Chapter 3 Reading SANADIN KENAN 3 BY SUMAYYA TAKORI.txt Arewa Novels

SANADIN KENAN 3 BY SUMAYYA TAKORI.txt

Author :  Sumayya Abdulkadir Takori Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 20.1K words

ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa. Ba ta san sanda ya mike ya nufi kofa ba. Sai da ya murda marikin kofar ya dan ba da karaAmina ta dawo daga duniyar tunaninta. A tsakiyar kanta ta tsinkayi sautinsa yana fadin.
"In kin gama kintsawa Akilu na jiranki. Ameena za mu wuce Ji-kas da ita, ki gaida Ilyas!". Ya fice.
Ta mike cikin sanyin jiki ta ci gaba da harhada yanata-yanata da kayan amfaninta. Ameena ta yi kuka ta gaji, ta bingire ta yi bacci a wajen. Wannan damar ta samu ta silale da akwatinta biyu. Duk kayan sanyawar da ta tarar a gidan ta yi amfani da su a nan ta barsu, ba ta dauki ko daya ba.
****
A cikin mota suna tafe suna gaisawa da direba Akilu, ta ji shigowar sako a wayarta. Ta dauko ta duba, sakon shigowar kudi (Alert) ne daga Kwamishina Usman Turaki. Adadin kudin sun ba ta tsorofiye da na baya, sun tada hankalinta. Da hanzari ta dannawa malamin nata kira.
Dr. Turaki ya san za a yi haka, kuma tuni ya shirya karbar kiranta, don haka tana kira ya yi murmushi ya dauka.
"Dr. Amina ya aka yi?"
Amina ta feso ajiyar zuciya. Ta tsane gumin daya tsatstsafo mata a goshi da hankicin ta.
"Doctor wannan kudin sun fi karfina, me na sayar muku? Me na yi muku na wahala haka? Doctor na fi son iya cikon albashina, Goggo za ta yi zargi, wanda dama kullum cikinsa nake a gurinta".
Ta jero maganganun a jere babu shan numfashi,amma cikin taushin murya mai nuna ladabi da damuwar da take ciki a fili.
Dr. Turaki ya yi magana cikin muryar kwantar da hankali.
“Take it easyAmina. Me na gaya miki sanda za ki fara aikin nan? In ban manta ba na ce da ke, 'Allah ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar, ina addu'ar tukwicin hakan ya zamo naki ne'. Anyi haka ko ba’ayi ba?
Kinyi kokari sosai a kan Ameena, ta samu lafiya a hannunki.Idan Ma'arouf ya mallaka miki rabin abinda ya mallaka ba zai ji komai ba fa. Sai bai yi hakan ba, ya yi daidai hankali da tunani don kada ya razana ki. Ina so ki sani, wane neGwamna kuma Engnr. Ma'arouf Ji-kas, wannan tukwicin da ya ba ki kwatantawa ne ba kankat ba a kan son da yake yi wa 'yarsa Ameena. Ki sanya a rankiilminki ne ya ba ki ba Ma’arouf ba. SANADIN KENAN!
Ki yi wa mahaifiyarki bayani kada ta damu, ilmin da ta tsaya miki ki ka yi ne ya ba ki, babu matsayin da ilmi ba ya baiwa mutum a rayuwa. Sannan a wajen His Excellency wannan kamar an fitar da allura daga kogi ne (so relax please, say thanks to Almighty Allah, not Ji-kas)".

Amina ta yi murmushi ta sauke wayar daga kunnen ta. Tunda ya kashe tasa alamar bai son (anymore word from her) karin wata kalma daga gare ta. A kalla ta samu peace of mindyanzun (kwanciyar hankali). Ta yarda da duk abi da ya fada. Ta shiga tunanin zama karamar attajira mai zaman kanta sanadin ilminta, ta samu zuciyar mutum irin Ma'arouf Habibou Ji-Kas SANADIN ILMINta. Dadin-dadawa ta samu (exposure) na rayuwa kala daban-daban a gidan gwamnati, wanda za su taimaka mata wajen tafiyar da zamantakewarta har karshen rayuwarta.
Har Akilu ya yi fakin a kofar gidansu tana wadannan tunaninnikan. Sai da ta ji motar ta daina motsi ta farga.
"Sai watarana Akilu, sai watarana! Daga yau an gama!!!".
Murmushi ya yi, a ransa yace “yanzu aka fara dai”, a fili kuma ya ce,
"Ranki ya dade mungode, Allah ya kyautata rayuwarki,yadda ki ka kawo karshen matsalar ubangidanmu Allah ya kawo karshen matsalolin rayuwarki.Allah ya kara wa Ameena lafiya".
"Amin Baba Akilu, sai watarana!". Ta fadi tana 'waving' dinsa ta shige gida tana jan kafarta, sakamakon nauyin data yi mata, ga wasu tawagar hawayen sabo da suka shimfido mata, shi kansa Akilun kewarsa take, zuciyar ta na gaya mata ta rabu dasu fa kenan, ta bar gidan gwamnati har abada! Alfarmar ubangidan nasu ba mai yiwuwa ba ce agareta, ba shine irin mijin da ya dace da ita ba, ina ita ina kishi da Anty Laila?
Aka ce yaro tsaya matsayin ka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka! Kwarya ta bi kwarya in tabi akushi sai ta fashe. Jikas, (as a governor) mijin mata da yawa ne ba shine Mr. Right dinta ba.
Tunaninta yafi karfi ga cewathe best is yet to come.....A ra’ayin ta data tsara a zuciyarta tun lokacin da ta soma mallakar hankalin kanta:Tanaso ta auri mijinta ita kadai don tanada tsananin kishi, yaro matashidaidai ita, wanda bai mallaki komai ba sai kwalin ilmin boko, wanda bai taba yin aure ba, akanta zai fara, wanda zasuyi fafutukar rayuwa tare su gudu tare su fadi tare su tashi tare, amma Jikas ai mijin mace hudu ne.
A lokacin da ta tuna alkawarin data yiwa Goggo kafin ta barta ta fara aikinsai hankalinta yayi mugun tashi......

“Duk mijin da ya fara zuwa ko waye zata bar aikin tayi aure.....”.
Akan haka suka tsaya itada Goggo, kafin ta amince mata zuwa gidan gwamnati. Ta tuno da maganganunnoble laureateZainab Alkali inda take cewa.

“Dreamsare conceived, but not all dreams are born alive, some are aborted. Others are stillborn”. (Mafarkai kamar ‘ya’ya suke, ana yin cikin su, amma ba duka ake sa’ar haifesu a raye ba, wasu tun suna ciki ake zubar dasu, wasu kuwa a mace ma ake haifarsu). In hakane ba lallai ka samu duk abinda kake so ba a rayuwa kuma ka zauna lafiya???

Akilu direbadai sai bada kayanta ya yi aka shigo mata da su don ya lura kwata-kwata bata cikin hayyacinta har ta shige gida. Abin ya wuce ace kewa ce kadai ta sanya ta a wannan halin, ga dukkan alamu akwai wani muhimmin al’amarin a tare da ita kamar yadda suke hasashensa daga ubangidansu.
Jikin sa ba laka ya ja motar ya tafi shima cikin kewar Amina.Yana addu’ar allah ya maido ta cikin rayuwarsu bada jimawa ba. Yarinya ce mai matukar kirki, girmama manya da shiga zuciya,wadda ba zuciyar Jikas kadai ta shige ba har ta wadanda ke zagaye dashi sabida halayenta ababen so.
*****
Goggonta kadai ta samu a gida, suka yi murnarsu har suka gaji. Wannan karon ma ba ta gaya wa Goggo adadin kudin da ke cikin asusunta ba. Tasan Goggo tsorata zatayi ko ta darsawa ranta zargi, ta dai gaya mata ya biya ta albashinta cikakke, da kudin tantabarunta. Ta ce masa kyauta ta ba shi, ya ce in ba ta karba ba, zai maido mata kayanta.
Goggo ta ce,
"A'a ba a yi haka ba, ki karba".
Ta yi murmushi,
"Na karba Goggo".
Sun yi sallar isha a daren ranar, bayan Amina ta idar da shafa'i da wutiri ta ji wayarta na kara. Ta dauka ta duba mai kiran 'HAJIYAN JI-KAS' Kamar yadda ta adana sunan, shi ke yawo a fuskar wayar.
Ta juya ta kalli Goggo, sai ta ga lazimi ta ke, da cikakkiyar nutsuwa, da ladabi mai yawa ta amsa kamar yadda ta saba amsa wayar Hajiyan.
"Assalamu alaikum Aminatu".
"Amin wa'alaikumus-salam Hajiya, Ya ya Ameena?"
Hajiya ta ce, "Kya bari mu gaisa ai, Uwa Mai Ameena, kwana uku baya ya kamata in bugo wayar tun sanda na ji Ameena ta mike a kan kafafunta.
To garin in kira ki saboda zumudi da farin ciki hannun nawa karkarwa ya shiga yi na jefa wayar tawa a ruwa, sai yanzu da ya zo ya hada min wata (tana nufin Ma'arouf).
Ubangiji shi Ya nufa, amma da kokarinki da sadaukarwarki. Mun gode, madalla Amina. Ba ni mahaifiyarki in tana kusa mu gaisa".
Amina ta mika wa Goggo,
"Hajiyan Ji-kas ce".
Ba tun yau ba Goggo Hauwa ta san Hajiyan Ji-kas, Amina ta sha hada su su gaisa idan ta zo (weekend) Hajiyan ta kira ta. Don haka da sanayya suka gaisa Hajiya ta yi mata godiya a kan taimakon da Dr. Amina ta bawa jikarta.
Goggo ta ce, "Babu godiya a tsakani, ai aikinta ne. Ko ba ta yi wa Ameena karama ba za ta yi wa sauran al'umma ko ba ko sisi balle Amina da ake biyanta".
Ita dai Hajiya Saude godiya ta ke tana karawa har suka yi sallama. A ganinta basu da abinda zasu biya Amina duk tarin dukiyar su.
****
Kwana daya, biyu, Amina ba ta da kuzari, ta rasa kwarin gwiwar isar da sakon Ma'arouf ga Goggo. Ta barwa zuciyarta wannan al'amari mai girma da ya tunkaro ta. Ta kasa aiwatar da abubuwan da ta saba yi yadda ya kamata saboda tunanin amsar da za ta bai wa His Excellency da kwarin gwiwar sanar da Goggo. Tuni dai zuciyarta ta riga ta gama nutso da ninkaya cikin maliyar So. So irin wanda ba za ta iya fassarawa ba.
Tun tana ignoring fassarar abubuwan da take ji din da ganganakan Ma’arouf, da kalubalenta kala-kala marassa madafa, ba shine Mr. Right ba da sauransu, wannan da wancan,har ta yarda ta fassarasu da Son Ma’arouf ne. Idan akwai abinda yafi Mr.Right to Ma’arouf to Ma’arouf Ji-Kas ne. Ta yarda da Zainab Alkali.
Wanda ba lokaci daya ya shiga zuciyarta ba, ya dade yana kassara ta, yana huda kasusuwa da bargonta a hankali a hankali (like a biological VIRUS). Bata bashi muhimmanci ba ne tun lokacin da ya soma samun muhallin, don sanin cewa abune da ba zai taba yiwuwa ba, zuciyarta yaudararta ta ke yi. Don ba ta taba ganin wata alama da ke nuna hakan daga Ma'arouf Ji-kas ba. Mutumin da ko cikakken kallo ba ta ishe shi ba a baya.
A hankali suka soma shakuwa, shakuwa mai yawa akan siyasarsa, duk da haka babu wata alama makamanciyar wannan data gitta a tsakaninsu.
Sannan kuma ta kan tuna matarsa 'yar kwalisa Anty Laila. Ina ita ina iya shiga kishi da wannan kasaitacciyar mace? Wadda bata ajiye kanta anan kusa ba? Yaushe ma ta kai wannan matsayin banda giggiwa irin na zuciya? Beside, tana jin kamar lokacin yin aure ya wuce mata, babu wanda zai kara cewa yana sonta daga shekaru ashirin da shida. Tunanin komawa karo ilmi ne a ranta da zarar ta bar gidan Gwamnati, don haka ta dauko gingimemen bulo da katon dutse ta danne gurbin da kedarsa soyayyar Ma'arouf a zuciyarta (A baya kenan).
Amma daga kwana uku bayada ya furta neman soyayyarta da ra’ayin sa na son aurenta da kansa ba waya ba ba aike ba, gaba daya sai ta ji kamar an sauke wannan bulo da dutsen da ta adana tsofaffin ajiyarta suka fito suka yi yabanyakoriya sharr suka lullube zuciyarta.
To amma da wane harshe za ta gaya wa Goggo? Ya ya Goggon za ta dauki al'amarin? Kada ta zarge ta da cewa tun can baya soyayya ta ke yi ba aikinta ba, duk da ta san Goggo ta yarda da ita dari-bisa-dari. Hasashen zuciyarta ne wannan kawai. Gaskiyar magana shi ne, kunyar Goggo ta ke ji. Bari ta yi shiru abinta kawai. A ina zai ganta har ya bukaci jin amsa daga bakinta? Ta san yawan ayyukan da ke kansa ba za su bari ya kara tunawa da wata Dr. Amina ba.
Don haka ta like bakinta da (super glue) ta shiga sabgoginta da kula da tantabarunta. Lokaci-lokaci littleAmeena Ma'arouf na fado mata a rai, sai tace cikin ranta, ko an kaita makarantar kwanan? Ko ba’a kaita ba? Ko me take ciki? Amma in ta tuna tana hannun Hajiyan Ji-kas sai ta ji damuwarta a kan kewar yarinyar ya ragu. Tana da yakinin tana samun kauna da kulawa yadda ya kamata fiye da na Babanta.
Ta lura shi kansa ba ya alakanta rayuwar diyarsa da matarsa Laila, ko me ye dalili? Oho!

*****

MA’AROUF JI-KAS!
A ofishinsa yake, bayan tafiyar Dr. Amina da kwana uku. Mutanen da ke son ganinsa sun fi dari. Ayyukan da ke gabansa wadanda suke bukatar ya sanya hannu (signing) sun fi guda hamsin. Amma me? Ya kasa yin ko daya, ya kasa (attending) ko mutum daya. Idan ya tuna in ya koma gida ba zai tarar da Dr. Amina da Ameena ba sai ya ji wani irin kadaici da damuwa sun taru sun lullube shi. Kamar shikadai ya ragea duniyar Subhana.
Ya kasa aiwatar da komai wadanda ya saba yi a rayuwarsa. Hatta kiran waya damuwa yake jefa shi don jira yake ko Amina za ta turo masa sako, ko ta kira shi ta ba shi amsa kan bukatarsa, na zamowarsu abokan rayuwar juna na har abada, amma har aka cinye kwanaki ukun, babu 'text' ko wayar Dr. Amina.
A karshe ya gane mafitar daya ce, ya bar komai ya ajiye komai dake gabansa, ya yi yakin mallakawa zuciyarsa abin da ta ke so da kauna, wannan preciousgem mai daraja wato AMINATU don ya zauna lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wata da watanni yana dannewa, yana boye halin da zuciyarsa ke ciki.
Amma yanzun an zo wani limit(geji) da ya fahimci cewa, ci gaba da dannewar nan ba abin da zai haifar a gare shi sai (psychological depression), mafitar kawai ita ce mallakarAMINA.
Wadancan falsafofin na son rai wato nagudunauren mace fiye da daya, a yau ya sauke su a gefe, ya cinna musu ashana ya kone su kurmus! Dama bai taba rantsuwa a kai ba. Ya kan fada ne dai kawai a matsayin ra’ayin sa. Ya fahimci in ya tsaya ta jin amsa daga bakin Amina zai shekara bai ji ba, soyayyar da ke cin zuciyarsa ta zauta shi. Ya yarda ko Amina ba ta sonsa to ba ta kinsa.
Ya amince zai aure ta ko da ba ta sonsa, in dai har zai mallake ta cikin gidansahe believed zai samu soyayyar a hankali, kai ko tana kinsa din ya amince ya aure ta a hakan, in dai za ta dawo cikin rayuwarsu shi da Amina, ta bar downstairs ta koma upstairs wannan shi ne babban burin zuciyarsa a yanzu, ya yanke shawarar sauke rawanin Gwamna ya nada na yakin neman soyayyar Amina da aurenta.
Ya dauki wayarsa ya kira mataimakinsa Prof. Yusuf Bugaje, ya ce duk ayyukan nan da ke gabansa ya yi masa, ya ci gaba da handling komai, zai yi hutu na kwanaki uku. Farfesan ya amsa da girmamawa komai ya koma hannunsa.

*****
Ilya ya shigo gidan da yammacin ranar da Amina ta yi kwanaki uku da dawowa. Goggo ta shiga makota barka. Ya ji dadin samun Amina ita kadai. Tana suyar awara ne da ta tashi da marmarinta tun azahar ta ke aikinta. Ta gama soyawa tana kwashe wa Ilya ya tsaya a kofar kicin din.
"Anty Amina, ina nawa? Raina ya biya wallahi".
Ta ce, "Dauki guda daya, shugaban kicin din gidan Gwamna da kwadayi, ban taba ji ba".
Ya kyalkyale da dariya ya mika mata farar leda.
"Ungo ga guzurin gidan Gwamnatin na yo miki ke ma, don na san kwana biyu kina kewarsu".
Ta galla masa harara, "Wa ya ce da kai ina cin abincinsu? Wanda na saba ci shi nake dafawa da kaina".
Ta dai karbi ledar ta leka, (shawarma fal, soyayyun kaji da samosa, springroll da wani dunkulallen cake). Ita da ta ke cewa ba ta ci, sai ga ta tana cika baki tana taunewa tana hadiyewaharda lumshe ido, kunnenta har motsi yake. Ilya ya dinga yi mata dariya, ya yi kyau ya yi kiba, ya yi tsaf farinsa na Fulani ya fito. Amina har mamaki ta ke yadda Ilya ya murje cikin 'yan watanni ya waye sosai, kamar ba shi ba.
Ya ja kujera 'yar tsugunne ya zauna, "Ke muhimmiyar magana ta kawo ni, gidan Goggo ya kammala fa, har an yi fenti. yanzu kudaden abubuwan da za a zuba za ki tura ta account dina, ga takardar abubuwan cikin gidan su kujeru, air-conditions, kayangado, labulaye, cooker gass, carpet, kayan kicin da sauransu. Ga list din da kudin komai a rubuce a kasansa".
Amina ta karba tana dubawa, ta yaba da komai, Ilya dan baiwa yana ba ta mamaki, ya san kaya na zamani masu tsada, amma da quality da nagarta, ban sha'awa da burgewa. Ta zabi kalolin da ta ke so wanda Goggo sune kalolin da ranta ke so, ruwan madara da brown, ta ce, "An jima zan sako (transfer) in na gama ciye-ciyen

3 / 7