Author : Janafty Category : Hausa Book Store
ne kuma window ɗin su na haraban gidan ne.
Sai ya miƙe daga shi sai bakin wando da singleti ya fita falo sai ya ga Sadiya kwance a falon yara kallo take yi ko kawai ta na kwance ne bai sani ba.
Ina daga kwance na ga fitowarsa sai na yunƙura na miƙe zaune ina faɗin" Ina kwana."
Sau ɗaya ya kalleni sai kawai ya yi gaba ya na faɗin" Lafiya lau.'
Bari na je waje na ji ana buga get."
Ya na gama faɗin haka ya buɗe kofa ya fice na rasa shi da kallon mamakim to wai har na fara masa baƙi a ido ne da ya sa Yallaɓai daga jiya zuwa yau ba ya son haɗa ido da ni? Zaune na ke ina mamakin shi, ni ko shigowar mota ma ban ji ba sai dai na ji kamar mgana daga falo sai na miƙe na kawo gabda ƙofa zan buɗe sai ya rigani turowa ya shigo sai muka haɗe ya kalleni na kalle shi.
"Nene. Nene ce ta zo."
Cikin mamaki na ce" Nene fa?
Saboda ni dai tun da muka dawo gidan nan sau ɗaya ta taɓa zuwa shima rashin lafiya Baby ta yi shi ne ta zo duba ta. A wancan gidan kuwa har muka tashi ba ta taɓa zuwa ba.
"E. Ta ce ta na son mgana da ke."
Haka ya faɗa min kafin ya wuce.
"Magana da ni?
Na maimaita a cikin raina.
"To wata mgana ce?
"Ta wuce ta auran Yusuf da Gimbiya"
Kamar wahayi haka na ji zuciyata na saƙa min magana.
Uhm kawai nace a saman leɓena sannan na bi bayan shi domin na ɗauko hijabina ina shiga na ganshi ya saka riga zai fita ya raɓa ta gefena ya fice ni kuma na shigo ciki na ɗauko hijabin sallah na saka nima na bi bayan shi amma ni sai da na fara biyawa ta kitchen na dauko mata ruwa da lemu lokacin safe ne domin tara ma ba ta yi ba, bayan tafiyar yara makaranta ne ba daɗewa na kwanta a falon da Yallaɓai ya fito ya ganni kwance.
*Janafty*
*TKG*
05.
Da sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi.
Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne.
Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma kan kujera na zauna sai na koma na zauna kan kujera mai zaman mutum biyu da ke gefen in da Nene ta ke zaune.
"Anty Sadiya ina kwana."
Musbahu ya gaisheni yana kallona na amsa ina faɗin kwana biyu idon sa kenan ya na yar dariya ya ce" Yallaɓan na ki ne har yau bai cire min ranar hutu ba shi ya sa bakya ganina"
Mirmishi na yi amma ban yi magana ba, yadda Yallaɓai bai kalleni ba nima ban damu da na kalle shi ba domin tunda na shigo falon kansa na ƙasa ya yi shuru kamar wani mara gaskiya. Ko da ya ke ai mara gaskiyan ne tunda menene maraban dambe da faɗa?
"Ina takwarata da Maimunatu? An tafi makaranta ko?
Kaina na ƙasa na amsa ma da Nene da cewa" E Nene.'
Sai ta rausayar dakai kafin ta ce" Allah ya ba da sa'a. Allah ya sa a samu karatu mai albarka."
Muka amsa da Amin gabaɗayanmu.
Shuru na wani lokaci domin shi Musabahu wayarsa yake ta latsawa ganin haka ya sa na gyara zama ina faɗin" Nene a kawo abun karyawa?
Da sauri ta ce" A'a Alhamdulillah. Sai da na karya a gida na fito sai dai in Musbahu ga shi nan."
Ta faɗa ta na kallon shi, sai da ya ɗan yi shuru kafin ya ce" Tea kawai matar Yallaɓai."
Sai na miƙe ina faɗin bari na je na haɗo masa, har na fice daga falon ba wanda ya ce mini komai, daman already akwai ruwan lipton a cikin fulas, sai kawai na soya masa ƙwai guda uku ina cikin soyan ma ya leƙo ya ce gashi a falon su Jidda sai na ce to ina gama soya kwan na kai masa nan tare da mug da fulas ɗin ruwan zafi sannan na kwaso masa kayan tea ɗin har da buredi.
"Sannu da aiki Anty Sadiya."
"Yauwa."
Na amsa masa ina ɗan mirmishi hannuna na wanke sannan na koma falon wajen Nene na koma na zauna kenan Nene ta kalli Yallaɓai da ke zaune jugum kamar wani marayan da ya zo neman abin sakawa a bakin salati.
"Tafida."
Ta kira sunan shi sai ya dago ya na kallonta lokaci ɗaya kafin ya ce" Na'am Nene."
"Ba mu waje. Zan yi mgana da Sadiya daga ni sai ita."
Da ni da shi gabaɗaya mun kalli juna sannan muka juya muna kallon Nene sai ta gyara zama kafin ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta na ƙara jadadda mganarta.
"E haka na ce. Ka ba mu wuri mu yi mgana Tafida."
"To Nene."
Haka ya faɗa sannan ya miƙe a hankali kamar wanda ƙwai ya fashe ma a ciki haka ya fice daga falon lokaci ɗaya ya na mai rufe mana ƙofar falon a sannu kar ta yi ƙara. Da ga ni har Nene da kallo muka bi shi ni kuma da ita kowa a cikin ranshi ya na da nashi tunani, ni dai ko tausayinshi ban ji ba domin a ganina wannan shi ake kira daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.
Shuru na ɗan wani lokaci kaina na ƙasa ina wasa da gefen hijabina na ji Nene ta kira sunana.
"Sadiya."
Sai da na ɗago na kalleta kafin na ce" Na'am Nene."
"Na zo ne mu yi wata mgana da ke. Kuma kar ki yi tunanin ko mijinki ne ya turo ne"
Na kalleta sai ta gyaɗamin kai kafin ta cigaba da faɗin" Ko ɗaya bai ma san zan zo ba. Bai kuma san da abin da na zo da shi ba, ni ce kawai na yi tunanin na ga lalle ya dace na zo na same ki mu yi mgana baki da baki."
"Haba Nene don wannan shi ne sai kin zo da kanki? Ai da kirana kawai za ki yi a waya na je gida na same ki "
Na faɗa cikin sanyin murya amma cike da biyayya. Ko ban ɗauketa a matsayin uwata ba na ɗauketa a matsayin uwar mijin da ta haifa min miji na aura sannan uwar mijin da ban taɓa samun matsala da ita ba. Tsakanina da ita akwai girmamawa da mutuntatawa mai yawan gaske.
"A'a maganar ta ki ce, shi ya sa na ce gwara na zo da kaina."
Ta faɗa ta na kallona, sai na jinjina kai ban yi mgana ba.
"Sadiya kan mganar auren Tafida da Saudatu ne."
Duk da na san maganar, kuma daman a cikin wani shashe na zuciyata na faɗa min ƙila dalilin zuwan Nenen kenan amma a yadda na ji maganar a bakinta ya sa sai da gabana ya amsa. Wannan abun da ya tokaremin a ƙirji na ji ya taso min amma sai na danne ban nuna komai ba illa kai da na gyaɗa mata amma na kasa iya furta wani abu.
"Na san kin ji labari. Tun da jiya Tafida ya je cikin damuwa ya na sanar da ni kin ji labari ba tare da shi ya sanar dake da bakin sa ba."
Kaina na sunkuyar domin na rasa ma abin da zan ce, Au ashe daman ya san na sani? Na rasa ma wani suna zan kira Yallaɓai da shi a dai dai wannan lokacin ba ma, kawai kai na rausayar ina jin kamar duk duniya ko marayu ba su kai ni zama a bar tausayi ba.
"Ba ki ce komai ba Sadiya."
Nene ta ƙara katsemin tunani da maganarta na ɗago na kalleta itama ni ta ke kallo cikin karantar yanayina rasa abin da zence ne ya sa na gyaɗa mata kai kafin na ce" E. Na sani."
"Tun yaushe kika san da labarin?
"Tun a ranar da aka ɗaura auren."
Na bama Nene amsa kai tsaye sai ta jinjina kai kafin ta ce" Ba zan yi mamaki ba. Domin mgana in ta wuce mutun ɗaya ta fara kirga uku to ba ka isa ka rufe bakin kowa ba, in ka rufe na wani, na wanin ba za ka iya dakatar da shi daga mgana ba. Ba kuma zan matsa sai na ji daga wajen da kika ji ba, zan je kai tsaye kan batun da ya kawo ni wajen ki Sadiya."
Kaina dai na ƙasa ina ta wasa da gefen hijabina amma zuciyata zafi ta ke yi, kiran sunana ta sake yi na amsa sannan ta ce" Zan ba ki labarin yadda lamarin ya faru, ba domin ki yarda Tafida ba da gangan ya ƙi faɗa miki ba sai domin na ƙara samar da kyakyawan fahimtar juna a tsakanin ku."
Ba tare da ta jira cewata ba ta fara gaya min yadda komai ya fara, ta in da aka hau da kuma ta in da aka sauka ta karishe da faɗin" Wallahi Allah ɗaya ne Tafida ya so na bashi ko kwana daya ne domin ya samu damar sanar da ke, ni kuma na ga duk ɗaya ne, ko ya sanar da ke kafin a ɗaura ko bayan an ɗaura tunda sai daga baya za a yi tariyan. A gabana kuma ya roƙi yan'uwansa da cewa su yi shuru da bakinsu ba ya so ki samu labari a bakin kowa sai daga bakin sa ba ki ga yadda ya ɗaga hankalinsa a jiyan da ya zo ya sameni ya na faɗa min ya haɗu da yayanki har ya yi masa murna sannan ya sanar masa ke kika faɗa masa. Ya damu ya ce ya na jin kunyar ki shi ya sa tun kwanaki ya kasa iya faɗa miki ba kuma domin don ya aikata haramci ba, a'a sai domin ke ɗin kina da daraja da ƙima a wajensa kina da mutumcin da ya ke tsoron ya sanar da ke labarin da zai ɗaga miki hankali, ya na jin kunya da nauyin faɗa miki ya yi aure ba tare da ya sanar da ke kafin auran ba. Yau da safe na kira shi ya sanar da ni bai faɗa miki ba sai na yi tunanin ya kasa shi ya sa ba tare da sanin kowa ba na ce Musbahu ya kawo ni domin ni na zaunar da ke na warware miki dukkan abin da ya faru na kuma ƙara tunatar da ke abubuwa ma su girman gaske da Ubangiji ya ba ki wanda nan gaba kar kishi ya rufe miki ido ki manta da su ko kuma ki kasa kallonsu a wani baiwa ko nasabar da Ubangiji ya ba ki Sadiya."
Nene na magana amma idanuwana sun cika da ƙwalla ina ƙoƙarin hana su zubowa a saman fuskata. To bayanin na menene! Ba ta saka shi ya auri ɗiyar ƙawarta ba to ni kuma me ta ke so ta faɗa min? Wannan fa shi ne an cuceka amma ana so a hana ka yin ihu da kuka, har ga Allah na ga baƙin Nene me ya sa ba za ta bari Yallaɓai ya yi mgana da ni kafin a ɗaura auren ba? Sai na ji zuciya ta sosu kuma a ganina ta yi min rashin adalci da za ta ce a yi min kishiya kai tsaye ba ta re da shiri ko tsammani ba."
Runtso idanuwana na yi, hawayen da na yi ta riƙewa suka zubomin shar! Duk Nene na kallona amma sai na kasa gefen hijabina ina sharewa a lokacin in za a tona zuciyata daga Uwar har ɗan duk haushin su na ke ji amma ina ƙoƙarin dannewa kuma a saman fuskata ina karyata abin da na ke ji a cikin zuciyata.
"Ki yi hakuri Sadiya. Ki yi hakuri."
Nene na bani haƙuri ina jin kamar ta na ƙara ma ciwo na barkonu ne, ina ta danne kuka na amma ina share hawaye ne wasu suna ƙara sauka kamar an buɗe famfo tun kuma da labarin auran nan ya zo min ko Yallaɓai ban taɓa zubar da hawayena a gabansa amma yau sai na ji na kasa iya wannan dauriyan ganin hawayen sun riga sun taho kai tsaye sai kawai na barsu suna ta zuba sharr, in suka kwaranya a saman fuskata har suna gangarowa a saman hijabin jikina, Idanuwana suna mai kallon zanen cafet ɗin da ke falon, ina jan hanci irin na masu kuka, so na ke yi na samu keɓewa ni kaɗai na fashe da kuka na yi birgima ko domin na ji sauƙi sauƙin abin da ke suka na acikin zuciyata.
"Ki yi haƙuri Sadiya. Daure na san kishi. Na san kishi ya na da zafi Sadiya amma in aka yi haƙuri za a ci riba wata rana."
Kalamanta ya sa na kalleta, tabbas ta san kishi, ita da aka auro ma uku. Kenan itama ta san irin zafin da na ke ji a cikin zuciyata sai na ji na godema Allah a cikin raina ko banza za ta fahimci kwataƙwacin irin ɗacin da na ke ji a cikin zuciyata.
Kaina na ƙara maidawa ƙasa lokaci ɗaya ina share hawayen saman fuskata da gefen hijabin jikina muryata har ta fara chanzawa na ce.
"Bakomai Nene. Allah ya ba mu zaman lafiya da juna."
Ta amsa da Amin Amin cikin mirmishi kafin ta ce" Sadiya wallahi ban yi ma Tafida ta yi auran Saudatu domin na ga kin gazamin ba. Ko na ga shi kin gaza masa ba, sai dai kamar yadda na faɗa miki tsohon kuduri ne a zuciyarmu ni da Hajiya ina kuma son na cika shi kafin na bar duniya shi ya sa auran ya zo bagata tan. Amma wallahi Allah ɗaya kenan ba ki taɓa min wani abu cikin sanin ki ba ko ma kin yi min a cikin rashin sani na yafe miki na sha faɗa a gaban idon ki a kuma bayan idon ki bakomai a tsakanina da Matar Tafida sai mutumtawa da Darajawa saboda haka kar ki saka a ranki ko kin gaza ne, ko kuma na ware ki, da ke da Tafida da Saudatu ɗaya kuke a wajena, ba bu bambamci a tsakaninku kamar yadda Saudatu ta ke ƴa a wajena kema ƴa ce domin iyayenki ranar da kika zama ɗaya daga cikinmu ni suka ba ma amanarki suka kuma ce min ni uwa ce a gare ki na yi miki gyara in kin yi kuskure tamkar yadda zan yi ma ƴaƴana na cikina ko kin manta Sadiya?
Kai na gyaɗa ai ba zan manta wannan ranar ba. Inna Mariya ce ta riƙa jadaddama Nene ƴa suka kawo mata ba suruka ba.
Kai na ƙara jinjinawa kafin na ce" Haka ne Nene."
Sai kuma na kalleta kafin na ce" Na gaza Nene. Na gaza wajen ba ki jikoki masu yawa daga tsatson Tafida kamar yadda kike so."
"Kul kar ƙi ƙara wannan mganar Sadiya. Ba ki gaza ba kin kuma biya ni domin kin haifa min takwara kin kuma haifa min ƴa. Ni ko me na ke nema a duniya da Allah bai ba ni ba? Allah na tuba ni jika wanne ne ba a haifa min ba Sadiya! Ki godema Allah kina da biyu wata ɗayan ma ba ta samu ba shi ta ke nema. Ki kuma gode ma da Allah da ya baki har biyu sai ki yi ma Allah butulci da cewa gazawa ce? Maza ki nemi gafaran Allah domin ya yi miki kyauta ba ki gode masa ki nemi gafaran shi ki gode masa sai ki ga ya ƙara miki da ni'imar da ta fi irin Ni'imar da ya baki a baya."
"Astagafurilla. Astagafrilla."
Haka na shiga furtawa da sauti, domin sai na ji tsoro kar na batulce ma Allah ya ƙi ƙara min wata haihuwar domin nan duniya ba ni da wani buri sai na ganin Allah ya sake ba ni haihuwa ko da guda ɗaya ne. Zuciyata har rawa ta ke yi in na yi hasashen ƴaƴa biyun da Allah ya ba ni wata rana in ya so zai iya ɗauke kayansa sai na ji jikina har ƙwaƙwalwata ya na amsawa cikin wani yanayi wanda ba ki ba zai iya misaltawa ba.
Nene ta ga yanayina ina ta rawan jiki sai ta ce na yi ta kiran sunan Allah har sai na samu natsuwa innalillahi na cigaba da maimaitawa a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai ga shi na dawo cikin natsuwa Nene ta durkusa da kanta ta buɗe ruwa ta zubamin a kofi ta ba ni ta ce na sha da bismillah. Ban yi musu ba na karɓa na sha da yawa na miƙa mata kofin ta karɓa ta maida shi saman farantin sannan ta koma ta zauna ta na kallona ina ta sauke numfashi.
Sai da ta fahimci na samu natsuwa sannan ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da cewa duk abin da na ga ya faru da bawa daga Ubangiji ne kuma duk abin da ya aikata dai dai ne shi ba ya kuskure, mu ƴan adam mu ke kuskure amma shi Ubangiji duk abin da ya yi a garemu mai kyau ne. Ta umarce da shawaran da daaina tunani na fauwalama Allah komai. Wataƙila jinkirin alheri ne nan gaba Ni'imar za ta fi ta baya yawa. Ina gyaɗa kaina cikin gamsuwa ina faɗin.
"Allah ya sa. Allah ya sa. Na gode Nene Allah ya saka da alheri"
Ta amsa da Amin kafin ta ce" Ina fatan kin fahimce ni. Sannan a mganganuna kin fahimci irin matsayin da kike da shi a zuciyar Tafida ko?
Sai na kalleta alamun bangane ba sai ta gyara zama kafin ta fara da kiran sunana.
"Sadiya ba ki fahimci irin martaban da ubangiji ya yi miki a acikin zuciyar mijin ki ba? To ko kin fahimta ba ki gane ba. Ni bari na warware miki irin taki baiwar da ubangiji ya yi miki ba ki sani ba."
"Sadiya."
Ta ƙara kiran sunana na amsa ina kallonta sai ta nuna kanta kafin ta ce" Kin san kishiyoyi uku Marigayi mahaifinsu su Tafida ya auro kafin rasuwarsa? Ba ta damu da mganata ba ta cigaba da faɗin" Zan faɗa miki wani sirrin da ban taɓa faɗa ma ko ƴaƴana ba. Ina yar yarinyata ya ƙara aure