SIHIRIN KAUNA COMPLET BOOK by Indo Ce.doc

Author :  Indo Ce Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 16

33K to 36K   out of 47.8K words

juyar maka da hankali??, bazan iya ba indai banga mijinta ya dawo duniya ba to babu dalilin da ze sa nafasa haWa auren ka da YaaYa kuma idan kaga auren ya Wauru to ka rabu da aljanar can, idan ba haka ba kuma kai zakasha wahala, tashi kabani guri nagaji da magiyar nan kayi abunda nace shine zefi alkairi"

tashi yayi ya koma Wakin su ya tarar da Minoji tana zaune a inda ya barta, zuba mata ida yayi maganganun Ayiya suka shiga dawo masa, "yanzu sai na rabu da ita duk irin son da nake mata??"

Ya jefawa kansa tambaya, da sauri ya girgiza kai cikin ransa ya?ara cewa, "aa Minoji ta ba aljana bace bazan rabu da ita ba tare zamu kasance har ?arshen rayuwarmu"

Cikin rawar murya me alamun rauni tace, "Umarul'Farook mahaifiyarka tana son raba mu ko? bansan wane laifi na aikata mata ba da yasa ta tsaneni, a iya sani na banyi mata komai ba"

?arasawa yayi ya zauna a gefenta ya rungume ?afafun ta yana shashshekar kuka, "da gaske ke ba mutum bace?? karki Soye min dan Allah ni mijinki ne Minoji"

Tambayar da ya watsa mata kenan wadda tasa wutar kanta ta Wauke, da sauri ta shiga jujjuya kai tana hawaye jikinta ya hau rawa zuciyarta tafara bugawa da mugun gudu, hannu ta Wora akansa tana shafawa har na Wan wani lokaci kafin tace, "Yaaye Ni mutum ce kamar kowa, bansan..."

Katse ta yayi da cewa, "nasani karki damu kanki duk neman hanyar da za'ai mana katanga akeyi, bazan taSa rabuwa dake ba kema kiyi min wannan al?awarin"

Ya faWa yana kallon fuskarta.
Da sauri ta buWe ido tarrr akansa hakan yasa yayi saurin kauda nasa idon, "Mariama tana min barazanar zata Wauke ni idan ya kasance wata rana ya neme ni ya rasa ya matsayin al?awarin da nai masa kenan?"

tunanin da yafara kunno kai cikin zuciyarta kenan,
tarar tunanin nata yayi da cewa, "kenan baza muyi rayuwa me tsayi tare ba?? ashe wata rana zan rasaki?"

Da sauri tace, "aa bazaka rasani ba, bazan bari ba zan zauna tareda kai bazan barka ba nima"

Kwantar da kansa yayi akan cinyarta ya cigaba da rera kuka itama tana tayashi.



gama Alwalarta kenan ta tashi zata gudu Waki Yarinya ta busa wani kusur me ?arar tsiya, rintse ido tayi atake kanta yafara juyawa lokaci Waya hankalinta yafara barin jikinta tafara tangaWi tana ?o?arin faWuwa.

Dukan su ido suka zuba mata dan kuwa zuwa yanzu abun nata yafara wuce kwanyarsu.
sai da ta Wan daWe tana katan-tanwa a tsakar gidan kafin tafara dawowa hankalinta tayi saurin shigewa Waki tana numfarfashi,
Yarinya zata bi bayanta YaaYa ta daka mata tsawa.
Ayiya tace, "daga hura kusur kuma?? a hakan kuma sannan ace ba aljana bace"












*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 23=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE






YaaYa tace, "duk abunda ma za'a faWa ai daga baya ne amma wannan dai babu suffar mutane a tareda ita"

Ayiya ta rausayar da kai gami da cewa, "tohh! Allah yayi mana tsari dai dan na lura ta riga ta fara susuta Yaaye sai addu'a sai munyi da gaske kafin ya gane gaskiya"

YaaYa tace, "gardama ce dashi shiyasa amma ai yaci yanzu ya gane dan yana ganin abunda take ba wai sani ne beyi ba"

Ayiya tace, "ai bari Babar Fiddau ta shigo kafi zamu nema wanda ze hanata zaman gidan da kanta ta gudu macuciya"

Haka suka cigaba da tattauna ta yadda za'ayi su ganar da Yaaye da kuma yadda zasu kori Minoji.

ta daWe a zaune sai rintse ido take tana girgiza kai kuwwar kusur Win ta ?i wucewa sai wujujuwa take mata tsikar jikinta sai tashi suke har Wan zabura take saboda yadda suke yarrr, sai bayan Wan wani lokaci sannan ta samu dai-daito har ta gabatar da sallah, sai da tayi addu'o'i sosai sannan ta tashi ta koma bakin gado ta zuba tagumi tana rarraba ido.

Yanzu jiran shigowar Yaaye take domin kuwa cikinta yafara kukan yunwa gashi bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba neman da Yaaye ya fita duka dashi suka dogara har sai ya dawo ze kawo abunda zasu ci idan Allah ya sa ya samu.

tin tana zaune har tagaji ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita, kukan Yarinya ne ya tashe ta tayi saurin fita tsakar gidan, Yarinya tana zaune sai Sarza kuka take, dur?usawa tayi a gabanta cikin tausasawa tace, "Yarinya kukan fa??"

Ba tareda ta dena ba tace, "abinci zanci kuma YaaYa tace babu"

Ido Minoji ta zuba mata cikin matu?ar tausayi sai da tayi nazari sosai kafin tace, "babun nan sam bata da daWin ji kiyi ha?uri kinji? Yaaye shi me ?o?arin nema mana ne kuma ya fita neman be kamata ki zauna kina masa kuka ba, addu'a da fatan nasara ya kamata kiyi masa shine abunda yafi bu?ata a garemu, duk rintsin da ka shiga Allah ya fika sani idan ka kai kukan ka gareshi yakan share kukan ka idan yaso, ki nutsu Kiyi tunani sosai zaki gane abunda na faWa miki gaskiya ne"

Share hawayen ta shiga yi tana turo baki gaba, sai da ta gama share ?wallar sannan tace, "to yaushe ze dawo??"

Minoji tace, "ba da daWewa ba yana gaf da shigowa in da zaki ?irga goma kafin ki gama ya shigo "

Washe baki tayi cike da ?uruciya tace , "bari nayi sauri na ?irga dan ya shigo da wuri"

Tana fara ?irgawa iyakacinta bakwai sallamar sa ta katse ta.
Da gudu tayi kansa tana faWin ga Yaaye ga Yaaye .

YaaYa da Ayiya sukai kallon kallo kafin Ayiya ta sauke gwauron nishi tace, "tir?ashi babbar magana, to Yaaye yanzu ga ka ga ita sii ta faWa maka ta yadda akai tasan zaka shigo yanzu, mutum dai indai na gaske ne babu yadda za'ai ya gane hakan cikin sau?i gata nan ka tuhume ta"

da ido ya rakata ita kuwa sai tayi ?asa da kai kamar ta fashe da kuka.
Rausayar da kai yayi kafin yace, "Ayiya dan Allah kuyi ha?uri da irin maganganun nan be zama lallai hakan ta kasance ba abunda kawai tunanin ku yake baku ne amma ba gaskiya bane"

Ayiya tace, "iye?? lallai idonka sun rufe nidai tambaya Waya kawai nake so ta amsa maka indai da gaske ba Aljana bace, ka tambaye ta waye ya sanar da ita zaka shigo yanzu? iyakar wannan ma ai sheda ce da zaka gane ta"

Fashewa tayi da kuka tana cewa, "wallahi ba haka bane nima kawai faWe nayi dan Yarinya ta dena kuka babu wanda ya gaya min"









*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 25=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716





cikin sauri ya?arasa kanta yana kiran sunanta tareda jijjiga ta amma shiru sai da ya yafa mata ruwa sannan taja dogon numfashi, fashewa tayi da kuka tana cewa, "aa banaso katafi dan Allah"

Cikin mamaki yace, "saboda me bakyaso??"

ta buWi baki da nufin yin magana numfashinta ya sar?e tafara sha?uwa cikin lokaci kaWan tagama galabaita.

Ganin abun
yayi yawa yasa yayi saurin neman sabulu ya wanke hannunsa Sannan ya dawo kanta yafara ?o?arin dai-daita nutsuwarta,
Sai da yayi da gaske sannan numfashinta yafara dai-daituwa sai dai tanajin jiki matu?a, lamarin ya gama Waure masa kai yakasa gane komai a ciki bashi da zaSin da ya wuce tambayarta ko ze samu gamsashshiyar magana dan kuwa ya shiga tantama sosai wani Sangare na zuciyarsa yana son gazgata zancen Ayiya wani Sangaren yana kwaSar sa da yin hakan.

Minoji kuwa kuka take Sarzawa da iya ?arfinta.

yana ?o?arin yimata magana ihun da Yayyi ta ?wallara ya dakatar dashi, cikin sauri ya fito dan ganin abunda yake faruwa,
A tsakar gidan yayi karo da ita ta faWi yaraff tana tirje tirje Ayiya da YaaYa sai sallallami suke.

Dur?usawa yayi a gabanta yana kiran sunan ta amma shiru sai wani irin gunji da takeyi tana majaujawa a ?asa.

Ayiya ta share hawaye sannan tace, "Yaaye idan mun faWi gaskiya sai kace ba haka ba gashi matsalar da Minoji ta kawo mana a gidan nan, ciwon aljanu ko a ma?otan mu ba'ayi bare a gidan mu a Wakin mu yanzu wannan ba tozarci da zalumci bane?? menene laifin Yayyi? babu laifin da ta aikata mata amma zatayi mata wannan mummunar sakaiyar nidai ban yafe mata ba ba kuma zan yafe ba"

Shiru Yaaye yayi ya cigaba da yiwa Yayyi addu'a,
Bayan wani Wan lokaci ta sake ?walla ihu sai kuma tayi shiru jikinta yayi salaf kamar an zare mata laka sai kuma ta fashe da kuka.

A tausashe Yaaye yace, " Yayyi?? meke faruwa meyesa ki kuka kodai baki da lafiya ne"

Cikin tsananin azabar da take sha tace, "Yaaye kaina zan mutu wayyo Ayiya ki temakeni kaina ze fashe Yaaye ku cire min bazan iya ba"

yace, "kiyi ha?uri ki dena kukan addu'a zakiyi ze dena kinji ko?"

Ayiya tace, "oo ni wannan lamari ya fi ?arfin mara ?arfi, Yaaye akan wata ?a bazan yarda a jefa min ?ata cikin wani hali ba dan haka ka Wauki matakin da zaka Wauka "

A marai-raice yace, "Ayiya dan Allah ki dena maganar nan mana ki bari ta samu lafiya sannan ko me za'ayi sai ayi"

Kallon YaaYa tayi tace, "kinga kama min ita mu kai ta Waki".

Kamata YaaYa Tayi suka shigar da ita Waki saka fara ?an ?o?arin su amma abin ya ci tura sai kukan ciwon kai takeyi,
sai da takwashi lokaci tana ciwon kan sannan ya sassauta har ta samu ta Wan sha ruwa.

Tin daga lokacin take fama da ciwon kai har ma da wasu abubuwan ga yawan firgita.

A Sangaren Ayiya kuwa ganin haka yasa ta?ara daukar himmar shiga tsakanin Wanta da Minoji.
Yaaye kuwa mugun halin da ya jefa Minoji ta sanadin turaren da Ayiya tabashi yasa tausayin ta ya hanashi wani ?wa??waran motsi dan kuwa tindaga ranar batada lafiya.

Yau
Yana zaune a gefenta yayin da take kwance tayi shiru sai ?ifil ?ifil take da ido kallonta yayi kafin yayi magana cikin sanyi yace, "Minoji dan Allah zan tambayeki"

Kallonsa tayi gami da gyaWa masa kai.
Ya Wan sosa ?eya a daddafe yace, "dama game da maganar da su YaaYa sukeyi ne dan Allah ki sanar dani gaskiya, koda yaushe cikin tunane tunane nake gara naji komai daga gareki akan na Wauki irin maganganun su"

Ido ta zuba masa kafin ta Wan murmusa sannan tace, " bazan iya gaya maka ba sai dai ka jira Mariama tazo"


"Mariama??"

Ya maimaita sunan cikin sigar tambaya.

Batace komai ba sai ma gyara kwanciya da tayi.


Yau Yayyi ta tashi da matsanancin ciwon kai gashi ta?i cin komai har sai da dare yayi da Yaaye ya dawo sannan ya lallaSa ta taci tana gamawa kuwa takama amai tana kakari har da jini ga wani mugun ciwon ciki da ya saukar mata.

Dukan su sunyi iya bakin ?o?arin su dan ganin sun shawo kanta amman sun kasa sai dai suka zubawa sarautar Allah ido.

Minoji kuwa ranta duk ya gama Saci a fusace ta tashi ta nufi tsakar gidan a tsaye ta tsaya ta kame ?ugu ta zubawa Yayyi ido.

Yaaye ya kalleta ganin ta burkice yasa ya mi?e yana cewa, "koma Waki Minoji ai jikin nata da sau?i"

Dakatar dashi tayi ta hanyar Waga masa hannu sannan ta maida kallonta ga Yayyi wadda daga zuwan Minojin ta dena kukan da takeyi tayi lif ko motsi babu.

Cikin tsawa tace, "waye?? meyesa zaku zo ku takurawa yarinyar da bataji ba bata gani ba?? waye ya baku umarnin zuwa nan??"


A ladabce Yayyi tace, " Ki gafarce mu ranki ya daWe Yarima ne"

Cikin tsawa tace, "har yana da ikon aiko ku inda ban aike ku ba??"

Sai da kowa na gurin ya firgita saboda tsawar da ta doka mata..
Cikin rawar jiki tace, "ranki ya daWe Yarima.."

Kafin ta?arasa ta katse ta da cewa, "ku koma ki gayawa Gimbiya Malika a Waure ku har zuwa lokacin da zan dawo zan Wauki mataki da kaina, shi kuma Yarima ku gaya masa zan dawo kuma zanyi hukunci"

Tana rufe baki Yayyi ta sule ta kwanta sharaf sai bacci irin na huce gajiya.
Da ido kowa ya bita musamman Yaaye da abun ya gama sha masa kwanya.

Kallon su Minoji tayi sannan tace, "yanzu kun gane abunda kuke tantama akai???, ni ba kamar Minoji nake ba banida sau?i indai aka taSa mutunci na zan kasance tareda ku na Wan wani lokaci zaku gane banbancin tsakanina da ita dan kuwa ni ba'a yimin abunda raina be so ba, ta sanadin abunda kuke wa Minoji kuka jazawa ?ar ku faWawa komar Yarima, yanzu zan kasance makwanci Waya tareda Wanki idan kinajin ke kika haife shi kuma kin yarda da kanki sai ki hana"

Daga haka taja hannun Yaaye suka koma Waki tabar su Ayiya da sakakkun bakuna, yau ko irin maimaita zancen nan basuyi ba saboda tsoro dandanan kowacce tayi Wakinta ta kulle.

Suna shiga Wakin ta sake shi ta juya masa baya a kausashe tace, "shashashan namiji amma ba sunan ka bane, kana da ?o?ari tabbas tinda ka iya fita ha??in iyalinka amma baka amsa sunan ka Umar ba Yarima na kamar wuta yake yayin da na kasance tamkar mai hakan yasa yake azabtar dani ta hanyar da yaso, Yarima Umar shi fa bashida ha?uri amma kai salihi ne akwai bambanci tsakanin ku, naso ace shima ya kasance me ha?uri tamkar kai amma naso kai kuma ka kasance me zafin nama da himma kamar shi"

?ara sakin baki Yaaye yayi yana kallon bayanta dan kuwa baya ta juya masa, cikin rawar baki yace, "kece Mariama? shi kuma Yarima me sunana waye? ita kuma matata wacece?"

Jinjina kai tayi gami da cewa, "hmm tambaya me kyau Sarauniya Mariama ?ar sarki Sulaiman Aljani ziryan kenan, Mahaifiyata Bilkisu rikiWaWWiyar Aljana kuma balarabiya, Yarima Umarul'farook Wa ga Yarima Yusuf ?ani ga mahaifina, shine wanda yake iya dakatar dani akan abunda nai niyya matsalar da aka samu mahaifiya ta tafi son shi akaina kuma tana da ?arfin ikon da tafi mahaifina tasiri hakan yasa yake shimfiWa mulkinsa akaina duk da kasancewata Sarauniya"











*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 26=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716








Yaaye yace, "abun mamaki kenan itama Minoji ?ar uwarku ce??"

Girgiza kai tayi alamar "aa" sannan tace, "ita ba kamar mu take ba amma ta bambanta da mutane sakamakon ruhin mu yana tareda juna, mahaifiyarka bata san wacece Minoji a gurina ba shiyasa take ?o?arin shiga tsakanin mu, tin ina yarinya mahaifiyata babu yadda batayi ba akan ta rabamu amma abun ya?i yuwuwa an rabani da sarauta ta da duk wani abunda ya shafeni saboda ita amma nakasa rabuwa da ita saboda itace Duniya ta ban damu da ?yale ?yalen da suke masarauta ba ko wani jinkai na mulki kasancewa tareda ita yafi min komai, farin ciki na kwanciyar hankalina duk yana gareta, har ta kai ga yanzu tazama Waya daga cikin ahalin mu nima kuma na zama Waya daga cikin su, nakan zauna tareda su itama ta zauna taredani, irin rayuwar da takeyi ba itace zahirin rayuwarta ba duk yanayina shine yake

12 / 16