Author : ESHAAT SMILER Category : Romantic Hausa Novels
se dai yaje a b'oye ba tare data sani ba.
Kuma indai zasu bashi umurni to seya aikata ko ita bata isa hanashi yi ba.
Amma ta mallake shi yanda take so, duk abinda taga dama shi za'ayi.
mik'ewa hajia tayi ta ruk'o hannun salma tace toni zan tafi. Mik'ewa A.A yayi dan ya rakata amma ta dakatar dashi,kayi zamanka nagode. Jiki a sanyaye ya koma ya zauna ALLAh yasa badai fushi Momynsa tayi dashi ba.
Har takai bakin k'ofa zata fita ta juyo tace maganar malam musa me gadi ban yarda a canja shi ba. Da hanzari ya amsa mata, duk miskilancin A.A baya yima iyayenshi saboda baya k'aunar b'acin ransu. Aikuwa nan humaira ta dad'a cika dan tasan bata isa tayi masa komai ba tunda wannan tsohuwar ta hana.
Fuuuu... ta mik'e ta shige daki cikin tsanin b'acin rai. da kallo kawai ya bita ba tare da yace mata komai ba.
Kai aradu nagaji wanga typing ya ban wuya, har ya cinye min chaji kowa wamin karo-karo.
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:36PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
ZAB'IN MAHAIFINA
π³π³π³π³π³
Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)
πHAJOW ππ
ππ©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎβπΎβπΎπ
Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI
Page 19
Wannan page d'in nakine takwarata Sadiya Abubakar ina yinki irin sosai d'innan ALLAh ya barmu tare k'awataβ€πβ£ππ
Suna isa bakin mota hajiya ta mik'ama salma emvelop d'in da Alh. Abdul-razak ya bata, sannan tace ki dinga yin girkin ki da kanki karki yadda akawo miki wani abu kici,zuwa gobe zan turo miki da yarinya wanda zata rik'a yi miki aiki, Cikin girmamawa salma ta amsa sukayi sallama hajia halimat ta shiga mota driver yaja suka tafi,salma kuma ta juya ta shiga ciki tana shiga ta wuce d'akinta ko kallon A.A dake zaune a falon batayi ba.
Ita kuma humaira tana shiga d'akinta ta fashe da kuka tana tsinema hajia halimat. "Wlh bazai tab'a yuwuwa ba koda zanyi yawo tsirara se yarinyarnan tabar gidannan, wata zuciyar tace kin manta tace idan har ya saketa kema zakibar gidan. tsaki tayi tace aikuwa da alama ajalinta yazo dan kuwa bazan tab'a bari ta zauna min a cikin gidana ba. (kuji fa jama'a kamar ita ta gina gidan da kud'intaπππ)
Waya ta d'auko tayi dialing wani number, can aka d'auka hellow humy kina lafiya? aka fad'a daga d'aya b'angaren, ina fa lafiya lina wancan shegiyar tsohuwan yanzunnan tabar gidannan, wata tsohuwa? lina ta tambaya.
Mahaifiyar Abdul mana, to me tazoyi? lina ta sake tambaya. Waita kawo masa amarya, wani uban ashar lina ta sake sannan tace ki jirani ganinan zuwa wallahi seta raina kanta. To kiyi sauri dan ALLAh humaira tace sannan ta kashe wayarta.
ta nemi bakin gado ta zauna, bata dad'e dazama ba lina ta shigo cikin d'amammun kaya riga da wando, kanta ba ko d'an kwali se wani siririn gyale data yafa a kafad'a.
tana shiga suka rungume juna, ke ina amaryan take? lina ta tambaya, tana d'akinta, to tashi muje muci uwarta, zatasan ta shigo gidan bala'i. Basu sami A.A a falon ba da alama ya bar gidan.
ko neman izini basuyi ba suka cusa kai cikin falon salma, salma tana zaune ta sake wanka ta had'e cikin riga da skert na atamfa, d'inkin ya kamata ya fiddo da shape d'inta, kanta ba d'an kwali se gashinta da tayi parking wanda yasha gyara ya sauk'o mata har gadon bayanta.
Plat ne a hannunta tana cin abinci da alama girki tayi. ba humaira ba hatta da lina se da ta raina kwalliyarta dan humaira irin siraran matannan ne wanda basu da k'iba ko kad'an se dai kyau a fuska, dama dama lina tana k'iba se dai bata da shape ko kad'an, sukub take kamar namiji.
kallo d'aya tayi musu ta d'auke kanta kamar bata san da mutane a wajenba. Kallon juna su humaira sukayi da alama wannan ba kamar wanda aka saba kawo musu bane.
Lina ce tayi k'arfin halin zuwa ta tsaya akan salma tace ke inason yanzu-yanzu ki tattara kayanki kibar gidannan, in har kina son tsira da ranki da kuma lafiyar ki.
Kallonta salma tayi up and dawn sannan tace a matsayinki nawa kike bani umurni? mijina ko iyayena ne kad'ai suke da ikon bani umurni nabi amma ba ke ba.
ke barima kiji ko megidannan duk da zaman shi nakeyi to shima be isa yace nabar gidannan ba.
shi me gidan be fad'a miki cewa nice nake da iko da gidan da abinda yake cikinta ba? ko shi a k'ark'ashin ikona yake kinga kuwa se yanda nayi dashi, humaira ta fad'a tana k'arasowa cikin falon.
Murmushi salma tayi tace idan su kina iko dasu to nikam baki isa kiyi iko dani ba wallahi dan nafi k'arfinki.
Nunata humaira tayi da yatsa tace wallahi ke baki isa kizo har gidana kice zaki yimin rashin kunya ba, kodan kinga tun farko na k'yaleki banyi maganin ki ba, to ki kiyaye harshen ki tun kafin ki had'u da mummunan sakamako.
Mik'ewa salma tayi tace don't point your pinger at me or else... "me zaki iyayi? humaira ta katseta tana huci"
Duk randa kika sake nuna min yatsa wallahi sena karyashi, kuma da kike cewa ina miki rashin kunya ai kece baki rik'e girman ki ba. kuma baki isa kiyimin komaiba se abinda ALLAh ya k'addaro min. sannan ta nuna musu kofa, ku fice min daga falo yanzu ko kuma na nuna miki abinda zan'iyayi yanzu.
Tsaki humaira tayi tace wallahi salma se naga bayanki ki rubuta ki ajiye dan ni kad'ai akayi Abdul kuma dani kad'ai zeyi tarayya babu wata 'ya macen da ta isa ta zauna a matsayin matar sa bayan ni, sannan ta ruk'o hannun lina wanda ta kasa magana suka bar falon dan taga alamar salma bata da mutunci.
suna fita salma taje tasama kofarta key ta dawo ta zauna taci gaba dacin abincinta,tana mamakin kanta yanda ta iya sa'insa da humaira ba tare da taji tsoronta ba abinda bata tab'ayi ba. lallai idan kaga mutum baya magana to ba'a tab'o shi bane ta fad'a a fili.
Daki suka koma lina ta kalli humaira tace lallai humy wallahi sekin tashi tsaye,dan naga yarinyar nan ba kamar wad'ancan bane dan bata da tsoro da alama ta taki wani abu.
Ajiyar zuciya humaira tayi, tace lina banci ta zama ba, yanzu zamu tafi wajen boka me gani har hanji, idan nayi sake yarinyar nan zata rusamin budget, kin dai san dalilin da yasa na auri Abdul bawai dan tsananin k'aunar sa bane kawai dan dukiyar sa ce.Wannan ne dalilin da yasa nake zubar da ciki idan na samu, k'arshe zuwa nayi aka fitar da mahaifar saboda bana buk'atar haihuwa balle idan ya mutu d'an ya gajeshi.
shiyasa nake son nasashi ya rubuta sunana a dukkan kadarorinsa kafin na aikashi zuwa lahira.
ihu lina tasa irin nasu na 'yan bariki tace shiyasa kike burgeni k'awata, dan bakya wasa da hanyar samun kud'i. yanzu ki tashi mu tafi wajen bokannan dan kinsan masu iya magana sunce da zafl-zafi akan bugi k'arfe,kuma ba'a bori da sanyin jiki.
tashi humaira tayi ta d'auko gyalenta ta yafa ba wanda zai ganta yayi zaton matan aure ce. Wata benz arsh colour naga sun shiga, da k'arfi ta danna horn cikin hanzari me gadi yazo ya bud'e mata get da mugun gudu ta fita dan kad'an ya rage ta take masa k'afa, girgiza kai yayi yana yi masu fatan shiriya.
Jin fitan motane yasa salma ta fito ta kawowa me gadi sauran abincin data dafa, har k'asa mallam musa ya durk'usa yana yi mata godiya, dan tunda ya fara aiki a gidan ba'a tab'a bashi abinci ba se dai a kawo masa daga gida.
readers ina son na dena posting har sena gama typing nayi muku gaba d'aya amma menene ra'ayin ku???? ina jiran amsoshin ku.
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:36PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
ZAB'IN MAHAIFINA
π³π³π³π³π³
Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)
πHAJOW ππ
ππ©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎβπΎβπΎπ
Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI
Page 20
Wannan page d'in nakine ne my daughter(hapsert bnt hassan Ameen) kinfi kowa son novel d'innanπππ ina yinki irin sosai d'innanβ€
Wani k'ungurmin jeji naga humaira sun shiga, ba gida ko daya a wajen, tun a bakin jejin suka ajiye motarsu, da k'afa suke takawa ga uban nisa. A can na hango wani bukka wanda shi kad'aine a wajen, suna k'arasawa sukaji an daka musu tsawa, saida suka firgita, karku yadda ku k'araso ku tsaya daga wajen da kuke, saboda sarkin aljanu da mutanensa suna zaune a wajen, meke tafe daku???
Cikin rawan murya humaira ta fara magana, dama akan maganar kishiyar da aka min ne. Me kike so ayi mata?? bokan ya tambayeta wanda basa ganin shi sai dai suji muryar sa. Ina so a bani maganin da zai zamo ajalinta. Bushewa yayi da dariya wanda saida jejin ya amsa, yace ke humaira lallai yanzu na tabbatar baki da iyami, tabbas irinku muke buk'ata. Amma zan fad'a miki gaskiya wannan yarinyar idan bakiyi da gaske ba ita ce silar tonuwar asirinki.
Aljanun mu baza su iya zuwa kusa da ita ba, saboda jikinta akwai tsari, kuma tana yawan addu'a bata zama babu alwala, aikinki akwai tsada.
Cikin sauri tace boka kasan kud'i ba matsalata ba ce,ko nawa ne zan biya. Zaki bada dubu d'ari biyar,aciki za'a siyama sarkin aljanu bak'ar saniya da bak'ar tinkiya, da bakin bunsuru da bakin zakara, za'a yanka mishi saboda jinin yake buk'ata.
Da hanzari humaira ta ciro kud'in ta ajiye a wajen. tana ajiyewa aka wurgo musu k'ullin magani. Ki d'auki wannan maganin kisa mata a abinci, ki tabbatar taci, dan iya abinda zamu iya yi miki kenan, danko kusa da ita bazamu iya zuwa ba, wannan ne temakon da zamu iya baki.
sunkuyawa humaira tayi ta d'auka, sannan suka fara tafiya da baya da baya, har saida suka dena hango bukkar tukunna suka juya, dan haka dokar bokan take.
K'arasawa sukayi wajen motar su suka shiga suka tafi. A hanya humaira ta kalli lina tace, nifa bansan ta yaya zan saka mata maganin nan a cikin abinci ba, dan nasan ko na bata abu baci zatayi ba.
Amma humy har yanzu kwakwalwar ki bata ja wallahi. ina ce mijin a hannun ki yake? kuma kinsan se abinda kika tsara masa yake yi, gyad'a kai humaira tayi.
to yanzuma haka zakiyi, kawo kunnen ki kiji,gani nayi lina ta fad'a mata wani magana sukayi dariya suka tafa, ko me tace mata oho.
Bayan sun koma gida suka shige bedroom suka rufo k'ofar, direct kan bed suka nufa tun kafin su k'arasa naga sun fara shafa junansu.
A'UZUBILLAHI. Abinda na furta kenan, dama su 'yan lesbian ne? A guje na juya na bar musu d'akin ina nema musu shiriya,
Bayan sun gama watsewar su, lina ta fito ta tafi tana jaddadawa humaira akan tasan yanda zatayi ta bata maganin taci
MENENE DANGANTAKAR LINA DA HUMAIRA???
Humaira sun had'u da lina ne a wajen party, asalin lina bayarbiya ce amma ba musulma ba ce.
tun tashin lina yarinya ce hatsabibiya tun wana k'aramar ta take bin maza, data girma ta zama budurwa ne idanunta suka dad'a bud'ewa, daga k'arshe tattarawa tayi tabar garinsu OYO ta biyo saurayinta suka zo BAUCHI.
Tunda tazo ta bud'e bariki kala-kala ba iya bin maza ta tsaya ba, hatta hajiyoyi d'aukanta sukeyi
sun had'u da humaira ne a wajen birthday partyn da saurayinta ya had'a mata, tun daga lokacin suka k'ulla k'awance, ita ta koyama humaira lesbian da bin bokaye,(ALLAh ka had'amu da k'awaye nagari AMEENππ)
Da daddare bayan A.A ya dawo yana zaune a falo, humaira ta fito cikin shigar riga da skert english wears, sun kamata se dai ko kadan basuyi mata kyauba, kasancewarta siririyar mace da bata da shape ko kad'an, se tayi kamar an d'aura wa muciya zani.ππ
Kusa dashi tazo ta zauna tana mishi barka da dawowa kamar ba abinda ya faru(duk plan d'in lina ne). Ya amsa mata cikin jin dad'i, saboda shima fargaba ce ta hana shi dawowa gidan tun da ya fita da safe.
tace mishi su tashi suje suci abinci, wanda me aikinta blessing ta girka ta jera akan dining table. mik'ewa yayi suka nufi kan dining d'in, bayan sun kammala cin abincin suka dawo falon suka ci gaba da hiransu suna kallo kamar yanda suka saba.
Humaira ne ta dubi A.A tace babyna daman akwai maganar da nake son muyi dakai, ina jinki ya amsa mata ba tare daya kalle ta ba.('yan mulkin sun juyo kanta kenan).
Naga har yanzu baka kirata ka fada mata yanda tsarin gidan nan yake ba. Kallonta yayi sannan yace wani tsari kenan??? had'e rai tayi tace ina so ne ka fad'a mata duk wacce take da girki ta fito a dinga cin abinci tare da ita, ban yarda kowa ta dinga yin nata ba.
kauda kanshi yayi cikin jinkai yace kije ki kirata, tashi humaira tayi ta nufi part d'in salma.
k'wank'wasa k'ofar tayi, salma dake zaune tana kallon tashar Arewa 24 ta taso ta bud'e k'ofar, tana ganin humaira ta b'ata fuska tace lafiya?
murmushin mugunta humaira tayi, tace "kizo mijina yana kiranki" ta juya tayi tafiyarta. d'an tsaki salma taja tace da wayace ba mijinki bane? (ina fatan salma ba haushi kikaji baππ) juyawa tayi ta Koma cikin daki ta dad'a gyara fuskarta ta fesa turare me dad'in k'amshi, ko hijab bata d'auka ba ta nufi falon da suke.
Tunda ta doso wajen yake binta da kallo, kasancewar kayan baccine a jikinta riga da wando cotton, sun kamata tsam rigan me hannun shimi ne, wandon a iya guiwa ya tsaya mata, ta saka hulan turban kalan kayan pink.
tana zuwa ta nemi waje ta zauna ba tare data ce musu komai ba, humaira da tun fitowar salma tayi dana sanin kiranta da tace ayi ganin irin kallon da A.A yake mata. Gashi ba daman tayi magana kar plan d'inta yargajeπ€£π€£π€£π€£
Ta wurga ma salma harara sannan ta juya ta kalli A.A daya maida hankalinsa ga kallon t.v ta daure tace "babyna gatanan ta fito ka fad'a mata" beko kalle ta ba yace ki fad'a mata mana tunda tsarinki ne hakan.
Da sauri ta dube shi jin tana mishi magana yana bata amsa wani iri. wai meke faruwa ne kodai asirin da namishi ya fara warwarewa ne? daga zuwan ta komai ya fara warware wa, aikuwa zanyi saurin aikata lahira tun kafin komai ya kmab'e min, tayi maganar cikin zuciyarta.
duban salma tayi dakanta yake kallon wani gefe na falon tace "to amarya dama maganar girki ne, kinsan hajiya tace yayi miki kwana 7 d'inki kafin araba kwana bibbiyu. saboda haka yanzu duk wacce take da girki zata fito a had'u a dinga cin abinci tare. Akwai wacce take yi mana girki, ina fatan ba matsala?" ta k'arasa tana murmushin yak'e
mamaki ne ya kama salma,tabbas akwai abinda take shiryawa dan tasan ruma baya tsami banza, ita zata nuna ma kirsa? wato dan tana gaban mijinta shine zata nuna ita na ALLAh ne, aikuma zata nuna mata itama macece tana da irin nata salon.
Murmushi salma tayi tace "haba Aunty ai duk abinda kika yanke dai-dai ne, amma ni inso samune nafison na dinga yima mijina abinci, dan banason masu aiki su dinga yima mijina hidima.....
Tun kan salma ta k'arasa humaira tayi saurin katseta, ganin tana neman wargaza mata plan. tace"haba k'anwata kamar ke kina auren Alh. A.A me dala ace kina girki da kanki. ai wannan abin kunya ne a gare mu.
girgiza kai salma tayi tace ba abin kunya bane Aunty tunda aikin ladane kuma wa mijina zan yima, ni inaga ai ba lefi aciki.
A.A da yake kallon news a t.v amma hankalinsa yana wajensu,yana jin maganganun da sukeyi, ya juyo ya kalli humaira yace "tunda tace zata iya ki rabu da ita mana, kun cika