DAFIN HARSHE BOOK 2 COMPELET HAUSA NOVELS BY IYAM.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 39

15K to 18K   out of 116.4K words

gumin da na haɗa kana na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na shiga ciki, na yi sallama aka amsa mini kana na shiga na iske wata mace zaune tare da wasu yara biyu masu tsananin kama da juna dukkan su maza sun yi shiga iri guda. Na tsuguna na gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ta na bi na da kallo.

"Hajiyar ta nan kuwa?".

"Lafiya kike neman ta?".

"Ita ta ce na zo".

A wulaƙance ta ce"to sai ki jira ta ta fito".

"To". Na amsa da shi a taƙaice zan zauna akan capet ta ce na sauƙa ƙasa, ban yi mata musu ba na yi kamar yadda ta ce. A ƙalla mun yi fiye da awa ɗaya zaune a wajen muna jira kafin ta fito tana fitowa yaran suka yi wajen ta da gudu suka rumgume ta. Ta riƙo hannunsu suka ƙariso suka zauna kafin ta ce"Altine ku da muka yi da ke za ku yi kwana biyu a can, ya ya kuma na gan ku yau?".
Matar da ta ƙira da altine ta kaɗa baki ta ce"wohoho Hajiya ai Alhaji ƙarami ne ya je gidan gaida Hajiyarki dagan kuma ya ce a dawo da su, ko kuma shi ma ya haɗa kayansa ya koma can ayi hutun ƙarshen makon a shi".

"Saifullah ke nan shi dai ba ƙaunar yaran nan su yi nisa da shi".

"Ƙwarai kuwa Hajiya, ai ni tun da nake ban taɓa ganin ƙauna irin wannan ba. Hajiya ga baƙuwa nan kin yi. Sai a lokacin ta lura da kasantuwana a cikin falon ta kai idon ta kaina"ki ƙariso ki zauna mai kyau mana". Ban ce komai ba na tashi na iso gaban ta na zauna tare da gaishe ta ta amsa tare da zarce wa da faɗin"mun yi magana da shi ya kuma amince don haka za ki iya fara zuwa daga gobe, albashinki naira dubu ashirin ne duk wata sannan aikin da za ki na yi shi ne sharan cikin gida, mopping da kuma girki. Idan na yaba da tsaftan da kuma ƙarewarki akwai yiyuwar na ƙara miki albashi".

Take na durƙusa ina ta jeranta mata godiya kamar zan yi aron baki ta nuna mini cewar babu komai. Ta ba ni naira ɗari biyar ta ce na yi kuɗi mota sai gobe na fara fitowa aiki lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen sallan magriba. Haka muka yi sallama raina fari ƙal kamar nono kindirmo ina ƙoƙarin fitowa daga falon na yi karo da mutum har sai da abin da yake hannunsa ya faɗi ƙasa.
Waya ne da ya faɗi na tsuguna da sauri na ɗago na miƙa masa ina faɗin"ka yi haƙuri wallahi ban lura da kai ba ne.......".

Miɗik na haɗiye ragowar zancen saboda firgitan da na yi. Na tsaya cak ina kallonsa tare da wassafo inda na taɓa ganin fuskarsa. Take na nufa inda na taɓa ganin sa shi ne wanda muka haɗu da shi yau da asuba har ya ba ni sallaya na yi salla a kai.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 4️⃣7️⃣

"Ke ce? Me ya kawo ki nan?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa saboda ba zan iya juran irin kallon da ya katse ni da shi da ya fi kama da na tuhuma ba. Kafin na kai ga ba shi amsa tagwayen yaran suka fito a guje har suna rige-rigen rumgumansa ya tsuguna akan gwiwansa tare da ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa.

"Uncle Saif tun ɗazu Inna Altine ta dawo da mu, ba mu gan ka ba". Ya shafa kan yaron da ya yi magana tare da cewa"Aryan na tafi wajen aiki shi yasa, amma ai na je can gidan Hajiya Maman ai na gan ku kafin na tafi". Ɗayan yaron ya yi caraf ya amshe zancen"ai Hajiya Mama ma ta yi ta masifa bayan tafiyanka, Anty Talatu ma cewa ta yi wai....". Kafin ya dirar zancen ya rufe masa bakinsa"Ayan ba na hana ka yawan sutura ba? Kai duk abin da ya faru zai ka kaso ka faɗa. Shi yasa Aryan ya fi ka hankali". Take Ayan ɗin ya cuno baki gaba gami da buga ƙafa yana kai wa Aryan ɗin da yake yi masa gwalo duka ya zame.

"Wallahi bai fi ni hankali ba, ai Mummy ma ta ce ni ne babanta Aryan kuma ba babanta ba ne tun da shi sai kukan banza". Tana ƙare zancen ya bi Aryan ɗin da gudu suka shige cikin gidan, na bi su da kallo don ba ƙaramin burge ni yaran suka yi ba, kamansu guda, yanayinsu, girman jikinsu hatta muryar su kala ɗaya ne. Sai dai abin da na lura da shi ɗaya ya fi ɗaya suturu.

Figigi na dawo cikin hankalina saboda fizge wayarsa da ya yi daga hannuna bai ce da ni komai ba, ya bi bayan yaran yana ƙira sunan Ayan, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ja ƙafafuna da suka sanƙare na bar wajen, kafin na isa gida har an fito daga masallacin sallan magrib ina zuwa na karɓa makuli na buɗe ƙofan ɗakin na shiga na ɗauko buta na zo na yi alwala na koma ciki.
Sallan magrib na yi na haɗa har da na isha'i na zauna a wajen ban motsa ba na zuba uban tagumi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma na waigo ko ina ban ga alamar alƙur'ani ba.
Na runtse idanuna wasu siraran hawaye suna gangarowa daga gefe da gefen idona, a bayyane na furta"Allah ya jiƙan ka Abba, Allah ya yi maka rahama ya kai haske cikin kabarinka".

"Amin".

Na ji an amsa da shi da hakan ya tursasa mini buɗe lumshashshun idanuna, na kafe La'aniyatu da su har ta iso inda nake ta zauna a gaba na.
"Kin dawo kenan?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan"kin ce za ki ba ni labarin aikin da kika samu idan kika dawo".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na kwashe komai na juye mata tas, sai da na dire zancen ta ce"Allah ya saka mata da alkhairi, amma gaskiya ta kyauta kuma ta na da kirki. Amma har dubu ashirin kuɗin da yawa gaskiya".

Na jinjina kaina"ni ma haka na gani, kuma a hakan ma ta ce za ta ƙara mini wani abu idan ta ga yanayin kamun ludayina".
Ta riƙo dukkan hannayena"Allah ya sa a fara a sa'a".
"Amin na gode sosai". Na furta ina ƙoƙarin samar da annuri a bisa fuskana, haka muka ɗan taɓa hira da ita kafin muka yi sallama tare da yi wa juna sai da safe.
Tsabar farin ciki kasa bacci na yi na kwanta kawai ina ta juye-juyen ji nake yi kamar gari ba za ta waye ba balle har na fara fita wajen aikin.

Ina daga kwance na ji an bankaɗo labulen ƙofar ɗakin an faɗo cikin ɗakin, duk da a cikin dubu ne amma ina gani gizon mutum yana nufo inda nake. A kiɗime na rarumo ɗan kwalina da ya zame daga kaina na mayar kaina.

"Waye ne wannan? Waye ne?". Na yi maganar harshena har yana harɗewa, ba a amsa mini ba aka ci gaba da nufo inda nake zaune, babu shiri na tashi na miƙe tsam akan ƙafafuwana da suke rawa, babu wadataccen hasken da zai ba ni kallon fuskarsa balle na iya bambamce wane ne, har lokacin ba a amsa mini ba haka nan ba daina nufo inda nake ba, ya kawo hannu da niyyar kawo mini cakfa na yi hanzarin zamewa ya faɗi akan tabarman ruf da ciki. Yana wani irin numfarfashi kamar ragon layan da aka zarcewa wuya za a yanka shi.

A guje na bazamo waje ina kurma ihu, take waɗanda suka rage a cikin gidan ba su fita ba duk suka fiffito suka dallo ni da tocila.
"Ke dalla banza mene ne kika fito ki ma hurmawa mutane ihu?".

Ɗaya daga cikin ƴan matan da suke tsaye a wajen ta furta a zafafe kamar za ta kai mini duka. Hajiya Babba ta fito tana gyara ɗaurin zanin jikinta da yake ƙoƙarin zame wa.
"Wa ye yake son ya tada min da hankali da daren nan?".
"Hajiya wa ye kuwa ban da wannan kucakar yarinyar mai zubin ƴaƴan aljanu, duk ta fi ta fitsine mutane a cikin gidan nan". Hajiya Babba ta nuna wacce ta yi zancen da ƴatsarta"ke Zuby ba na son ɗiban albarka, daman har masu zubin ƴaƴan aljanu ne a cikin gidan nawan ban sa ni ba?".

"Hajiya ga ta nan ai sai ki tambaye ta abin da yake faruwa ta yi miki bayani". Zuby ta ƙarƙare zancen tana yi mata nuni da inda nake tsaye har zuwa lokacin ban dawo daidai daga kiɗimar da na yi ba.
"Ke wace ce kike da suna?".

"Amatullah".

"To Amatullah lafiya kike zake ƙarfinki ki na kurma mana wannan ihun, gobara ce ta tashi ko kuma ƴan fashi ne suka yi mana da'iri ban sani ba?". Na girgiza mata kaina alamar a'a.
"To mene ne?". Ta yi zancen cikin tsare gida da turmuƙe fuska babu alamar wasa ko wargi a tattare da ita.
"Wani ne ya faɗo mini ɗakina yanzu ma haka ya na ciki, ban san wane ne ba?".

"Wani kuma?". Ta jefa mini tambayar cikin mamakin ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta juya ta shiga cikin ɗakin yayin da ragowar matan suka rufa mata baya, babu jima wa suka fito tare da mutumin da yake ta layi duk ya ɓata jikinsa da alama a matuƙar burge yake na fitar hankali.
Cikin maye ya ce"sorry sister mance ɗakin cikas ɗin tawa na yi na faɗa na ki". Ban ce da shi uffan ba har ya gama galantolinsa ya gama.

Zuby da tun farkon lamarin take tsaye a ƙofar ɗakinta ba ta gusa ba, ta dafe ƙirji tare da fiffito da idanu waje"na shige su ni Zubaida ɗiyar Sani mai kayan koli, wannan ai Habu ne saurayin Hafsy ƴar jama'are me ye ya kai shi cikin ɗakinki?".

Idanuna ya yi tsilli-tsilli kafin na furta"wallahil azim ban san shi ba, ko fuskanshi ma ban gani ba saboda babu haske a cikin ɗakin". Ta galla mini hararar da ya tursasa mini yi wa bakina limzami babu shiri.
Hajiya Babba ta ce"yanzu ina ita Hafsyn take wannan abun ya faru?".
Zuby ta kada baki ta ce"Hajiya ta tafi club da wani sabon kamun da ta yi". Cikin zafin rai Hajiya ta ce"to kama shi ki san yadda za ki yi da shi, na kashe wannan case ɗin kowacce shegiya ta koma ɗakinta". Tana kama zancen ta juya gare ni"ke kuma ina so ki nutsu ki san inda kike". A dunƙule ta jefa mini zancen ba tare da ta warware mini ƙulin ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta, na kasa jan ƙafana na bar wajen har sai da kowa ya watse ya bar ni a waje, masu shiga ɗakunansu da samarinsu suka shige masu shirin fita suka fita.

Sai da na ja dogon gashin na fesar kafin na nufi cikin ɗakina ina doso ɗakin na ji wani gungumemen wari ya doki hancina babu shiri na toshe hancina da tafukan hannayena. Ba n i da tocila balle na haska na ga abin da ya haddasa warin haka na ci gaba da tsayiwa a ƙofar ɗakin tun ina tsaye har na zauna, a nan ƙofar ɗakin na kwana.
Sanyin asuba da ya soma ratsa ni shi ya farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya sace ni. Na farka na shiga na ɗauko buta na yi alawa a ƙofar ɗakin na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, sai da na ɗan jira gari ya yi haske kana na koma cikin ɗakin.

Na tsaya cak tamkar gumki ganin yadda aka ɓata kan tabarman da amai ya yi kaca-kaca, ni na yi tamkar na ɗaura hannu a ka na dinga zunduma ihu ko zan ji sauƙin takaicin da ya cika mini zuciya. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara gangarowa daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin su na yi a bisa fatan fuskana. Ba ni da ajiyayyen ruwa ko kaɗan illa wanda na rage da na yi alwalar sallan asubahi.
Na fito na ga La'aniyatu ba su buɗe ƙofa ba, na rasa yadda zan yi. Ina waigawa na ga wani bokati na ɗauka na fita domin ɗeba ruwa, layin sharau don har zuwa wannan lokacin gari bai gama waye wa sosai ba. Ina tafiya ina kuka har na isa wajen ɗeban ruwan na ɗeba na ɗaura akaina na juyo zan tafi kenan na hango shi yana fitowa daga cikin masallaci.

Ban san dalili haka kawai na ji jikina ya ɗauki rawa ya kafe ni da ido kamar yadda ni ma na ɗaura idanuna akan sa, bai ce da ni komai ba ya zo ya wuce ni ma na ɗauki hanyar komawa gidan. Tun daga zaure na ji ana kwararo ruwan ashariya, har na shigo cikin gidan ba a fasa ba ina shigowa aka nuno ni.

"Kin ga shegiyar da ta ɗaukar min bokati". Zuby ta yi zancen tana nufo inda na ke tsaye gadan-gadan, kafin na na yi aune ta tankaɓar da ruwan da yake kaina ya malale a jikina ya yi mini lijif.
"Yanzu ke don kuturun wulaƙanci ki rasa bokatin wacce za ki ɗauka a cikin gida nan sai bokatina?. To wallahil azim zan ja miki layi da kayana a cikin gidan nan". Tana dire zancen ta wafce bokitin ta yi shigewarta cikin ɗakin. Na dubi jikina da ya yi lajab na tuna irin dogon tafiyar da na yi kafin na je na ɗebo ruwan kawai sai na ji hawaye suna sauƙa daga idona, na koma ƙafan ɗakina na zauna na zabga uban tagumi.

A haka La'aniyatu ta fito ta iske ni ta nema jin ba'asin abin da yake faruwa na irge mata komai cikin kuka, ita ta taimaka mini da ruwa da wanke ƙazantar da Habu ya yi mini akan tabarmata, na fito da ita na shanya akam igiya na koma ciki na sha lemo da biskit daga cikin abin da Hajiya Muhibbat da ta ba ni. Sai da na jira tabarman ta bushe kayan jikina ma ya bushe na shigo da ita ciki na shinfiɗa, duk da ban da agogon da zan duba lokaci na fahimci lokaci ya ja don hasken rana ya game ko'ina, sai da a rufe ɗakin na ba da ajiyan ɗan makulin a La'aniyatu kafin na tafi.

Kamar ƙafafuna za su tsinke haka na ke ta zabga sauri har ƙafafuna suna sarƙewa, ina isa ƙofan gidan na ƙwanƙwasa mai gadin ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi kafin na shiga cikin gida.
Na yi sallama Altine ta fito ta watsa mini wani matsiyacin kallo, na rusuna na gaishe ta maimakon ta amsa sai ta jefo mini tambaya.

"Ke sai yanzu kika yi niyyan zuwa aikin? Wannan in ke za a tsaya jira sai kin zo ki girka ai kuwa watarana ba za a ci abinci a gidan ba".

A nutse na ce"ki yi haƙuri wani uzuri ne ya sani na makara. Amma in sha Allah ba zan sake maimaita irin hakan ba".
Ta gallo mini harara"Dalla can rufe min baki sai wani fiƙi-fiƙi kike yi da idanu kamar ta Allah. Sai ki jira don karin kumallo suke yi". Daga haka ta juya ta bar ni tsaye a wajen, haka na ci gaba da tsayiwa har sai da na gaji na zauna a bisa dakalin wajen. A ƙalla na fi mintuna talatin a zaune a wajen kafin Altine ta fito ta cikin izgili ta ce na shigo. Da rawan jiki na tashi na bi bayanta muka shiga, suna zaune a falo tare da tagwayenta da ba su wuce shekaru biyu da haihuwa ba a hashashena kenan, na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa.

Kafin ta ce wani abu na soma da ban haƙuri"Hajiya ki yi haƙuri na makara wani uzuri ne ya riƙe ni, amma in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Fuskanta ɗauke da maɗaukakin murmushi ta ce"kar ki damu ba komai, ai jiki da jini dole daman wataran a sama irin haka, yanzu mu je sai na zagaya da ke ki ga gidan ko?". Na gyaɗa mata kaina ina jin wani daɗi yana mamaye mini raina na fahimtan da ta yi mini, har na yi gaba zan ji ta a baya muka jiyo sautin da ya tilasta mata tsayawa.

"Anty wace ce wannan?". Ta waigo tana kallonsa yayin da su Aryan suka nufa wajensa.
"Ita ce sabuwar ƴar aikin da na yi maka bayani akan ta jiya". Yana ɗaura agogo a damtsen hannunsa ya ce"Anty a sallame ta, a nema wata kawai". Babu shiri na ɗago kai ina kallonsa ƙirjina yana tsananta bugu, jikina ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 4️⃣8️⃣

Cike da maɗaukakin mamaki a bisa fuskan Anty Muhibbat ta ce"Saif me yasa wani abun ka ga ta yi?". Har yanzu idanunsa yana kan agogon da yake ɗaurawa a tsintsiyan hannunsa ya furta"Anty kawai yarinyar ba ta yi min ba ne, ki dubi yanayinta da kuma ƙarancin shekarunta ba na tunanin da za iya yin duk aiyukan da kika lissafa min jiya. Zai fi dace a sallame ta a nema wata kasai". Dukkanmu biyun muka yi sakeke muna kallonsa ni kam na gaza cewa komai saboda sanyin da jikina ya yi ƙalau tamkar jinjirar kazar da ruwa ya yi mata ɗan banzan duka.

"Saif ba wannan za ka duba ba, na lura tana cikin tsananin buƙatan wannan aikin ko don ta kula da rayuwarta a matsayinta na ƴa mace. Mata nawa ne masu irin shekarunta suke yawon ta zubar? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke sayar da jikinsu don su sama abin da za su ɗauki nauyin kansu? Mata nawa ne masu irin shekarunta da suke iskanci don su sama abin da za su saka a baki salati? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke faɗa harkan banza da na shaye-shaye?. Ga

6 / 39