Author : Janafty Category : Hausa Book Store
gori.
Abin fa ya tsaya min a zuciya cikin sanyin jiki na miƙe ina tattara tarkacen abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen. Na gaji baya na har ciwo ya ke yi na saka anemin wata ƴar aiki, amma ba a samu ba can kwanaki na yi ma Inna Mariya mgana ta kawo min wata yar anguwan su amma ko sati ba ta yi da fara zuwa ba na ce ta bar shi kawai saboda ba ta iya aikin ba in ma ta yi sai na sake yi, in za ta yi shara bara da bana in mopping ne ta jiƙa min gida da ruwa. In kuma wanke wanke ne duk ta haɗe masu karni waje ɗaya kuma su yi ta warin omo ba ta wankewa da kyau ballantana ta ɗaureye su da kyau shi ya sa kawai na haƙura amma ni kaina na san zai yi wahala na samu mai aiki kamar Saude.
Ɗaki na koma na zauna a gefen gado cikin sanyin jiki. Na rasa me ke min daɗi haka kurum zuciyata sai ta cunkushe, na zauna shuru kawai ina ta nazarin rayuwa ƙaran wayata da ke gefena ya dawo dani daga tunani mai zurfin da na faɗa ina dubawa sai na ga Munnira ce amma har wayar ta katse sai na kira ta daga baya. Duk da ban san dalilin kiran ba amma ina tunanin kan batun bikin autar su Hauwa ne Sakina da za a yi nan da sati biyu. Mun yi ankon can Rano sannan mu ma mun fitar da anko mu uku.
Saboda duk duniya Hauwa ba ta da wasu ƙawaye makusanta ta a Kano irin ni da Munnira. Haka nima duk da dai ga su facololina amma kuma sun riga sun zama aminaina ma su taya ni kuka in dariya ne mu yi tare in kuma na baƙin ciki ne su ta ya ni su ne mutane na farko bayan iyayena da ƴan'uwana ma su zama kusa da ni a duk yanayin farinciki ko baƙin ciki. Nima shi ya sa in sha'anin su ne na ke ɗaukan shi da muhimmaci yanzu ma muna maganar gudummuwar da zamu haɗa ma Mamansu Hauwa mu aika da shi kafin lokacin bikin ne.
Nima har wayar ta katse ba ta ɗauka ba sai na ƙyaleta na miƙe kenan zan bar ɗakin sai ga shi ta sake kirana sai na koma na zauna. Cikin fara'a na ɗaga kiran ina faɗin.
" Mata a gidan Nasiru."
"Uwargidan Alhaji Injiniya Tafida ba"
Sai na ƙyalƙyace da dariya, itama ta na taya ni ina ji Samir na kuka yaron da ta ke goyo. Yanzu haka daga ita har Hauwa goyo su ke yi sun sake haihuwa. Ni ce dai Allah bai kawo karshen lamarin ba in kuma shi ne na ƙarshe to ina masa godiya domin ya yi min ni'ima ni'imar da ya tsame ni a cikin waɗanda ma bai taɓa ba ma haihuwan ba.
Bayan mun gama gaisawa da tambayan yara sai muka gangara kan mganar mu. Mun tsaya akan cewa za mu haɗa ma Hauwa 50k Munnira za ta turo min sai na haɗa na tura ma Hauwan mu ce gudummuwar ce ba yawa.
"Hakan ya yi. Zan tura miki zuwa anjuma. To mganar tafiyar mu fa?
"Mu je ana gobe biki. Sai mu dawo ranar lahadi ko?
Na ba ta amsa, sai ta ce hakan ma ya yi itama daman ta riga da tambaya ni ko na faɗa mata ba ma mu yi mganar ba.
"To sai ki yi ƙokari ki yi masa magana duk da na san ba zai hana ki ba."
"Uhm yanzu nan ya gama ƙare min tanadi Munnira."
"Me ya faru?
Munnira ta tambaya ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Kin ji yadda ya ta so min Munnira? Har ya na ce min wai ni wani irin suna ne ba ya kira na da shi a gabanta ita ba ta taɓa nuna damuwa ba sai ni. Har ya na ce min na kama girma na."
Munnira ta bushe da dariya har da ƙyatatawa. Har sai da na ji haushin ta ina faɗin.
"Ban son iskanci fa Munnira."..
Da ƙyar ta tsagaita da dariyarta ta na faɗin" Wallahi abin ne ya ba ni dariya. Lalle an nuna miki iya duniya Sadiya ke ma me ya kai ki? Ina ruwanki da sunan da ya ke kiranta? Ba Daugther ba Allah ya sa ruhinsa zai kira ta bai ma kamata ki nuna kin san yana yi ba, ballanta har ki nuna damuwar da zai samu damar faɗa miki mgana"
"Ni fa haushi ya ke ba ni. Abu kaɗan ya ce Daugther."
"To ina ruwan ki? Ke ma wallahi laifin ki ne, ke kika jawo duk maganganun da ya faɗa miki maganar gaskiya fa kenan"
A daƙune na ce" To na ji ai shike nan"
"Ba maganar shike nan. Gaskiya ce. Ke ma yadda na san ki da kama kanki me ya kaiki shiga abin da bai shafe ki ba wannan karon?
"Ttsautsayi."
"Allah ya raba mu da tsautsayi to."
Munnira ta faɗa ta na min dariya sai na ji haushi na kashe wayata na bar ta ta na min dariya.
Nima sai daga baya na yi ma kaina Allah ya ƙara da ban yi magana ba, da bai samu damar faɗa min maganganu son ran shi ba, da haka na yaƙice tunanin haka na shiga ayyukana amma a ƙarƙashin zuciyata ina ta auna maganganun Yallaɓai ba wasa ba ya faɗa min mganganu masu zafi amma tun da ni na shiga huruminsa duk ma abin da ya faɗa min ai ni na jawo shi.
Ɗan wannan maganar ashe shi Yallaɓai ya ɗauka da zafi da ya dawo gidan ina masa sannu da zuwa, da ƙyar ya amsa ni kamar na faɗa masa cuta ina ganin haka na kama kaina domin nima ina da zafi ba zan bari ya ɓata min rai ba, in hakan ta faru to ni da shi ba za ta yi mana kyau ba. Abinci ma da na haɗa masa nan ya bar min kayana bai taɓa ba da safe ma tea kawai ya sha ya fice jira ya ke yi ƙila na sake bashi haƙuri bayan duk haƙurin da na bashi jiya ai ko sai da a yi zama a haka.
Ranar daman ya bar gidana kuma har ya koma gidan Gimbiya ya gama kwanakinsa bai kirani ba, sau ɗaya ya zo gidan daddare shima wasu takardu ya zo ɗauka. Yadda ya basar da ni nima haka na basar da shi, tun da har na bashi haƙuri da farko ni kuma a raina na ƙudiri niyyar ba zan ƙara bashi haƙuri ba kuma. Kar ma ya haƙura shi ya sani.
Ga shi ina son na tambaye shi maganar zuwa Rano amma ba fuska. Cefane ma Salisu ya kawo min kuma da in zai kawo Yallaɓai na kiran waya ta ya faɗa min amma ranar bai kirani ba, ni kuma da ya zo gidan ban yi masa mgana ba.
Ranar da zai dawo wajena ranar Matar Musbahu ta zo min yini Mubeena mai kirki da ita. Yadda Musbahu ya ke ɗan gidana itama haka ta ke a wajena domin shi da kan shi ya nuna mata ta daraja ni shi ya sa ta ke girmanani. Ta na zuwa gidana sosai ta yi min yini. Ni ko bai fi sau biyu na taɓa zuwa gidanta ba da lokacin bikin su sai kuma da muka je tare da su Hauwa, na ji daɗn zuwanta da ya ke ta na da wayewa ta na ma karatu ne anan BUK Kano sai dai ta na shekaran karshe ne, ga ta ba ta son jiki in dai ta zo tare muke yin ayyukan mu, ita da bakinta ta ke faɗa min acikin hira Anty Bahijja har gida ta je ta na yi mata faɗan wai ta kama ni kamar ni ce yayar mijinta. Su za ta kama domin su ne dangin mijinta ni ma bare ce kamar ita. Da ta faɗa min dariya kawai na yi ni yanzu ai sun daina ba ni mamaki harkan gabana kawai na ke yi, tun da aka yi mana tsakani ba ta ƙara haɗo mu ba, duk da dai suna yi ta bayan fage. Yanzu har Halima na daina ganinta a gidana ta koma yar tsagin Gimbiya.
Ƴaƴansu daman ba sa zuwa gidana amma gidan Gimbiya har truruwa suke yi mata ni wannan bai dame ni ba. Amma nima ƴaƴana sun daina zuwa musu hutu tun da abin na su ya koma wariyan lautin fata kowa ya riƙe na shi, ko da ya ke yanzu sun daina mararin su sun koma mararin su Khalipa yanzu su ne komai suka samu na su ne ni na manta rabon da su yi ma su Jidda ma wani abun ma ban damu duk da na san a baya sun yi daga baya da suka samu waɗanda suka maye musu gurbinsu sai suka manta da su. Ban lura da wannan domin babu abin da ƴaƴana suka nema suka rasa. Yallaɓai mai yi ma iyalan shi ne shi ya sa ban cika damuwa da wasu abubuwan su ba.
Waina na yi ranar Mubeena ta ta yani muka yi aikin wainar. Har dare ta na gidana sai da Yallaɓai suka taho tare da Musbahu sannan suka koma gida tare bayan shima ya ci wainar a nan na kuma saka musu a kula su ka tafi dashi. Yallaɓai ya ɗan sake amma ba sosai ba har yanzu da sauran cin mgani a muryansa da ayyukansa ni kuma sai na nuna kamar ban ma san yana yi ba zuwa washegari sai ya saki ya dawo ya na min magana kamar ba shi ne ya ke ci min mgani ba. Fuskar da na gani ya sa na yi masa mganar bikin Rano nan ta ke ya amince ya kuma turamin 30k ya ce na yi na mota da guddumuwa.
Da ya yi maganar yara na ce ga Jidda za ta iya kula da gida. Shi fa a ganin shi har yanzu Jidda yarinya ce ita kanta ta na bukatar kulawa sai na ce to ya kwashe su zuwa gidan Gimbiya kafin na dawo sai ya ce sai abin da ya gani.
Ko Munnira ban kira na sanar mata an bar ni ba. Sai dai na faɗa ma Hauwa muna tafe ranar jumma'a ta na ta murna. Ita tun ranar litini ta na can, da na tura mata kuɗin da muka haɗa kamar ta yi kuka da ta kirani ta na min godiya na ce mata ai mun zama ɗaya. Marwa na kira ranar al'amis ana gobe tafiyarmu na ce mata muna tafe ta buga tsallen ihu ta na murna daman ai ta san da bikin tun da ni da kaina bayan bikin na su na je Rano na ɗauki Marwa na kai ta har gidan su Hauwa na yi ma ta uwar ɗaki da mamansu Hauwa da ƙannenta.
Su ka kuma karɓeta hannu biyu suna zumunci yanzu bayan gidan iyayen mijinta ba ta da kamar gidan su Hauwa duk da har gidan su Gimbiya ta na zuwa amma sai wani abu ya faru na jaje ko na murna. Kawu Abba kulle gare shi ba ya son yawo ko Kano tun da Marwa ta yi aure sai da ta yi wata biyar sannan ta zo ganin gida daga nan kuma sai da ta dawo gida jego da ta koma ba ta dawo ba sai bikin Antin Ya Murja na su Jawahir ba su kwana ba a ranar suka zo tare da matan su Kawu Sa'adu a kuma ranar suka koma.
Kafin safiyar jumma'a na shirya kayana tsab don ma telana ya ɓata min lokaci akwai kala ɗayan da bai gama min ba sai da na jira. Munnira ta biyo min, ba mu tafi ba sai da su Jidda suka dawo makaranta sannan muka ɗau hanyar Rano. Yallaɓai ba gidana ya kwana ba a waya muka yi sallama. Mun isa Rano da wuri shi ya sa ko su Anty Bahijja acan suka iske mu, mun baje ana komai damu a ka gaggaisa kusan ita Anty Bahijja ko yaya ne sai ta taɓa hali sai da ta ce ma Munnira wai ka ga Aminan yayar amarya har an hallara akan lokaci Munnira ta ce tabbas dole mu hallara akan lokaci domin ta Hauwa shirye shirye a matsayin mu na Amininta.
Marwa nan gidan su Hauwa ta so muka haɗu da mangariba ta tafi za ta ce gida ta shirya ta na da aikin dare ne ranar. Mu kuma nan gidan su Hauwa muka kwana washegari aka tashi da yinin biki da ɗaurin aure, ni kwata kwata tun bayan saukan mu ba mu yi waya da Yallaɓai ba kuma bai faɗa min zai zo ba, duk da na san zai zo ɗin amma ban ɗauka tare da matarsa za su zo da yara ba sai ganin su Jidda kawai na yi wa ya kawo ku? Wai tare muke da Anty Gimbiya da Abba. Sai ga Khalipa da ita kanta Gimbiyar ɗauke da Anwar kenan shi ya tuko su alhalin ni bai nuna min ma za ta zo ba. Ban nuna mata wani abu ko a fuskata ba muka gaisa. Lokacin ni ban ma yi wanka ba sai daga baya ankon less ɗin da muka yi mu uku muka saka gabaɗayanmu wani marroon da baƙi yi yi mana kyau duk in da muka gifta sai an ce kai leshin nan ya yi kyau. Har cikin gida su Yallaɓai suka shigo Allah ya sanya alheri da shi da Kawu Abba da Tariq sai Musbahu sai Nasir da Muttaka. Sannan a ɗakin samarin gidan su Hauwa suka zauna aka kai musu abinci ni dai ban je ba domin na ga Gimbiya ce ke kai da kawo sai na bar mata amma dai mun je dukkan mu mun gaishe da mazajen namu.
"Madam kin fa samu duniya"
In ji Yallaɓai ya na kallona ni ko sai na kalle shi ina yi masa fari kafin na ce.
"Allah ko! In ma duniyar ce ai kai ka ba ni ita a hannuna Yallaɓai."
"Wannan gaskiya ne Uwargidan Alaji Tafida ba."
Tariq ya faɗa ya na dariya Kawu kan cewa ya yi." Ba dole ya ba ta duniyar ba. Saboda ita ce ta san shi tun kafin duniyar ta same shi."
"Tariq ya su Farida? Sai ban gan ta ba."
Na faɗa ina kauda maganar Kawu Abba tun da na ga Gimbiya ta shigo lokacin Yallaɓai sai fama da yara ya ke yi, Khalipa ya manne masa ga Anwar a jikinsa duk sun ƙi bari ma ya ci abinci ni dai ina gefe a raina na ce can ku ƙarata.
"Wallahi ba ta samu zuwa ba saboda makarantar yara."
Tariq ya ba ni amsa, zan yi magana Munnira ta ja ni muka fita waje ta na min raɗa.
"Ke na ga matar nan sai wani rawan kafa ta ke yi ne"
Sai na kalleta ban ce komai ba na wuceta ina faɗin" Ta yi ta gama Munnira."
Daga haka na koma cikin gida na bar su, can ma aka fara ƙidan ƙwarya muka je can muna chasewa da aka ce filin na yayyen amarya ne, muka shige fili ni da su Hauwa muna ta rawa ana yi mana liƙi sai can da yamma su Jidda suka ce za su tafi Gimbiyar ma ba ta min sallama ba a raina na ce a gayas, to uban gayyar bai min sallama ba ballanta ita.
Amarya cikin garin Kano za a kaita a daran aka tafi da ita amma mu ba mu je ba. Tun da muna gari muka ce sai mu sa rana mu je daga baya.
Ranar a gidan Marwa muka kwana washegari muka yi shirin dawowa gida. An ba mu kayan biki su cincin da dublan da kayan robobin da aka raba can muka bar Hauwa sai ranar talata za ta dawo. Amma tare muka taho da wasu dangin su kuma za su je gidan Amarya.
Ko da na koma gida ba kowa, sai da na buɗe ashe suna can sharaɗa gidan Gimbiya. Yallaɓai bai kirani ba sai ni da kaina da na kira shi na ce na dawo. Shi ne da daddare sai gashi sun taho da yaran har da Khalipa da na ke murnan kwana biyu ya bar ni na huta ashe ba haka ba ne. Ranar ga gajiyan biki hayaniya ta yi yawa a can ba mu wani samun barci, amma yaron nan haka ya hana mu barci a ɗakin su Jidda na kai shi ya kwanta saboda ya fara barci a falo amma sha biyu saura muna kwance a ɗaki muka ji ihun shi dole Yallaɓai ya je ya ɗauko sa ya saka shi a tsakiyarmu kamar wani yaro haka ya tashi cikin dare daga ya ce zai sha ruwa sai ya ce zai ci abinci. Gabaɗaya ya hana ni barci, ni ƴaƴana ba su hana ni barci sai ɗan kishiya. Yaro kamar an haife shi da makirci da kissa a daran Yallaɓai ya tashi ya haɗa masa tea. Ban san yadda aka yi ya cire masa pampers ɗin jikinsa ba, kawai sai farkawa na yi da asuba na ga Khalipa ya kelayamin fitsari a sabuwar katifa ta.
Tsabar baƙin ciki ma na kasa mgana. Wallahi ko su Jidda ba su yi zaman yi min fitsari a kan katifa ba domin tun zamanin napkin shi na ke yi musu in zamu kwanta. Kuma ba na bari su sha ruwa daddare ko su sha tea amma saboda iskanshi shi Yallaɓai cikin dare ma ya ke tashi ya na ɗura ma yaro ruwa ba dole ya yi fitsari ba da na ga kalli wajen har sai da ya yi shaida a zanin gado kawai sai na kalli Yallaɓai lokacin ya dawo daga sallar asuba Khalipa na can ɗakin su Jidda.
"Yallaɓai cire ma Khalipa pampers ka yi? Ji fa yadda ya yi min fitsarin kwance."
Kai tsaye ya ce" E jiya ne ya na ta rigima sai na cire masa sai na ga ma duk ya cika shi da fitsari."
Ban sake magana ba sai shi ne ya ɗago ya kalleni kafin ya ce" Ba komai ai fitsarin yaro ne. Ki kuna fanka kawai ni bari na je can ɗakin na ɗan runtsa."
Daga haka ya fice ya bar ni ina bin shi da kallon takaici. Sai da na cire zanin gadon sannan na