Chapter 7 Reading ZABIN MAHAIFIYATA Book Complete BY ESHAAT.txt Arewa Novels

ZABIN MAHAIFIYATA Book Complete BY ESHAAT.txt

Author :  ESHAAT SMILER Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 7

18K to 20.8K   out of 20.8K words

ni kuma na rike addu'aπŸ™πŸ™ kuma da yardan Allah ba abinda kika isa kiyi min.

Mu zuba ni dake aga wanda zeyi nasara,humaira ta fad'a kafin ta juya ta fita daga falon. tsaki salma tayi, taci gaba da kallonta.

Driver ya kai abinci office d'in A.A masinja yayi masa izinin shiga bayan yaje ya fad'a masa yayi bak'o, tura k'ofar yayi ya shiga da sallama.

Duban shi A.A yakeyi cikin mamakin ganinshi, yace lafiya kuwa mallam haladu? lapia lau Alh. k'arami(dayake haka suke fad'a masa) gaishe shi yayi kafin yace "daman hajiya karama ce tace na kawo maka wannanπŸ‘‰ . duban basket din A.A yayi yana yamutsa fuska kafin yace wacece kuma hajia karama?

Amaryanka nake nufi ranka ya dad'e. kallon basket d'in ya sakeyi cikin mamaki yace "gidan kaje"? eh ranka ya dad'e hajia ce ta aikeni nakai mata 'YAR AIKI. Gyada kai yayi ya nuna masa kan centre table yace ya ajiye a wajen.

5000k ya mik'a masa, karb'a drivern yayi yana zuba godiya kafin ya fece daga office d'in. basket d'in ya d'auko ya ciro cooler da jug d'in. Ya bud'e ya zuba abincin tare da had'in coslow, sannan ya fara ci.


yana ci yana lumshe ido rabon daya ci abinci me dadin wannan harya manta, ko abincin restaurant dayake aikawa asiyo masa ba yanda ya iya ne kawai, gidan hajiyar sa ne idan yaje yake cin abinci kamar wannan. to shikuma yanzu ba zuwa yakeyi sosai ba. dan ko yaje baya dad'ewa bare har yaci girkinta me dad'i.

sosai yaci abincin yasha zob'on, a ransa yana jinjina ma yarinyar dan komai nata dabanne, gaskiya yanzu yana farin ciki da ZAB'IN MAHAIFINSA. kiran masinja yayi ya bashi saurae abincin, zob'on kuma ya saka a fridge, zuwa anjuma zai sha dan yayi masa dad'i sosai.




🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
ZAB'IN MAHAIFINA
🌳🌳🌳🌳🌳

Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)

🌐HAJOW πŸ“πŸŒ

πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐

Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI

Page 24

Da daddare salma ta tuka tuwon shinkafa miyar egusi wanda yaji ganda, da jallop din taliya da kifi, ta hada da sauran zob'onta na cikin fridge. bata kai abincin dining ba saboda bata yarda da humaira ba. Me aikinta ta kira ta bata abincin su dana megadi.


Kwalliyarta tayi cikin riga da skert na jan leshi, babban falon taje ta zauna tana jiran dawowar A.A. tana zaune humaira ta fito waje ta nema ta zauna se zabga ma salma harara takeyi.


Da sallam ya shigo falon cikin husky voice d'insa, mik'ewa salma tayi tana amsa sallamar, k'arasawa tayi ta karbi briefcase d'in hannunshi, cikin yanga tayi mishi barka da dawowa.


d'akinta ta wuce taje ta ajiye briefcase d'in, ta hada masa ruwan wanka, ta d'auko masa jallabiyya da gajeren wando ta ajiye masa akan gado ta fito daga dakin.

A kusa da humaira ta same shi kome suke tattaunawa oho musu da alama dai rarrashinta yakeyi. Aranta tace kudai kuka sani jarababbu kawai🀣🀣🀣🀣, kuma insha Allahu duk sihirin da tayi maka seya karye in dai kana shan zob'on nan.


Cikin murmushi ta kalle shi tace na hada maka ruman manka. dubanta yayi shima murmushin dauke akan fuskar sa ya amsa mata, sannan ya tashi ya shiga d'akin. Mugun kallo humaira ta jefa mata tace "tsabar iya karuwanci ne harda had'a masa wani ruwan wanka?" murmushi salma tayi tace aiba lefi bane tunda wa mijina nayi, kuma kowa yasan ban taba yawan bin maza ba, bare a kirani da sunan karuwa tayi wucewarta d'aki. bin bayanta da kallo humaira tayi dan tasan magana ta fada mata, wato ita ce tayi yawan karuwancin lalle wannan shine in kasan nafad'a bakasan na mayarwa ba.

Atare suka fito yayi wankan shi se kamshi yake zubawa, ita kuma tana dauke da abinci akan tray, se da ta bari sun k'araso cikin falon sannan ta kalleshi tace " Akan dining zaka ci ko na ajiye akan carpet?

A k'ule humaira ta ce kin taba ganin munci abinci akan carpet?? murmushi salma tayi kafin tace aunty wai ai naga ya dawo daga aikine ya gaji bansani ba ko zai iya hawa kan dining d'in.

ki ajiye akan carpet d'in, inaga zaifi. ya fada yana zama akan kujera, ajiyewa salma tayi sannan ta zuba musu. Abincin suke ci ba wanda yake magana a cikin su, sosai yaci abincin dan ya manta rabon dayaci tuwo, dan shine best food d'insa amma humaira bata taba sawa anyi masa ba. Humaira ma taci taliyar sosai amma bata sha zob'on ba, exotic ta dauko a cikin fridge din falon.

Bayan sun gama salma ta tattara kayan takai kitchen, ta sake wanka tasa kayan bacci tayi kwanciyarta. Ganin salma bata dawo bane yasa A.A yima humaira se da safe, ya ce mata bacci yakeji dan ya gaji da yawa, be jira jin abinda zata ce ba yayi shigewar sa part din salma, ya barta a zaune ta rasa ma abinda ya dace tayi.πŸ™‰

Yana shiga dakin ya cire jallabiyar ya saka kayan bacci, kwanciya yayi ya jawota jikinsa yayi musu addu'a.

yauma haka suka tashi cikin dare sukayi sallah,da karatun alqurani. da asuba bayan sunyi sallah, ganin da salma tayi fuskar sa a sake yasa ta dauko hisnul muslim ta mik'a masa tace ya karanta azkar d'in. beyi musu ba ya karb'a ya fara karantawa.

bayan ya gama ya dubeta yace " please idan akwai saura tuwon nan kiyi min dumamensa" Amsawa tayi sannan ta gaishe shi, ta tashi ta had'a masa ruwan wanka.


A gurguje ta hada breakfast tayi wanka ta shirya. Bayan da suka gama karyawa ta d'auki briefcase d'in, har bakin mota ta raka shi. Basket d'in jiya ya ciro mata, tayi masa fatan alkhairi, har ya tayar da motan ya lek'o yace "kina da waya kuwa?" Kallon shi takeyi cike da mamakin canjawar shi. kafin ta girgiza kai, bece komai ba yaja motar sa ya fita bayan me gadi ya bud'e masa get.


Da rana tayi jallop din cous-cous wanda yasha kayan lambu da hanta, tayi had'in coslow, ta had'a zob'onta kamar yanda tayi jiya, tunani takeyi yau wazata samu yakai masa? sega jamila me aikinta ta shigo "aunty ga drivern gidan hajia yazo"


fitowa tayi bayan sun gaisa yake ce mata " hajia ce ta aikoni akan zan dinga zuwa ina kaiwa Alh. karami abinci, saboda jiya dana koma take tambayata ya akayi na dad'e shine nayi mata bayani"

Godiya salma tayi ta d'auko abincin ta kawo masa,ta mika masa bak'in leda wanda ta saka turmin atamfa da shadda se turaruka masu tsada, tace ya kaima hajia. Duk da tasan suna da kudin da zasu siya wanda yafi wannan amma ihsani yana da dad'i.


Aikuma hajia halimat taji dadin kyautar dan har Abdul takira take fad'a masa, sosai yayi farin ciki k'imarta ya sake daduwa a idanunsa (mata mu kula yin kyauta ma 'yan uwan miji yana dada miki kima a idanun mijinki, koda su d'in basa kaunar ki to karki ce baza kiyi musu komai ba kiyi musu gwargwadon iyawan ki ALLAh yasa mu dace)

Da daddare da A.A zai dawo ya siyo ma salma waya ki'ran iphone 7. sosai salma tayi farin ciki,tayi masa godia sannan tace ya bata numbern hajia tana son zasu dinga gaisawa, yaji dad'i kuwa ganin yanda take nuna tana son iyayen sa.

Atak'aice haka suka cinye kwana 7 ba abinda ya tab'a shiga tsakanin su na auratayya, sannan kullum se sun tashi cikin dare sunyi nafila da karatun alqur'ani da safe ta bashi littafi yayi azkar ga kuma zob'o da take hada masa da ganyen magarya da ayoyin shifa dan karya sihiri.


Acikin kwana 7 dinnan kusan duk wani sihiri dake jikinsa ya karye, har tunani yakeyi ta yanda ya auri humaira.

Yanzu kullum seyaje ya gaishe da iyayensa ga wata irin shak'uwa da ta shiga tsakanin su, sosai yake jinta aransa. Iyayensa sunyi farin cikin ganin yaron su ya dawo gare su lallai sun yarda salma ALKHAIRI ce a gare su.


🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:36PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
ZAB'IN MAHAIFINA
🌳🌳🌳🌳🌳

Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)

🌐HAJOW πŸ“πŸŒ

πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐

Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI

Page 25

A gidan su salma washegarin da akayi yini 'yan uwa suka shirya domin suje ganin dakin amarya saboda aranar kowa zai watse. Har zasu tafi mallam amadi ya shigo yake tambayar su ina zasu je? suka fada masa, masifa yahau yi yace ba wacce zataje kalan suje su bata musu gida, haka kowa ya tattara ya kama gabansd.


Wata rana suna zaune a majalisan su na dattawa, wani daga cikinsu yake bada labari "wato wani mutumi ne ya aurawa 'yarsa wani mekudi, wai shi a zaton sa idan 'yar ta auri Alhajin shima za'a bashi dukiya ne, ashe be sani ba Alhajin d'an yankan kai ne, tunda ya auri yarinyar aka kaita gidansa har yau har gobe ba'a sake ganin suba" ansha zuwa gidan da aka kai yarinyar se a tarar da bakowa agidan.

kuma daman beyi bincike ba ya aura mata mutumin, besan kowa yana shi ba, kudi kawai ya zuba mishi. Tunda mallam Amadi yaji wannan labarin hankalinsa ya tashi, ya shiga damuwa sosai, fatansa kawai Allah yasa kar wani abu ya samu salma, duk da yasan mijinta baida wani mugun hali amma yasan kishiyarta muguwar mace ce.


Da sallama ya shigo gidan inna saude tana zaune akan taburma tana ninke kayanta data wanke,ta amsa masa sallamar tare dayi masa sannu da dawowa.

A kusa da ita ya zauna ya kalleta yace nikam saude kinajin labarin halin da salma take ciki kuma? kallon shi inna saude tayi cikin jin haushin tambayar tace " mallam ai kai zan tambaya, tunda 'yarka ce, kuma kaika aurar da ita, nida ko gidanta bansani ba zaka zo kana tambaya na?

shiru yayi cikin nadamar abinda ya aikata, kasa daurewa yayi ya jefo mata wata tambayar "ina ce su hadiza sunje sunga gidan? me zasuje suyi mallam? ko ka manta bakayi mata komai bane? duk da yaron yace baya bukatar akaita da komai amma ai ya kamata ko gara kayi mata. data maka magana kace ko cokali baza ka saya ba. inda kasaya ne to da wanda suka kai se susan gidan.

kuma ai kasan ba gidanta aka fara kaita ba gidansu mijin aka kaita se washegari ta wuce gidanta.kuma a washegarin 'yan uwa aka shirya za'aje kace baza'aje ba ko ka manta?

dan haka nina riga na fidda tunanin salma a raina tunda ta riga ta shiga wannan gidan.

tana gama magana ta tattara kayanta ta shige d'aki ta barshi a wajen cikin tsananin mamaki, dan be tab'a tunanin zata iya kallon idon shi ta fad'a masa wad'annan maganganun ba, lallai me hakuri be iya fushi.

tashi yayi ya bita cikin dakin ya nemi waje ya zauna sannan ya fara magana "saude kiyi hakuri nasan ban kyauta muku ba, amma ki dubi girman Allah ki fada min halin da salma take ciki"

hawayen da take b'oyewa ne suka zubo ta kalleshi tace "mallam kenan se yanzu ne ka damu da halin da salma take ciki? tunda salma ta girma ta mallaki hankalin kanta kake tsangwanar ta, duk da ita kadai muka haifa hakan besa ka kyautata mata ba a matsayinka na mahaifinta, duk da haka bata fasa yi maka biyayya ba.


A karshe ka aura mata mijin da matar sa tafi k'arfinsa duk dan saboda abin duniya. se yanzu da lokaci ya kure zaka zo kace a fada maka halin da take ciki to nima bansan halin datake ba, se kaje ka samu uban mijin ka tambaye shi.

Girgiza kai yayi yace tabbas nasan ni me lefine amma wallahi saude ki yarda nayi nadama dan Allah ki yafe min insha Allahu zan canja daga yanda kika sanni.

Mallam ni ai baki min komai ba saboda haka kama dena neman yafiyata, ta fad'a tana barin d'akin, dan idan taci gaba da zama tana iya yi mishi abinda bai tab'a zato ba.

。。。。。

Humaira tana zaune ta zuba tagumi ta rasa abinda yake yi mata dadi, tanaji tana gani komai ya kwab'e mata, gashi lina cta gari tayi tafiya bare susan yanda zasu b'ullowa al'amarin.


Amma tunda gobe zata karbi girki zatasan yanda zatayi ta zubama yarinyar nan maganin taci ta mutu kowa ma ya huta.

Washe gari da safe bayan sunyi wanka sun shirya A.A yace yau baza'a bani breakfast bane? kayi hakuri yau ba girki na bane aunty humaira ce zatayi maka breakfast.

b'ata fuska yayi yace ashe yau kina son natafi office da yunwa kenan?? ita da take bacci yaushe lokacin tashinta yayi bare har ta bani breakfast? ki tashi kawai ki nema min abinda zanci dan lokaci na k'urema ya fada yana kallon agogon dake daure a hannun shi.

mik'ewa tayi ta shiga kitchen ta hada mishi tea ta soya mishi kwai ta dauro akan taray. akan centre table d'in dake tsakiyar falonta ta daura mishi. Bayan ya kammala ta raka shi zuwa bakin k'ofar falon ta mik'a mishi briefcase din, kallonta yayi yace yau kuma anan zaki barni?

yaufa ba girki na bane, dukda bata tashi ba amma ya kamata na kiyaye wani abin saboda gudun shiga hak'k'i dan ko mani akayima haka bazanji dad'i ba. sannan ya ba lallai ne akawo maka abinci ba saboda bani ce da girki ba.


karb'an briefcase d'in kawai yayi ya juya ya tafi, tana mishi a dawo lapia beko kulata ba.


🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:37PM, 2/7/2018] β€ͺ+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
ZAB'IN MAHAIFINA
🌳🌳🌳🌳🌳

Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)

🌐HAJOW πŸ“πŸŒ

πŸŒπŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾✍🏾✍🏾🌐

Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI

Page 26

Yana zuwa office ya kira mahaifiyar sa akan ta aiko masa da abinci da rana,

" ina matan naka suke da zan aiko maka abinci daga nan?" ta tambaya

"Momy yau fa girkin humaira ne"


"Ita 'yar mulkin naka bazata iya aikowa da abincin ba kenan ko?"


to momy yaushe ta tashi ma bare tayi wani girki ita da take tashi 11:00am ko breakfast batayi ba alokacin bare ayi maganan na rana.

"Allah ya kyauta"

tace sannan ta kashe wayarta.

karfe d'aya ta aiko driver ya kawo masa abincin.


Da rana humaira tasa blessing tayi jallop din shinka fa da wake da nama, ta aikawa salma dashi.


Zuciya d'aya salma ta karb'a, har zata faraci sega me aikinta ta shigo.

Tsugunawa tayi a gnfenta tace

"sannu aunty"


Kallonta salma tayi ta amsa, sannan tace lapia dai jamila??ko kina bukatar wani abu ne?


sunkuyar dakai jamila tayi kafin tace "aunty daman akwai maganar da nake son zan fada miki amma dan Allah kar kice a bakina kikajiπŸ™πŸ™"


"Ina sauraronki" salma ta fad'a.

dan Allah Aunty kar kici abincin nan, yanzu blessing take fada min wai tazo shiga falon taga hajia tana zuba wani abu a cikin abincin.

kuma tace ta tabajintana waya akan zata zuba miki magani abinci kici ki mutu.

"Nagode!jamila" amma dan ALLAh banason naji maganar nan a bakin kowa."

"to aunty" jamila ta amsa

tashi salma tayi ta dauko bakin leda ta juye abincin aciki ta mika mata

"gashi kije ki saka a cikin shara amma ki boye kar wani ya gani"

karba jamila tayi ta saka a cikin hijabinta ta fita.

Ajiyar zuciya salma ta sauke, tanayi ma Allah godia daya kubutar da ita daga fadawa kaidin humaira.

karfe 8:00pm abdul ya shigo gidan, be tarar dasu a falon ba kamar yanda suka saba zama.

part din salma ya fara shiga, a kwance ya sameta tana chatting, tun randa ya bata wayar tayi dawlooding whatsapp da facebook.

ba wasu mutane bane a contact dinta daga numbern surukanta sena kannen shi sannan nashi.

wani group ta shiga a whatsap .

"UMMU AFFAN NOVELS"

wanda hafsat kanwar shi tayi adding dinta a ciki.

gaskiya ana turo littafai masu dadi da ma'ana.

yanzu ma wani littafi take karanta KAINUWA (dashen Allah) na ayusha littafin yayi mata dadi sosai.

sallama yayi ya shigo falon, ajiye wayar tayi ta mike ka karbi jakar hannu shi, tana mishi barka da dawowa.

waje ya nema ya zauna,yana cewa

"wash!gaskia na gaji da yawa, hada min ruwan wanka nayi, Ko gajiyan zai ragu.

kusa dashi ta zauna kamar zata shige jikinsa tace "wannan ai aikin aunty humaira ne yau"

jawota yayi jikinsa yana shakar daddad'an kamshinta, se da ya gaji dan kansa sannan ya saketa ya dauki briefcase dinsa ya fita ya nufi part din humaira.

kuyi hakuri da wannan wallahi se da nayi ya goge.


🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳






7 / 7