AURE YAKIN MATA HAUSA NOVELS COMPLETE BY SAJEERAH.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 33

45K to 48K   out of 96.2K words

shi lashe baki yace "Ba haka bane, nima ai mijin aure ko? Magana ce zamuyi dake ta sirri, dan Allah ki daure ki shigo sai kiji."

Sake rab'awa tayi zata wuce ya sake cewa "Wallahi idan baki tsaya kika saurareni ba har gidanki zan biki."

Cak ta tsaya ta kalleshi tace "Malam me na maka? Me kake nema a tare dani? Dan Allah ka barni nayi tafiyata naji da abinda ke damuna."

Wani murmushi yayi yana k'are mata kallo yace "lambarki kawai nake so, idan kika bani saina barki ki tafi."

Sunkuyar da kanta tayi tana hararenshi ta k'asa, a hankali taji yace "Karb'i nan."

D'agowa tayi tana tozali da wasu sababbin kud'i har turiri suke, da sauri ta girgiza tace "A'a nagode."

Murmushi yayi yace "Idan baki karb'a ba gidanki zan aika miki su, ni fa alkairi nake nufinki dashi ba sharri ba."

Kallonshi tayi gabanta na ci gaba da fad'uwa ga tsoro fal a ranta, saida ta shiga karanta addu'a a ranta ta zura hannnu yana kakkarwa ta karb'a, wani murmushin ya sake mata ya mik'o wayarshi yace "Lambar ko?"

A sanyaye ta karb'i wayar ta saka mishi lambarta, tana mik'a masa ya karb'a ya kalleta yace "Ina da yanda zan ganoki idan ma ba daidai kika saka ba."

D'aga madubinshi yayi yana fad'in "A sauka lafiya matar manya."

Kasa motsawa tayi har ya juya ya bar wurin, da sauri ta shiga takawa tana kallon kud'in tana so ta gano ko nawa ne amma ta kasa, taxi ta shiga da hanzari ta nufi gida da wannan yanayin tsoron a tare da ita.


*Gidan Leila*

Rana tsaka tana madafa tana duba girkinta ta ji sallamarta yayarta, da sauri ta fito da murna ta tarbeta suka shiga d'aki tana fad'in "Aunty *Umma* daga ina haka da rana tsaka haka?"

Saida ta zauna tana cire mayafin tace "Bari kedai, daga wajen barkar haihuwa nake."

Fridge ta nufa tana fad'in "Bari na kawo miki ruwa."

Da kallo ta bita har ta je ta kawo mata ruwan ta bata tana kallonta, saida tasha ta aje kofin ta kalli Leila data zauna kujera mai fusskantarta tana fad'in "Nan kusa akayi haihuwa aunty?"

Da alama son jin labari ta gyara zama tace "Ke ba wannan ba, me ya sameki naga duk kin lalace? Dama ke ba mai jiki ba amma naga kin k'ara sab'ewa."

Murmushi tayi tace "Ba komai aunty Umma, ban rame b芒 fa."

Girgiza kai tayi tace "Sa'anki ce ni Leila da zaki k'aryata abinda nake gani a zahiri?"

Girgiza kai tayi tace "Da gaske aunty ba komai, dan kin jima baki ganni bane."

Sake girgiza kai tayi tace "Leila, ciki ne dake?"

Da sauri ta kalleta tace "A'a."

Sake kafeta tayi da ido tace "To me yake damunki? Ba kya cin abinci ne?"

Cikin k'ufula tace "Aunty na ce miki ba komai, ba komai wallahi ki yarda dani."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan tunda ba zaki fad'a min ba, zan je gida yanzu na samu Hajia na fad'a mata akwai matsala, watak'ila ita ta zo ta sakaki gaba kin fad'a mata."

Da sauri tace "A'a dan Allah aunty Umma, karki fad'a mata."

Hararenta tayi tace "To fad'a min me ke damunki."

Ajiyar zuciya ta sauke kanta k'asa da tunaanin ta yanda zata fara, saida ta ja dogon numfashi ta sauke kafin tace "Aunty Umma ina cikin matsala, bansan ya zaki d'auki abun ba, amma dai wannan damuwar ce ta hanani sakewa a gidana, Aunty wallahi har bna so naji Kader ya shigo cikin gidan nan, idan na tuna sunanshi gabana fad'uwa yake, idan naji motsin k'ofa ana bud'ewa cikina yamutsawa yake, idan na ganshi a gabana wallahi tsorata nake, kuma ba komai ya jawo haka ba sai na cin shi gareni."

D'aga kanta tayi ta kalleta tana hawaye tace "Aunty baya gajiya da saduwa, safe rana dare aikinshi kenan, aunty yace fuskata ya kalla sha'awata yake, idan ya ganni gabansa rasa tunaninshi yake yi, wallahi na kasa jura na kuma kasa sabawa da wannan rayuwar har yanzu, ko sau goma zai nemeni baya jin ya gaji saidai ni nayi kamar zan mutu, aunty babban tashin hankalin irin yanda baya jin gajiya, wani lokacin ko damar hutawa baya bani, ba zan iya ba aunty na gaji wallahi."

Wata nannauyar ajiyar zuciya Umma ta sauke tace "Leila, ke kuwa zaki iya da mijinki, zaki iya da wannan buk'atar tasa insha'Allah."

A tsorace ta kalleta tace "Aunty Umma ta y'a ya?"

Wani murmushi tayi ta mik'e ta d'auki gyalenta tace "Ke ina zuwa banga ta zama ba, bani awa d'aya naje gida na dawo yanzu."

Da mamaki ta bita da kallo ita dai har ta fita ba tace mata komai ba, mik'ewa tayi ta koma madafa dan k'arasa aikinta da kuma jiran dawowar auntyn na ta tajie zata zo mata da shi.



*Alhamdulillah*
03/11/2021 脿 13:45 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

_DAGA ALK'ALAMIN_

*SAJIDA*

_TARE_

*SAMIRA HAROUNA*

_('Yan Mutan Niger)_

_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *AURE YAK'IN MATA*, hak'ik'a nasan wasu sun san labarin, dan kuwa mun farashi yanayi yasa baku gama ba. To mun dawo da yardar Allah, yanzu zamu ci gaba duba da masoyan da littafin suka samu, saidai wani canji da aka samu littafin zai zama na kud'i ne._

_Duk wata mai aure da ma wacce ba ta da aure ta yi k'ok'arin samun wannan littafi dan zai k'ayatar, zai warware wasu matsaloli na gidajen aurenmu, wannan labari ba wai k'ik'ira bace, zamuyi duba ne da rayuwar da mukeyi tare da mutane mu saka a ciki, hakan yasa zamu kasashi izuwa gida daban daban, kar ku bari a baku labari, indai kana da aure ka karanta zaka samu maganin matsalarka a ciki, idan baki da aure ki karanta zaki d'auki mataki na rayuwarki ta gaba._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari uku (300) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai d'ubbin darusa a ciki._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2377403479* zenith bank, Khadija Umar Abubakar. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *94-98-56-52*_

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

2锔忊儯4锔忊儯


Tana gama fad'a ta fincike da k'arfin balaki ta fice ta gefensa ta wuce waje.

Gaba d'ayansa tamkar mutum mutumi ya zama sakamakon kalmar rabuwa da ta fito daga bakinta, bai tab'a tunanin akwai ranar da zata iya yin hakan ba, kai daidai da wannan amsar da ta bashi a haka bai tab'a tunanin cewar zata iya bashi ita a haka ba, hakan ya saka shi d'aukan yan mintuna tsaye kamar wanda ya suma domin bai san abinda yake wakana a kusa da shi ba.

Irin manyan motocin nan ne zasu wuce motar ta bada wani irin ihu biiiiiiiiiiiiiiiiiiiip na odo d'in da mai janta ya danna hakan ya saka shi zabura kamar an gaura masa mari ya kai dubansa daidai tsayinta dan har ya manta ta fice a gidan ya gyara tsayuwarsa zai yi magana ya ga wayam, ai a lokacin yace "Kai." yana mai zaro idanuwansa.

Da sauri ya juya ya fita wajen gidan, sai dai ba ita ba alamunta ba burbud'inta kamar bata fito bama a gidan.

Hannunsa d'aya ya d'ora saman kansa yana ta waige waige kafin ya juya da sauri ya koma cikin gidan dan tattara yaransu biyu k'ananu wanda basa zuwa islamiyya ya fito da su yana rufe gidan gaba d'aya hankalinsa a tashe, basu tab'a haka ba, hakan bai tab'a faruwa da su ba.

Yana tuk'i amma hankalinsa baya tare dashi, yaran nata hayaniyarsu suna mishi hira amma sam bai san sunayi ba, saida suka je k'ofar gidansu Maryama yaja ya tsaya ya kalli soron gidan, ajiyar zuciya ya sauke tare da jin wata matsanciyar kunyar had'a ido da iyayenta, a tsayin shekarun da suka d'auka bata tab'a ko da yaji ba, yau gashi ta zo gida kuma yana da tabbacin shi ne marar gaskiya, yasan yan da kishi sosai kuma lokuta da dama zuciyarshi kan tunzurashi yayi abinda ba daidai ba.

Kallon yaran yayi ya bud'e musu motar yace "Ku shiga ciki mamanku tana nan, zan dawo anjima saina d'aukeku tare mu koma gida."

Da farin ciki suka fita da gudu suka shiga gidan yana kallonsu har suka b'ace mishi, tayar da motar yayi ya wuce da tunanin yana idar da sallah magriba gidan tsohuwarshi zai je ya lallab'ata ya had'ata da Allah annabi ta je ta bata hak'uri ta dawo tun kafin ma malam ya san da me ya faru, dan gaskiya yasan mak'ura ne ya kai Maryama.

Yaran na shiga gidan a d'aki suka samu maman ta su tare da mama, ganin mamansu na kuka tana magana da kakarsu yasa su yin shiru suka zauna suna kallonsu, cikin kuka da b'acin rai take fad'in "Allah mama ba zan koma gidanshi ba na gaji, yanzu ba kishina bane yake zargina yake, Mama ina aure da zargi zaiyi k'arko? Abun takaici d'an taxi zai tsaya yana zargina dashi saboda na zama wata karyar titi."

Mama data buga wani irin zama hankali a tashe ga alkunya ta 'yar fari ga fargaban kar abokan zama su fahimci me ya faru ta girgiza kai tace "Balaraba (bata kiran sunanta sai ranar data haifeta) hak'uri zakiyi ki tashi ki koma gidanki, yanzu da kike cewa ba zaki koma ba ya za'a miki kenan? Sakinki kike so yayi? Yaushe autarku ta zo nan take neman tallafawarku a kan nata auren? Shi ne yanzu ke da girmanki da yayanki har budurwa kike da a gabanki zaki kwaso ki ce yaji kikayi."

D'auke kai tayi daga gareta tana fad'in "Um um! Ban lamunta ba kinji tashi ki koma, kar ma ki bari malam ya sameki a gidan nan wallahi kinsan ba zaki ji dad'i ba."

Fashewa ta sake yi da kuka tace "Mama zargi fa, d'an taxi yake zargina da shi daga ya d'aukoni, mama na gaji da zaman auren nan."

Girgiza kai mama tayi tace "Shikenan tunda haka kika ce, ki zauna idan malam d'in ya dawo sai ki fad'a masa kinzo kenan ba zaki koma ba, kinga saiya karb'o miki takardarki da kanshi ai."

Mik'ewa tayi ta kalli yaran ta kama hannayensu tace "Muje kuyi alwala ko."

Binta sukayi yar macen tana fad'in "Mamie, abbanmu ya kawomu kuma yace zai zo ya d'aukemu tare da Mama."

Jinjina musu kai kawai ta yi cikin alhini suka fita a d'akin. A farfajiya ta samu abokan zaman na ta guda biyu sun had'a kai suna k'usk'us, suna ganinta aka kwashe da dariya, amaryar dama ita ce tafi fitsara, dan haka ta mik'e da butarta a hannu tana fad'in "Allah na tuba, ai da felek'e da kuri ake mana saboda ganin duk yaran sun auri maza masu rufin asiri, gashi nan dai ana girban abinda aka shuka, yau waccen ta zo gobe waccen zata zo."

Wata dariyar suka kuma bushewa da ita sai ta tsakiyar mahaifiyarsu Badariya da tace "Kika sani a cikin mazan akwai mai likid'a duka da mai shan gida? Ai tar muke kallon komai shiru ne mukayi saboda gudun fitina."

Girgiza kai kawai tayi ta d'auki butar ruwanta ita ma ta shiga yin alwala tare da yaran, suna kammalawa suka koma d'aki tana jinsu suna ci gaba da maganar ita dai kamar ma bata jinsu.


*Gidan Hassana*


Tana sallah magriba ya shigo ya wuce d'akin baccinsu, har ta idar da sallah bai fito ba hakan ya tabbatar mata wanka ya shiga, gyara zamanta tayi a kan sallayar ta kalli d'an yaronsu Abdul daya fito daga d'akin yanzu tace "Yaya wanka ya shiga ne?"

"E, wanka yake." Ya amsa mata dashi, mik'ewa tayi ta cire hijab d'in ta fito ta shiga yar k'aramar madafarsu, tana shiga miyarta data yi tunda yamma ta d'ora a wuta dan tayi zafi, ta d'ora kenan tana cikin goge kwanukan da zata saka abinci ta ji muryarshi a bayanta dan ko shigowarshi bata ji ba yana fad'in "Ke ina kud'ina dana aje yanzu n shiga wanka?"

Da mamaki da kuma al'ajabin sabon halin da yake neman k'ak'aba mata ta juyo ta kalleshi tace "Kud'i kuma yayana? Wane irin kud'i?"

A hassale ya nunata da yatsa yace "Ke bana son iskanci Hassana, wane irin kud'i kika sani ke a rayuwarki?"

Tsaf ta gama fahimtar yanayinshi, wato yau kuma ta yamma aka tatako aka taho sauke mata tsautsayin ko? Tab'e baki tayi ta juya ga tukunyarta tana fad'in "Ban gansu b芒 gaskiya, tunda ka shigo ai ko d'akin ban lek'a ba ma."

Matsowa yayi cikin madafar yana fad'in "To ina ruwana, ke zaki fito min da kud'i ko saina tattakaki a wurin nan? Jaka d'ari hud'u da hamsi na aje yanzu akan gadonki zan shiga wanka, saina fito na nema yanzu babu saboda bak'in halinki."

A hassale ta juyo ita ma tana fad'in "Ban gane ba wai yayana, kana nufin ni na d'auki kud'in? Tunda muke da kai ka tab'a neman kud'inka ka rasa ne?"

"To ni ina ruwana, na sani ko dan kinga ina shigowa a buge kina anfani da wannan damar kina d'aukarmin kud'ina, tunda ke kike cire min kaya wani lokacin."

Wata malalaciyar dariya tayi tana fad'in "Ahayye! Ka ji wani sabon salo kuma yau ga wannan bawan Allahn, to ni yanzu na rasa wa zan ma sata sai wanda yasha yayi tatul ya shigo a buge? Salis nawa ka tara? Nawa ka aje da zan d'auka? Dama kana tara kud'i ne kai? Ai na d'auka kullum a giya suke k'arewa, tunda na ciyar da gidan nan a sanda baka da kai har tufafi na d'inka ma kaina na d'inka ma d'anka kuma na d'inka maka, shi ne yanzu zaga zargeni da d'aukar maka kud'i."

D'amararshi ya cire yana nufa kanta cikin muryar maye yana fad'in "Dan ubanki nine zaki gora ma dan kin min d'inki, ni miye ban miki ba a gidan nan? Da aka kawo ki haka kika zo gidan nan? Ina ce anan kika zama wannan rubd'ed'iyar banza da wofin, ba ni na ciyar dake ba da har kikayi k'arfin da kike iya d'irkata..."

Kaucewa tayi tana ihu da neman taimako tana fad'in "Kar ka tab'ani Salis, kaga dai k'yaleka ne kawai nake yi ko? Kuma na fad'a maka ka daina saka iyayena a cikin haukanka wallahi."

Ganin suna ta zagayen madafar bai kamata ba yasa shi d'aukar duk abinda ya tari baganshi yana jefa mata yana fad'in "Dan ubanki anje an zaga, zaki fito min da kud'ina ko sai na fed'eki a gidan nan, ba zanyi asara ba dan ban santa ba kinji na fad'a miki."

Wata k'ara tayi sanda ya jefa mata wuk'a har saida ta daki goshinta ta fad'i k'asa, bai kula ba sai ma wata k'aramar muciyar katako daya d'auka ya jefa mata yana fad'in " Ke na gaji, wallahi ki fiddo min kud'ina sannan ki tarkata banzayen komatsanki ki bar min gidana, na sakeki Hassana bani bake har abada, shegiya yar iska mai kama da giwa."

Hannu ta d'ora a kai ta fashe da kuka tace "Na shiga uku ni Salis ka saka a cikin maye? Saki biyu fa kenan? A cikin maye ka sakeni saboda ban sani ba."

Tsura mata ido yayi alamar abinda ta fad'a ya gindayar dashi, aje muciyar yayi ya matso yana fad'in "Hassanata, wallahi ni ban sakeki ba, sub'utar baki ce kinji kiyi hak'uri, shikenan a bar maganar kud'in ma na yafe."

Girgiza kai tayi tana fad'in "Ba zai yiwu ba wallahi, ni b芒 jaka bace kaji in fad'a maka, gidan mu zanje dan na gaji da wannan halin naka."

Da sauri ya durk'ushe ya had'e hannaye yana fad'in "Hassanata kiyi hak'uri kar kije, idan kika je ba zasu barki ki dawo ba, dan Allah ki zauna na tuba ba zan kuma ba wallahi."

Tsaki tayi tace "Rantsuwarka ta banza, gobe ba zaka sak茅 ne Salis tunda ka ce giya ce abokiyar rayuwarka, haka na farko da kayi ka hanani tafiya gidanmu, wallahi yanzu sai naje ko ba komai su san meke faruwa saboda halin rayuwa, gidanka kuma na bar maka Salis."

Rab'ashi tayi ta wuce da k'arfi ya mik'e yana bin bayanta yana mayar da d'amararshi yana kiran sunanta da bata hak'uri, canza riga da siket d'inta tayi na zaman gida zuwa doguwar rigar atamfa tare da had'a kayanta a jaka, yana gefenta yana bata hak'uri shi dai dan da fari daya nemi k'watar jakar tureshi tayi har ya nemi fad'uwa. Tana fitowa Abdul ta samu a falo da wayar Salis d'in yana wasa, fizge wayar tayi ta aje kan kujera ta kama hannunshi ta kalli Salis tace "Gas yana aiki a madafa, ruwanka ne ka kashe ko kuma ka k'ona kanka."

Kamar zaiyi kuka ya shiga marin fuskarshi yana shan gabanta da fad'in "Hassana karki tafi, dubi kinga na mari kaina ko? Kinga fa na yi k'warai, dan Allah ki zauna."

Sama da k'asa ta harareshi taja tsaki suka wuce da yaron suka barshi, taxi ta d'auka ita ma ta nufi gidansu saidai tana shiga motar ta fashe da kuka saboda ciwon da take ji a zuciyarta.


*Gidan Hawa'u*

Wani sanyayyen mumushi ya sakar mata yana ballon yanda ta dage tana feshe shi da turarenshi zai fita, saida ta gama suka fito yana gaba tana take mishi baya, a falon suka samu k'annan Bashir d'in da suka shigo yanzu, murmushi ta sakar musu da mamakI tana fad'in "...



*Kuyi hak'uri da wannan*
03/11/2021 脿 13:45 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

_DAGA ALK'ALAMIN_


*SAJIDA*

16 / 33