Author : Sumayya Abdulkadir Takori Category : New Hausa Novels 2026
daga idanunta, ta karasa ta rungume ta na mintuna, sannan ta kamo hannunta suka fito. Karo na biyu a tsayin zamanta tare da su, da ta ga ya kamata ta kira Ma'aroufJi-kas a waya.Ma’arouf din da a baya take ganin bazata taba iya kira a waya ba. To komai dalili yakeyi, wannan dalilin yayi dalili.
*****
Yana fadar shugaban kasa tare da sauran gwamnonin Najeriya gaba daya na Kudu, na yamma, na gabas da na Arewa, suna tattaunawa ne a kan yadda za a habaka harkar noma a Nigeria da yadda za’a magance hauhawar farashin man fetur nababugaira babu dalili da ake fama dashi. Kiran Amina ya shigo wayarsa da ke aljihu, wadda ya manta bai kashe ba kafin shiga dakin taron.
"Ameena's Doc" ke yawo a kan fuskar wayar, in bai manta ba, tsayin watanni goma sha daya da suka yi tare wannan ne karo na biyu kacal da ta taba kiransa a waya. It must be important.
Wani nishadina bazata ya ziyarci zuciyarsa da shi kansa ya ba shi mamaki. Murmushin fuskarsa ya fadada. Idan akwai mai kallon sa zai gane (Ma’arouf is in love). Soyayyar da shi kansa har yanzu bai gama yardarwa kansa ita ba.Tsam ya mike ya fito daga dakin taron zuwa harabarsa, ya amsa kiran da dukkan kulawar da ya mallaka.
"Dr. Ameena, ya aka yi ne?" Ya fada cikin taushin murya, da kokarin boye eager din sa.
Amina bakinta har rawa yake, ga in'ina ta kasa fadin takamaiman dalilin kiranta. Dadi da farin ciki da suna kisa, da yau sun kashe ta. Saidai Ma’arouf yazo ya tadda gawarta.
"Um-um-um Ameenah ce......"
"Me ya samu Ameenar???"
Ya fada cikin jin faduwar gaba.
"In ba’a nesa kake ba, nace umm-um idan bakayi nisa ba, ka zo ka gani da kanka zai fi. Amma fa alkhairi ne, mu wuni lafiya". Ta kashe wayarta.
Ma'arouf Ji-kas ya dade rike da wayar a hannunsa, yana kallon ‘screen’ dinta har hasken ta ya mutu, ya kasa tantance yanayin da ke cikin sautinta, farin ciki ne ko tashin hankali? Ya ji 'yar damuwa ta ziyarce shi. A sanyaye ya juya ya koma dakin taron.
Haka aka karasa taron da shi a daddafe ba tare da ya kara fahimtar abin da ake tattaunawa ba.
Bai kwana ba kamar yadda ya tsara, a daren ya nemi jirgi ya taho Bauchi.
Amina da Ameena, sun yi wankan barcinsu. Amina ta sanya wa 'yar tata kayan barci, ita kuma ta nemi doguwar rigar atamfa da kallabinta ta sanya suka bi gado suka kwanta, suka rufa da bargo bayan Amina ta gama ba ta magungunanta. Carbi ne a hannunta tana ja, idonta a lumshe. amma ba ta kai ga yin barcin ba.
Knocking aka yi, ta tashi zaune ta yi lullubi, sannan ta bada izinin shigowa. Ya shigo cikin jamfa da wando na shadda 'Excelsior' ruwan makuba, babbar rigar da ya cire rataye a kafadunsa, kansa babu hula kamar koyaushe ya shigo gida cirewa yake yi, ba ya tara sumaa kansa sam, yanada yawan saisaye.
Akwai 'yar damuwa a kan fuskarsa na rashin sanin me zai tarar, duk da tace alkhairi ne, amma ya yi kokari kwarai wajen boye ta. Daga bakin kofar ya tsaya, idonsa ya sauka cikin na Dr. Amina.
"Me ya faru?" Ya tambaya cikin tsaka-tsakin yanayi. Babu fargaba kuma babu tashin hankali.
Kawai sai Amina ta dan girgiza Ameena karama. Yarinyar ta bude ido nan da nan, dama barcin nata ba wani nisa ya yi ba. Ta nuna mata bakin kofa.
"Je ki Daddy ya dawo".
Ta kalli Babanta, sai ta tsallako daga gadon da gudu, ta nufe shi ta rungume.
"Daddy yau ka ga ina takawa da kafata, babu karfe".
Ma'arouf ya tsaya standstill, ya kasa ko da motsi. Domin bai amince idonsa biyu ba, ya fi gasgata mafarki yake yi, ire-iren mafarkansa a dan tsukin, Ameena rungume ta ke da kafafunshi tana ta ba shi labarai. Yawanci dai duk na abubuwan da Auntynta ta yi mata ne, wanda ke sa ta farin ciki, irin su danwake, wainar fulawa, kai ta bakin ruwa a wheel-chair da sauransu.
Lokaci ya ja, in mafarki ne ya kamata zuwa yanzu a ce ya farka, amma shiru! Don haka ya sanya hannuwa a kan 'yar tasa yana shafawa a hankali. Daga bisani ya rage tsawo, ya zama daidai tsawonta ya rungume ta.
Sunkuyar da kai ya yi ba tare da ya saki Ameena ba, sai kuma ga hawaye suna disa dis-dis a bayan Ameenar. Ya zarce da fuskantar alkibla ya yi sujjadah. Ameenah karama da ta ga ya dago daga sujjadar, sai ta kai 'yan kananan yatsunta tana share masa hawaye, tana tambayarsa.
"Daddy me ye ka ke kuka? Daddy na warke fa".
Ya tsane hawayensa da hankicinsada ya zaro daga aljihunsa, ya yi mata murmushi. Ya rike dukkan hannayenta biyu cikin nasa,
"kukan farin ciki nake yi Ameena, ko ba ki ga kafafunki sun warke ba? Da taimakon Allah da na Dr. Amina?".
Ameena ta dubi kafafun nata, "Ai kuwa, tun dazu na watsar da karafan Daddy, na ce Aunty ta yi maka waya ta gaya maka, ta ce za ka zo, Daddy na warke".
"Ce ne alhamdulillahi Ameena, mun gode wa Allah, mun kuma gode wa Dr. Amina".
****
Kwana uku bayan nan Dr. Amina ta soma harhada tarkacenta don barin gidan gwamna Ji-kas, bayan ta kara tabbatarwa a lafiyar Ameena karama babu sauran kalubale.
Sai dai kuma abin da ya ba ta mamaki, duk yadda ta kai ga murnar komawa gaban Goggonta abin da ta fi so a rayuwarta, jikinta a matukar sanyaye yake. Ta fara samun kanta cikin wannan sanyin jikin bayan murnar warkewar Ameena, ga wata irin damuwa da zuciyarta ta shiga in ta tuna lokacin rabuwa ya zo da Ameena da BABAN TA.
Baban Amina kuma???
Wata zuciyar ta tambaye ta, bata amsawa zuciyar ba, illa kawai ta san tayiwani mugun sabo da shi a tsayin shekara guda ba kadan da suka yi tare. Ma'arouf Ji-kas, ya samu wani irin muhalli a zuciyarta da ba za ta iya fasalta shi ba.
Ta dade tana nazarin halaye irin nasa masu wuyar samu a wannan zamanin. Ga nagarta, ga tsare mutuncin kai dana duk wanda ke karkashinsa, da tsare nasa mutuncin a kan-kansa. Shugaba ne abin koyi, wanda kowane talaka ya bude baki a jihar Bauchi, alheri yake fada a kansa. Su da ke cikin gidansa ma, sun shaida hakan; Aadali ne. Ma'arouf ya tsaya a zuciya da ruhinta da matsayin da ba ta san wane iri ba ne. Ta dai san akwai shakuwa. Tana jin rabuwar nan har cikin bargonta ba zuciyarta kadai ba.
A hankali ta ke ciro kayanta daya bayan daya daga wardrove tana ninkewa tana jefawa a 'trolley' dinta, Ameena na gefenta tana cin abinci da kanta, ta dube ta ta ce,
"Aunty yau ba juma'ah ba ce, naga kina hada kaya, ina za ki je? Don Allah ki tafi da ni".
Amina ta dube ta idonta cike taf! Da kwallah. Ta kasa ce mata komai, ta dau diyar Gwamna ta kai gidansu a wane dalili? Yaushe ta kai wannan matsayin? Amma ko da zai ba ta da ya yi mata babban adalci. Cikin ire-irenadalcinsa da basa karewa agareta. Da duk wannan damuwar kashi hamsin cikin dari ta kama gabanta.
Tana tare da jinin Ji-kas, ai kamar Ji-kas ne suka ci gaba da rayuwa tare. Watakila watarana har ta ganshi a dalilin diyarsa.
A'ah! Wai me ke damuna ne ni Amina Mas'ud?" Ta tambayi kanta,
"Ma’arouf Ji-qas!”.
Zuciyarta ta bata amsa. Ba tun yau ba sunan nan yake yi mata wani irin nauyi azuciya da kwakwalwar ta. Tun sanda ta fara jin sunan,ba ta iya fade a bisa dalilin da bata sani ba, saidai tafi danganta hakan da girmamawa.
Amma a yau ta fahimci bayan girmamawa, akwai wani kebantaccen al'amari da zuciyarta ke lullube dashiakan wannan bawan Allah, mai girma da tasirin da ya bi ya mamaye zuciyarta, wanda yasa sunan nasa yi mata nauyi a harshe da zuciya. Wasu dumammun hawaye suka ziraro daga idanunta wanda ta tabbatar na kewa da sabo ne. Wanda tasan zasu cigaba da gudana har karshen rayuwarta.
Ta daura hannu a kan Ameena tana shafawa a hankali. Daga bisani ta ture akwatin gefe ta rungume ta, kuka sosai ya kwace mata.
An yi (knocking) har sau biyu Ameena da Ameena ba su ji ba, dukkanninsu kuka kawai suke yi. Ameena Ma'arouf ta gane Antinta barinta za ta yi, tunda ta warke, in tayi duba da yadda tayi parking komai nata, ita kuma ba za ta iya zama a gidannan babu Antinta ba.
Cikin kuka ta ke fadin, “Aunty ni binki zan yi, wallahi ba zan zauna da Anty Laila ba!".
Amina ta dago fuskarta jike da hawaye, ta soma yiwa yarinyar magana cikin lallashi.
"Cool down Ameena, da Daddy za ki zauna ai ba da Anty Laila ba...".
"Kullum ba ya nan, Aunty ni ma ba zan zauna ba.......". Sai kuka.
Amina ta rasa abin da za ta ce mata, sai ta biye mata suka dunkule wuri guda suna ta rera abinsu. Sabo turken wawa!!!
Alamu Dr. Amina ta ji na an zauna a gefensu. Ta yi saurin bude ido, ta juya inda ta ji alamun zaman mutum din da kamshin turarensa na koyaushe ya gaya mata MA'AROUF JI-KAS ne.
Hadiye kukan ta yi baki dayansa ta saki Ameena ta ba shi baya. Bata so ya ga kukan ta ba, bata so ya ga hawaye a idonta ba kada ya yi zargin tana kuka ne don za ta bar Government House.
"Kukan naku ya yi yawa...".
Ya fada a hankali.
Ba ta ce komai ba, ya koma kan diyarsa.
"Kukan me ki ke yi haka Ameena?"
Ta share hawayenta da tafukanta biyu, kafin cikin shessheka ta ce,
"Aunty ce take hada kaya za ta koma gida yau, wai saboda na warke. Daddy ni ma ba zan zauna ba. Aunty zan bi Daddy......".
Ya janyo ta jikinsa, ya aza ta gefen kafadarsa ta dama yana lallashinta, "Ameena makaranta zan sanya ki, wadda ake kwana acan. Dr. Amina ta gama aikinki za ta koma asibiti, tacigaba da taimakawa wasu marasa lafiyan, za ta yi aure ta haifa maki kanne. Ba kya son wadannan ci gaban ga Auntyn taki?"
Ta yi sheshsheka.
"Ina so Daddy. Amma ita zan bi, bana son makarantar kwanan......".
Rigima sosai Ameena ta ke yi, ta birkice musu, hatta Dr. Amina ta tsorata da borin da yarinyar ke yi, ta juyo ta kamo ta tana nata lallashin. Amma Ameena ta fizge ta tubure.
Ya kai hannu ya cire hular kansa da ya mayar ya ajiye a gefe, sai gumi yake duk da na'urar sanyaya daki da ke aiki babu kakkautawa. Idanunsa sun kada don ko fushin Ameena ba ya so balle kukanta, shi ma ya san zamanta da Laila ba zai yiwu ba, Ji-kas ne waje na farko da ya yi tunanin maida ita ta zauna wajen Hajiya.
Amma lokacin shiga makarantarta ya yi har ya wuce, ya kamata a ce tana Primary 1 amma ko nursery ba ta fara ba, shekarunta shidda. Abin da ba ta sani ba shi ne; ya fi ta jin tafiyar Dr. Amina.
Wata maceguda daya tal a duniya da ta shigo cikin rayuwarsa ta sauya ta. Rana daya ta yi fatali da bulullukan da ya gina rayuwarsa a kai na falsafar auren mace daya. Ya dade yana nazarin kansa akan Amina kafin wadannan bulullukan su ruguzo. Bai taba haduwa da mace mai kyawawan halayenta da nasibobinta ba, (he’s sorry to say) hatta A’ISHA.
Amina Mas'ud Shira, ta dade da canza wannan tunanin, ta kawo sabo fil ta gina, kullum kwana yake ya tashi da tunanin ta, ta inda zai tunkareta kai tsaye ya kasa. Ba wai ba zai iya gaya mata ya yanke shawarar hada rayuwa da ita ba ne, a'ah! Azancin fadar hakan ne babu, tunda ya gama cika duniya da furucinsa na mace daya ta ishe shi rayuwa, a talabijin ne, a jaridu ne, a radiyo ne da sauransu. Shi ya sa ba a so mutum ya ce ya tsara wa kansa rayuwa, muna namu Allah na naSa, rayuwarmu tun haihuwarmu tana rubuce ne a allon lauhul mahfuz. Ya nisa a hankali ya dan saci kallon Dr. Aminah, wadda ke faman fyatar hanci, ta ci kuka har ta gode Allah. Itada little din baisan wadda tafi tikar kuka ba.
"Ki daure ki kara kwana biyar, ban gama sallamarki ba ai, da bakina nace na sallameni ne iye da kike faman hada kaya?Kokari kike ki sallami kanki, albashin wannan watan bai shiga account dinki ba, tun jiya ban zauna ba balle inyi magana da Turaki, kaina yayi zafi ki barni in gama da abubuwan da ke gabana please".
Ta sunkuyar da kai, cikin ladabi ta soma magana da murya mai tsananin taushi. "I’m sorry You’re Excellency, na riga na yi waya da Goggo, na fadi mata yau zan koma, alreadynace ina hanya......".
Ya bude idanu sosai ya dube ta daga kankance su da yake yi a baya.
"Da iznin wa kika yi hakan? Ok. Sai ki fadi yadda za a yi da Ameenah......".
Da sauri ta dago ta dube shi, jin yadda yayi maganar fada-fada, bata ga laifi cikin abinda tayi ba, wannan wace irin tambaya ce? Shi ya kamata ya fadi wannan ai, ita ya za a yi ta sani, shi da 'yarsa?
Ya karanci abin da idanunta suka fadi, ya kara janyo Ameena jikinsa suka hadu suka narke mata,kallon ta yake straight into her eyes, wani ‘chemistry’ na fita daga narkakkun kwayan idanunsasuna shiga nata. Ita ta fara dauke idonta. Ilahirin jikinta babu inda baiyi la’asar ba, da karbar wani sabon yanayi da bata taba tsintar kanta a ciki ba.Data sake dagowa ta dubesusai suka bata tausayi. Ba ta san lokacin da ta bude baki ta yi magana ba.
"In za ka ba ni ina so, da ma Goggo ba ta da wadatar 'ya'ya. I'm sure za ta hada mu ta rike da amana".
Murmushi ya yi, domin ya lura iya gaskiyarta ta yi furucinta,cike da wauta da gabunta irin na ‘yan fari zai ce ko auta?.
"Ku kuma ‘physiotherapists’ haka ku ke zama gaban Goggonninku ba kwa ko tunanin yin aure? Al’adar ku ne yin hakan? Dube ki don Allah (close to 26)amma ko kunyar ambatar Goggo za ta rike kuba kya yi bayan ke ma kanki kin isa zama Goggon wasu irin su Ameenata. Amina Mas'ud Shira, in kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena. Ina nufin, ina sonki, ina kaunarki ina ra’ayin aurenki ba don Ameena ba, I just love you, so do I since..... Amma fa idan har ban yi miki tsufa ba.
Ina son dukkan halayenkiAmeena wadanda su suka ja ni ga kwadayin ki zamo cikin iyalina. Wannan sakona ne gare ki da Goggo, na ba ki kwana uku ki yi tunani dakyakkyawan nazari ki kuma yi shawara da Goggo. Ban yarda kiyi shawara da kowa ba sai ita. Kwana uku bai yi kadan ba? Dr. Amina ki ba ni amsa!".
Amina wadda ta mutu a zaune, tun daga farkon furucinsa, 'In kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena...' ta daskare ta kasa motsawa, sai dai abinda ya bata mamaki shi ne; jin can wani lungu na zuciyarta ya yi sanyi daga azabtar da yake yi na rabuwa da Ameena da Babanta,
"........ Amma fa in har ban yi miki tsufa ba...”.
Ta tuno jimlarsa ta gaba.
A wannan karon sai ta yi murmushi. A shekarun nasakwarai zai yi wa 'yammatayara irin masu shekara 18 da yawa tsufa, to ita mai 26 ta ce me? Kada dai sake-saken zuciyar nan yana nufin tuni zuciyarta ta aminta da soyayya da kaunar Baban Ameena?
Mutumin da duniya ke so, ba abin mamaki ba ne in itama ta so shi. Sai dai fa nata feelings din daban suke da na sauran al'umma irin su Yayanta Ilya, natanare extraordinary; ba na citizen ga leader dinsa bane, bata taba jin irinsu a kan kowa a duniya ba.
Kamar da ma suna ajiye a wani sako na zuciyarta ne, jira suke a sanya kara a zunguro su. Kuma yanzun aka zunguro sun. Kamar tun da ma can an halicce su a cikin kirjinta ne.
Ta yi nisa a duniyar sake-saken nan,