Author : Janafty Category : Hausa Book Store
saka ruwa da omo na goge wajen na saki fanka zanin gado kuma na fita waje na jiƙa shi ina ta ɓata rai da sassafe ya sakani wahala, ba fitsarin ne abin haushi ba na ga dai ba jariri ba ne, ba zan hana shi kwana a gidana ba amma ba a ɗakin da na ke kwana da mijina ba har kuma ya kwanta ya yi min fitsari.
Shi ya sa ko su Jidda ba su ga fara'ata ba har shima ko da ya fito na haɗe rai na. Amma bai hana nai yi ma Khalipan wanka na sauya masa kaya ba. Ni kuma na je na wanke zanin gadon da ya yi min fitsari na shanya. Duk da Yallaɓai ya siya mana in ji min wanki amma da hannuna na wanke shi tun da guda ɗaya ne. Da Yallaɓai zai fita nan ya bar min shi wai maman shi ba ta nan za ta je asibiti Anwar ne ya kwana ya na ciwon ciiki. Ya fita ya bar ni ina ta aikin a kitchen ina can ina wanke wanke bayan na gama gyara duka ɗakunan na saka turaran wuta. Cartton na kunna ma Khalipa na yi masa jan ido da cewa in ya sake ya tashi sai na yi masa bulala ashe yaron nan bai ji ba ina can ina wanke wanke shi kuma ya samu dispanser ya danna ya yi min ta min ɓarin ruwa har ya gangaro ya jiƙa min cafet ruwa ne cike fa sai da ya yi rabi da shi kamar an ce na leƙa falon na ci karo da mummunan aikin da ya aika ta min
Na ko kama shi na yi masa bulala biyar, saboda haushi ko ɗana ne ya yi min ɓarnan nan sai na dake shi sai kawai ya fashe da kuka ko tsayawa bi ta kan shi ban yi ba haka ya ja min aiki sai da na naɗe cafet ɗin nan na fita dashi na shanya. Sannan na koma na sake goge wajen yaro nan neman ya yi ya saka min hauka ranar ina can ina aiki amma ina fargaban abin da zan je na tarar na ƙudira a raina zan yi ma Yallabai magana sai dai duk abin da zai ce ya ce. Ga barcin gajiya a idanuwana amma ban isa na kwanta ba domin in na kwanta na san abin da zan ta shi na tarar shi ya sa bayan na gama aikin jikina da zuciyata na son na kwana na huta amma na kasa, tun da in dai na bar shi na kwanta sai ya jawo min gagurumin aiki shi kuma ga shi ba ya barcin rana ballantana mu kwanta tare.
Ba ni na samu na huta ba sai da yamma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfiɗa wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yallaɓai ma ya shigo. Na dai haɗa masa abincin sa a dining, ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice lokacin har Yallaɓai ya farka shima kuma ya kunna hasken ɗakin ma.
Waya ta na jawo a gefen gado na duba lokaci ɗaya da rabi na dare. Hankalina ya tashi na ɗauka wani abu ne sai da na ga Yallaɓai ya buɗe ƙofa sai ga Jidda ta ɗauko Khalipa ya na kuka ya na ganin uban ya maƙale masa ya na kuka, shi kuma Yallabai sai ya rumgume shi ya na faɗin.
"Shii ga Abba nan shii."
"Abba ya tashi ne ya na ta kuka ya na cewa sai an kawo shi wajen ka."
"To Jidda je ki kwanta. Sai da safe."
"Sai da safe."
Ta faɗa kafin ta juya, shi kuma sai ya rufo ƙofar ya ɗauko Khalipa, ina zaune sake da baki ina kallon abin mamaki yau ɗin ma wataƙila kamar kullum ya fara barci ne aka kai shi ɗakin su Jidda shi ne ya na farkawa ya ga bai ga Uban ba shi ne ya saka musu kuka.
Na kasa magana ganin Yallaɓai ya kwantar dashi a tsakiyar mu, har ya na lulluɓe shi da bargo.
Zuciyata ta ciwo ni yau ko ɗana ne sai na yi maganinsa ballanta ɗan kishiya. Ina iya ƙoƙarina amma yau kam an zo ƙarshe.
A fusace na miƙe sanye na ke da doguwar rigar barci hulan kaina ma ta saɓule. Kitson kaina shiko ne har ya ɗan fara ma tsufa tun da ban yi kitson bikin nan na Rano ba.
"Me hakan ke nufi Yallaɓai?
Na faɗa ina kallon shi, ƙoƙarin kwanciya shima ya ke yi kafin ya ce" Zai kwana tare damu. Me ya sa kike tambaya?
"Saboda ban gane ma'anar abin da kake yi min ba."
Sai ya kalleni kafin ya ce" Me ye ba ki gane ba? Kwanan Khalipa tare da mu?
"E."
Na faɗa afusace saboda na fara harzuƙa ma da tambayoyin shi.
"Miye a ciki? Ai ba yau aka fara ba ko? Kin san ai Khalipa ba ya iya barci sai tare da ni ko can gidan ne ita kanta Daugther ta san haka."
Ya na gama faɗin haka ya koma ya kwanta ya na faɗin" Ki rage mana haske."
Sai na ga yaron ya yi shuru Yallaɓai na kwanciya ya wani maƙale shi, baki na saki ina kallon shi, na ma kasa magana amma na ji a raina yau dai sai dai Yallaɓai ya zaɓa ko kwana da ni ko kwana da ɗansa.
"Yallaɓai ni ce zan fita na bar maka ɗakin ko kai da ɗanka ne za ku fita ku bar min ɗakina?
Na faɗa kai tsaye ina kallon shi, sai ya yi shuru bai motsa ba. Ina ganin haka a fusace na fizgi filo na kuma janye bargon da suka rufu da shi da ƙarfi ina faɗin" Zan bar muku ɗakin."
Sai kawai na ga Yallaɓai ya miƙe a fusace ya riƙe bargon da na fizge ya na faɗin.
"Sadiya me kike shirin aikatawa haka?
"Abin da ka ji ka gani mana "
Na bashi amsa a fusace saboda raina tuni ya gama ɓaci. Kawai sai ya fizge bargon ya shimfiɗa ma Khalipa. Yaron ya lumshe ido ban sani ba ko barci ya ke yi, har gabana ya tako ya na kallona kafin ya ce.
" Sadiya yaushe kika koma haka? Yaushe kika zama haka?
"Yaushe dai ka zama haka dai Haba ba ka yi min adalci. A ina ne aka ce dole sai da yaro zamu riƙa kwana? Ko ƴaƴana ka fi kowa sani suna shekara uku da wani muke raba shimfiɗa da su. Me ya sa shi ba za ku koya masa hakan ba?
"Na faɗa miki a can ma haka ya ke. Ba ki ga yaro ba ne? Zuwa gaba zai daina."
"To ni ina ruwana da can ma haka ya ke yi, ai can ɗin in ya yi wajen uwarsa ne, haba ni fa na gaji na yi kara na yi kawaicin amma ba ka gane ba. To daga yau ta kau in za ka kwana da ɗan ka, ka sauya ɗaki ko ni na bar maka daƙin gabaɗaya amma ba zan ƙara kwana da Khalipa ba."
Har na gama faɗa na ya na kallona. Sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba sai kin bar mana ɗakin ba, tun da ɗakin ki ne mu za mu fita mu bar miki ɗakin."
"Beter."
Na amsa masa ina girgiza jikina.
"Amma kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka kike ba Sadiya. Ashe gudan jinina ba jinin ki ba ne? Ashe Khalipa ba ɗaya ya ke da Jidda da Baby ba?
"Ɗaya suke domin ko su ba ka ga ina kwana a gado ɗaya da su ba."
Hannu ya ɗaga min ya na cigaba da faɗin" Sai yanzu na gano ki. Baƙin ciki kike yi a kan yara nan Sadiya ba tun yau ba, sai dai ban saka abin a raina ba saboda ina ƙaryata hakan sai ga shi yau kin tabbatar min.'
Ya faɗa ya na kallona sai nima na kalle shi cikin mamakin kalamansa.
"Baƙin ciki? Baƙin cikin me?
A fusace ya ce" Baƙin ciki Daugther ta na haihuwa ke ba kya yi shi ya sa kike jin haushin su Khalipa ashe duk ƙarya ce da kike faɗin ƴaƴana ƴaƴan ki ne? Ashe duk yaudara ne? Tir wallahi kin ban kunya sannan kin ba ni mamaki "
Na ma kasa magana sai nuna kaina na ke yi amma na kasa mgana.
"A kan ƙaramin yaro kin kasa ɓoyo kishin ki da baƙim ciki Sadiya. Ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba amma ba zan ce miki komai ba sai na gode."
Ya juya zai wuce bakin gadon na sha gaban shi da sauri ina nuna kaina kafin na ce" Ni ce yau ka ke kira ina baƙin ciki da ƴ'ayan ka Yallaɓai?
"E baƙin ciki kike yi in ba baƙin ciki ba me kike yi! To ki sani ba ni na ce ki je ki yi planing ya ba ki matsala ba sannan ba Daugther ce ta kai ki ta baro ba, ke kika kai kan ki kika baro saboda haka ki daina zargin kowa sai kanki, haihuwa yanzu Daugther ta fara ƴaƴa kuma ba ki da hurumin tsanar su kuma ba ki da hurumin hana su zama gidan nan domin gidan na uban su ne ba na ki ba "
Kafin Yallaɓai ya gama mgana ƙafafuwata sun kasa ɗaukata sai ga ni zuɓe a kasa. An ce kuka rahama ne sai yau na fahinci haka domin na kasa kuka, ina kallon Yallaɓai baki buɗe na ƙasa mgana amma kalamansa na shiga kaina suna kuma min amsa kuwwa!
Ni yau Yallabai ke ma gorin haihuwa? Ni yau Yallaɓai ke cewa ni na kai kaina na ɓaro?
A gaban idanuwana ina bin shi da kallo ya ɗau Khalipa suka bar min daki. Ni ce yau na zama yar baƙin ciki a wajen Yallaɓai ya kira ni da kowani suna sannan daga karshe ya ce nan ɗin ba gidan ubana ba ne gidan shi ne.
Na so na yi kuka amma na kasa zuciyata na ƙuna. Baƙin ciki da takaici sun cika min zuciya anan wajen na haɗe kaina da gwiwa na saki kuka amma ba hawaye ina kuka amma kuma zafin da ke zuciyata sai ƙaruwa ya ke yi, har da ihu na yi na kwanta ina birgima amma ban ji ko ƙwatan abin da na ke ji a ƙasan zuciyata ya ragu ba. Barcin da ban koma ba kenan idanuwana biyu a ka yi asuba yadda zuciyata ta soye haka idanuwana suka soye suma.
Ina jin fitan Yallaɓai masallaci da dawowar shi, duk ina zaune na kasa tashi domin sai na ji gabaɗaya jikina ya yi min wani irin nauyi kamar ba nawa ba na kasa tashi ballanta na shiga tiolet na kama ruwa na zo na yi sallah. Ban iya motsawa ba sai shidda saura na safe na iya miƙewa ina jin kaina ya yi min wani irin nauyi, ina riƙe da shi na shiga tiolet na kama ruwa sannan na yo alwala na zo na yi sallar asuba sai bayan da na yi sallar ne ina jan casbaha na ji hawaye na gangaro min saman kumatuna ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka ba, Allah ya sa na sakaya ƙofar bedroom ɗin na ji Jidda ta zo ta na bugawa lokaci ɗaya da kiran sunana amma na kasa motsi ina zaune kamar status amma kuka na ke yi hawaye na sauka wasu na korar wasu. Ina jin gwara dai na yi kukan kar baƙin ciki ya kashe ni Yusuf Inuwa ba shi da asara.
Ni yau Yusuf zai kalla ya kirani yar baƙin ciki kalmar ta fi baƙantamin rai amma lokacin da ya yi min gorin haihuwa sai na ji komai ya tsaya min cak. Lalle na yarda da kalmar nan da hausawa ke yawan faɗin namiji ƙanin Aljali, namiji ba ɗan goyo ba ne ni Sadiya Sulaiman Yashe ni Yusuf Inuwa zai kalla ya ce ina baƙin ciki da y'ayan shi kuma har ya na ce min haihuwa yanzu Gimbiya ta fara wato sai dai na mutu sannan har ya na min gorin gida. Kuka na yi ta yi kukan abubuwa da dama ne, na ji gabaɗaya gidan ya yi min wani irin ƙunci ji na ke yi ko numfashin da na ke shaƙa a gidan ma gurbattace ne.
Na daɗe a cikin ɗaki, har wajen goman safe na ji fitan yara zuwa makaranta. Ina zaune a in da na yi salla ina kuka Yallaɓai ya yo wanka ya shigo ya sauya kaya bai ce min ba ni ban ma kalle shi ba amma na san ya ji yadda na ke jan hancina da macijana ya toshe min saboda kuka a haka ya sa kai ya fice shi da ɗansa. Ya jima da fita sannan na miƙe ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu ga wani maƙaƙi da ke damuna a maƙoshina.
Ko ta kan gidan ban bi ba na faɗa tiolet na yo wanka bayan na fito ko mai ban shafa ba na zura wata doguwar riga ta atamfa ƙaramin akwatina na jawo na fara haɗa kayana. Ban san ina zan je ba amma ji na yi zuciyata na tunkaɗani da tunanin na bar ma Yallaɓai gidan shi tun da ya ce ba gidan Uba ba ne, sannan me ye amfanin zaman nawa? Tun da duk sadaukarwar da na yi ta tsawon shekaru sha takwas da aure na da shi duk ya ta shi a banza to ai ban gama amfanin zama dashi ba. Duk wani abin da zan bukata sai da na haɗa shi a cikin akwatina sannan na ɗauki jakata na saka waya ta da Atm ɗina na duba kuma akwai kuɗi a ciki ya kai 10k. Hijabina dogo na zura na ɗau key din gidan ina jin cikina na jin yunwa amma bakina ya bushe ba na jin zan iya cin wani abu.
Sai da na kulle gidan sai kuma ga ni ya bakin gidan ina tunanin to ni yanzu da na fito ina zani? Ɗorayi?. Wata zuciyar ta ce min a'a bai kamata na je gida yanzu ba. Aurena shekaru sha takwas ban taɓa zuwa da wata matsala ba bai kamata yanzu a ganni da ƙaton akwati da kaya ba. In kuma a ka tambaye ni me zan ce? Yallaɓai ya yi min wulaƙanci na dawo gida? Ya ji na yi ko mene ne?
Hawayen baƙin cika suka zubo min a saman fuskata. Ba ni da in da zan je. Dangin Mama duk suna gandun albasa kuma bai kamata suma na je musu a wannan yanayin ba, duk in da na yi tunani sai na ji bai kamata na je ba. Har Ya Aina ta kawo min arai amma sai na ji iskar garin ma gabaɗaya ba na so na cigaba da shaƙa gwara na tafi wani waje nesa da in da na baro ko zan ba ma zuciyata damar da za ta samu natsuwar da za ta yi tunanin abin da ya kama ce ta.
Sai kawai na sumgumi akwatina na fara tafiya zuwa titi na tari adaidaita na ce ya kai ni tasha. Muna zuwa tasha na ga motoci ana ta lodi na rasa in da za ni. Kawai sai ga wani ɗan union ya zo gabana ya na faɗin.
"Kaduna. Kaduna. Kaduna za ki je Hajiya?
Sai na bishi da kallo ban san bakina ya furta kaduna zan je ba ni dai kawai na ga an saka kayana a mota nima na shiga na zauna.
Har motan ta cika muka ɗau hanya tunanin makomar sunan tafiya ta na ke yi? Ya ji na yi ko kuwa kashe aurena zan yi? Tun aurena da Yusuf yau shekara goma sha takwas. Ina da budurwa ƴa a gabana ban taɓa zuwa gida da sunan yaji ba, ban taɓa jin na gaji da auran Yallaɓai ba sai yau, ban taɓa jin in na yi yaji ban yi abu mara kyau ba, in har a shekarun da muka yi tare da Yusuf bai ji ko sau ɗaya na yi masa alfarma ba to bai kamata ni na yi masa wannan alfarman ba. Tun da muka yi aure ban taɓa kai ƙaran shi gidanmu ko gidan su ba amma yau abin da ya faru ya yi munin da ba zan yi zama a cikin gidansa ina tuna munanan kalamansa akaina ba. In na cigaba da zama baƙin ciki zai iya kashe ni.
Mun fara nisa amma tunani kawai na ke yi, gabaɗaya ji na yi zuciyata na tashi, kaina ya yi wani girma ya na sara min. Kawai sai na fiddo wayata da ke cikin jakata kai tsaye lambar Yallaɓai na laluɓo na shiga bangaren tura masa saƙo ba tare da wani tunani ba na yi masa rubutu.
"Ina so zan je Kaduna."
Wayar na hannuna sama da mintina goma sannan ya dawo min da amsa.
"A dawo lafiya."
Kenan ya amince na tafi duk in da zan je bai damu ba. saboda ya gaji da ni yanzu ba ya buƙata ta a cikin rayuwarsa. Sai kawai na kashe wayata na mai da ta cikin jaka a kusa da window na zauna sai na jinginar da kaina ina kallon giftawan motoci hawaye masu zafi suna bin kumatuna, sai na saka hijabina a cikin rabin fuskata saboda kar hankalin mutane ya dawo kaina. Amma ni dai na san mun daɗe muna tafiya sannan har muka shiga kaduna kuka na ke yi.
A tashar Kaduna na sauka ana ta kiraye kirayen sallar azahar. Ko da na sauka har jiri na ke gani, drop ɗin adaidaita na samu zuwa anguwan Rimi in da gidan Amina ya ke. Allah ya sa ban ɗauko wani kaya ba daga ƙaramin akwati sai ƙaramar jakata. Bayan na sallami mai adaidaita ina jan jikina da na ke ji kamar na faɗi jikina har ya na rawa rawa bakina ya bushe kamar yadda zuciyata ta bushe.
Get ɗin na buga megadi ya buɗe ya na tambayana wajen wa na zo sai na ce masa matar gidan, bai sanni ba domin kamar an sauya megadin ne.
Kafin ma ya tsaya min wani magana na ce masa ni yayar matar gidan