Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
a haka ranar daya huce to karki d'auka wai zai karb'i hak'urin dana bashi ne a baya, sai nayi bacci a tsakiyar dare zanji mutum kawai ya durfafe ni yana sukuwa a kaina, wai shi yafi k'arfin ya tashe ni ma mu had'a ido da shi bare har na fahimci rauninshi, to fa kinji tawa kalar rayuwar kenan, kuma idan zamu yi wata yana wannan gabar dani babu ni babu fita ko da kuwa larura ce, dan ko yara ne babu lafiya sai dai shi ya kaisu asibiti da kanshi, ni kuma duk abinda zai faru a cikin dangin a wannan lokacin kam sai dai ya wuce ni."
Wani kuka Ule ta fashe dashi ta kallesu d'aya bayan d'aya tace "...
*'Yan mutan Niger ne*馃槏
03/11/2021 脿 13:14 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_DAGA ALK'ALAMIN_
*SAJIDA*
_TARE_
*SAMIRA HAROUNA*
_('Yan Mutan Niger)_
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *AURE YAK'IN MATA*, hak'ik'a nasan wasu sun san labarin, dan kuwa mun farashi yanayi yasa baku gama ba. To mun dawo da yardar Allah, yanzu zamu ci gaba duba da masoyan da littafin suka samu, saidai wani canji da aka samu littafin zai zama na kud'i ne._
_Duk wata mai aure da ma wacce ba ta da aure ta yi k'ok'arin samun wannan littafi dan zai k'ayatar, zai warware wasu matsaloli na gidajen aurenmu, wannan labari ba wai k'ik'ira bace, zamuyi duba ne da rayuwar da mukeyi tare da mutane mu saka a ciki, hakan yasa zamu kasashi izuwa gida daban daban, kar ku bari a baku labari, indai kana da aure ka karanta zaka samu maganin matsalarka a ciki, idan baki da aure ki karanta zaki d'auki mataki na rayuwarki ta gaba._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari uku (300) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai d'ubbin darusa a ciki._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2377403479* zenith bank, Khadija Umar Abubakar. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *94-98-56-52*_
3锔忊儯
Kamar wacce zata fad'i wani lamari mai kyau sai ta dubesu tace" Haka kuke zaune da k'artin maza kuna haihuwa kuna wahala da d'auke can gyara can kuna masu abinci suna ci aman kuma suna wulak'anta ku? Walahi ba zan yi auren zagi ba! Ba zan iya rayuwar wulak'anci haka ba!"
Mik'ewa Humaira tayi ta mayar da ita zaune, irin dungura mutun d'in nan,
Sai da ta yi taku biyu sannan ta dawo ta kai mata rank'washi a kitson da akai mata k'ananu masu shegen kyau da zafi, rasa me zata ce da ita tayi ta k'ara d'aga hannu zata kuma kai mata mazga, sai Hawa'u ta yi gaggawar matsawa jikin k'afar babar yayarsu ta rakub'e ta kwantar da kanta jikin gwuiwarta.
Humaira ta dubi yanayin yayar tasu, fuskarta ta nuna tsantsar damuwar irin tunanin Auta, haka kuma bata son abinda zai tab'a lafiyar auta, dan kuwa wani irin so take yiwa yarinyar sosai, ita ta goyeta ta sha kashinta da fitsarinta, bata son ganinta cikin wani yannayi, kai da za'a bincika zuciyarta ne a ji ra'ayinta, da ta isa ta tank'wasa lamarin namiji, da ta tank'wasa mijin auta ya kasance yanda take son ya zama, fuskarta ta nunawa Humaira bata so, kar ta daketa, dan haka ta ja ta tsaya tana dubansu, domin Humaira dai akwai saurin d'aukan zafi, sannan gidansu an hore su ne da babba ya isa da k'arami ba zancen raini ,
Humaira ta koma ta zauna kafin ta turo d'an kwalinta gaba ta kaiwa Hawau wani duba na kirki kakausa tace"Ki farka banza! Dan ubanki duk abinki kar ki yiwa Allah izgili, jarabawarsa na iya zuwar maki ta inda ba kya zato bakya tunani, kar ki yarda bakinki ya zama linzamiki, tikiten rashin zaman lafiyarki na duniya da kuma k'iyama, Banza!" Ta fad'a tana kawar da kai,
Husseina ta dubeta tace" Auta, dan Allah ki nutsu ki farka kin ji? Mata? Mu kuwa muke mata, mune abin mangari, abin hange, abin kwatance,
Kin san me yasa na fad'a maki haka?
Duk irin tashin hankalin da muke ciki muke fuskanta, Allah mad'aukakin sarki baiyi mutuwar aurenmu ba, haka kuma bamu tonawa kanmu asiri ba, halin da muke ciki bai saka mun saki hanya ba, halin da muke ciki bai sakamu fitsarewa ba, Auta cikinmu dai ai harda wada miji ke iya wata bai waiwayeta ba ko? A yanzu an fad'a maki, amma Allah ya kareta da zina, da wace shima sai ya yi watannin ba abinci ba kyakyawar kulawa itama tana zamanta, ga mai langwui kin ga itama tana zamanta, yau aka ce ana aure ko sunna a gari ko a gidan nan kalarmu daban, takunmu daban, ke rayuwar gidan miji mun d'auketa a yanda ta zo, mun yi hak'uri bisa tallafawa da kuma wa'azin iyayenmu da 'yan uwanmu, muna saka abinda muke so , muna cin wanda ranmu ya yi mana, dan kuwa koda basu mana ba , muna sana'a, sannan Allah ya rufa mana asiri iyayenmu na tsaye kanmu, me ma kika fara? Me kika gani?
Yaushe aka yi?
Kinga ni bara na yi gaba, indai kan irin haka ne dan Allah ki zama mai hak'uri kin ji Auta?" Tana gama fad'a ta shige wajen mamansu dan yi mata salama.
Babar yayarsu ta kamo hannunta tana dubanta tace" Ule, ba wahala bane, haba auta, neman ladane, neman aljana ne, neman gamawa da duniya lafia ne, kin manta a islamiya aka ce aljanarka na k'ark'ashin k'afar mijinka? Kin tab'a gannin bauta ba'a wahala ba? An tab'a cin nasara ba'a hau matakai ba?
Kin san Allah? Duk yanda mijina ke dukana ina mugun son abu na a haka."
Shatata tayi da baki tana dubanta, murmushi ta myi ta rufe mata bakin tace"Ai yanzu kin girma auta zan iya fad'a maki wasu abubuwan, kinga saiya dake ni, na je d'aki na lab'e gudun kar 'ya'yana su ga hawayena su tashi da tsanarsa, da an jima zai biyoni d'akin nan ya rarrasheni kamar yayi kuka da alk'awaririkan yana so na, ba dan baya sona bane yake saka shi dukana, na taya shi da adudu'a dan Allah karna k'aurace masa."
"Kin san Allah? Bama fitowa sai da fuska washe koda kuwa ban wani sake ba, dan kar nayi gagawar sakewar ya kuma dukan nawa da wuri, ke akwai wani mari da yayi min saida d'an kunne na ya fice fit jini ya kunce min sai gashi yana min pansement da kanshi."
Hawau kam zuwa yanzu ta gama gane matsalar yayunta, kai ba komai ke damunsu ba sai rashin sannin ciwon kai, ya haka? Wai da gaske Abbansu mai son 'ya'yan nan, mai kare du wani martabarsu ya san ana wulak'anta masa 'ya'ya haka kuma bai kashe masu auren ya dawo da kayansa gabansa ba, bayan Allah ya hore masa abin rik'e su ya wadatar da rayuwarsu?
Humaira dake kad'a k'afa tana kallon yanda auntynsu ke wani ririta auta tana wani k'ara kwatanta mata tayi murmushi a zuciyarta ta ayyana dama barinta kuka yi, dan walahi Auta ba mai d'aukan magana bace sai taga haza!
Tab'ota da aunty ta yi ya sakata yin firgigit tana dubanta, hakan yayi daidai da kukan wayarta.
Sai da ta d'an ja aji irin na kafin a d'aura aurensu ta d'aga ta kara ta yi shiru, irin dai yanda take masa kafin aurensu, shima shirun yayi yana mamakin salon iskancin Hawau, jira take sai yayi magana kennan ko? (Ai a da birgeka yake hakan inji hawa馃樄)
"Ke kina ina na zo bakya nan?"
Bakinta ta turo irin shagwab'ar nan ta ce" bb na zo gida ne wajen mama."
"Aman da izinin wa kika fita?" Ya fada cikin dakakiyar murya.
Amsa shi tayi ta hanyar fad'in"Zaka fara ko? Meye kuma dan na zo gidanmu?"
Kansa ya shiga gyad'awa yana jin kalar amsar da ta bashi, ruwan daya kunna ya tari hannunsa ya kuskure bakinsa ya kashe pampon yace" Wallahi nan da minti talatin idan baki zo gidan nan ba saina kirta maki rashin mutuncin da har yanzu ba'a zana shi ba a doron duniya!"
Ido ta zaro jin abinda ya ce, kafin ta bashi amsa har ya kashe wayar,
Mik'ewa ta yi ta bi 'yan uwanta da kallo, muryarta ta d'aga tace" Mama, bara na je na dawo, aunty ina zuwa."
Ficewa tayi ta shiga motar mijin da ta shigo ta d'auki hanyar gidanta tana ayyana bara na je mu zauna da bby ya fad'a min takamaiman me yake nufi da ni, nice zai ce zai yiwa rashin mutunci dan na fita zuwa gidan iyayena ba yawon ta zubar ba ? Ni zai ringa k'ok'arin juyawa tamkar wata tanda tamkar ba wace take da gatanta ba? Yau zamu yita ta k'are da wannan mutumen idan har ya daina so na ne ya sake ni ehe!
*To fa, ku taro ta ....ta bale, Ule sannunki*
Comment d'in ku zai saka mu sakin sabon page
03/11/2021 脿 13:15 - Mom Khalid: 馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_*AURE YAK'IN MATA*_
馃拲馃拲馃拲馃拲馃さ馃徎馃懓馃徎馃拲馃拲馃拲馃拲
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
_DAGA ALK'ALAMIN_
*SAJIDA*
_TARE_
*SAMIRA HAROUNA*
_('Yan Mutan Niger)_
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *AURE YAK'IN MATA*, hak'ik'a nasan wasu sun san labarin, dan kuwa mun farashi yanayi yasa baku gama ba. To mun dawo da yardar Allah, yanzu zamu ci gaba duba da masoyan da littafin suka samu, saidai wani canji da aka samu littafin zai zama na kud'i ne._
_Duk wata mai aure da ma wacce ba ta da aure ta yi k'ok'arin samun wannan littafi dan zai k'ayatar, zai warware wasu matsaloli na gidajen aurenmu, wannan labari ba wai k'ik'ira bace, zamuyi duba ne da rayuwar da mukeyi tare da mutane mu saka a ciki, hakan yasa zamu kasashi izuwa gida daban daban, kar ku bari a baku labari, indai kana da aure ka karanta zaka samu maganin matsalarka a ciki, idan baki da aure ki karanta zaki d'auki mataki na rayuwarki ta gaba._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari uku (300) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai d'ubbin darusa a ciki._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2377403479* zenith bank, Khadija Umar Abubakar. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *94-98-56-52*_
4锔忊儯
Tana zuwa ta fito daga motar da jakarta a hannu da waya ta tunkari cikin falon, yana zaune yana hangota ta gilashin k'ofar yana tambayar kansa wai me ta d'auke shi da har zata fita bada izininsa ba? Harta bud'e k'ofar ta shigo suna kallon juna, zaune tayi kusa da shi tana aje jakarta gefe tana fad'in "Bb gani na zo, amma meya dawo da kai a wannan lokacin?"
Mik'ewa yayi ya nuna ta da yatsa yace "Ke dakata! Dama na tsaya jiranki ne dan na fad'a miki ban yarda ki sake fita ba tare da izini na ba ko da kuwa k'ofar gidan nan ne, shin Hawa'u me ma kika d'auke ni? Sakarai ko lusarin namiji? Haka kawai daga fita ta daga gida ke ma saiki saka k'afa ki fita kamar wata tunkiya, to wallahi karki sake kinji na fad'a miki, idan kuma baki ji to duk abinda na miki ke kika siya da kud'in ki."
D'aukar makullin motarshi yayi ya juya zai fita, Hawa'u da take ganin idan bata taka masa birki ba ita ma fa zata zama d'aya daga cikin yan uwanta, dan haka ta mik'e tace "Ko da kuwa gidan iyayena ne?"
Juyowa yayi yana d'an cije leb'e da tunanin abinda zai fad'a mata, rik'e k'ugu yayi ya nuna ta da makullin motar yace "Wallahi har gidan zan sameki na tata miki rashin mutumci, sai dai a k'arshe a ga rashin kunyata, idan kuma kin fasa zuwa Hawa'u ba kya k'aunar Allah."
Juyawa ya sakeyi zai fita bata san lokacin data furta "Lallai ma mutumin nan."
Juyowa ya sakeyi yace "Idan kina ganin da wasa nake ki jaraba ki gani idan ban wurgaki ta katangar nan ba."
K'wafa yayi ya juya yana fad'in "Duk da yaushe mukayi auren? Yaushe na sakar miki gaban nawa da har zaki ce zaki raina ni haka? Ke da har yanzu baki gama gani na da kyau ba."
Hawa'u kam girgiza kai tayi cikin k'arajin murya tace "Ina! Wallahi ba zai yiwu ba! Wannan ne auren dama? Kai ba gaskiya bane, marubuta aiba haka suke rubutawa ba."
Zaune ta koma tayi tana tafa hannayenta ta kafe wuri d'aya da ido, ya zatayi yanzu? Ya zatayi ta shawo kan matsalar nan? Meyasa ita rayuwar aurenta zata zo da haka? Zunbur ta sake mik'ewa ta rarumi wayarta tana fad'in "Wallahi lambar marubutan zan nema su warware min kai, wannan ma ai maganar banza ce, suna rubuta rayuwa a novel mutum yana karantawa yana gani a idonshi kamar shine a bad'ini, sai kuma na zo na ga ni tawa rayuwar daban, sannan naje gida dan yiwa tubkar hanci amma sun tsare ni da wani banzan labaran rayuwarsu masara dad'in ji, haba."
Shiru kuma tayi tana kallon wayar ta ta, to lambar wa zata nema ma? Wata zuciyar tace mata "Wanda kika fi karanta labaransu mana."
Da sauri ta k'yasta hannunta ya bayar da sautin k'at cike da jin dad'i tace "Hazik'an marubuta na zan nemi lambarsu, marubutan da ko ba komai *'yan k'asata ne*."
Nan ta shiga WhatsApp d'in ta tayi connect茅 ta shiga groupe d'in da babu fashi ake turo da litattafansu ta tura sak'o kamar haka "*Salam yan gidan nan, dan Allah ina neman lambar *Aunty Meerah* marubuciyar *Sanin masoyi* (sai Allah), *Jihadi*, *Itace k'addararmu* da sauransu, da kuma lambar *Aunty Sajida* marubuciyar *Duk k'aryar kada*, *'Yar mahaukaciya*, da *Bak'a ce*, please mai su ya taimaka min dan Allah karku share ni."
Sak'on farko data samu daga admin d'in grp d'in ce take fad'a mata ita kanta idan ta samu lambarsu saita saka su grp d'in, idan kuma Allah yasa ta dace ta samu to ta mata magana ita ma saita bata, har wunin nan ya kusa k'arewa Hawa'u na neman lambobin marubutan nan a duk grp d'in da take, amma kowa sai yace dama yana ganin novel d'in su ne saiya dinga turowa, da k'yar ta samu wasu a grp biyu suka ce zasu tambaya mata a grp d'in da suma suke samun novel d'in nasu, wannan zaman jiran samun lambar yasa har yamma ta take mata lak'was ba tare data d'ora musu girkin dare ba, kiran sallah magrib ne ya fargar da ita ta tashi afujajan tana fad'in "Wannan dake son zamar min jarababbe idan ya dawo bai tarar da abinci ba aina shiga tara ma ba uku ba, ni kuma yanzu banda lokacin ka, ina samun lambobin nan zan samo shawarwarin da zasu gigita tunanin ka dole ka zama *namijin novel* kamar yanda zaratan mazan nan ke komawa a hannun matansu, irinsu *Wardugu*, *Abbas*, *Mubbashir*, *Umar faruk* da su *General Irfan*."
*************
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyarta wanda ke tsayar da bugawar zuciya nan take, farin cikinta ne ya kasa b'oyuwa har hawayen dad'i suka zubo mata, cikin rawar murya ta kalle shi da kyau tana zubar da hawaye tace "Hubby, kana nufin duk wannan kyautar tawa ce saboda kawai na kawo maka abinda ni a ganina ya zama dole gareni dama na kawo maka shi?"
Shima cikin wani tsadaddan murmushi yace " *Leila* ke kinsan haka, amma sauran yan matan babu ruwansu da wannan tunanin, kin cancanci na baki kyauta fiye da wannan ma, dan a wannan zamanin da muke ciki samun mace mai shekarunki kuma ta kawo budurcinta gidan mijinta abu ne mai matuk'ar wuya."
Wasu 'yan k'walla ta share tare da fad'awa jikinshi ya rumgume ta sosai, sun jima a haka kafin ya d'an lek'a fuskarta yace "Ya jikin naki to yanzu? Har yanzu da zafi ne?"
D'an dukanshi tayi a k'irji ta k'ara lafewa shi kuma dariya yayi yace "My Leila kar ki tona zuciyata kiji farin cikin da nake ciki, matar da nake so kuma take so na, matar da muka jima muna soyayya, matar dake da shekara ashirin da biyar, matar da ke da wayewa da ilimi na kowane fanni, matar da ke rayuwa a cikin wannan gurb'atattacen zamanin, matar dake cikin k'awaye masu ido bud'e, matar dake k'awance da waya, wannan matar ce Allah ya mallaka min kuma a daren farkonmu sai na sameta a yanda nake so, ta zo min da abinda yafi komai daraja, ni, ni na fara sanin abata, ya Allah kasa ni zanci gaba da sanin kayata har abada."
D'agowa tayi d'aga k'irjin shi tace "Ka daina zuga ni haka mana, sai kasa naji kamar wani abun kirki ne nayi, bayan kuma ba komai bane nayi illa abinda ya dace."
Murmushi yayi zaiyi magana sukaji sallamar da dukansu sun gane mai muryar, mik'ewa yayi yace "Yanzu hankali na zai kwanta idan na fita saboda na samu wacce zata kula min da ke."
Kallonshi tayi tace "Wai K'awata ce zata kula maka da ni?"
Hannu yasa aljihu yace "Eh