Chapter 3 Reading MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt Arewa Novels

MAWAKIYA Book Complete Document original by Zee MD.txt

Author :  Zee MD Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   3 / 23

6K to 9K   out of 66.3K words

tasamu Umman ta ta tana Sallah , wata ajiyar zuciya taja lokacin Jidda ta k'araso itama , Jidda ta kalli Nabeela tace " Alhamdulillah tunda munsa mu Umma lafiya , Rik'o hannun Nabeela Jidda tayi sukayi hanyar Soro sannan suka tsaya , Jidda ta dubi Nabeela tace " inaso kibani labarin abinda yafaru dake a gidan Alhaji Ghali , Nan Nabeela takwashe komai daya faru da ita da Hajiya Sara tafad'a mata , Jidda tazaro ido tana duban Nabeela tare da fad'in " Innalillahi munshiga Uku 'Yar uwa , muna zaman mu muna rayuwar mu cikin kwanciyar hankali gashi munjefa kanmu a gidan halaka , Nan Jidda itama ta kwashe komai da yafaru tsakaninta da Alhaji har Hajiyar tafad'a mata , Sannan tak'ara da cewa " Abinda nakeso dake Nabeela shine karmu kuskura mufad'awa iyayenmu wannan maganar , dan indai sukaji hankalinsu zaitashi sosai , inaso mu rik'e abin a zuciyoyin mu muga abinda hali zaiyi , Nabeela ta goge hawayen idonta tace " tabbas nayi dana sanin zuwa gidan wad'annan shed'anun , Jidda tace " bake kad'ai ba 'Yar uwa nima kaina inayin dana sanin wannan neman aikin , sundad'e suna tattauna damuwar sunkafin Umman Nabeela tafara kiranta tana fad'in " ta idar da sallar , Sallama Jidda tayiwa Nabeela ta tafi gidan su ita kuma tashigo cikin d'akin....


Nabeela ta dubi Umman ta tace " Ummana nadawo yana sameki ? Umman tace " lafiya lau Nabeela ta , sai dai yau gidannan nadinga jin motsin mutane dayawa a tsakar gida , nayi magana sosai bawanda ya amsa min kuma sosai naji motsi , Nabeela jitayi k'irjinta ya buga take tsoro ya shige , tabbas Hajiya Sara abin nata da gaske take wannan wacce irin jarabace , shurun da Ummana taji nayine yasa tace " Nabeela kina jina kuwa ? firgigit nayi nace " Inajinki Ummana , Abinda nake tunani kawai indai zanfita zandunga kaiki gidan su Jidda ki zauna , inna dawo sai mudunga tahowa gida ko , Umman tace " to hakan dai zaifi gaskiya , kinga gidan sai a dunga rufosa kawai , nace " Ae hakan za'ayi kawai , tashi nayi nace "Bari nayi arwala nazo nayi sallah sai a d'ora mana abinda zamuci....


Bayan na idar da sallah nafito na kunna gawayi na d'ora mana Abinci , ina girki amman hankalina baya tare dani , wani mugun tsoro nakeji tamkar naga wani dodo , a hakan na kammala girkin nakwashe na kashe wutar na nufi d'aki , tunawa nayi ban kulle mana gida ba tuni natashi naje nasaka sakata , duk da k'yauren gidan namu bugu d'aya ma akayi masa sai ya cire amman yafi babu , Nazubo mana Abinci nida Ummana Amman nidai lomata batafi uku ba naji banason ci , wasa nake da cokali nakasa cin Abincin , jinayi Ummana tana cewa " Nabeela wai meyasa meki ne najiki yau wata iri dake tunda kika dawo ? dubanta nayi take naji wani tausayinta ya kamani cikin zuciyata nace tabbas tsakanin Uwa da 'Da sai Allah , sauri nayi na goge hawayen dake idona nace " Ummana wallahi nagaji dayawa ne yau , kinsan basabawa mukayi da aikin irin haka ba sai ahankali zamu saba , cike da nuna tausayi tace " Allah sarki Nabeela ta , Allah yayi miki Albarka nasan dole dama sai ahankali zaki saba , in kuma kinga aikin da wahala sosai ko ki hak'ura ki nemi wani aikin , Murmushin k'arfin hali nayi nace " Bakomai Ummana inna saba bazan ji wahala haka ba , cike da nuna damuwa tace " Allah yasa Nabeela Allah yakuma biya miki buk'atarki wacce kika saka a gaba , Nabeela ta amsa da Ameen Ummana ....

Sosai dare yaraba Amman nakasa Bacci saboda tunanin halin da muke ciki , tabbas bazan iya cigaba da zuwa aiki gida Hajiya Sara ba , nikad'ai nake wannan sak'e sak'en nawa , ahaka Bacci barawo yayi a won gaba dani...


Jidda ma anata b'angaren haka ta kasance , babu irin tambayar da 'Yar uwarta Sa'ade batayi mata ba amman sai tace kanta keyi mata ciwo , saida ta raba dare sannan tayi Bacci ....


Washe gari yadda Nabeela tasaba da karanta littafin wak'a yau batayi haka ba , a hankali ta gyara musu gidan sannan ta yi musu abin kari ta dafa musu ruwan wanka , Bayan sun karya tacewa Ummanta tana son zuwa gidan su Jidda , Umman tace " to kigaidamin da Innar tasu , Nan nafito nakama hanyar gidan su Jidda , ina tafe naga wata motar ta tsaya a gaba na da bak'in glass , bana ganin na ciki amman shi yana ganina , zuwa nayi zan wuce naga anbud'e k'ofa anfito , wani k'aton mutum ne wanda kana ganinsa kaga d'an daba yasha gaba na yace " ke ina zakije kika fito haka ? dubansa nayi jiki nayimin rawa nakasa magana , dan bansan waye shi ba bare na amsa masa tambayar sa , ya dakan wata tsawa yace " kiyi sauri ki juya ki koma gida tunkafin ki rasa Mahaifiyarki , inajin yace hakan najuya da guduna na nufi gidan mu , tabbas da da mutane a unguwar sai sunbiyoni danjin tambayar lafiya nake wannan gudun , ina shiga cikin gidan nafara k'walawa Ummana kira , har cikin d'aki nashiga da gudu , samunta nayi tana Baccin ta hankali kwance , zubewa nayi a gabanta ina ajiyar zuciya tare da wani irin hawaye yana zubowa , Allah yaso Ummana bata tashiba duk irin wannan kiran danake yimata , kasa fita nayi koda tsakar gida har aka kira sallar Azzahar....
Tashi nayi nayo arwala nayi sallah , addu'a nayi sosai akan Wannan musifa data tunkaro mu Akan Allah ya tsaremu , ina zaune ina jan casbaha sai ga sallamar Jidda , tashi amsawa nayi sannan na mik'e nafito daga d'akin , kujera na d'auko mana kowa yazauna , dubanta nayi naga tayi zuru zuru itama nace " kema nasan baki samu bacci ba 'Yar uwa ? Jidda tace " wanne bacci Nabeela wallahi ban rintsaba sai wajen asuba , yau kuma muna tashi da safe a gidan mu mukaga k'yaure gidan a bud'e , kuma Yaya Sa'ade tace taga fitar wasu mutane su biyu daga cikin gidan , wallahi nasan duk sharrin su Hajiya Sara ne da mijinta , tund'azu naso inzo gidannan amman naga wata bak'ar motar a k'ofar gidan mu a ajiye , sai yanzu dana lek'o naga babu ita shine nayi sauri nataho , Nabeela najin Abinda Jidda tace takuma jin fad'uwar gaba , take itama tabawa Jidda labarin Abinda tagani lokacin da ta fito dan zuwa gidan nasu , Jidda jiki na rawa tace " Yanzu meye abinyi wallahi da gaske muta nen nan suke rin wannan bala'i , wallahi nayi dana sanin zuwa neman aiki gidan Alhaji Ghali , kuka sosai sukeyi sai da sukaji muryar Umma nacewa " wanakeji a tsakar gidan nan kamar ana kuka ? da sauri Nabeela ta goge hawayen ta ta had'iye Kukanta tace " Ummana ba kuka akeyi ba nice da Jidda muke hira , Umman tace " Au daman baku tafi gidan aikin ba ? Nabeela tace " yanzu dai zamu tafi Ummana , kama hannun Umman ta tayi takaita Band'aki takama ruwa , Bayan Umman ta ta tayi arwala tazo ta tada sallah sannan Nabeela ta dubi Jidda tace " Yanzu meye mafita a wannan lamarin ? Jidda tace " Mafita d'aya ce kawai mu Amincewa su Hajiya Sara , Nabeela da sauri ta dubi Jidda tace " Mu amince fa kikace Jidda ? Jidda tace " Ae wallahi banga ta yadda zamu iya fitar da kanmu a wannan tarkon nasu ba , inajin tsoron halin da zansaka Su Inna ta aciki , tunda abin yakai da ana shigomana gida ana kwana , yanzu haka fitowar danayi wallahi duk hankalin Innata a tashe yake kinga kuwa dole in kiyaye musu abinda zaisa su a damuwa , Nabeela tace " Haba Jidda meyasa zaki amince da wannan mummunar Rayuwa , dan Allah kar ki amince Jidda , Jidda ta mik'e tace " bani da zab'in da ya wuce hakan , idan kuma kina da mafitar da zaki samo mana wacce zata kub'utar damu tare da Iyayen mu to a shirye nake nabita , yanzu nidai zanwuce zuwa gidan Alhaji Ghali dan cigaba da aikina , dan karki manta a cikin sharud'an ta tace " k'in komawar mu gidan yana nufin koma meye tayi mana kenan , Nabeela jikinta duk yayi sanyi amman cikin zuciyar ta haryanzu bata Amince mata data koma gidan Alhaji Ghali ba , kuma batajin zata iya Amincewa da buk'atar Hajiya Sara , kasa magana tayi har Jidda tagaji da tsayuwa ta wuce ta tafi , Nabeela tana zaune tana nazari tare da tunanin mafita taji muryar Umman ta tana kiranta , mik'ewa tayi jiki babu k'wari ta nufi cikin d'akin nasu , Umman tace " ina Jiddar take ita ? Nabeela tace tatafi yanzu , Umman tace " to kemeyasa bazakije gidan aikin ba yau ko duk gajiyarce haka ? Nabeela tace " kai na yana ciwo Ummana saidai zuwa gobe sainaje , umma tace " to kitashi ki karb'o magani sai kisha mana , to kawai Nabeela tace dan batajin ko soro zata lek'a bare waje.....


Jidda na zuwa gidan Alhaji Ghali Hajiya Sara tadubeta tace " wato ita bata amince ba kenan ko ? tunda naga kinzo ke kad'ai nasan ita bazata amince ba , itadai Jidda kasa cewa tayi komai har saida Hajiya takira Larai tace tabata aikinta.....


Nabeela kuwa tuni zazzab'i ya rufeta amman bata nunawa Umman suba , lokacin Umman su Nabeela na zaune tanajin Radi'o ana wani shiri me suna Dandalin Mawak'a , bakin Umman yak'i rufuwa sai cewa take " in Allah ya yarda wata rana haka zanji Muryarki Nabeela na kina rera wak'a , Nabeela tana jinta takasa magana , ita kuwa Umma satake bacci Nabeelar keyi Abinka da Makauniya , suna zaune a haka har magariba tayi sannan ta tashi tayi sallah tadawo ta zauna , Umman ta ma tashi tayi tayi sallar sannan tazauna tana jan Nabeela da hira , daga tace E sai tace a'a , Bayan an idar da Sallar isha'i saiga sallamar Jidda , da sauri Nabeela ta kalli Jiddar tana so taga yatakoma , gani tayi yadda ta tafi d'azu haka take ma yanzu bawani abinda ta canza , gaisawa Jidda tayi da Umma sannan ta dubi Nabeela tace " sannu da gida ya kika wuni ,? Nabeela tace " kinfi kowa sanin Yadda zan yini Jidda , wata k'atuwar leda Jidda ta ajiye tana fad'in " d'auko kwano ki d'ibar wa Umma tuwon Semo nataho musu dashi ita da Inna , Nabeela tace " Banajin xan iya mik'ewa a yadda nake yanzu , tashi Jidda tayi yaje ta d'auko kwano ta zubawa Umman Tuwon Semo miyar Kub'ewa d'anya wacce taji Naman kaji , bayan ta zuba mata tacewa Nabeela nidai zan wuce sai zuwa gobe da safe , tashi Jidda tayi tana d'aukar ledar data shigo da ita , da sauri Nabeela itama ta mik'e tana biyo Jiddar .....
Tsayawa sukayi a soro Nabeela tace " dan Allah Jidda karkice min kinbawa Alhaji dama ya aikata abinda yakeso dake ? Jidda tayi wani murmushi wanda kana ganinsa kasan na dole ne tace " ni yau har naje nagama aikina nataho wallahi banga Alhaji ba , kuma Hajiya Sara batamin wata magana ba , sai dai farkon zuwana da taga babuke taji haushi nagani , Nabeela wata ajiyar zuciya tayi tace " naji dad'i da Allah bai had'aku da Alhajin ba , zaki iya tafiya sai da safe kar in tsaidaki kingaji dayawa , Jidda ta wuce ta tafi ita kuma Nabeela ta rufo musu gida dan tasan ba fita zasuyi ba......


Cikin dare kamar daga sama Nabeela taji ana tab'a ta , da sauri ta bud'e Ido dan ganin waye , Hajiya Sara tagani tare da wasu k'artan maza wanda kana ganinsu kaga mara sa imani , da sauri Nabeela ta tashi zaune jikinta ya hau wani mazari , saida ta wara idonta sosai taga ai ba gidan su bane nan d'in inda aka kawota , kuka tasaka tafara kiran" Ummana nashiga Uku wayyo Ummana , wata tsawa da d'aya daga cikin Yaran Hajiya Sara ya daka mata yasa tasaki wani wahalallen fitsari.....



*Comment* *Kawai* ✍🏻


*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🥰🌹*MAWAK'IYA*
🎤🎤🎧🎤🎤




_NA_
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






🅿️ 5.


Dubanta yayi cikin kakkausar Murya yace " kina san Umman taki kika bijirewa maganar uwar d'akin mu ? shuru tayi tana shashshekar kuka , ya matso kusa da ita har Numfashin sa na bugun nata yace " zaki amince da buk'atar Uwar d'akin Namu ko Yaya ? da sauri Nabeela tace " Na amince wallahi dan Allah kukaini gun Ummana , wata dariya suka saka dukansu sannan sukace " kowa ya tuba dan wuya ba lada , ai samuke ke gwanar taurin kai ce da yanzu munyi watandar jikinki , Hajiya Sara tayi gyaran murya alamar kowa yayi shuru , sannan tace " tunda kin Amince inaso Gobe naganki kinzo aiki gidana , sannan kuma banason wannan maganar tafita gurun wasu tabbas zaki ga hukuncin dazan saka a miki indai tafita , Kuma mutuk'ar kika kuma sab'a Alk'awari wallahi komai kika gani kiyi kuka da kanki , hukuncin gaba dazan miki wallahi basani ba sabo ko kad'an , sannan ta dubi yaran nata tace " inaso ku d'auke ta ku maida ta gida sai kuzo ku anshi sak'on ku , tuni suka saka Nabeela a gaba suka maida ta har gida sannan suka juya suka tafi....


Nabeela da sauri ta shiga d'akinsu tasamu Umman ta na bacci , zama tayi tafara rera kuka tana dana sanin zuwa Neman aiki gidan Alhaji Ghali , ganin Umman ta na motsi yasa tayi shuru tamkar me bacci , shikenan yanzu haka zata Amince da buk'atar wannan Mata ? Tabbas da suna da 'Yan uwa a wani garin wallahi da gobe da safe sai sunbar garin nan , ahaka gari ya gama wayewa Nabeela batare da ta rintsa ba .....


Washe gari da ciwon kai ta tashi dan dak'yar ta kunnah wuta tayiwa Innah d'umamen tuwon da Jidda takawo mata , Bayan ta kai mata tuwon tashiga wanka ko zata samu ciwon kan yaragu ,
ko Abincin kasa ci tayi sai zaman tunani Duk tafad'a ta rame lokaci d'aya , Umman ta tace " wai Nabeela ta meye yake damunki kwana biyu nan ? naji wak'ar ma dakike yi kullum yanzu kindaina , sainaji kinyi shuru tamkar bakya cikin gidan , Nabeela tayi murmushin Yak'e tace " Ummana kinsan tun jiya kaina keyin ciwo kuma haryanzu bai daina ba ,
Umman ta tace " to kinsha maganin kuma ? Nabeela tace " babu kud'in siyan magani a hannuna Ummana , ni yanzu tunanina ma meza muci in anjima , muna da sauran shinkafa amman babu kud'in sarrafata , Umman tayi shuru tana Nazari sai can tace " kidaure yau kije gidan aikin nan ko zaki samo mana Abincin , tunda kinga jiya Jidda sun bata Abinci , Nabeela sai da gabanta yafad'i data tuna gidan Hajiya Sara , tafi minty 2 kafin tacewa Umman ta " To bari anjimar tayi sai naje mugani , Umman ta tace " Yauwa Nabeela na Allah yayi miki Albarka....


Bayan sallar azzahar saiga Jidda ta shigo d'auke da Sallamar ta , Umma ce ta amsa mata sannan suka gaisa , lokacin ina cikin d'aki a kwance kan wani k'aramin gadon mu , shigowa cikin d'akin Jidda tayi tasamu gefen gadon ta zauna , dubana tayi tace " 'Yar Uwa yakike naga kinyi zuru zuru anya lafiya kike kuwa ? Nabeela ta gallawa Jidda harara sannan tace " lafiya ai banda ita tundaga randa muka taka wancan tsinannen gidan , amman inajin ke kinsamu lafiya dan naga ko ajikinki , Jidda taji rashin dad'in Maganar amman sai tabasar tace " Rashin dad'i Nabeela bake kad'ai ba ai , ni bani da mafitar da ta wuce hakanne shiyasa kikaga na Amince da buk'atar su , Kuma kafin na Amince saida nace dake "kine mo mana mafita wacce zamu fita salin Alin amman baki nemo ba , Nabeela tayi shuru batare da tace komai ba , Jidda mik'ewa tayi tace " ni zan wuce gidan Aikin saboda yau tace nazo da wuri tana da bak'i , Nabeela tunowa tayi da sharud'an Hajiya na jiya da ta yimata , sannan ta tuna yadda akayi taje wajensu bata ma saniba , take tsoro yakuma kamata tabbas matar nan shu'umace zata iya komai kan hakan , mik'ewa tayi tacewa Jidda " tsaya

3 / 23