AURE YAKIN MATA HAUSA NOVELS COMPLETE BY SAJEERAH.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 33

9K to 12K   out of 96.2K words

k'arancin abun yi, amma abun ba haka bane, bana da lokacin waya indai mijina ya shigo gidan, hakan yasa ma ban d'auki kiranki ba tunda naga bak'uwar lamba ce."

Wani mugun mamaki ne ya kashe Hawa'u, me matar ke nufi? Da sauri tace "Aunty Meerah kina nufin ba kya d'aukar waya idan mijinki na gida? To amma taya kike rubutu?"

Murmushi Meerah tayi har saida taji sautinsa kafin tace "Yer uwa ai shi kanshi rubutun ban fara ba saida izinin mijin nawa, sannan mijina mutum ne mai son ganin ya samu kulawa daga gareni duk sanda ya shigo gida, hakan yasa ma ina jin tafiyarshi akan matakala nake aje waya ko da ina tsaka da chatting ne dan bana so yaji ba dad'i ko kad'an."

Tab'idjam! Cewar Hawa'u, jin tayi shiru yasa Meerah cewa "Ko zan iya sanin dame zan iya taimaka miki?" Da k'yar ta iya cewa " Aunty Meerah aure nayi, amma gaba d'aya mijina wani irin mutum ne, na kasa gane gabansa da bayansa, yanzu haka saida ya ci mutumci na kafin ya bar gidan..."

Da sauri Meerah tace "Subhanallahi! Hawa'u ko?"

Cikin yanayin sangarta ta amsa da "Eh."

Cike da jan kunne tace mata "Yanzu yer uwa taya zaki fara sanar da ni sirrin gidanki daga jin muryar juna yau? Ina ganin hakan bai dace ba, sirrinki, sirrin mijinki yakamat su zama naki, ko mahaifiyarki idan har ba shawararta zaki nema ba to ki koyi b'oye sirrinki wajenta, sakin baki yana sa ka zama sakarai wajen mutane, sakin sirrinki ko na mijinki zaisa ki rasa kima da daraja, dan Allah ki kiyaye yer uwa."

Jin haka sai yasa Hawa'u jin ta ma fasa fad'an abinda tayi niyya, ita ma Meerah da taji shiru saita fahimci kamar bata ji dad'i bane, dan haka cikin sallama dan su rabu lafiya ta kuma gyara mata wasu kurakuren sai tace "Yanzu fad'a min wace shawara kike nema? Insha Allah zanyi iya bakin k'ok'ari na."

Duk da dai tasha jinin jikinta amma tsaf ta kwashe komai ta fad'a mata wanda hakan yasa Meerah yin dariya tace "Hawa'u! Wace matsala kike ciki? Dan ni duka a cikin labarin nan naki banji matsala ko wani k'alubale ba, to wai ma a misali waya fad'a miki dan na saka *Abbas* ya bawa *Sameera* kyautar gida saboda ya kusanceta ya zamana ke ma dole sai an miki kyautar nan? Hawa'u, karki bawa kanki wahala ta hanyar yarda da duk wannan sauki-burutsun da kike gani muna rubutawa, abune da muke rubutawa mu kanmu da fatan samun irin wannan rayuwar, nasan kinsan kowace mace na da burin son jin dad'i da kuma samun nagartacciyar kulawa daga gurin mijinta, hakan yasa a duk lokacin da muka d'ora hannunmu zamuyi rubutu muke saka abinda zai k'ayatar ya kuma birge, domin kuwa idan muna rubutu lokuta da dama mu kan ji wani abu kamar damu ne yake faruwa, wanda hakan na tasiri a jikinmu har muji shauk'in abun a tare damu, idan tausayi ne zakiga wani lokacin har kuka mukeyi kafin mu aiko muku kuma kuyi kukan, kinga kenan ba duka abinda muke sakawa bane ya zama gaskiya, dan haka Hawa'u ki rumgumi mijinki hannu biyu tun kafin lokaci ya k'ure miki."

Da tsananin mamaki Hawa'u tace "Aunty Meerah yanzu kina nufin kema baki samu kyautar daren farko ba? Sannan mijinki bai kaiki ban d'aki da kanshi ba?"

Murmushi Meerah tayi tace "Bana ce miki a'a ban samu ba, saidai kyautar bata kai inda kike tsammani ba, sannan ni mijina ya zo min hankali kwance tare da dubaru wanda yasa ban jikkata ba bare har sai ya kai ga d'auka ta, sab'anin yanda muke sakawa an zo mata da k'arfi har saida aka d'inketa ko aka gasata."

Jiki a sanyaye Hawa'u tace "Kenan idan na fahimta Aunty Meerah duk irin soyayyar nan da kuke rubutawa k'arya ce? Babu ita a zahiri? Ku kanku baku sameta ba? Kawai k'irk'ira ce."

Wata dariyar ta sake yi tace "Waya fad'a miki haka? Alhamdulillah Hawa'u nagode Allah, *ni da mijina* babu abinda zance sai godiyar Allah, soyayya mai tsabta da tsarki mijina ke nuna min, kuma nima ina iya k'ok'ari na, ke Hawa'u na tak'aita miki domin bana son sakin sirrin gida na, kema ina fad'a miki duk wannan ne saboda na bada gudummuwa a gyara rayuwar aurenki, a tak'aice Hawa'u akwai wasu kalamai da kalar soyayya da nake sakawa a novel d'ina wanda ina arota ne daga gurin mijina, misali idan kika duba littafin *Auren Had'i*, akwai abubuwa dayawa dana saka a ciki na soyayya da kulawa wanda ni ce abun ya faru dani, ke har ma da ciwon da Ummi taji a cikin labarin da ni ce abun ya faru, haka idan kika duba littafin *Kallon Kitse* na saka wasu abubuwa wanda suma dani suka faru, amma fa na soyayyar da kulawa da kalaman, dan haka ba zance miki duka soyayyar k'arya muke sakawa ba."

Cike da gamsuwa tace "Yanzu aunty Meerah wace shawara zaki bani?"

Cewa tayi "...

馃憦馃憦馃憦
03/11/2021 脿 13:18 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*AURE YAK'IN MATA*
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�


_DAGA ALK'ALAMIN_

*SAJIDA*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*

_('Yan Mutan Niger)_

馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

_DAGA ALK'ALAMIN_


*SAJIDA*

_TARE_

*SAMIRA HAROUNA*

_('Yan Mutan Niger)_


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *AURE YAK'IN MATA*, hak'ik'a nasan wasu sun san labarin, dan kuwa mun farashi yanayi yasa baku gama ba. To mun dawo da yardar Allah, yanzu zamu ci gaba duba da masoyan da littafin suka samu, saidai wani canji da aka samu littafin zai zama na kud'i ne._

_Duk wata mai aure da ma wacce ba ta da aure ta yi k'ok'arin samun wannan littafi dan zai k'ayatar, zai warware wasu matsaloli na gidajen aurenmu, wannan labari ba wai k'ik'ira bace, zamuyi duba ne da rayuwar da mukeyi tare da mutane mu saka a ciki, hakan yasa zamu kasashi izuwa gida daban daban, kar ku bari a baku labari, indai kana da aure ka karanta zaka samu maganin matsalarka a ciki, idan baki da aure ki karanta zaki d'auki mataki na rayuwarki ta gaba._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari uku (300) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai d'ubbin darusa a ciki._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2377403479* zenith bank, Khadija Umar Abubakar. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *94-98-56-52*_

_Bismillahir rahamanir rahim_

7锔忊儯


"Zan fad'a miki wasu abubuwa wanda nake ganin inhar kika rik'esu to insha Allahu zaki samu abinda kike so, ban ce miki mijinki zai zama kamar bawanki ba ko ki juyashi yanda kike so ba, amma dai zai girmamaki ya mutuntaki sannan kiyi fice a zuciyarsa ta yanda ba zai iya had'aki da wasu matan ba."

Cikin farin ciki tace "Yawwa aunty Meerah ina jinki dan Allah fad'a min."

"Hawa'u babban abu na farko shine hak'uri, ki zama mai hak'uri da mijinki, dan wani lokacin zai iya yi miki abu a matsayinsa na d'an adam ajizi, ke zaki iya kallon abun kamar yayi dagangan ne ko dan ya muzantaki, to idan kikayi hak'uri sai kiga an zauna lafiya. Wani lokaci kuma ke ce mai gaskiya a yayin da kuka samu sab'ani, amma saiya mayar da laifin kanki ya hukuntaki ko da ta hanyar yi miki fad'a ne, amma in kikayi hak'uri kika shanye da kanshi sai kiga ya baki hak'uri ya gano kurenshi ne."

"Abu na gaba kuma shine ki zama mai ladabi da biyayya ga mijinki, idan har yace miki bana son wannan abun to ki kiyaye, idan yace miki kiyi to kawai kiyi indai bai sab'a ma addini, idan ya hanaki kuma to ki hanu ba tare da kin nuna masa baki ji dad'i ba, idan kikayi haka Hawa'u mijinki zaiji har a ransa cewa kin girmama shi."

"Abu na gaba kuma shine tsabta, Hawa'u ki zama mai tsabta hakan ba k'aramin kankaro miki mutumci zaiyi ba a wurin mijinki, tsabtar nan kuma ta kasu kashi kashi kamar yanda muka sani, akwai *tsabtar jiki*, *tsabtar muhalli* da kuma *tsabtar tufafi*, nasan kinsan rabe raben duka wannan dana fad'a miki, idan aka ce tsabtar jiki to wanka, wanke baki, cire gashin gaba dana hamata, duk wani matse matsinki ki tabbatar kina bashi kulawa ta musamman, wanke kai da gyara shi yayi kyau da k'amshi, cire faratu akai akai, yin lalle na gargajiya ko na zamani, sannan uwa uba gabanshi, wanda wannan zama na musamman ya kamata muyi domin kuwa shine zai iya b'antaro miki darajar da bakiyi tsammani ba, yanzu zan d'auki kad'an daga tsabtar jiki na fad'a miki d'an abinda na sani."

"Hawa'u duk rintsi duk wuya karki yarda ko da wasa ko da a mafarki ne mijinki ya ji wani odeur a jikinki da ba k'amshi wanda zai kwantar masa da hankali ba, ki tabbatar duk abinda zaiji ko ya gani daga gareki to mai kyau da gani ne kuma mai kyau da k'amshin shak'a, hakan fa na nufin ko da a cikin larura ne, Hawa'u na yarda akwai rashin lafiya da laulayi na ciki, amma karki yarda ki zauna da k'azanta a jikinki da uzurin cewa wai baki da lafiya ko kuma ciki ne da ke, ko da kwance kike yanda ba kya iya yin doguwar kwalliya, to kiyi wanka ki wanke duk wani wuri dake ajiyar d'auda da kuma wari. Sannan ki zama mai wayan saka lalle a k'afafunki da kuma hannayenki, karki yarda faratunki suyi fari fat kamar na namiji."

Hawau dake sauraronta ta sauke wani gauron ajiyar zuciya tana mai bin akaifunta da kallo, a kalla ta kai wata biyar bata yanke farce ba, so take su yi girma su zama zako zako yanda zata je saloon a daidaita su su bada kalar na yan gayu, kunshi kuwa zata iya cewa rabonta da kunshi tun na aurenta, wato wanda aka tirsasata akai mata na amarya, bata son kunshi bale kitso, kitso takan tsaya ne kasan shower ta wanke kanta idan ta fito ta busar da shi ta shafa masa mai, gashi ita ba wani mai gashin nan na yayan novel ba, a gaskiya gashin kanta idan bata saka masa shampoo ba zai iya yanke hannun garji

Meerah ta ce " ki yi hakuri Hawa'u iya gaskiyata nake son fada maki,
Ke ko da boka da malan masu yi a wahalce suke , domin dai hanya ce marar kyau aka dauka, wace dole za.a ratse, dole za.a zauna cikin fargaba...haka kuma koda abin na ci yanda ya dace sai ki ga suna gannin ba haka ba domin shirkar da suka yi ta girmama ta kawo masu tsari mai muni da suke gannin shi ne daidai

Sai da meerah ta nisa ta ce" to wai inama jin dadi takama jin fiert茅 a namijin da ka mayar solofiyo? Solofiyo mana namijin da shi zai yi magana ki mike jikinki na bari ki aiwatar ya dawo ke ke yin magana yana bari ya aiwatar kuma a kirayi haka da soyaya?

HAWA.U ki godewa ni.imar Allah, kar ta kai ki da godewa azabarsa

Hawa.u dake sauraronta jikinta ya nuna ta mugun yin sanyi, a hankali ta ce"



Daga alkalumman Samirah da Sajida
03/11/2021 脿 13:19 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*AURE YAK'IN MATA*
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�


_DAGA ALK'ALAMIN_

*SAJIDA*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*

_('Yan Mutan Niger)_


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *AURE YAK'IN MATA*, hak'ik'a nasan wasu sun san labarin, dan kuwa mun farashi yanayi yasa baku gama ba. To mun dawo da yardar Allah, yanzu zamu ci gaba duba da masoyan da littafin suka samu, saidai wani canji da aka samu littafin zai zama na kud'i ne._

_Duk wata mai aure da ma wacce ba ta da aure ta yi k'ok'arin samun wannan littafi dan zai k'ayatar, zai warware wasu matsaloli na gidajen aurenmu, wannan labari ba wai k'ik'ira bace, zamuyi duba ne da rayuwar da mukeyi tare da mutane mu saka a ciki, hakan yasa zamu kasashi izuwa gida daban daban, kar ku bari a baku labari, indai kana da aure ka karanta zaka samu maganin matsalarka a ciki, idan baki da aure ki karanta zaki d'auki mataki na rayuwarki ta gaba._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari uku (300) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai d'ubbin darusa a ciki._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2377403479* zenith bank, Khadija Umar Abubakar. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *94-98-56-52*_

馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

8锔忊儯


"Nagode aunty Meerah, insha Allahu zan rik'e abinda kika fad'a min."

Cikin farin ciki ta amsa mata da "Ba komai Hawa'u, ke dai kawai ki zage damtse sosai wajen farantawa mijinki, Allah ya baku zaman lafiya."

"Ameen nagode." Ta sake fad'a da murmushi a fuskarta kamar suna gaban juna, cikin girmama juna sukayi sallama kowa ya shiga wata sabgar, har saida ta gama shirin baccin cikin k'ananan kaya kafin Bashir ya dawo gidan, sosai yayi mamakin canzawarta saboda har hak'uri ta bashi, sun raya darensu cikin so da k'auna da farin ciki.

Ko da suka wayi gari ma ta shirya abin kari ya ci ta raka shi ya fita, ko da ta dawo cike da kasalar rashin sabon k'ok'arin da tayi ta zauna kan kujera ta shiga WhatsApp, abun mamaki shine a cikin wanda ta nemi lambobinsu sai gashi yanzu ma an sake turo mata lambar aunty Sajida, dad'i taji sai kawai take a wurin tayi watsi da shawarar aunty Meerah da tunanin aunty Sajida zata bata wasu shawarwarin masu zafi wanda zata kama Bashir a hannu tunda taji ance ita d'in buzuwa ce, nan danan ta shiga lambar ta d'aga mata hannu tare da yin sallama, kasancewar safiya ce anyi sa'a uwar Lalla bata komai sai kula da yarmu a lokacin馃槈, saida ta gama aikawa oganta zafafan addu'a duk da kuwa ta mishi kafin ya fita kafin ta fara duba sauran lambobi, a cikin haka ta ci karo da lambar Hawa'u, kamar yanda karamci yake aikinta ta shiga lambar ta amsa mata cikin mutumtawa, gaisawa sukayi sosai kafin Hawa'u ta fad'a mata damuwarta, a cikin kalamanta ta fahimci harda sangarta na damun yarinyar, dan haka ma tayi dariya son ranta kafin tace "Tunda kinji ance ni buzuwa ce?"

Saida tayi jim kafin tace "Aunty Sajida, dan Allah dan annabi ki taimaka min, ki d'auke ni tamkar k'anwarki ta ciki d'aya, ki saka ni a hanyar da kike bi nima ko zan dace da mulki a cikin gidana yanda na ga dama."

Wani shirun Sajida tayi na d'an lokaci tana karanta message d'in Hawa'u, kanta ta girgiza tace "Ina so ki dubi Allah ki fad'a min dalilin da yasa kika yi tunanin ni Sajida zan iya samar maki damar mulkar gidanki yanda kika ga dama, gidan naki ma Hawa'u mijin ki?"

Zama Hawa'u ta gyara ta dnana voice note ta karanto mata magana kamar haka "Aunty ke buzuwa ce, aunty birni da k'auye waye bai san buzaye na juya mazajensu tamkar waina a tanda ba? Aunty waye bai san idan ka yarda akai maka kishiya buzuwa ka kad'e har buzunka ba? Aunty ku fa kune da sirri, ku kuka iya rik'e mazajenku a tafin hannayen ku, bakwa aikin komai a gidajenku an zuba maku ma'aikata masu muku shara wanke wanke, raino wanki, masu kawo muku abinci harta da d'auke kwano aunty, ki yi hakuri ba zaginki nayi ba, dan na ji kin ce na dubi Allah ne na fad'a maki abinda nake tunani."

Murmushi kawai Sajida ke saki daga inda take zaune, d'aga kai tayi ta kuma bin gidanta da kallo wanda ta gama k'yalk'yale shi ta saka turaran wuta haka kuma ta kimtsa 'ya'yanta suka zauna sunna hutawa kafin a dan jima ta d'ora girki dan ma mai gidan nata a ranar baya saukowa daga aiki da wuri da tuni ta gama komai ta shiga ibada.

Turo mata message ta yi cewa" shekararki nawa a duniya? Sannan kwananki nawa da aure?"

Hawa'u cikin zumud'i ta rubuto "Shekaru na ashirin ba d'aya a duniya, sannan ina cikin wata na biyu da aure."

Kai sajida ta girgiza cikin jin takaicinta, wata biyu aman har yanzu bata gane yaren ba? Ko bata zuwa islamiya? Ko bata cud'anya da mutane? Ko kuma makauniya ce kuma kurma?.

Ba tayi k'asa a gwiwa ba ta rubuto mata amsa kamar haka " Hawau, shin an tab'a shan romon miya ba'a sha wahalar dafata ba? Hawau Aure? Aure? ban sanki ba, ban san inda kike ba da k'anwata ce ke ta ciki d'aya sai na nemi dorina na je gidanki na zane maki jiki! Kar kiyi mamaki abin haushi ma hasalani, Ke yaya zaki ce zaki yi anfani da rubutun cikin novel wanda aka k'awata dan labari yayi dad'i kice haka kike son gani a naki gidan? Da ake tsara film ake haskawa haka suke a rayuwar gaskiya? Ke Hawau kiji tsoron Allah ki sauko daga inda kika hau domin ba hanya mai kyau bace, da kike maganar buzaye sirri, shin mu kayan halitarmu da

4 / 33