

Daren ranar mun fi awannin biyar muna waya da Saifullah yayin da na ji ya ƙara shiga cikin raina sosai, ya ba ni Hajiya Muhibbat muka gaisa a waya har da kukanmu ni da ita. Washe gari tun da asuba Anty Sawwama ta ƙira don ta ji daga gare ni akan abin da Anty Zulaihatu ta ƙira ta sanar mata, na kuwa tabbatar mata da zancen ta yi hamdala tare da yi mana addu'a. Take aka soma shiri da shirye-shiryen tarban iyayen Saifullah gobe ranar Anty Zulaihatu a gidan ta kwana, washe gari da yamma lilis magabatan Saifullah suka zo su gidan Anty Sawwama neman aurena a hannun Yaya Alhassan aka kuma ba su tare da sanya auren nan da sati huɗu masu zuwa. Ranar wuni na yi da zazzaɓi da boda fargaba da zulumi da dare muka sha kukanmu tare da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu sa boda tuno Abba da muka yi da hashashen irin farin cikin da zai yi don ganin wannan ranan in da yana raye.
Bayan kwana biyu Amir ya ɓullo da wani zancen wai na je na yi gwajin genotype, Anty Sawwama ta yi kai da fata ta ce ba zan je ba, har da faka hujja da cewar su a lokacinsu duk ba a yin wannan gwaji ga shi kuma har suka gama haihuwarsu lafiya sumul, daga su har ƴaƴan. Sai da ta ga shi ma kansa Saifullah ɗin ya goya bayan a je a yi gwajin sa boda gujewa afkuwar matsala, sannan ta saduda ta zubar da makaman yaƙinta. Muka cire ranar da za mu je mu yi gwajin lokacin ana sauran sati uku bikin, duk da tun kafin lokacin shi Saifullah ya shaida mini cewar na shi AS ne don ya daɗe da sanin hakan.
Rananr gwajin tare muka je da Anty Zulaihatu da kuma Umar muka je aka yi mana gwaji ni da shi, aka je mu ɗan jira kafin sakamakon ya fito haka muka jira aka fito sakamakon Saifullah da Umar suka shiga amsowa.

Babu jima wa suka fito ba su ce da mu komai ba muka shiga mota muka tafi, maimakon mu koma gida sai muka ƙara wuce wa wani asibitin, Anty Zulaihatu ta gaza jurewa har sai da ta tambaya ko lafiya suka ce da ita lafiya kawai su na so tabbatar da wani abu ne.
Wani gwajin aka ƙara yi mana, kamar karon farko Saifullah da Umar ne suka shiga suka also sakamakon. A wannan lokacin yanayin da suka shiga ya yi muni sosai haka muka shiga mota zuwa gida ya faka a ƙofar gidan, ya ce mu shiga ciki ga shi nan shiga wa, haka muka sauƙa ni da Anty Zulaihatu muka shiga cikin gidan, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa.
[12/27, 5:50 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 8️⃣1️⃣

Tun da muka shiga cikin gidan na kasa zaune balle tsaye ɗaki na shiga na yi ta safa da marwa, yayin da tunani kala-kala suke ziyartar ƙaramar curin kwanyata. Cikin wannan halin Anty Zulaihatu ta shigo ta ƙira ni ta ce na zo falo ana nema na, haka na biyo ta a baya har suka iso cikin falon inda muka iske Umar da Anty Sawwama zaune a cikin falo. Muka ƙariso ciki muka zauna.
"Da kuke asibitin ya ya aka yi? Na ga kamar gabaɗayanku hankalinku ba a kwance yake ba. Ko dai wata cutar aka ce ɗaya daga cikinku yana ɗauke da ita?". Anty Sawwama ta yi tambayar tana kafe Saifullah da ido da ya kasa cewa uffan illa sadda kansa ƙasa da ta yi. Anty Zulaihatu ne ta yi magana a madadinsa"wallahi Umma mu ma ba mu san abin da yake faruwa ba, sun dai ce mu shigo ciki ne kawai ba tare da sun sanar da mu komai ba".

Takardan sakamakon gwajin Saifullah ya miƙa wa Anty Zulaihatu ta amsa yayin da yake koro jawabansa.
"Mun je asibitin farko aka yi gwaji inda sakamakon ya nuna cewa ni da ita Amatullah gabaɗayanmu AS ne, daman ni na san nawa na zo ne don a ƙara tabbatar wa, ban yarda da sakamakon don a wasu lokutan ana samun matsala dangane da kayan aikin gwaji ko kuma daga su kansu ma'aikatan hakan ya sa muka ƙara zuwa wani asibitin aka ƙara gudanar da wani binciken, nan ma ba a sama canji daga wancan gwajin na farkon ba. Tabbas ta tabbata ni da Amatullahi dukkan mu AS ne".

"Me ye hakan ke nan ya ke nufi ɗan nan? Shi AS ɗin mene ne aibunsa? Ni fa shi yasa tun farko ban yarda aje a yi wannan gwajin ba sa boda gudun wanzuwar matsalolin da wannan nan mutanen masu jajayen kunnuwan nan suka kawo".

"Umma hakan ya nufin aure a tsakaninsu ba zai taɓa yiyuwa ba, sa boda ko da an yi auren matsaloli da tashin hankalin da za su biyo bayan auren sai ya tushe duk ginin soyayyar da aka yi ta wargaza komai". Anty Zulaihatu ta yi zancen tana juya farar takardar sakamakon gwajin da yake riƙe a hannunta.
"To sai me ye don dukkan su AS ne? Mu da can a lokacin mu ana wannan gwajin ne amma ba ga shi mun yi auren mun haihu lafiya sumul ba. In sha Allah babu abin da zai hana auren Saifullah da Amatullah". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta yi shigewarta cikin ɗakinta, da kallo dukkaninmu muka bi ta kafin Anty Zulaihatu ta saka salati cikin tsananin damuwa da rashin mafita da kuma madafa.
"Anty yanzu ya ya za a yi a fahimtar da ita illan da yake tattare da hakan?". Saifullah ya yi zancen muryarsa har rawa take yi yayin da yake tsayar da idanunsa akan Anty Zulaihatu.

"Wallahi ban san yadda zan yi wa Umma bayani ta fahimta illan wannan abun ba. Amma bari na ƙira Yaya Alhassan na sanar da shi halin da ake ciki".
"A'a kar ki ƙira shi alhalin yana can wajen aikinsa, idan ya dawo kawai ki yi masa bayani ni ma in sha Allah zan ƙira shi mu yi magana a waya".

"To shi kenan duk yadda ka ce haka za a yi".

Sai a lokacin Umar ya buɗe baki ya yi magana damuwa jingim a tattare da furucinsa"ni na ma rasa abin da zan ce, gabaɗaya lissafina ya katse". Dafo kafaɗarsa Saifullah ya yi cikin salon ƙarfafa masa gwiwa ya soma faɗin"haka Allah ya ƙaddara Umar, sannan ko wani Bawa ba ya wuce ƙaddararsa a

37 / 39