Author : Sumayya Abdulkadir Takori Category : New Hausa Novels 2026
don yaki da ya bata musu kasa ba.
Kasar Sierra Leone tana cike da plantations na kwakwa, tanada kyau gwargwado, saidai babu shuwagabanni nagari da zasu ciyar da kasar gaba.
****
Jirgin ‘Arik’ ya sauke Amina da mahaifiyarta Hajiya Hauwa a tsubirin Lungi(Lungi International Airport) wanda ya kasance Airport dinkasar Sierraleone, Amina sai rarraba ido ta ke tana kallon ababen mamaki, wato al'adu daal’ummatai da suka sha bamban da wadanda ta saba gani. Tsayin shekarun da Hajiya Hawwa ta yi a Nigeria bai sa ta manta yadda zata yi ta sadu da mahaifarta ba wato gidan iyayenta a Lardin Kenema.
Goggo ta biya kudin ‘ferry’ nata dana Amina (Leone 20000) daidai da naira (1000) kudinmu na Nigeria. Sun shiga VIP ne saboda Amina na tsoron ruwa. Ferry baya sauri yau don haka saida suka shafe mintuna talatin sannan suka shigo garin Freetown.
Daga Kisi Road suka hau mota mai tafiya Kenema, tafiyar awanni shidda cur sannan suka iso, Hajiya Hawwa bata sha wahalar gane gidan iyayenta da kakannin ta ba duk tsayin shekarun nan. Babban gidan gandu na Alhaji Ibraheem Sissey.
Ta gode wa Allah da ya sada ta da iyaye da 'yan uwanta lafiya, ana ta murnar zuwansu kamar me amma murnar ta fi karkata ga ganin Amina. Wadda sai a hoto suka taba ganinta, hoton ma na tun tana karama, ta samu mahaifinta ya rasu, Allah bai yi zasu gana ba, wasu da yawa a bayanshi ma duk sun rasu. Amma mahifiyarta na raye. Wasu sun hayayyafa, 'ya'yan sun girma. Haka aka yi ta kai su suna zaga dangi dake cikin Kenema ita da Amina.
Kwanansu uku a Kenema sun huta sosai sannan suka tafi Lardin Bo, inda danginsu na can suke, kannen mahaifinta uku suna can da iyalansu, suka kwana daya sannan suka wuce babban birni Freetown inda kannen Goggo guda uku suke aure; Zainaaba (Jal’an) Aisata (Aishatu) da Fatimata (Fadimatu). Jal’an na aure a Aberdeen, mijinta babban ma’aikaci ne na hukumar tsaro ta kasar, Fatimata na Lumly, mijinta jami’in custom ne, Aisata na Waterloo tana auren wani babban dan kasuwa. Kar kiso ki ga Amina a tsakiyar (aunties) dinta da kyawawan ‘ya’yansu masu kama da ita. Kowacce na nan-nan da ita, don ma basu iya hausa sosai ba, sau-tari sai Goggo ta shiga tsakani tayi musu tafinta, in ba haka ba rabin hirar da kwatance ake yin ta, gashi basa jin turanci sai yarensu ‘kiryo’.
Lokacin da Hajiya Hawwa ta gayawa Aisata, Jal’an da Fatimata cewaAmina amarya ce tarewa zatayi da sun koma, tafiya Aisata tayi da ita gidanta ta soma yi mata shirin amare irin nasu.Jal’an da Fatimata ma ba’a barsu a baya ba kowacce ta kawo gudunmuwarta, suka gyare ‘yarsu tsaf ciki da bai dinta, hatta gashin kan Amina ya sanja launi, ya koma na mutanen Sierraleone. Amina ta canza kwata-kwata ta fito a cikakken asalinta (Sierraleonean). Amina ta ga ‘gata’ irin gatan nan na dangin uwa, wanda bata sameshi ba a tsayin rayuwar ta.
Kuka take sosai tana rungume su Aisata daya bayan daya, a lokacin da suke sallama zasu koma Kenema,inda daga nan zasuyi shirin komowa gida Nigeria, Amina cike take da ganin beken Goggo, ashe tanada irin wannan gatan ta barsu sukayi ta ragaita?
A Kenema, Mahaifiyarsu Goggo Kaka Maryaama, wadda ta tsufa ainun ta ce da Goggo cikin yarensu,
"Ina fatan kin dawo gida kenan Hauwa'u? Tunda ba aure ki ke da shi ba, ki samu miji a nan ki yi aurenki yafi tunda ba wuce auren kikayi ba, kuma tunda kin ce kin aurar da Aminatu tarewa za ta yi".
Ai kuwa Amina ta balle musu da kuka da aka fassara mata abinda kakarta tace,
"Na roke ki kada ki kara fadin haka Kaka. Ki yi wa Allah ki bar min Goggona a kusa da ni. Ni kadai ta haifa ba ni da dan uwa ko abokin shawara sai ita. Ba ni da burin da ya wuce duk sanda nake son ganinta in ganta, ke kuwa kinada su Anty Jal’an da ‘ya’yansu. Kaka don Allah ki yi hakuri ki tausaya min,ina rokon ki ke ma ki bi mu, muna bukatar dayan ku cikinmu mu ci gaba da rayuwa tare, da yardar Allah bazamu kara yin dadewar da mukayi bamu zo ba, zamu dinga zuwa akai-akai".
Kukan Amina ya yi yawa, sai da Kakarta ta dafa ta tana lallashi.
"Na bar miki uwarki Aminatu, na amince zan biku mu koma tare in zauna tare da ita, nimain ke ganinta duk sanda nake so. Amma ku yi min alkawari ke da mijinki duk sanda mukeso zaku kawo mu gida nida mahaifiyarki".
Duk da hausar tasu ba irin ta Nigeria ba ce, Amina tana ganewa. A take Dr. Amina ta kira His Excellency sukayi magana ta gaya masa ko me kenan da abinda Kaka Maryaama keso, yace ta bashi Kakarta, kasancewar tana jin hausa sosai, magana yayi mata da Amina bata san me suka ce ba, ta dai ga Kaka ta hau hada kayanta ta ce ta amince zata bisu Nigeria kuma tare dasu Jal’an bakidaya da kannen mahaifin Goggo za’a tafi, zasu raka ta dakinta sai su dawo, ita Kaka da Goggo su zauna tare har illa masha Allah. Kukan dadi Amina ta fashe dashi ta shige daki ta rufo kofa ta kira angon nata.
A bakin ‘swimming pool’ din gidansa yake zaune bisa fararen kujeru, cikin gajerun rumfunan gargajiya (hut) wadanda aka fi sani da bukka, sanye yake da jallabiyya mai yankakken hannu ruwan madara, a gabansa tebir ne karami shake da kayan marmari.
Yammaci ne mai lumshi da kadawar iska mai sanyi kasancewar damuna ta kawo kai, mujallu da jaridu ne fal a gabansa,wadanda duk shafukan su na farko(cover photo) kyakkyawar fuskarsa ce ta mamaye su, yana duba wadanda zai iya yana wucesauran, yana ganin yadda gwamnatinsa ke tafiya ne tareda ra’ayoyin talakawa a kanta, masu dadi da marassa dadi.
Wayarsa daya tayi ruri da wani irin ‘tune’ mai taba zuciya da shikadai ya san wanda ya sanyawa shi. Murmushi yake yi sosai a lokacin da ya amsa kiran, kamar dama jiran kiran yake yi.
“Sierraleoneans!”.Abinda yafara fada kenan cikin taushin murya. Murmushi tayi mai sauti. Bai bata damar ta amsa ba ya dora.
“Tunda aka samu dangi kuma sai aka manta da miji, wannan wace irin Amina ce? Ni idan na kira baya shiga, ki kirga dakikun agogo, awanni nawa ne suka bada kwana shidda? To duk sun tafi ne tareda bugun zuciyata na rashin samun wayarki, ina fatan kun daure kaya? Jirgin ku zai taso daga Lungi karfe biyu na ranar gobe ne insha Allahu”.
Ta sauke ajiyar zuciya.
“In nace nagode yayi kadan fa! Ban san da kalmar da zan gode ba, ina rokon Ubangiji Ya fini godewa”.
Murmushi yayi mai sauti, wai don ya kwaso mata danginta take wannan godiyar, bata sani ba, in duk kasar Sierraleone zai kwaso mata don tayi farin ciki zai yi hakan in yanada iko. Balle mutum goma.
“Akwai hanyoyi da yawa na godewa mijiba da fatar baki ba. Akwai hanyoyin da za’a gode min din ai. By the way, in baki san su ba zan sanar dake a gadon baccin mu. Ina jiran ki Amina da bashin da ni kaina bansan yawansa ba. Kiyi barci mai dadi da mafarkin Ma’arouf a cikinsa. Na barki lafiya, ki gaida Goggo”.
Cikin mutuwar jiki da rudewa Amina ta sauke wayar daga kunnenta, wata irin murya Baban Ameena ke magana da ita a yau da bata taba jinsa da irinta ba, batasan ya zata kwatanta tasirin muryar a dukkan gabban jikinta ba, ta san dai ta kurda kowanne sako da kowanne lungu na jikinta ta yi masa illah, ta saukar mai da wata irin kasala mai wuyar fassarawa.
Washegari sun cika kwanansu bakwaicif, suka yi sallama da sauran 'yan uwan Goggo, wadanda suke (far-relation) wato wadanda ba na jiki bawadanda baza’a taho taredasu ba, ta Bo suka bi suka dauki kannen mahaifin goggo su uku da ‘ya’yan Yayar shi biyu, suka zarto Freetown suka tadda su Aunty Aisata sun gama shiri. Tuni Ma’arouf ya gama yi musu shirin tikiti da komai na jirgin Arik suka taho Nigeria.
****
Mu karasa a littafi na 4, kuma na karshe Insha Allahu.
-Takori
Ina baku hakuri makaranta da littafin ya kai har 4 bayan nace iyakacin sa 3. Yanayin rubutu ne ya janyo hakan domin labari shi yake jan zarensa da kansa. Kada ku damu tare suke. Taku har abada
TAKORI.
DANDANO DAGA
AUREN KWANGILA!
(Littafin Takori mai zuwa)
H
awaye masu dumi suka biyo idanun Ambassada Hamza, bai damu da ya kai hannu ya share ba, haka ya barsu suka yi ta malala akan kundukukinsa, abokan nasa suka ci gaba da ba shi baki, ba su san kuka biyu yake yi ba; kukan rashin mahaifiyarsa da kukan nadama...!!! Rayuwa kenan.
Hafsat bata san bidirin da Daddy ke yi da zuciya da kwakwalwar sa ba, ta sayo wa Mammah katin wayar da ta aike ta ta kamo hanyar dawowa. Tafiya take kanta a sunkuye don bazata iya daga ido ta dubi taron mazan nan dake zazzaune a kofar gida ba. Kamar ance da ita ‘dago kanki’ gab da zata shiga gida ta dan daga kai sabida jikinta ya bata ana kallonta sosai, ai kuwa karaf! Sai idanunta cikin na Daddy. Ta ganshi yana shatatar hawaye kamar karamin yaro, sukayi ido hudu dashi. Tuni ta gigice ta saki katin wayar da canjin kudin ta ci uban tuntube da wani katon dutse dake kofar shiga gidan an tare kofar dashi, ta fadi kiff! A kasa. Don tayi tsammanin a cikin mutanen nan balbaleta zaiyi da balbalin bala’in nasa.
Ji tayi ansa hannu biyu an dago ta, ta ji zafin faduwar sosai da sosai, gwiwoyinta duk sun kukkuje leben ta ya fashe jini ya wanke bakin. Ta cira ido a sannu cikin dauriya ta dubi wanda ya daga ta; Hamza Atiku Dakata ne.
“Wace irin tafiya kikeyi haka Addah? Ba kya kallon abinda ke gabanki, Addah in don ni kika rude haka don Allah kiyi hakuri, kar ki sake firgita in kin ganni, ba dodo bane ni, BABAN KI NE!!!
Hafsat-Suhaana, ta runtse idanunta, mafarki ne kawai ire-iren mafarkan da ta saba yi akan Daddyn, saboda yadda tasa damuwa da lamarin sa a ranta. Ta ki bude idon don bata so ta farka daga wannan daddadan mafarki. Daddy yasa hannu ya dauko hankicinsa daga aljihunsa fari tas dashi ya shiga goge jinin da ke zuba daga bakinta. Mutane wajen bakwai suka taso suka isko su.
Nan da nan labari ya isa ga Mammah, daga bakin dan Anty Mariya, wai Addah ta fadi a waje. Daddy ya sa an tafi da ita a mota a kaita asibiti. Sai taji maganar banbarakwai, ina ruwan Daddy da Suhaana har da zai ce a kaita wani waje a mota? Kar dai fa ya aika da ita GIDAN MARAYUN da yake ikirari? Tayi wata irin zabura ta mike, da gudunta tayi waje har zaninta na kwancewa ko mayafi babu a jikinta tayi hanyar soro, uban karo suka gabza da Daddyn yana kokarin shigowa saura kadan su fadi. Jikinta na bari, muryarta na karkarwa cikin son fashewa da kuka ta kama shi tana girgizawa.
“Ina Hafsat? Ina Addah ta? Ina ka tura a kaita? Ina ‘ya ta ina ‘yar amana ta???”.
AUREN KWANGILA!
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
(Goron Sabuwar Shekara)
Yana zuwa ba da jimawa ba insha Allahu.