Chapter 14 Reading MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt Arewa Novels

MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt

Author :  Zee MD Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   14 / 23

39K to 42K   out of 66.3K words

Anwaar* Allah yabiya maka buk'atun ka na Alkairi , Allah yaja da ran Hajiya yabarku da ita har k'arshen rayuwarka , shima russunawa yayi Numfashin su na dukan juna yace " Nagode da addu'a , burina yanzu guda d'ayane a duniya shine "samunki a matsayin mata ina mutuk'ar k'aunarki Nabeela dan Allah ki karb'i soyayyata , tun randa na d'ora idona a kanki har yau bank'ara samun bacci ba , kullum zuciyata da Soyayyarki take kwana take tashi plss accept me my Beela ta , d'agowa Nabeela tayi sannan ta mik'e dukanta tayi hanyar waje , saida taje wajen fita sannan tace " I Luv You so Much am Accept You my Ya Anwaar ta fice da gudu ,
Wani tsallen murna yayi tare da godiya da Allah yabita shima ya fice......




Acan Asibiti kuwa jikin Junaid yayi tsanani sai kiran sunan Nabeela yakeyi , Daddynsa da Mumynsa tuni suka rud'e likita yace " ku kwantar da Hankalinku yanzu abinda zakuyi shine kuje kukawo masa yarinyar daya yawan kira , wata k'ila ganinta zai saita komai na zuciyar sa , Daddynsa yadubi Mumyn yace " inane gidan su Yarinyar kizo muje kikaini narok'eta Alfarma tazo wajen d'ana , ba musu Mumyn Junaid ta wuce suka fita dan zuwa gidan su Nabeela......


Jidda ankaita asibiti andubata sosai likitoci sun tabbatar da babu abinda yasamu cikinta , sosai Alhaji Ghali yaji dad'i yayi godiya ga Allah , sao dai ya saka a nemo masa Sara duk inda take saiya yi maganinta......


Hajiya Sara da Hajiyar Dubai sundawo daga watsewarsu suka shiga d'akin dasuka ajiye Jidda wayam suka gani , babau inda basu dubaba amman babu ita babu dalilinta , da sauri suka nufo k'ofar gate suna tuhumar me gadi , sai dai ya sheda musu bawacce ta fita sai Bahijja da k'awar ta kuma suma a cikin motar suka fice, Hajiya Sara tuni hankalinta yatashi "yau ta shirya kashe Jidda tare da d'an cikinta amman ace ta gudu , tabbas saita nemo wanda yake da hannu a guduwar Jiddar........




*Comment* plss





*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 😍🌹*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤




_NA_
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪 https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






🅿️ 23.


Nabeela sosai takasan ce cikin farin ciki da ganin wannan Studio d'in , tana zuwa tafad'a jikin Ummanta tana murna , da sauri Umman tata tace " meyasa meki haka Nabeela naga kina cikin farin ciki ? murmushi tayi sannan tace " Ummana kinga Studion buga wak'a da Yaya Anwaar yayimin kuwa ? wallahi tayi kyau sosai Ummana inama ace kina gani dakin ganta , Umma tayi murmushi tace " wata rana inda rabo zangani Nabeela na , ina fatan kinyiwa Yayan naki addu'a Allah yabashi abinda yakeso , Hajiyar Anwaar murmushi takeyi me cike da jin dad'i , bayan Anwaar a duniya bata tab'a ganin wanda yadamu da Mahaifiyar sa kamar Nabeela ba , tabbas Nabeela tanason Ummanta iya yadda sukeyi insuna tare shi zai sheda maka hakan....
Sai lokacin Nabeela ta tuna da Hajiyar Anwaar ta juya tace " Mumy kitayani godiya gurin Yaya Anwaar , murmushi Hajiyar Anwaar tayi sannan tace " kunfi kusa keda Yayan naki ai , nidai kiyimin wak'a me dad'i irin wacce kikayi a Album d'inki me suna *Masoyi* murmushi Nabeela tayi tana sunkuyar da kanta cikin ranta take fad'in " dama Hajiya tanajin wak'a itama ? sai jin muryar Hajiyar tayi tana cewa " kina mamakin taya nasan wak'ok'inki ko ? to Anwaar ne ya koyamin jin wak'a sosai harya fara kunna min wak'ok'inki , tun muna Abuja yake samun wak'ok'in a kan youtube har muka dawo gida , hankalinsa bai kwanta taba har saida yaje yasameki a wajen aikin ku , ya kaimiki aikin wak'a r Birthday d'ina , koda ya dawo gida bakiga yadda yadunga min sambatu wai yaga maiyin wak'ar Masoyi yau , kuma kyakkyawa ce 'Yar k'arama da ita , Umma tace " ai tun Nabeela na k'arama take mutuk'ar k'aunar wak'a , harta fara girma duk inda zaka ganta saika ganta da littafin da abin rubutu tana rubutawa , murmushi Hajiya tayi tace " Allah ya amsa mata burinta tunda gashi tafara suna , Nabeela tuni ta fice ta koma b'angarensu tana bawa Raihan labarin Studion da Anwaar yayi mata......


Mumyn Junaid sunje k'ofar gidansu Nabeela sai dai sunsamu labari cewa 'Yan gidan sunyi gobara sun mutu , sosai Daddyn Junaid yashiga damuwa , yanzu yazaiyi da 'Dan sa wanda yake da buk'atar Yarinyar gidan ? Mumy tayi shuru tana nazari cikin ranta tace " kodai Hajiyar Dubai ce tasa akasa musu wuta a gidan ? tabbas tasan Hajiyar Dubai akan Bahijja babu abinda bazata saka ayi mata ba , amman bari su koma ta d'an bugi cikin ta taji..


Haka suka baro k'ofar gidan su Nabeela suna jimamin yadda zasuyi , suna zuwa Asibitin suka samu Junaid yayi bacci , likita ya tambayesu ina yarinyar da sukaje taho da itan take ? Nan Daddyn Junaid yafad'a masa yadda akayi , sosai ya jimanta musu tare da cewa " insha Allah inya farfad'o bazai kuma neman ta ba , shiga d'akin nasa sukayi suka zauna zaman jiran farkowarsa........


Jidda tunda tasamu kanta take kukan rasa Nabeela datayi , tabbas tarasa wani jigo a cikin rayuwar yanzu yazatayi ? kuka tashiga yi sosai su Innarta suna bata hak'uri suma sosai mutuwar su Nabeelar ta dokesu ,....


Hajiya Sara tuni suka nufi lagos gidan k'awarsu wacce tayi aure acan , suna zuwa suka shiga bata labarin komai da komai rashin kirkin da Alhaji Ghali yayi mata , nan k'awar tasu tace " Su shirya akwai wani boka a lagos d'in wanda yake aiki tamkar me , duk wasu masu ji da kansu da matan Governoni da su kansu Governonin suna zuwa wajensa , Hajiya Sara tace " yanzu naji bayani inaso adawomin da Alhajina tamkar yadda muke da , sannan inaso shegiyar yarinyar nan yarabu da ita ya wulak'anta ta yace kuma cikin jikinta banasa bane , Hajiyar Dubai ita kuma akan a mallakowa 'Yar Junaid yazamo nata ita kad'ai , haka sukaita shirya muguntar da zasu saka bokan yayi musu sannan suka dulmiya aimin sab'on su.......


Anwaar tuni ya nemowa Nabeela me koya mata komai , Oganta ba irin neman da baiyi mata ba amman baisa meta ba , gashi Anwaar kwata kwata yak'i gaya masa Nabeela natare dashi , tuni Nabeela tafara iyawa saboda tsabar maida hankalinta datakeyi , Raihan kuwa tuni ansamar mata wata sch ta kud'i tafara zuwa ...



*Dan Allah kuyimin afuwa* 🙏🏻🙏🏻 *wani aikine yatasomin na gaggawa* *kuyi* *maneji zuwa gobe*🤝🏻🤝🏻🥰*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤




_NA_
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






🅿️ 24.


Wani daji me duhun gaske Hajiya Naja taja su Hajiya Sara da Hajiyar Dubai , wani k'asurgumin boka ne yake a ciki yake aiki . Lokacin da sukaje wasu manyan Alhazawa sukaci karo dasu suma sunje , Bayan yagama sallamar Alhazawan su Hajiya Sara suka shiga , Nan suka fad'a masa buk'atunsu yafad'a musu mak'udan kud'in dazasu bashi sukace badamuwa , Nan suka bashi wani abu daga cikin kud'in tare dayi masa alk'awarin dawowa nan da kwana biyu suka wo masa cikon kud'in , basu magani yayi tare da gaya musu yadda zasuyi amfani dashi , tuni suka ansa suka fito daga cikin bukkar tasa , koda fitowar su sai sukaga wad'an nan Alhazawan basu tafi ba , suna zuwa tagabansu sukayi musu inkiya irin tasu ta 'yan bariki tuni suka jone abinsu harda Hajiya Najar itama.........


Nabeela tafara aiki a cikin Studion ta wacce take a cikin gida , wak'a lafiyayya ta shiryawa Hajiyar Anwaar , sosai wak'ar tayi dad'i lokacin Anwaar baya gari lokacin yaje Abuja , shima saida tayi masa wak'a me dad'i wacce tayi mata suna *Karramawa* ....


Anwaar yana Abuja amman zuciyarsa na Kano waken Nabeelar sa , gashi ita bata da waya bare yaji muryar ta , insunyi waya da Hajiyar sa kullum saiya tambayi su Nabeelar tace lafiya lau take , Yauma da begenta yatashi tare dason ganinta , Allah Allah yake yagama abinda yaje yi yadawo gida yaga Beela bbynsa.


Jidda cikinta ya isa haihuwa shiyasa tadawo gida Gurin Innar ta , sosai take samun kulawa wajen Alhaji Ghali , Jidda kwata kwata bata wani sukuni tun lokacin da akace mata Nabeela sun mutu , kullum a cikin jikinta tanajin tamkar Nabeela bata mutuba tana nan a duniya , amman to tana inah ? shine tambayar data keyi Wa kanta , Ranar wata Asabar Naguda takama Jidda kafin aje asibiti ta Haifi santaleliyar 'Yarta , murna wajen Alhaji Ghali harda kuka , dama ashe yana da rabon ganin irinsa a duniya tabbas Jidda Alkairi ce agaresa ya k'udurta a ransa bazai k'ara kula matan banza ba , ranar suna na zagayowa yarinya taci suna Nabeela Jidda sosai taji dad'in yadda Alhaji Ghali yasa sunan Aminiyar ta , suna kiran Yarinyar da Habebty sosai akayi hidima Nera tayi kuka a gurin sunan Habebty......


A b'angaren Nabeela itama kullum tana tunanin ina zataga Jidda , zuwanta uku gidan su wanda suka koma ana cewa suntashi haka ta hak'ura takoma gida....
Nabeela tana cikin Studion ta ta kunna wak'ar datayi wa Anwaar tana bin wak'ar idonta a rufe , sai murmushi take tanajin wani dad'i nashigar ta , Anwaar yana tsaye ya rungume hannunsa a k'irji sai kallon ta yake , k'ara dawowa tayi da wak'ar baya tana kuma ji saiji tayi ankashe wak'ar , da sauri ta bud'e ido sukayi ido biyu da Anwaar yasa kar mata murmushi , da sauri ta yi k'asa da kanta tana dariya , cike da girmamawa tace " sannu da zuwa Yaya Anwaar dafatan kadawo lafiya , murmushi yayi ya zauna gefen kujerar datake yace " gaskiya tunda naje Abuja nake fama da rashin lafiya , da sauri ta d'ago tana dubansa tace " meyasa meka Ya Anwaar ? ciwon sonki da kuma kewarki datayi min yawa , murmushi Nabeela tayi cikin shagwab'a tace " harkasa naji tsoro Allah kuwa , kwaikwayon maganar ta yayi yace " nima harkinsa naji sonki Yakuma k'aruwa Babyna , dukansu Murmushi sukayi sannan yace " wannan wak'ar yaushe kikayi ta sosai tayimin dad'i ? yau kwana uku dayinta kuma sadauk'arwa ce ga *Masoyi na gaskiya* , Anwaar yace " zanso sanin waye wannan masoyin na gaskiya ? kauda zancen tayi da kunna masa wak'ar datayi wa Hajiyarsa tana fad'in " d'an saurari wannan wak'ar kaji a binda baiyi ba kafad'amin , Anwaar yai shuru yafarajin wak'a tuni yaji yana rausaya kai daga haka sai rawa , Nabeela tafara masa dariya tana sunkuyar da kanta , jitayi ya rungumeta ya manna mata wani Hot kiss yana thanks my Beela Bbyna wak'a tayi Hajiyata tana godiya , tuni Nabeela tayi mutuwar zaune saboda wani abu dataji ya ratsata.......


Su Hajiya Sara tunda suka had'u da Alhazawan nan suka tare a garin Lagos , kwata kwata sundaina tunanin komai saboda irin kud'in da suke samu , ai tuni Hajiya Sara ta manta da wani Alhaji Ghali tasamu Alhaji Millioners , kud'i kawai suke sakar musu tamkar basu san ciwon suba , Hajiyar Dubai sai dai tayiwa Bahijja aiken kud'i wacce ta tare a hotel dazama ......
Junaid tunda yafarko yadaina magana kwata kwata , Likitoci sun yi iya k'ok'arinsu amman sunkasa gano matsalar , Daddynsa tuni yayi musu visa suka wuce dashi India .......


Ranar Birthday d'in Hajiyar Anwaar Nabeela taga manyan mutane , har 'yan jarida saida sukazo wajen , dayake a Babban waje akayi Saboda Manyan k'awayen Hajiyar da suka zo daga garuruwa , Nabeela ita da Raihan sukaje da Hindu , Umman ta tana gida tace ita bazata jeba , lokacin da aka kira Nabeela zatayi wak'ar Da tayiwa Hajiya Anwaar tuni yajata cikin wani d'aki yabata wata leda yace tasa kayan ciki , ansa tayi yajuya ya fita itakuma ta bud'e ledar , wani had'edd'en less tagani sai d'aukar ido yakeyi d'inkin riga da siket , fito dasu tayi tasaka tamkar dan ita akayi kayan , harda mayafi da jakarta me masifar kyau , tana fitowa Anwaar yayi mutuwar tsaye dan badan yasan kayan ba wallahi zaice ba itabace saboda had'uwar datayi , tana hawa step d'in aka fara ihu mutane ana murna yau ga *Mawak'iyar* Datayi wak'ar *Masoyi* da *Halacci,* tuni 'Yan mata 'ya'yan manyan masu kud'i dasuka amsa sunan su a Nageria suka fara hawowa Step d'in dan yin Hoto da Nabeela.......





_Nima kufito muyi Pics d'in Juma'at Kareem Masoyana_ 🥰🌹🤝🏻😍


*'Yar Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🌹😍*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤



_NA_
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






🅿️ 25.


Nabeela Murmushi kawai takeyi najin dad'in ganin wannan rana , dama haka wak'ar ta tayi suna har mutane suka santa haka , godiya ta shiga yiwa Allah tare da Addu'a ga Junaid domin shine farkon wanda yafara kaita wannan matsayin dan haka baza ta tab'a mantawa dashiba , godiya ta gaba kuma ga Anwaar wanda yazamar mata jigo a cikin rayuwarta , duban wajen dayake a zaune tayi shida Hajiyarsa tayi masa wani murmushi , shima ya maida mata tare da d'aga hannu yayi mata jinjina , bayan jama'a sunkoma sun zauna nan Nabeela tafara nuna murna da zagayowar ranar Haihuwar Hajiya Amina me gwala gwalai wato Hajiyar Anwaar , tana gamawa Mc. Yasaka wak'ar datayi wa Hajiyar ita kuma tafara Mamin , ai tuni wak'a ta ratsa Hajiyar Anwaar ita da k'awayen ta take suka fito suka hawo wajen da Nabeela take suka fara yi mata ruwan lik'i , Dollars kawai kake gani suna tashi sama , waje ya kacame sosai da Manyan mata kowa sotake ta burge Hajiya Amina , sosai akayiwa Nabeela lik'i tamkar basu san darajar kud'in ba ....


Bayan Mc.Yayi sanar wa kowa ya koma ya zauna , bayan an raba abinci da kayan Drinks da manyan jakun kuna masu d'auke da hoton Hajiya Amina.....
Bayan angama ciye ciye nan Hajiya ta mik'e tare da manyan k'awayen ta suka rakata ta wajen da Cake yake , a lokacin Hajiya ta rad'awa Mc. Akan yakira mata yaranta sune zasu tayata yanka Cake , Nan danan Mc. Ya hau kiran Anwaar da Nabeela atare suka mik'e dan zuwa wajen Hajiya Amina , take Mc. Yasakar musu wak'ar da Nabeela tayiwa Anwaar d'in , takun da sukeyi atare tamkar dansu akayi wannan taro , kowa dake gurin ba k'aramin burgesa sukayiba , sai sannan Nabeela taga kayan jikin Anwaar kalar less d'in daya ke jikinta ne , suna hawa Step d'in Anwaar ya rik'o Hannun Nabeela har wajen Hajiyar sa , tafi aka shiga yi musu ita kanta Hajiyar sai da ta tafa musu yadda taga sun burgeta , suna zuwa suka saka Hajiya a tsakiya tare da d'ora hannuwan su akan nata , Nan aka fara k'irga musu number daga One zuwa Three ta yanka Cake d'in , take aka fara tafi Anwaar ya gutsura yasawa Hajiyar tasa abaki ansa tayi tana murmushi aka hau tafi , itama Nabeela yadda taga Anwaar yayi itama haka tayiwa Hajiyar , ansa tayi tare da gutsura sannan tasawa Nabeela itama abakinta , tuni masu Video da hotuna sunzagaye su sai aikin su suke , Nan Hajiyar takuma gutsura tasawa Anwaar abaki sannan tasa shima yabawa Nabeela abaki itama tabashi , Abu yayi kyaufa kowa fad'i yakeyi sundace sosai , bayan angama yanka Cake kowa ya koma ya zauna sai kid'a dake tashi a wajen , Dayake duk manyan matane masuji da Naira tare da Manyan yaransu masuji da kansu bawanda yake rawa duk suna zaune suna hirarsu , Mc. Da yaransa ne suke k'ayatar da wajen da rawa..........


A can Lagos kuwa Hajiyar Dubai ta b'arke da Amai da gudawa , koda su Hajiya Sara suka kaita asibiti

14 / 23