Author : ESHAAT SMILER Category : Romantic Hausa Novels
ango yasha babban riga da 'yar ciki kai kace shine ma angonπππ
Acikin gida kuwa ana daurawa anty hadiza ta sake guda, salma tana zaune a bakin gado tayi tagumi,tayi kwalliyarta cikin swiss lace red colour da ratsin blue and white.tasha sarkan gold da awarwaro ba karya tayi kyau sosai. Abokan wasanta sa'anninta suna gefe se tsokanarta sukeyi, da yake salma ita ba ma'abociyar kawaye bane indai ka ganta da kawa to 'yar uwanta ne. Yanzu ma su suka zame mata kawaye kowa a cikin su tasha ado se zuba kamshi suke yi.
Aunty hadiza ne ta shigo tana fada musu akan sunce yanzu zasu zo su dauki amaryan su, saboda mahaifiyar A.A ta hada walima a gidanta.
salma tana jin haka ta fashe da kuka.
Rarrashinta aunty hadiza ta shigayi, inna ce ta shigo dakin ta zauna a gefen salma ta ruk'o hannunta ta fara mata nasiha.
Salma nasan ke yarinya ce me biyayya da hakuri "ina so ki rik'e wannan a zaman auren ki" ki kasance me tsabta da rik'o da addini karki yadda mijinki ya shinshino wari a jikinki, ki kasance kullum cikin k'amshi. karki zamo me sa'insa da miji karki raina abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wanda ta girme ki, karki shiga harkan ta koda ta nemiki da fada.
tsakaninki da kowa girmamawa, ki kasance me hak'uri a gidan mijinki, kiji kik'i ji, ki gani kik'i gani wannan ne zesa ki zauna lafiya a gidanki. ki zama me girmama 'yan uwan mijinki, karki yarda mijinki ya fahimci bakya son 'yan uwansa. ki kasance me gyara SHIMFIDAR MIJINKI (princess eyshat Aysm)
A karshe ina miki nasiha da ki zama mace me yima mijinta Addu'a da rike sirrin mijinta, ki yawaita addu'a da kaima ALLAh kukanki, ki rik'e azkar safe da yamma insha ALLAhu zai zamo kariya a gareki.
ALLAh yayi miki albarka, ALLAh yasa gidan zamanki ne ππππ AMEEN aunty hadiza ta amsa.Inna tadan goge kwallan daya taru mata, tace hadiza rakata wajen malam kafin su k'araso. Aunty hadiza ta ruko hannun salma da tunda aka fara mata nasiha take kuka harda sheshsheka suka fita. Kofar dakin mallam Amadi sukaje sukayi sallama ya amsa musu ya basu umurnin su shiga.
Suka shiga suka nemi waje suka zauna. "Aunty hadiza tace yaya ga salma nan kayi mata nasiha sunce yanzu zasuzo daukan amaryan"Duban salma yayi wacce take kuka k'asa-k'asa yace "to salma menene abin kukan? keda za'a kaiki gidan da zaki huta" ba ruwanki da aikin wahala, to nidai abinda zance miki kawai shine kiyima mijinki biyayya, duk abinda yace miki karki yadda kiyi masa gardama. Karki sake ya kawo min k'aranki. in kuma kika bari ya kawo min k'aranki to wallahi ba abinda zai hana naje har gidan nayi miki shegen duka. Dan baza kiyi min bak'in cikin zuwa hajji wannan shekaran ba.
Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)Kallonsa kawai Aunty hadiza ta tsaya yi, tana jinjina son money irin na yayanta. an daura auren ma be dena abinda yakeyi ba maimakon yayi mata nasiha irin wanda iyaye suke yima 'ya'yansu amma ya tsaya yin maganar CIKAR BURIN SA (littafina na gaba insha Allahu)
Hadiza kamata kuje gashican naji ana neman amarya may be masu daukanta ne sukazo kar suyita jira. Maganar shice ta dawo da ita daga duniyar thinking data fada, kama salma salma tayi suka fice daga dakin ba tare da tace masa wani abu ba.
Dakin inna saude ta maida ita,ta dauko mata make-up kit tace ta sake gyara fuskarta. Bayan tadan gyara, Aunty hadiza tadan yi mata nata nasihan sannan tace karki yadda ki zama bora a gidan mijinki, kuma karki sake kishiya ta raina ki duk yanda za'ayi kiyi domin juyo da hankalin mijinki gareki kuma ki dage da addu'a. insha ALLAhu se kinfi k'arfinta. ba abinda ta isa tayi miki. kuma................ bata kai ga fadan abinda take soba sukaji sallamar masu daukan amaryan har sun k'araso.
Bayan sun shigo an gaggaisa Aunty hadiza ta rik'e hannun salma ta kaita wajen innarta sukayi sallama, sannan suka fito suka shishshiga motoci. salma se aikin kuka takeyiππππ tana bak'in cikin rabuwa da innartaπ‘π‘π‘.
Gidan su A.A dake unguwar tambari estate suka nufa. Babban Gidane ya hadu iya haduwa tun daga get zakasan nera tayi kuka. dan ko a layin yafi ko wani gida kyau da tsaruwa. A haraban gidan motocin sukayi parking, fito da salma akayi wanda kanta yake lullube cikin mayafi aka nufi cikin gidan da ita.
Wani hadadden falo naga an shiga wanda ban taba ganin irinsa a k'asar mu ta NIGERIA ba. se dai kasashen turawa. falo ne dayaji kujeru ash da baki ga chanise carpet da labulaye duk arsh da baki. ga k'atuwar plasma da home tiatre se aiki sukeyi kai gaskiya falon ya hudu.
Daga kan da zanyi na hango wata hamshak'iyar mata daga ganinta jin dad'i da hutu sun samu zama a jikinta. Kyakykawa ce doguwa fara tana da d'an k'iba amma ba sosaiba. baza ta wuce 55years ba amma idan ka ganta zakayi zaton batafi 45years ba saboda yanayin hutu da take ciki. Hajiya Halimat me dala kenan uwargida a wajen Alh. Abdul razak me dala kuma mahaifiya Awajen A.A.
Tana zaune tare da k'awayenta se murmushi take zubawa. Tasowa tayi cikin takunta na manyan mata ta k'araso ta rungume salma daka kalleta zakasan tana cikin farin ciki."well come to our family my daughter" ta fada tana murmushi, sannan ta jata suka zauna akan daya daga cikin kujerun da suke falon. Duk mutanen wajen ba wanda bata burgesu ba. wanda suka santa kam basuyi mamaki ba dan sun santa macece me son mutane bata da girman kai ko kadan.
Su aunty hadiza waje suka nema suma suka zauna, bayan 'yan gaishe-gaishe suka damk'a musu amanar salma, suka ce sun kar6a da fatan Allah ya tayasu ruk'o.
Agurguje
Salma na hango an fito da ita daga wani daki tasha lufaya milk colour fuskarta tasha make-up, tayi kyau sosai. Haraban gidan suka nupa wanda aka k'awata su da kujeru saboda gudanar da walimah. Batare da bata lokaci ba malama juwairiyya ta fara gudanar da lecture bayan ta bude taro da addu'a. Tayi bayani akan hakkokin miji akan matar sa da kuma yanda mace zata tafiyar da rayuwar aurenta da dai sauran su.
Bayan ta kammala ne aka rarraba bags wanda suke dauke da hoton ango da amarya a ciki akwai hankacif,memo,key holder,calender da juice kala-kala wanda suma suna dauke ne da pics din ango da amarya. se take away wanda akasa rabin kaza,donnut da meat pie. Ba'a tashi daga waliman ba se 5:00pm.
Wani daki na musamman aka kai salma,wata budurwa naga ta shigo dakin wanda batafi 21years ba,kyakykyawa doguwa bata da jiki sosai black beauty sadiya Abubakar kenan (my namecyπ) wanda aka daukota tun daga sokoto domin tazo ta shirya salma zuwa wajen dinner.
Toilet ta shiga ta hada ruwan wanka wanda yasha turaruka masu kamshi,ta fito ta umurci salma da ta shiga tayi wanka ta dauro alwala saboda lokacin sallar magriba ta k'arato.Bayan salma ta fito ta shafa mai se sady ta dauko make-up kit dinta ta fara tsantsara ma salma kwalliya. Wanda ya dauke su tsawan awa daya da rabi.
MASHA ALLAH abinda ya fito daga bakina kenan lokacin danayi arba da fuskar salma.
A gaskiya me karatu zanso kaga salma a lokacin.Indai ba farin sani kayi mata ba zeyi wuya ka shedata. nima dan na lab'e a lungun gado ne shiyasa har na ganeta.π Azuciyata kuwa nace anya A.A zai gane salma kuwa shida ko gama saninta ma beyi ba.
muje zuwa
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 14
Yau ya rage saura sati 1 biki gida ya fara cika da 'yan uwa na kusa da na nesa.
sallama akayi aka ce wai ana sallama da salma. Aunty hadiza ce ta cema yaron kace tana zuwa, da yake yanzu kusan kullum se tazo saboda hidiman biki.
salma kije ana sallama dake a waje aunty hadiza tace, tashi salma tayi ta dauki hijabinta tayi hanyar waje,kiranta aunty hadiza tayi, kina nufin haka zaki fita wai? ko kwalliya bakiyi ba bare ki fesa turare? maza jeki shafa ko hoda ce ki goga jan baki ki fesa turare.
tura baki salma tayi sannan ta koma daki ta danyi make up ta fesa turare ta fito. Har lokacin aunty hadiza tana tsaye a wajen data barta, to ko kefa ta fada tana murmushi da zaki fita kamar ba amarya ba,zakije wajen miji fuska farau-farau ba kwalliya.
ko kulata salma batayi ba ta fita ta barta tana ci gaba da maganar ta.
A jingine a jikin mota ta hango su, wannan karon su 2 suka zo, shida wani saurayi kamar shi black beauty dagani zeyi saukin kai dan fuskar shi cike take da murmushi. ba kamar A A ba daya hada rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa.
Tun da ta fito yake kallonta yana kare mata kallo, ba lefi tayi mishi kyau se dai fa shi kowacce mace bata burge shi inba matarsa humaira ba.
Sallamarta ne ya dawo dashi daga tunanin daya fada. kauda kai yayi se abokin sane ya amsa sallamar. Gaisawa sukayi sannan yace hajiya salma nasan baki sanni ba, sunana SALEEM nine babban abokin Abdul.
Munzo ne domin muji irin shirye-shiryen da kuke yi. seki fada mana event nawa zakiyi da yawan kudin dazai isheki se mu baki. cikin sanyin muryanta ta ce ba abinda zanyi kuma bana bukatar komai.tokai kaji abokina, ta yaya za'ace amarya bata bukatar komai? ai bazai yuwuba.
ko kallon shi A A beyi ba balle ya nuna yaji abinda yake fada. dan tsaki saleem yaja sannan ya maida kallon shi gun salma yace to mu ta bangaren mu akwai dinner da muka shirya bayan ankai amarya karfe 8:30pm. Ina fatan ba matsala?
Gyada mishi kai kawai tayi duk da a ranta bata so hakan ba, bude mota saleem yayi ya fito da wani leda tare da emvelop ga wannan kayan shi zaki sa a wajen dinner. wannan kuma ki rike a wajenki saboda hidiman biki duk da kince bazakiyi komai ba 500k ne ba yawa.
dan rusunawa salma tayi ta karba sannan tayi masa godiya. Murmushi saleem yayi mata dan ba karamin burgeshi tayi ba, bakomai amaryar mu ya fada sannan ya dubi A A ko akwai wani abin da ban fada ba? kauda kansa yayi cike da jinkai yace idan ka gama surutun zamu iya tafiya. ya fada tare da shigewa mota
Murmushi saleem yayi danshi ya saba da halin Abdul,mutum ne wanda baya son hayaniya se kayi magana goma be amsa maka daya ba. shiyasa baya damuwa da duk abinda zeyi masa saboda yasan halinsa in and out. Tun suna yara suke tare kasan cewar iyayen su aminan juna ne. ko sunyi fada a lokacin suke shiryawa
To amaryar mu, mu zamu tafi se munzo daukan ki nan da sati. godiya salma tayi masa tare da juyawa ta shiga gida suma sukaja motar su suka tafi.
salma tana shiga ta mikawa aunty hadiza ledan da kuma emvelop din, bude ledan tayi taga kayane a ciki. wani hadadden material ne purple colour da ratsin fari anyi masa dinkin doguwar riga. se farin takalmi hill da farin poss, se head purple da kuma sarka da dan kunne fashion purple da fari.
wannan kayan fa? aunty hadiza ta tambaya, bayani salma tayi mata. aikuwa kudinnan se dai a bude miki account a saka miki. bari na kaima innarki ta ajiye zuwa a gama biki se akai banki.
WAI WAYE A A ne???
ku biyo ni a next page domin muji cikekken tarihin A A me dala
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
*ZAB'IN MAHAIFINA*
π³π³π³π³π³
Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*
Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_
Page 15
Ina jin dadin yawan comment dinku da nake gani, nagode sosai ALLah ya bar kauna.
WANENE AA ME DALA??
ABDUL-AZEEZ ABDUL-RAZAK ME DALA shine cikekken sunanshi, mahaifinsa Alh. Abdul-razak me kudine na gaske yana da kamfanin saida motoci har guda uku bayan haka kuma dan kasuwa ne sosai. Abdul saurayine meji da kansa ga kyau ga nera uwa uba ilimin boko da arabic.
yayi karatunsa har zuwa matakin masters akan business. Abdul mutum ne miskilin gaske, danshi mutum ne da baya son hayaniya. Idan kaga yanda mata suke binshi abin zai baka mamaki,amma ko kallo basu isheshi ba.
Shikadai ne da namiji agun iyayensa,shine first born sai kannen shi mata guda uku Hafsat,Amina da ummul khairi. Sun samu tarbiyya a gurin iyayen su, kasancewar su masu arziki hakan besa sun sangarta su ba.
Abdul sun hadu da matar sa humaira ne a wani super market,sunje shopping shida abokinsa Saleem. tunda ta ganshi ta rikice akansa amma shi ko kallo bata ishe shi ba. hakanne yasa tabi duk hanyar da tasan zata jawo hankalin shi gareta kasan cewarta mace me budadden ido dan gidansu 'yan boko ne ita kadaice 'ya awajen iyayenta. ko kadan iyayenta ba ruwansu da irin rayuwar da take yi dan ko zata kwana a wajene ba wanda zai tambayeta dalili. wannan ne ya bata damar sheke ayanta yanda take so. dan gidan malamai ba wanda bata sani ba, idan dai taga kayi mata yanzu zata kai sunanka gun malaminta a mallake mata zuciyar ka. Hakanne ta kasance lokacin da taga A A.
tunda taga alamun dan jin kaine taje ta sanar da malaminta akayi mata aiki a kansa. Aikuwa aiki yayi kyau dan a hakane ta samu har ta aure shi. iyayensa basuso auren ba kasancewar ta me karancin tarbiyya, amma ba yanda suka iya tunda ya dage akan yana sonta a haka, se dai kawai suka ci gaba dayi masa addu'a.
Bayan anyi auren ne ta fara fiddo da asalin halayyarta, ko sau 1 bata taba daga waya ta kira iyayen mijinta ba domin ta gaishe su,ballantana ta taka da kafarta taje har gida.
koda kannensa sunzo bata bari su ganshi,se dai tace musu bayanan. daga karshe ma zuwa tayi ta samu me gadi akan ko sunzo kar ya yadda ya barsu su shigo gidan, duk randa ya barsu to abakin aikinsa.
Abdul mutum ne me son iyayensa da 'yan uwansa, hakan ne tasa suka fara samun sabani da ita. Wata rana da yayi mata maganar ta shirya suje su gaida iyayensa aikuwa ta rufe ido tace ba inda zataje. ranar taga bacin ran da bata taba gani tare da shi ba dan ce mata yayi indai bata je ba to saidai ta tafi gidansu. Badan ranta yaso ba ta bishi suka tafi.
Ganin hakan da yayi mata yasa ta koma gun malaminta aka hana shi zuwa wajen iyayen shi, a cewarta tunda akansu ne yace taje gidansu to suma seta rabashi da su. Indai kaga yaje wajen su to se dai ya saci hanya ba tare da tasani ba
Wani zuwa da yayi ne mahaifiyar sa take yi masa maganar karin aure,tunda shekaransu 5 da matar sa amma bata taba koda batan wata ba. ce mata yayi baida matar da zai aura se dai su zaba mishi kasan cewar sa mutum ne me biyayya, abinda basu sani ba humaira bawai haihuwa ne batayi ba, ta samu ciki har sau 2 tana zubarwa dan tace bata shirya haihuwa yanzu ba.
Aikuwa yasha albarka a wajen iyayensa. hakanne yasa suka aura masa 'yar kanwar Alh. Abdul-razak. kwata-kwata auren be wuce 2 month ba ya rabu da ita.
Bayan ita seda suka aura masa mata har guda 3,duk yana rabuwa da su. ta karshen kamma da hauka tabar gidan. saboda taso ta basu wahala kasancewarta ma'abociyar karatun al-qur'ani me girma. hakanne yasa tace kawai a haukatar da ita bokan yace gaskiya shi bazai iya ba, se dai a bari lokacin da bata da tsarki, Wannan ne dalilin dayasa ta samu galaba akanta. Tun daga lokacin basu sake aura masa wata ba dan ko sunje ba'a basu.
To a wannan karonne aka dace da mahaifinsa yazo wajen mallam Amadi nema masa auren salma,shikuma ya amince, saboda son abin duniya yajefa rayuwar 'yarsa a halaka.
yanzu labarin zai fara kudai ku biyo ni domin jin abinda zai faru nan gaba
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
ZAB'IN MAHAIFINA
π³π³π³π³π³
Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)
πHAJOW ππ
ππ©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎβπΎβπΎπ
Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI
page 17
Bayan sady ta gama mata make-up din salma ta saka hijab d'inta tayi sallar magriba dan lokacinsa harya kusa fita, tana idarwa aka kira isha'i. Tashi tayi ta yi sallar isha'i. Bayan ta idar tayi addu'o'inta aka shiryata cikin doguwar rigan material fitted gawn, wanda A.A suka kawo mata akan tasa ranar dinner. tasaka mahadin kayan ta fesa turare. Gaskiya salma tayi kyau dan kuwa my namecy taci kudinta, inso samune ayi mata k'ariπ.dan ta'iya shirya amare.
Hajiya halimat ce tayi sallama ta shigo dakin. wawοΌ my daughter kinyi kyau sosai,ta kai dubanta ga sady tace gaskiya takwara kin iya tsara kwalliya,ai wannan indai baka santa ba baza ka iya ganeta bama. Lallai kina da kyauta me tsoka tunda kika sa daughter tayi kyau haka.
Ita kuma sady jin an yabeta ne yasa ta fara magana cike da iyayi,ai hajiya inayi fiye da hakama. murmushi Hajiya halimat tayi ta kama hannun salma suka nufi falo. Kawayen amarya na zaune sunyi kwalliyar su cikin lace orange da touch din blue a jiki, se suka saka head blue suma sunyi kyau ba lefi.
Har bakin mota hajiya halimat takai salma, wata had'ad'd'iyar mota naga ta bud'e ta saka salma a ciki, galases din motar tint ne baka iya hango wanda yake ciki.
ta dubi saleem dake zaune a gaban motar tace ga amanar 'yata,kar ku bari wani abu ya tab'a min ita dan kunsan bazan bari ba. Sake juyowa tayi ta kalli A.A wanda ke zaune a bayan motar. yana sanye da shadda purple colour anyi design fari