Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
*SAJIDA*
_TARE_
*SAMIRA HAROUNA*
_('Yan Mutan Niger)_
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
1锔忊儯
Tunda ta fara magana yan uwanta da kuma mahaifiyarsu suka tsura mata ido, kan uba, innalilahi, dank'ari, rigiji gabji, wata sabuwa inji d'an daudu,
Sai da ta dasa aya tana mai share hawayen fuskarta mahaifiyarta dake kallonta tace" Auta? Inda zo nan kusa da ni, karaso kusana auta."
Mik'ewa ta yi cike da shagwab'a da lalaci ta k'arasa kusa da mahaifiyarta ta zauna inda ta nuna mata tana ciciko fuska tana cike da murnar an karb'i k'orafinta kuma ta tabbata za'a kirawoshi a ja masa kunne, tana zama ta ji an kama kunnenta an ja da d'an k'arfi sannan aka sakar mata rank'washi, uwar ta dubeta da kyau tace" Dan ubanki shekarunki nawa ne ni yanzu?"
Wace aka kira da auta ta rik'e wajen cike da mamaki tana duban uwar, me ta yi kuma?
Yan uwanta kuwa banda dariya ba abinda suke yi, domin yannayin da mahaifiyarsu ta nuna ya kashe su da dariya,
Fuskarta ta had'e tace" Kai da gaske nake, shirmen da ta gama zayano min ya saka ni rud'un shekarunta, na manta shekarunta nawa."
Babar yayarsu da takaici ya hanata dariya ne ta girgiza kai ta ce" Umma, ai shekarun *Hauwa* Ashirin ba biyu."
Uwar ta dafe kai tana dubanta , ta yi galala da fuskarta tace" Aman ai shekara ashirin da biyu bata yi yarinta ba ko? Ba za'a ce bata kai ahekarun auren ba aka yi mata? Ko dai sangartata na yi da yawa?"
Wace ke tsakiya ce ta ce" A ina muka ga sangarta Umma? Bamu ga sangarta ba,
Ke a ina kika samo tatsuniyar nan"
Wace ke bi mata wace ta bata shekara biyu ce ta tab'e baki tana duban mamansu tace" A ina kuwa zata samo banda a duniyar karatun *NOVEL*."
Yayarsu dake zaune mai sunna Nana Mariama ce tace" Aa, aa, Fadila, Novel d'in an gaya maki kowane ke d'auke da hauka da shirme? Sannan masu yin novel d'in an gaya maki suma irin rayuwar da suke yi kennan? Ko an gaya maki shi novel d'in ance ka dauki du wani abinda ke ciki ne? Ta dai san inda ta samo shirmenta, ko k'awayen zamani ko makaranta, aman kam bana ciki, Novel ai nima karantawa nake da shekaruna da yayana ma kuwa."
"Wai me nayi? Meye na yi? Ya haka kamar baku ji abinda na fada ba? Bakwa gannin cikin masifar da nake? Bakwa gannin irin tarin masifar da nake ciki?" Cewar Hawa'u
Wace daga babar yayarsu sai ita wato Humaira ce ta ce" ke da Allah banza ki daina kirar mana masifa a nan wurin bayan muna neman sauk'i, ke yanzu in ba batan basira ba...wai idan har kina da ita basirar ba, me ya had'a tunaninki haka? Ya zaki saka mu a gaba kinai mana kuka, ki kikiraye mu tun da duhun asuba kice kowace ta zo da sasafe kina son ganninmu kina cikin tashin hankali? Baki san mu a yanda muke ba ko a yaya zamu fito ba, mu zo du a birkice aman ki mike ki bud'i baki ki zayanno mana magana kamar haka, ke kin rasa gane kanki, yaya Bashir zai ringa irin wannan rayuwar da ke?
Du ki saka mu fita hayacinmu muna faman jin me yake maki da zafi haka sai kawai ki ce wai *BASHIR* baya kaunarki, bai san zafinki ba, shi ne ba ruwansa da tambayarki abinda zaki ci da sasafe a matsayinki na amarya duka duka aure wata guda, ba ruwansa da irin riritakin nan, ko da kika yi ciwon kai bai shiga kicin ya yi girkin abinda zaku ci ba, ina irin na mata da miji a d'auke ki a kaiki wanka a nad'o ki a towel ke bai tab'a maki ba, fisabililahi Hauwau dan ubanki baby ce ke? Ko rayuwar film aka kai ki gidan auren?"
Wace ke bi mata ta girgiza kai tana murmushi ta ce" kin manta aunty, harda washe garin aurensu bai bata ky d'in mota ya kira mata docter ba,
Idan ta yi kwaliya baya rikicewa ya yi ta santi yana yaba mata, ranar da ta yi masa girki kala hud'u sai ya shiga fad'an ya zata yi girki kala hud'u su biyu kawai , kar ta kuma.....ke auta ke 'yar sarkin uban waye ne ke? Kinma ci sa'a da bai d'auke ki da mari ba har ya d'auke maki jinki da ganninki."
Ummansu ce tace" Oh ni duniya da me ta yi kama! Yanzu auta, ina zaune gidan auren ubanki, na haifeku ku shida, a ina kika tab'a gannin haka? Ina zaune tare da kishiyoyina wace kika ga haka?"
Rau-rau Hauwa tayi da fuskarta tace" Aman umma, ku ai kun girma ko?"
Umman na ta ta dunk'ule hannayenta tace" amshi nan, nace d'ambulaninki Hauwa."
Yayarsu ce ta girgiza kai tace" *Ulena* zo nan, zo kusa da ni."
Hauwa ta mik'e tana dafe da rank'washin data sha tana duban yayar tata ta ce" Aman me zai saka na zo bayan umma ta gama rank'washina?"
Kanta ta girgiza tace" Zo mana..."
Takawa ta yi ta k'arasa ta zauna, aman du sai ta tatare fuskarta kar a kai mata mari, cikin nutsuwa tace" Ule, zauna ki ji wani abu kin ji, ina so ki rufawa kanki asiri, ki rufawa ummanki, ki rufa mana, ki koma gidanki, ki yi zaman aure, haba Hauwa haba auta, shi zaman aure fa ba wasa bane, ya zaki kawo k'orafi kan tatsuniya? Ke yanzu tsakaninki da Allah jibgegiya da ke idan yace zai d'auke ki sai ki yarda? Haba Ule, ke fa a aljana kike, idan kika ji wasu abubuwan da suke ganni a rayuwar auren ki ce me kennan?"
Cewar d'aya daga ciki "Aunty a fad'a mata ko zata yi hankali."
Girgiza kai auntyn tasu ta yi tace" Aa, ba za'a fad'a mata a tada mata hankali ba."
Mahaifiyarsu dake kallonsu cikin yannayin mamakin 'yar tata har yanzu ne tace" Kai, ku bata kad'an daga cikin rayuwar aurenku ko zata zubar da wannan lamarin."
Husaina dake zaune tun d'azu ana magana aman ita bata ce komai bane tace" Haba auta, me ya yi zafi? Du abinda kika zano ya hana maki ci, sha , sutura, ko matan banza yake kawo maki ne?"
Kafin ta bada amsa dayar ta ce" Aunty, ni da na rasa ci, shan, suturar nake zaune a d'akin nawa, hakan bai hana ya tafka min tsiya ba nace me?"
Ta tsakiyar ce tace" Hum, ni kuwa da idan an shigo mani gida karfe biyun dare sannan cikin maye , a d'udd'uran ashar fa nace me?"
Cike da mamaki take dubansu kafin tace" Kai, ina walahi aa, ba zan yarda da abubuwan da kuke fad'i ba, aunty dan Allah ki k'aryatasu."
Murmushi auntyn ta yi tace" Auta, ba k'arya bane."
Hauwa tace" Aunty, aman ai ke Abbansu Nadia baya wulak'anta ki ko? Mutun salihi, ko mu baya had'a ido da mu."
Murmushi ta yi tace" Alhamdulilah, ban rasa ci, sha , sutura ba, halayansa na gode Allah yana girmama mahaifiyata, mahaifina, yan uwana, ke halayarsa duka ba laifi idan kika cire duka, shi fa idan ransa ya b'aci sai ya daki wanda ke kusa ciki kuwa koda ni ce."
"Kan uba...." Hawau tace tana zaro ido tare da d'ora hannayenta saman kanta ta wani yi fik'i fik'i da ido.
*Kuna son labarin?*
*Daga*
*Mutanenku* ku garzayo da gudu ba da rarrafe ba, ku antayo mu tashi tare masoya.鉂わ笍鉂わ笍鉂わ笍鉂わ笍
03/11/2021 脿 13:13 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_DAGA ALK'ALAMIN_
*SAJIDA*
_TARE_
*SAMIRA HAROUNA*
_('Yan Mutan Niger)_
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
2锔忊儯
Cikin dafe k'irji tace "Aunty da gaske kike? Kina nufin Abbansu Nadia na dukanki wai?"
Gyad'a mata kai Nana Maryama tayi tana murmushi tace "Kamar yanda na fad'a miki yana da saurin hawa da zafin nama wajen kai hannu, ranshi na b'acewa indai har ina kusa dashi to babu abinda zai hana shi duka na, ke wani lokacin ma a waje za'a b'ata masa rai ya shigo cikin gidan, k'ank'anin abu zai gani da bai kai na magana ba sai kiga ya rufe ni da duka ko yara, har yau, har gobe bana tunanin zai daina wannan halin nashi, shin Hauwa in tambaye ki? Tunda kukayi aure da Bashir a d'an lokacin nan ya tab'a kuskuren d'aga hannu ya dake ki?"
Baki sake ido waje ta girgiza a hankali alamar a'a, wani murmushin ta sake yi tace "Ni kuma kwana biyu da aurenmu saida hannunshi ya tab'a lafiyar jikina, ba dan komai ba sai dan jimawa da nayi ban gama girki ba, daya fara min masifa kuma saina fito na baro mishi d'akin saboda ina da bak'ia falo, wannan ne ya tunzura shi ya jawo ni da k'arfi ya falleni da mar."
Wata ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi tayi rau-rau da ido alamar tana son yin kuka, fahimtar yanayin ba zai musu dad'i ba yasa mahaifiyarta su mik'ewa cikin dubara ta bar falon, kallonta tayi da kyau tace "Ule na, a wannan ranar, a wannan lokacin daya mareni naji abun kamar a mafarki ne, ban tab'a tunanin hakan zai faru tsakaninmu ba, bare har na kawo zai faru da wurwuri haka, nayi kuka a lokacin tare da fara dana sani, amma daga baya sai abun ya zamar min jiki, har yanzu da wannan nake rayuwa a gidan Abbansu Nadia."
'Yar k'wallar da take sharewa ne ta bawa Munira damar cewa " Hauwa, shin kinsan meyasa har na zo nan? Saboda ina tunanin matsalarki tafi wacce muke ciki ni da *Sagir*, hankali na ya kasa kwanciya tunda kika kira ni jiya, k'anwata kinsan wace irin rayuwa ni nake yi a gida na?"
Nan ma dai girgiza kai tayi, d'orawa Munira tayi da "Ba Sagir yayi aure ba? Shin da kike zuwa gida na har ki sakata ki wala ki ci abinda ranki ke so kin d'auka duk saboda duniya ta mana dad'i ne? Ko kad'an Hauwa, zan iya ce miki da fari muna cikin farin ciki, amma daga ranar daya k'aro aure komai ya lalace, Sagir ya juya min baya fiye da tunaninki, babu abunda nake yi ya birgeshi, hantara da aibatawa ne kawai ke shiga tsakani na da shi."
Nunfasawa tayi ta ci gaba da cewa "Ule wulak'ancin da nake fuskanta a gidan ba k'arami bane, shi ya min, matarshi ta min saboda tana ganin ita ce tafi soyuwa a zuciyarshi, sai dai duk da wannan matsalar ba zan ce miki ya tab'a bari na da yunwa ko k'ishin ruwa ba."
Humaira ce tayi saurin cewa "Tabbas k'anwata baki rasa ci da sha a gidan Sagir ba, amma ni na rasa, na rasa komai."
Da sauri Hauwa ta juya tana kallonta, Har ita dake mudil-mudil da ita akwai abinda ke damunta? Duk irin yanda take ganin tafi k'arfin komai da ma ba haka bane? Soyayyar da sukayi fa? Muryar Humaira ce ta dawo da ita dake fad'in "Ulen mu, nasan kinsan labarin soyayyar da mukayi da Aminu, to duk wannan yanzu ya zama tarihi, tarihin da bana jin ko a gidan kafa tarihi za'a bugashi a kafe."
Gyara zama tayi tana dafa kafad'arta tace "Kamar yanda kika san Aminu ba mazauni bane, baya cikakken wata d'aya a garin nan ya sake komawa fataucin *neman na kai*, to a duk lokacin da yake gari karki d'auka muna rayuwar jin dad'i ne, wallahi wata safiyar da k'yar yake iya bani d'ala dari ni da yara muyi abincin kari, na rana da kuma na yamma, karki d'auka ko muna da kayan abinci ne a jibge, masara da hatsi kad'ai yake iya yo mana watansu ya aje, wannan kayan sune muke sarrafawa muna rayuwa dasu, shin kinsan wani abu?"
Hauwa kasa motsi tayi dan haka Humaira tace "A hakan to idan yana nan munfi jin sauk'i, ko ba komai zan iya d'aukar sati d'aya ina rok'onshi ya bamu dala talatin na sabulu muyi wankin kayanmu, amma idan baya nan? Nasan kinsan da idan ya tafi yana yin har wata hud'u ma zuwa uku, to da jaka biyar muke rayuwar harya dawo, a ciki nake auno mana masara da cefanai, a ciki nake siyan sabulun wanka da wanki, a ciki nake siyan magani idan yara basu da lafiya, a ciki nake basu kud'in laraba da suke kauwa makaranta, sannan ranar da mukayi rashin sa'a aka fara mana wuyar ruwa a unguwarmu har ruwan siye mukeyi, to yanzu Hauwa a 'yar rayuwar da kuka fara kina ganin bai kamata ki kira rayuwar ki da aljannar duniya ba?"
Shiru d'akin yayi sai ajiyar zuciya da sauke nunfarfashi kawai, d'orawa tayi da "Allah ya sakawa iyayena da alkairi, ba dan su ba da watak'ila yanzu yunwa ta kashe mu ni da yara, tunda Abbanmu ya fahimci halin da nake ciki saiya fara taimaka min, da wannan ne ya bani jarin dana fara sana'a a cikin gida, da taimakon kayan abincin da suke mana ne muke walwala ni da yara, kuma kinsan meye abun haushin ma? Har yau bai tab'a tambaya ta a ina na samu kud'in da nake juyawa ba, sannan idan na dafa mai kyau na kawo mishi bai tab'a kallo na yace a ina na samu ba, shin yanzu irin wannan mijin kina ganin ko karuwanci kayi ka samu zai dame shi ne?"
Husseina ce tace "Ule kowane d'an adam da kikaga yana rayuwa to tabbas yana da tashi matsala, sai dai ta wani tafi ta wani, kinga duk matsalolin nan nasu, to zan iya ce miki ina gaba da su, dan su ko babu komai suna da sahihancin hankalin mazajensu, nasan zaki girgiza sosai idan har na fad'a miki *Salis* mashayin giya ne."
Waro ido tayi ta dafe k'irji tace "Me? Salis d'in? Giya fa kika ce? Na shiga uku, aunty Husseina dan Allah ki fad'a min gaskiya, yanzu duk yanda Salis yake zai iya shan giya dama? Oh ni 'yasu."
Murmushi tayi wanda yasa hawaye dararowa a fuskarta tace "Har na saba dama baya shigowa gida sai dare ya raba, Hauwa ban isa in rufe gida ba indai bai shigo ba, indai na rufe ya zo ya bubbuga na bud'e daga uwata har ubana babu wanda ba zai sha zagi ba, idan kuma na bar gidan bud'e nayi kwanciyata to har wanda ya haifi kakan ubana ma saiya aika musu da nasu rabon, idan kuma na zauna ina jiranshi to ni da yara babu wanda ba zai tsinewa ba."
A k'afe ta kalleta tace "To sai kiyi yaya kenan? Wannan ai kamar tsokar da ta k'i tamnuwa ne kuma ta k'i had'uwa."
Murmushi tayi tace "Tabbas hakane Ule, idan na rufe gidan ya bubbuga na bud'e zaice sai kace gidan ubana ko uwata da zan kama k'ofa na rufe bayan bai shigo ba, idan kuma na barshi bud'e nayi kwanciya ta sai yace tunda ba kakan ubana bane ya bashi kud'in daya zuba kaya a cikin gidan shiyasa zan wulak'anta masa dukiya, idan kuma na zauna jiranshi yace munafuka ce ni na tsaya jiran naga da wacce zai shigo shiyasa har yara ma na koya musu munafurci, Hauwa da wannan nake rayuwa a gidanshi, zaiyi amai na gyara wuri, yayi fitsari ke har kashi ma yi yake duk na tsabtace wurin, amma hakan fa baya hana ina aikin yana tsine min albarka, wani lokacin ma a cikin k'azantar nan zai turmushe ni ya sadu da ni ko kuma ya min tsinannan duka, amma a haka nake hak'uri iyayena ma suke bani hak'uri dan gidan nashi yafi min mutumci akan na zauna tare da su."
Hauwa ji tayi har jikinta ya d'auki zafi, wani zazzab'i ne ke neman rufeta ma a wurin, dama yan uwanta na fuskantar wannan rayuwar amma bata tab'a sani ba? Lallai abun azimun ne! Murmushi *Rahila* ce tace "Ni tawa matsalar tafi ta wasu kuma ta wasu tafi tawa, ni kinsan me nake fuskanta?"
Da ido kawai Ule ta bita hakan yasa ta mata murmushi tace "Bahagon mutum ne, zama dashi sai ka dage sosai ka kuma yi hak'uri, komai k'ank'antar abu sai yayi masifa da bala'i akai, namiji ne da baya da kawar da kai akan komai, idan aka ce miki ya shigo gida ni da yara duk jininmu a kan akaifa yake, dan ko motsi mai kyau kikayi baiyi masa ba saiya hau bambami yana surfa tashin hankali, maimakon ya zama mai sauk'in sakin abu saiya zama idan ranshi ya b'ace yayi fad'a, to kuma mun shiga uku kenan a gidan, a wannan k'aramin abun zai iya kwashe sati biyu har uku yana hushi dani baya kulani, ko gaisuwa wannan wallahi baya amsawa idan na gaishe shi, kinsan meya fi tayar min da hankali idan yayi hushi?"
Cikin matuk'ar mutuwar jiki Ule ta girgiza kai ita kuma tace "Idan har yana wannan gabar dani to har yara su kan horu da yunwa, daga ranar daya fara hushi dani to sisin kwabonshi bata shiga tsakani na da shi, idan har kayan abincinmu suka k'are a daidai wannan gab'ar to ko na fad'a mishi baya kula ni, idan na aika yara su fad'a mishi ma haka baya kulasu, Hauwa a *novel* ba kuna karantawa ba cewa idan jarumin ya ga jarumar a cikin wani shirin sai yaji ya manta da b'acin ranshi?"
Murya a raunane tace "Hakane aunty."
Murmushi tayi sosai tace "To *Rabilu* na daban yarinya, dan kayan bacci kowane iri zan saka masu d'aukar hankali basa fizgarshi izuwa gareni, haka ma idan zanyi tsaye tsirara a gabanshi wallahi sai dai ya kalleni ya bar min d'akin, amma fa