TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Author :  Janafty Category :  Hausa Book Store

Chapter   44 / 48

129K to 132K   out of 141.5K words

Asma'u da ke gefe ta kada baki ta ce ai domin ya na jariri ne in ya ƙara girma zai iya ma riƙida ya sauya kammani. Ni dai na yi musu shuru kawai Yallaɓai ya koma wajen matarsa suna mgana ƙasa ƙasa. Likita ne ya shigo ya ce kowa ya fita Yallaɓai ne kawai muka bari a ciki mu kuma muka fito waje sai can ba daɗewa suka fito tare da likitan shi ne ya ke faɗin likitan ya ce ba sa son hayaniya, ya kamata kowa ya tafi gida a bar mutum ɗaya saboda maijego ta samu hutu. Ina jin haka Yallaɓai na tashi tafiya na bi sa bayan na ba ma Baaba Asma'u abincin da na taho dashi ta karɓa da godiya. Duk da ga manyan kololi nan na san ba su da matsalan abinci ni dai na yi don Allah ko ban yi niyar abu ba in na tuna da maganar Alhajinmu da ya ce duk abin da zan yi to na yi shi don Allah kuma na nufe ta da alheri shi ya sa ma har na ɗibi abincin na tafi da shi.

Washegari ban koma ba, ko da Munnira da Hauwa suka kirani na ce ni jiya na je ba zan koma yau ba, na ce su je kawai ni ba zan je ba, ba su matsa min ba suka ce su za su je su yi barka, na faɗa ma duka yan gidanmu haihuwan ba saboda komai ba sai saboda Yallaɓai shima ya na yi min kara duk abin da ya samu ahalina sai in da ƙarfinsa ya ƙare. Sannan yanzu Ma'u munafuncin ta ya yi sanyi ko ma ta ji wajen Anty Bahijjan ba za ta nuna ta ji ba tun bayan faruwan lamarin ta kiyaye kanta, Ya Aina ta ce za su haɗu gabaɗaya su je asibitin su yi barka na ce ya kamata. Har Anty Zabba mun yi waya da ita ta ce ita ma Ya Usman ke faɗa mata da ya ke ba ta cikin group ɗin gidan su Yallaɓai tun lokacin auran Ya Usman ta fita daga ciki kuma ba a mai da ta ba, ta ce min za ta kira Yallaɓai ta yi masa barka. To sai da ya dawo da daddare ya ke faɗa min ta kira shi ta yi masa barka. Yallaɓai har wani jin daɗi ya ke yi in aka kira shi aka yi masa barka. 

Kwanan Gimbiya Biyar a asibiti aka ba su sallama suka dawo gida. Su Ya Aina a na gobe za a yi sallama su ka je gabaɗayan su har da Zaitunan Ya Abubakar kuma Yallaɓai ya ji daɗi tun da shi ya ke sanar da ni zuwan na su. Ni daman sau biyu na je asibitin ban koma ba tun da daman asibitin cike ya ke da su Anty Bahijja.  Sai da ta koma gida na sake komawa sau ɗaya a ranar ne ma Yallaɓai ke fada min ya yi raɗin suna. Sunan jaririn Muhammad Inuwa. Sai da idanuwana suka kawo ƙwalla sunan da Yallaɓai ya so na sake haihu ya saka sai ga shi ni Allah bai ba ni ba amma shi ya ba shi a jinin wata matar Allah mai tsara komai a yadda ya so.

Gwaggo ma kanta ta je har can Gwammaja ta yi ma Nene Barka ita da Ya Aina. Daga can kuma su ka wuce gidan Gimbiyar tare da Halima da ta zo za ta je gidan Nene ta ce su tafi tare su ka je suka yi ma Gimbiya barka. Sai bayan sun koma gida ne ma Ya Aina ta kirani ta na faɗa min. Shima Uban gayyar an faɗa masa sai ga shi ya zo ya na ce min ashe Gwaggo ta zo barka? Na ce eh sai ga Gogan na ta uban fara'a ban ga laifin shi ba ƙaruwa ya samu kuma ba zan ji haushi domin ya nuna murnansa ba.

An ɗaga sunan sai da wani satin ya sake zagayowa sannan aka gudanar da taron suna a gidan Gimbiya da ke sharaɗa. Ranar sunan Yallaɓai baya nan tun safe ya tafi Dutse akwai kwangilan da ya samu a can ne. Raguna biyu aka yanka ma Muhammad Inuwa(Khalipa) shi ne alkunyar da za a riƙa kiran da shi. Taron suna aka shirya na gani na faɗa. Na je sunan tare da ni da Hauwa da Munnira, sannan ba tare da sanin Yallaɓai ba na siya ma maijego atamfa mai kyau sai rigan yaro da pampers. Su Hauwa ma duk sun je da abin suna, mutanen Rano sun zo da yawa Sameena ma ta zo har da Faridan Tariq ma. Can muka haɗe da su muka yi namu rukunin ana hira. Jidda da Baby daman tun jiya suna gidan sunan an yi abinci kala kala har da su tsire sannan an kira mai hoto an yi hotuna ni dai ban tusa kaina ba sai da ita kanta Gimbiyar ta kirani tare da ni da ita da su Jidda muka ɗau hoton Suwaiba na cewa hoton nan bai cika ba tun da ba ginƙishin buɗe bakin Anty Maimuna sai ta ce ai shi Tafidan za su yi na su shi da Gimbiya da Baby ni dai ban ce ƙala ba, to wani dare ne jemage bai gani ba? Ai sai dai daran na shi mutuwar.

Muna gidan nan har yamma da ni aka gyara gidan bayan jama'a sun ragu daman aikin abinci ba a gidan aka yi ba kawo komai aka yi a dafen shi. Sai misalin tara na dare na koma gida na. Su Jidda nan na bar su duk da akwai makaranta ban isa na ce sai sun zo mun tafi gida ba domin na san ma ba za su zo ba gwara ma Jidda sai na bar su sai zuwa goben. Duk tare muka fita da su Hauwa kowa kuma ya hau adaidaitan da za ta kai sa gidan sa. Yallaɓai sai wajen sha biyu na dare ya dawo gidan a gajiye wanka kawai ya yi ya ci abinci ya kwanta. Washegari ban koma ba tun da ai ba hurumina ba ne sai yamma su Jidda suka dawo da nama mai yawa da su cake in ji Gimbiya na karɓa da godiya da fatan Allah ya raya mana Khalipa. Bayan suna da kwana uku Megidan ya ke ce min Gimbiya za ta koma Rano ta yi jegon ta na yi fatan alheri mota ya samo musu ta kwashe su, shi bai samu zuwa ba saboda sabon kwangilan da ya samu a Dutse ya sa ba ya samun zama yanzu.

Gimbiya sai da ta fi kwana hamsin a Rano sannan ta dawo. Ta na dawowa na ce Yallaɓai ya je can ya yi mata sati sannan ya dawo wajena ya yi ta murna ranar da suka cika satin ne ya kawo min ita tare da Khalipa da ya yi wani ɓulɓul da shi ya ƙara wayau gwanin ban sha'awa har da za su tafi ya na hannuna sai daga baya ne da Baby ta saka rigima na goya mata shi. Yallaɓai na ta kafa kafa wai kar ta yar da shi, gabaɗaya ya kasa sukuni sai wani kafa kafa ya ke yi da Baby kar ta tula Khalipa a ƙasa abin da na lura da shi Yallaɓai na son wannan yaron har kuma soyayyar na shi ba ta ɓoyuwa a saman fuskarsa da ayyukansa.

"Yallaɓai ka kwantar da hankalin ka. Ba za ta kada da shi ba, na ɗaure mata da kyau."

"To duka duka Baby nawa ta ke da za ta goya wani?

Haka ya ba ni amsa ganin haka ya sa na ce ma Baby ta zo na sauke mata shi, sai ta fara min kuka banza ai ba za a sauke shi ba, amma bai saka Yallaɓai ya haƙura ba shi a ganinsa kawai na yi masa kasada da ruhinsa ne, sai da Gimbiyar ta yi magana ta ce a bar mata shi ai za ta iya goyasa sannan ne ya yi shuru. Na kwana ina ta mamakin Yallaɓai ai ban gama mamaki ba sai da na ga a fuskar wayar shi ya cire hoton su Jidda da Baby da ya daɗe a wallpaper ɗin shi. Amma washegari da wayarsa ta faɗo hannuna na ga hoton shi ne tare da Gimbiya da Khalipa. Daman ai Anty Maimuna ta ce suma za su sha hoto aiko sun sha hoto shadda suka saka iri ɗaya mai ruwan sararin samaniya ni ban ma taɓa ganin Yallaɓai da kayan ba to tun da anko ne suka yi amaryan ƙarni da angon ƙarni daman ina zan gan shi da shi. Ta kwantar da kanta a saman kafaɗanshi suna dariya gabaɗaya suna kuma kallon Khalipa da ke hannunta. Ya shiga wanka ne daman ina gyaran gado wayar ta faɗo ban san a saman gadon ya ijiye ta ba.

Karambani ya saka ni dannawa haske ya kawo shi ne na yi mummunan gani. Ba zan iya tuna yaushe ne Yallaɓai ya taɓa sakani a fuskar wayarsa ba. Ya na dai saka Jidda a farko kafin mu samu Baby. Bayan mun haifeta kuma sai ya koma sakata wata rana kuma in ya ga dama kawai sai ya saka hoton masallaci na taɓa yi masa zolaya da cewa sai ya yi ta saka hoton ƴaƴansa ni fa? Sai ya ce min wai ya za a yi ya saka hoto na? Ko wani kare da doki ya samu ganina na ɗauka a lokacin martabawa ne Yallaɓai ya yi min sai yanzu na fahimci ba ni ce na samu martabawansa ba Gimbiya ce ni matsayina  ne bai kai na zauna a kan fuskar wayarsa ba shi ya sa bai taɓa sakani ba. Idanuwana suka kawo ƙwalla na yi saurin share su jin motsin fitowarsa. A lokacin ban yi masa mgana ba sai na yi kamar ma ban gani ba sai da na zo fita daga ɗakin bayan na gama gyaran shi kuma ya na saka kaya.

"Hoto fa ya yi kyau ƙwarai."

"Wani hoto kuma?

Ya faɗa da sauri ya na kallona ni kuma sai na yi kamar ban gani ba na yi masa mirmishi na fita. Ku san ai ya san abin da ya aikata sai ga shi muna ƙaryawa ya na yi min kame kamen su na maza in sun aikata wani abu na rashin gaskiya.

"Wannan hoton wai kike mgana?

Ya faɗa ya na nuna min wayarsa kallo ma bai isheni ba. Na cigaba da kurban tea ɗin da ke gabana.

"Daugther ce ta matsa min sai mun yi hoton nan. Har walpaper ɗin ma ina tunanin ita ta saka shi na gani ina ta son na cire sai na sha'afa"

Shi ya gama kiɗan shi sannan kuma ya yi rawan shi ban ce masa komai ba ganin haka yasa ya yi shuru shima bai ƙara mganar ba, ban sanin masa ba ko ya sauya sai can wata rana na ga ya saka hoton Khalipa da aka ɗauke shi ranar da ya zo duniya a raina na ce kai dai ka sani da munafuncin ka. Ko ya faɗa ko bai faɗa ba a irin soyayya da son da ya ke nuna ma Khalipa kowa ya shaida ya na matuƙar ƙaunar shi, ko ya na gidana ya dinga kallon hotunan Yaron da Video tare da yara suna nishaɗin su, wato ba zai iya ma kwana bai gan shi ba sai ya kalli hotunan shi ya ke jin daɗi. na san akwai abubuwa a gaba shi ya sa na roƙi Allah tun kafim zuwan lokacin ya ba ni haƙuri da juriya sannan ya ba ni wuyan ɗaukan koma mene ne zai faru anan gaba.

*****
*BAYAN SHEKARA UKU.*

KANO.
LODGE ROAD.
20 September 2019.
Lahadi. 11:30 na safiya.

Kwance na ke a kan makeken sabon gadona na kamfanin royal. Na lulluɓe kafafuwana zuwa cikina da lallusan bargo mai ruwan madara. A cikin barcin ina can ina mafarkin wai gani a makka na je gaban ka'aba ina ta addu'a ina kuka, har ina jin danshin hawayen a saman fuskata. Ƙara narkewa na yi har ina ƙara motsawa sai dai me? Ina jin danshin ruwa a fuskata har zuwa wuyana a tunanina mafarkin ne ina kuka ashe ba mafarki ba ne zahiri ne sai da na ji ruwa tsii na ta sauka a saman fuskata zuwa saman wuyana ya ƙi tsayawa sannan na fara dawowa hayyacina. 

Idanuwana na fara buɗewa a kasalance, ai da sauri na rufe saboda ruwan da ya yi min feshi a cikin idanuwana da sauri na kare fuskata ina ɗan yarfa hannuwana.
Dariya na ji ana yi ta yara ƙasa ƙasa da hanzari na zuro kafafuwana ƙasa ina goge fuskata.  Khalipa na gani a tsaye a gaba na da bindigarsa ta wasa mai ruwa a jikinta wacce Yallaɓai ya siyo masa da ya je Saudiya wannan shekaran. Yaron ya na kallona ya na dariya wani takaici ya cika min zuciya kuma saboda bai da kunya har ya na ƙara saitani da bindigar ya na faɗi cikin muryan yara.

"Umma faya faya."

Wai Umma fire fire, ɗan mirmishi na ƙakaro kafin na miƙe tsaye na riƙe bindigar na duka a gaban shi ina kallon shi yaro ne ɗan kimanin shekaru uku da wattani, sai da Khalipa ya fara girma sannan mutane suka ƙara gasgata da Baby ya ke kama har ya na yin jikinsu na gaza gaza kamar na ƴaƴan hutu ko da ya ke ƴaƴan hutun ne tun da uban su yanzu ya samu duniya a tafin hannun shi sai juya ta ya ke yi a yadda ya so.

"Khalipa ba ka ga Umma na barci ba ne?

Na faɗa ina shafa sumar kansa, sai kawai ya fara min dariya. Ya na mgana amma ba a ganewa sosai amma ya na kiran sunan kowa kamar ni Umma da Abban su, sai Ya Jidda da Ya Baby sai sunan Mami wato Gimbiya a bakin shi da sunan su Nene ya san sunan kowa kuma ya iya kiran su, ina ƙokarin sake magana ya ƙwace bindigarsa ya fice da gudu daga ɗakin na bishi da kallo har ya fice sannan na miƙe ina hamma gefen gado na koma na zauna na ƙura ma window da ke cikin bedroom ɗina ido ina kallon rana da ta fara hudowa ta na shigowa ta tsakanin labulayen da ke cikin bedroom ɗina da ya sauya kamar ba shi ba sakamakon komai sabo ne a cikin ɗaki har ta fentin ma gabaɗaya.

A cikin shekarun ukun da suka gabata abubuwa da dama sun faru masu daɗi da aka sin su. Masu daɗin sun fi yawa shi ya sa zan fara da su. Yallaɓai ya samu ƙaruwa ta arziƙi da dama a cikin wannan shekarun, karuwan kuma ba iya na dukiya ko arziƙi ba har na ƙara samun ƙaruwan ɗa namiji daga bangaren Gimbiya Khalipa da na shekara ɗaya da rabi ta sake samun ciki wannan karon ma aiki aka sake yi mata. Tun da ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda na farko ma ai an farka ta. Ta na nan yanzu haka ta na goyen Muhamamad Yusuf(Anwar) bayan haka kuma Yallaɓai ya yi ta shura ya na ta samun manyan kwangilolin gine ginen manyan makarantu da ma'aikatu da gidaje mafiyan shaharan ciki shi ne na gina makarantun aikin jinya la da gina makarantun manyan jamu'u  na gwammati da nayan kasuwa cikin shekarun ukun nan Yallaɓai ya samu ɗaukaka da shahara. Yanzu haka ya na nan ya na gina gma'aikatarsa ko na ce kamfaninda  anan zooa road ne ya siya wani tsohon ma'aikatan siyar da motoci ya buge shi ya na gina ƙaton kamfanin shi mai hawa uku amma dai suna nan suna aiki a tsohon offishin shi in da yanzu gabaɗaya sama da ƙasa ya zama duka mallakinsa sannan ya ɗau ma'aikata masu karatun abin da ya shafi fanni zane zane yanzu shi ba ya zane sai dai ya saka yaran shi su yi, sannan ya na da yara a bangaren masu leburan aikin gini sama da mutum ɗari uku a ƙarƙashin shi, ya na matuƙar taimaka ma matasa da aikin yi, yanzu haka gidajen bulo ɗin sa sama da guda biyar ne a garin Kano. A cikin shekaran nan ya biya ma kansa Makka shi da Nene suka je suka sauke farali suka dawo. Da ya dawo ne gabaɗaya rabin tsarabarsa kayan wasa ne na Khalipa da Anwar, Jidda da ta zama yan mata shekaranta sha bakwai tana kuma SS2 ne a babban sakandiri a yayin da Baby ke da shekaru goma sha ɗaya a duniya ta na ajin karshe a primary ne. Su kaya ya siya musu tun da sun girma sun wuce kayan wasa.

  Yanzu haka gidan da Gimbiya ta ke ciki Yallaɓai ya siye shi ya zama mallakin shi sannan ya siya wani ƙaton fili a Aluvenue, kimanin sama da miliyan ashirin in da ya ce zai gina mana ƙaton gida da zai haɗe iyalan shi waje ɗaya. Sannan ni da ita gabaɗaya ya sauya mana fenti a gidajen mu sannan ya siya mana sabbin furtures, ni dai tsoffin nawa wasu na ba ma Inna Mariya wasu kuma na aika da su Yashe domin suna bukata kujerun babban falo na da gadona kuwa Rahila na ba ma wa tunda na yi sabbi masu kyau da tsada. Sauran tarkacen kayan kitchen kuma Maman Saude na ba ma wa. Katifa ma ta ɗayan ɗakin Maman Nana mai yi min kitso na ba ma wa.

  Har gobe kuma ina nan da sana'ar sai da hijabaina kuma yanzu har sari ma na ke ba da wa.Maganar buɗe shagon saloon ta daɗe da shan ruwa. Yallaɓai bai sake min mganar ba nima ban ƙara yi masa ba. Ita dai Gimbiya kam yanzu shagon sai da abayoyi gare ta da takalma kuma Yallaɓan ne ya kama mata shagon da cewa ita ta kama da kanta da gadon ta na tsohon mijinta. kuma ta cigaba da oder kaya daga kasashen ƙetare. Akwai mai zama mata a shagon amma itama wani lokacin ta na zuwa ta zauna in ta na da lokaci. Kuma har gobe ta na cigaba da aikin ta na Gwammati. Cikin kuma ƙaruwan da aka samu shi ne na bukukuwan da muka sha kai da kai.

Farko dai na Marwa da Kawu Abba muka fara yi ita yanzu

44 / 48