Author : Sumayya Abdulkadir Takori Category : New Hausa Novels 2026
Dariya ta ba shi sosai,
"Ai ni ne mamallakin zuciyar. Daure ki yi min fashin baki a kan kalaminki. Ina so in dora shi a sikeli ne in yi miki bayani a kansa, wanda zai kwantar da hankalinki".
Amina ta nisa,
"Your Excellency, ina nufin matsayinmu ba daya ba ne, ni ba 'yar kowa ba ce, ba jikar kowa ba. Kowa ya ji ka aure ni zai yi mamaki, zai fadi abin da ransa ke so.......".
Murmushi ya yi, "Na fahimce ki Amina. Amma ko kin san a da ni malamin makaranta ne? Makarantar sakandire? Mahaifina ma haka, babu irin fafutukar rayuwar da ban yi ba. Irin wadda baki taba zato ba. To cut it short, babu wanda aka haifa da arziki, kowa a duniya yake samun rabonsa. Saboda haka kada ki kara yin wannan tunanin ko makamancinsa. Ina sonki, ina kaunarki, na yi wa Goggo alkawarin zan rike ki da soyayya da amana har karshen rayuwarmu!".
Hawayen farin ciki suka zubo wa Amina, ta kai tafin hannunta ta share su.
"Na amince Baban Ameena, ko gobe ka kawo sadaki a daura mana aure".
Runtse idanunsa ya yi yana gode wa Allah cikin zuciyarsa. Bai yi zaton al’amarin zai zo masa haka da sauki ba, a yadda ya fahimta Amina bata san so ba, bata san komai da ya dangance shi ba,bata da hope akan shi, she’s naive,innocent, yayi zaton zai sha wahala kafin ya karkato da zuciyarta ya fahimtar da ita har kafin ta amince masa. A fili yace.
“lefe kuma fa? Ko shima an yafe mini? Kamar yadda aka ce da Turaki an yafe mini Tantabaru?”
Dariya ta subuce mata, ta kai tafin hannunta ta rufe fuskarta. Yana jiyo sautin dariyar data ke yin da ya jefa shi cikin wani matsanancin nishadi, zuciyarsa tayi kal itama tata zuciyar tayi fes! Duk damuwoyin dake cikin ranta sai ta nemesu ta rasa.
Wani irin yanayi take ji a kirjinta mai dadin da bazai misaltu ba.Ta tambayi to kanta, to ko wannan shine ‘Son’ data ki amincewa da gangan shine saida ta samu zuciyar Jikas din?
“Ke nake sauraro Amina, ko shima lefen baza’a karba ba sadaki kawai za’a karba?”.
Matsananciyar kunya tayi mata lullubi, amma jin ita yake sauraro kuma yana son jin ta bakinta akan abinda yace din sai ta daure ta magantu.
“If my humble consultant ya kawo ai bani da ikon mayarwa saboda karfin ikonsa a kaina. In yace bazan karba ba ma Dr. Turaki ya isa da ni”.
“Naga alama, shiyasa nima yake juya ni yadda ransa yake so don ya san ya isa da ‘yar tasa. Well, yanzu ki bani labari, hira nake so mu yi, irin wadda bamu taba yi ba”.
Murmushi tayi “Baban Ameena kenan. Akwai hirar da bamu taba yi bane tsayin shekara guda?”
Hirar ai kala-kala ce kuma kowacce da lokacin ta. We always talked on politics, bamu taba yin hira irin ta zuciya da zuciya ba, ban taba gaya miki wacece ke a zuciyar Ma’arouf ba. Girman matsayinki, da yadda kikayi overwhelming ruhi da zuciyar sa ba.
Ke ko dan ‘Ji-kas’ din da ake fada ma ba ki iya ba, you always call meBaban Ameena? This is not my name.It didn’t deserve you. Ki ba ni wani sunan ko ki kira ni da sunan da iyayena suka ba ni, zan fi son hakan, zan fi farin ciki da shi".
Ajiyar zuciya tayi, in wani ya gaya mata MA’AROUF JI-KAS yana magana haka, yanada baki har haka zata karyata, kalaman sa na kullum a kayyade suke koyaushe masu tarin ma’ana da hikima musamman a media, zababbu kuma dai-daiku kafin ya furta, yau gashi yanata zuba kamar ‘ya’yan kanya. Yau ta yarda ta amince soyayya gaskiya ce kuma ba wanda yake iya iko da kansa akanta, ta tabbata da Ma’arouf bai so ta har haka ba.
Murmushi tayi, wani irin tattausan murmushi da batasan daga ina ya fito ba tsakanin zuciya da ruhi. Ta san dai na tsananin jin dadin kalamansa ne. Duk da bata taba ko da gwada fadar sunan Ma’arouf Ji-kas ba, saboda nauyin da yake mata. A yau zuciyarta ta amince ta fada din,tunda ya ce fadar za ta sanya shi farin ciki. Ita kuma burinta kenan, ya kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarsa.
"Good night MA'AROUF". Ta fada da dan sauri, ta yi hanzarin kashe wayarta, ta tura kasan filo, ta bi ta karkashin filon ta tusa fuskarta suka buya tare. Kunyar Dr. Amina yawa ne da ita.
Murmushi ya yi da ya fahimci ta kashe wayarta, zuciyarsa ta nutsu sosai, sai godiyar Allah ne fal a cikinta. Ya amince daga kwanaki casa’in masu zuwa zai fara wata irin rayuwar aure mai nagarta kamar kowanne dan Adam, irin tashi ta farko da wadda bazai taba mantawa ba koma fiyeda ita, ba irin wadda yake yi da Laila Ji-kas ba.
Burin da yake dashi akan rayuwar da zaiyi da Ameena mai yawa ne saboda soyayyar ta ma mai yawa ce, mai tsayi da fadi. Wadda ta cike filin zuciyar taf! Babu wani gurbi da wata ‘ya mace zata sake samu he believed.
****
Sati biyu da yin haka ya kara yin bad-da-kama ya zo don jin me Amina ta shirya wa aurensu?
A babban falon Goggo suke, Amina ta cika shi da ababen sha masu sanyi, wadanda ta sarrafa da hannunta daga 'fruits'. Yana kan kujera tana zaune a kan kilishi. Yanzu kunyarshi da ta ke ji ta ragu sosai, tana iya bude baki ta yi magana a gabansa babu jin nauyi. Sabida yadda yake jan ta da hira sosai a waya, ya maida kansa matashi dan ashirin da shidda kamarta. Tun daga ranar da suka yi wayar farko, duk dare sai ya kirata sun sha hira mai dadi da kara fahimtar juna da sanya dankon soyayya a zukatan su.
Amina ta muskuta ta gyara zamanta ta tattara hankalinta akan Ma’arouf din.
"Shirye-shirye nasu ne, bana son a sanar da daurin aurenmu a kowacce kafar sadarwa, a dauro a Shira, zan yi walima a nan gidanmu don 'yan uwa, iyaye, abokan karatu, na aiki da duk wasu abokan arziki. These are my programme of events your Excellency, please don't say no!".
Murmushi Ma'arouf Ji-kas ya yi, kwayar idanunsa a kanta da wani irin yanayi a cikinsu. Ita kuma sai ta sadda kanta cikin jin kunya. A tausashe ta tsinkayi furucinsa cikin kunnuwanta. Daga ji ba shi yake sarrafa kalaman bakinsa ba, suna sarrafa kansu ne tun daga karkashin zuciyarsa.
"A kan me zan ce NO? Bayan kowa da irin yadda yake tafiyar da tsarin rayuwarsa? Wanda ya tafiyar da rayuwarsa da sauki,ya kuma dauketa da saukin,shi ya huta. Ina da irin ra'ayinki a wasu bangarorin Aminahhh, ina sonki, ina yinki, ana mugun tare!!!".
Amina ta yi dariya, har fararen hakoranta suka bayyana, dariya sosai mai kyau da ban sha’awa, wadda ta nuna halin farin cikin da kalaman sa suka jefa zuciyarta.Shi ma ya taya ta. Sukayi abarsu mai isarsu. Goggo na daki tana jiyowa, da ma a kan sallayarta ta ke, ta idar da sallar lsha kenan, sai ta dungura ta yi wa Allah sujjadah, ta gode maSa da ya share mata hawayenta, Ya bai wa Aminanta irin mijin da kullum ta ke mata addu'ar samu, kafin Ya dau ranta. Tsarki ya tabbata ga Sarki Allah!!!
****
Don haka Dr. Amina bata koma aikin asibiti ba, ta kara jingine aikin, don Ma’arouf ya gaya mata bazai yiwu ba matarsa sa da aikin asibiti. Yana da shirin da yake yi mata a ransa don bazai bar ilmin data sha wahala ta nema ya bi iska ba dole al’umma ta cigaba da amfana da shiin one way or the other. Shi dai ta kasance cikin yi masa biyayya akan ra’ayinsa shine burinsa kuma ta amince.
Sun cigaba da fahimtar juna, bai fasa bad-da-kama yazo gidan Goggo ba, soyayya kamar a birnin Hindu, mai ma’ana kuma tsabtatacciya. A bar Goggo da kunshewa a daki. A daya bangaren,Amina da Goggo na cigaba da shirye shiryensu a hankali. Ma’arouf ma na nasa.
Ance rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya. Irin kudin da Amina taga Goggo na zarowa tana mata saye-saye sun bata mamaki, ta kuma yarda ba’a raina sana’a,kaji tsoron koda mai sayarda allura wanda ya tsaya sosai akan sana’ar tasa.
Kwana dai-dai har dari ba goma haka sukayi ta zuwa suna wucewa kamar kiftawar ido, suna kara kusanta Ma’arouf da Aminah, sun gama yarda they are meant for each other, an kuma halicce su ne don junansu, kuma Ameena karama itace SANADI, sanadin alkhairi a garesu bakidaya.Allah Ya kara mata lafiya.
Ranar wata juma'a aka daura auren Engnr. Ma'arouf Habibu Ji-kas da Amina Mas'ud Shira. A kauyen Shira ta jihar Bauchi. Akan sadaki mafi albarka wato mafi kankanta. Naira dubu dari kacal.
A can kauyen Jikas Hajiyan Ji-kas wato Hajiya Saude sai kukan farin ciki ta ke yi tana mika godiyarta ga Allah, da ya nuna mata wannan ranar da burin ta ya cika tana raye cikin koshin lafiya.
Da yamma kuma bayan an sauko daga masallaci aka daura na Ilyas da Sa'adiyya. Washegari asabar da yamma aka gabatar da kasaitacciyar walimar kamar yadda Amina ta tsara, ba abinda ba’a ci ba, babu irin abincin da ba’a yi guzurinsa ba bayan an ci an koshi,anyi guzurinsa, kowa sai sanya wa auren albarka yake yi.
Wasu kan tambayi junansu wane irin miji ne haka Amina ta aura? Su dai ba su taba zuwa walima mai wadatar abinci da abin sha irin wannan ba. An kayar da shanu an kayar da raguna har ba adadi, ba’a maganar kankanuwar halitta kaza.
Akilu ya kawo akwatuna guda goma sha biya shake da kayan lefe na fita hankali, ya ce da Goggo Yallabai ne ya turo shi a baiwa Ilyas, sai mukullin motamatrix dalleliya duk na Ilyas ne. Ina ruwan dan gaban goshin Jikas! Abu naku maganin a kwabe ku.
Goggo ta kawo tukwici mai yawa ta baiwa Malam Akilu ya tafi yana godiya. Har zuciyarsa shima cikin farin ciki yake da wannan al’amari, koda dai a matsayin sa na babba mai hankali da ke bibiyar mu’amalar likiciyar da ubangidanta, yasan bata tafi ba, zata dawo.
Watarana irin wannan na nan zuwa(which will alter the dream to reality). Sanda yayi driving dinta na karshe take fadin wai sai watarana! Malam Akilu daga yau an gama! A zuciyarsa ya ce “yanzu aka fara!”. Gashi kuwa Allah Subhana Ya tabbatar da alkawarinsa wanda ba ya tashi. Ya kawo farin ciki cikin rayuwar Ogansu kamar yadda yake sanya su farin-ciki da nau’o’in alkhairansa garesu marassa yankewa. Ya kawo AMINA SANADIN AMINA don ta sauya duniyar mahakurcin bawansa.
Suna addu’ar Allah ya sada shi dadukkan alkahairanta ya kareshi daga sharrinta in akwai.
Da ango Ilya ya zo har da taka rawa don murna. Yana tsokanar Amina, wai Yallabai ya fi sonsa a kanta. Ita ko dankwali bai bata ba. Ga Sa’adiyyar sa ta sha akwatuna na garari. Bayan ya san Goggo ce ta roki Hajiyan Ji-kas kada a kawo komai, in ta tare ya bata. Ita ba ta son 'yan tsegumi su cika mata gida. Ita da jama'arta suka dauka suka kai gidan su matar Ilya.
An sanya tarewar Amina kwana goma masu zuwa, don ta roki Hajiyan Ji-kas alfarmar a barta ta kimtsa a hankali ta yi sallama da danginta na Shira, ta raka Goggo kasarta ta haihuwa‘Sirrleone’ kamar yadda ta dade da burin sai ta aurar da Amina zata koma, za su yi kwana bakwai a can.
Da fari hankalin angon na Amina ya tashi a kan tafiya Sirrleone din nan. Amma daga baya da Hajiya ta gaya masa shekaru talatin da doriya kenan rabon Goggon da kasarta ta haihuwa da iyaye da ‘yan uwanta, kuma Amina ba za ta iya barin Goggo ta tafi ita kadai ba, a cewarta don kada ta ki dawowa, sai ya amince. Ya yi musu booking jirgin ‘Arik’ zuwa kasar Sirrleone.
*****
SIERRA-LEONE (West Africa)
Asalin su daga Lardin Kenema suke, manyan biranensu kenan; Bo da Kenema, in ka cire babban birni Freetown. Kenema shine birni na biyu mafi girma da shahara. Kakan Haj. Hauwa Alhaji Ibraheem Sissey Babban Malami ne wanda yazo Sierra Leone daga Guinea-Conakry ya haifi ‘ya’ya goma anan maza da mata,suka yadu sosai cikin kasar. Yanzu sun fi dari, ‘ya’ya da jikoki.
Goggo Hauwa itace babbar jika a family kuma dukkaninsu suna zama a Lardin Bo, Freetown da Kenema. Lardi yana nufin (province).
Mutanen kasar nada tsayi da girman jiki hadi da kyawun sura. Allah ya albarkaci kasar SierraLeone da albarkatun kasa musamman (diamond). Basu fiya noma ba, don basu da kasar noma, sannan kasar su jar kasa ce wato laka, don haka yawanci daga kasashen ketare ake shigo musu da kayan abinci, hatta albasa daga kasar Holland ake shigo musu da ita, fara, mai kyau, mai sa abinci kamshi da dadin dandano, sun fi shuka kwakwa da plantain kuma suna da albarkar kifi. Yanayin kasar yana yanayi da kasashen mu na kudu (garuruwan inyamurai a Nigeria).
Kasa ce da ba shahararriya wajen kyau da kyale-kyale ba, amma akwai kwanciyar hankali da bin doka da oda. Akwai kwakwa ko’ina a kasar da bishiyoyinta suna kiranta (jelly).
Currency dinsu shine ‘Leone’. Kasar Sirrleone tanada dadin zama, da talaka da mai kudi duk cimarsu daya. Komai talaucin ka zaka ci abinci mai kyau kuma mai dadi. Miyar ganyen rogo da miyar ganyen dankali sune manyan abincinsu/miyoyinsu, ana ce musu ‘keren-keren’ dasu ake cin shinkafa ba sa cin tuwo, basu san tuwo ba.
Kasa ce da turawa sukeso suka kuma nacewa, ko don albarkar ‘diamond’ da yanayi mai dadi da Allah Ya basu. Haka zaka ga manyan ‘trolls’ na karfe cike da ‘diamond’ a airport ana fitar dashi zuwa kasashen turai. Kada kaso kaga yadda manyan jirage ke tashi da sauka a kasar na manyan kasashen duniya abin gwanin ban mamaki.
Ga manyan duwatsun ‘hills’ a ko’ina. Ginin gidajen su akan ‘hills’ sosai. Zaka ga gidaje kamar 100 akan hills (tsaunuka) saboda basu da fadin kasa, ruwa ne ya kewaye garin Freetown yayi masa kawanya wanda yake daga Atlantic Ocean.
Babban yarensu shine ‘kiryo’ yana shige da ‘pidgin’. Fulan, wato (Fulani) da Mande da Timini da Soso sune manyan kabilu a kasar. Kabilar da Goggo Hawwa ta fito watoFulan, sune kan gaba, wato mafi kima da daraja a kasar. Mafi akasarin Fulan ba ‘yan kasar bane sunzo ne daga Guinea-Conakry wanda makotan kasar Sirrleone ne kamar Nigeria da Nijar.
Turawan yamma sunyi tasiri a wannan kasa wajen tura musu akidunsu musamman matasansu, matan su yawanci sai sun girma suke sanya mayafi. Don haka inda duk Amina da Goggonta dake sanye da Hijab suka gifta sai suka zama abin kallo abin sha’awa.
Hills da suke dasu ya sanya bazai yiwu ayi filin jirgi cikin birnin Freetown ba, sai aka je wani dan tsibiri nesa kadan da garin aka yi, ana cewa tsibirin Lungi.
Idan jirgi ya sauka a Lungi za’ayi tafiya ta akalla mintuna 25-30 zuwa bakin ruwa, inda daga nan za’a shiga jirgin ruwa (sovereignferries) ya shiga da kai garin Freetown tafiyar mintuna 30. Idan (ferry) yana sauri zaku iya isa a mintuna 15.
Lungi tsubiri ne kuma dan kauye, saboda haka kodayaushe (ferry) cike yake da (passengers) masu shiga ko fitowa daga garin Freetown.
Wani abin sha’awa harda motocinku zaku iya shiga (ferry) ya tsallakar daku in a mota kuka zo.Bayan ‘ferry’ ana hawa ‘helicopter’ ko Babur din ruwa.
FREETOWN
Babban birnin kasar kenan. Kisi Road babbar unguwa ce a cikin gari kuma mahada ta hada-hadar kasuwanci tamkar kana cikin garin Lagos.
Lumley, itace kamar GRA dinsu kuma unguwa data tara kusoshi da masu kudin kasar da sauran baki masu zuwa yawon bude ido kasar musamman turawa.
Kuma anan ne dukkan ‘embassies’ da ‘high commissions’ na kasashen duniya suke da kuma Quaters na ma’aikatan su.
Kusa da Lumley sai Aberdeen itama unguwa ce, a nan kuma ‘beach’ yake (Lumley Beach) da manyan ‘clubs’ da sai wanda ya isa yake zuwa.
Daga Kisi Road zakiyi tafiya zuwa Grassfield, sai ki wuce zuwa Waterloo, to kin fita daga Municipal na Freetown kin fara shiga kauyuka.
Shi Kisi Road itace babbar hanyar da zaki fita daga Freetown zuwa Bo,da kamar awa daya sai ki isa mahaifar Hajiya Hawwa wato Kenema.Nisan su daga babban birni Freetown kamar awa biyar zuwa shida ne.
Turawa yamma na son kasar SierraLeone sosai don yanayin kasar na zaman lafiya ba