DAN ISKAN NAMIJI HAUSA NOVELS BY FEEDYN BASH.txt

Author :  Farida Abdullahi (Feedyn Bash) Category :  True Hausa Novels

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 20.2K words

Allah sarki sis ba halinsa bane kinsan mutumin kirkine arfan din kawai tsautsayi ne suna meeting a office jiya aka kawo giya besantaba ya Sha shiyasa Amma haka baze Kara faruwaba




Cike da mamaki take kallonta wato harya tsarata ta tsaru dama ita Sam Bata da wayo duk abunda kace mata yarda take kamar yarinya take zuciyarta akwai saurin yadda Bata da zafafa fawa ta kalleta haka dai ya gaya Miki Amma Ni banyardaba anty kawai ki zamanki ke da mijinki Amma Ni bazan zaunaba aiko Zama Dole Bari kiga ta Kira babansu tagaya masa Bata da lafiya Kuma Maryam ta dage sai ta taho handsfree tasa ita maryamun eh baba Bata wayar ta karba tana turo Baki baba haba auta ta kwantar da hankalin ki Aina barwa nafeesa ke har aurenki nafeesa ta sheke da dariya itakuma tafasa ihu tana kuka nafeesa ta fusge wayar ta kashe




Ba kukan komai takeba sai na Zama gidan Dan iska tanaji aka sanar Mata da halinsa yaushe zata iya wannan zaman Sam bazata iyaba Zama gidan mashayi mazinaci ita kanta yayar tata tana tausaya Mata anmata lumbu lumbu an aureta bisa rashin sani tafado gidan Cikakken takadiri Dan iska Wanda duk wani abun iskanci Yana aikatawa tunda ance har caca yakeyi to meye bayayi na iskanci da haramci




Haka taita lallabata har yamma da kyar taci abinci wajen magariba sai ga shi ya shigo a nutse yai sallama suka amsa yaga taci kunu tayi dam sai Tai Masa kyau Dan yafi yarta kyau Dan dai ita batada hasken fatane a a lafiya nafeesa Naga kanwarmu nata fushi tana zumbura Baki wallahi gata Nan tun bayan fitarka taketa fushi Wai lallai saita tafi gida baba yace yabar Mana har aurenta wow gaskiya ya kyauta Mana mun gode Kuma tunda gidan takeso ku shirya na kaiku ku gaishesu nima na Kwan biyu banjeba bara nai wanka naci abinci mutafi ko




Cike da murna ta sakar masa kiss Tama manta da wata Maryam ganin haka Tai sum sum ta koma daki mutum a fuska a zuciya shedan mtsww Taja tsaki ku kainin wallahi bazan dawoba guduwa zanyi Nan shima ya rungumeta suka Fara shiga wata duniyar chak ya dauketa yai sama da ita saida suka gamsu sannan sukai wanka sukai sallar magriba sukaci abinci har Maryam sannan suka tafi gidansu




A hanya yake sanar dasu su Gama da wuri dan karfe goma da rabi ze tafi office ita dai Maryam abun yana bata mamaki wane irin aikine sai dare Shiba police ba ba soldier ba ba shi dawani kaki to aikin me take ta tambayi kanta ba amsa Nima tasani a tunani kujira mu tunano



*Naga alama book din Nan be muku ba Dan Haka na ajiye alkalamina daga yau indai Banga comment masu yawaba sannan banasan thanks ko sticker yadda nake typing nake rubutawa rubutu nakeso*



Nice Taku akoda yaushe


*Feedyn bash*
[10/3, 4:46 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN HALITTA*



*Wannan page din sadaukarwane ga kainuwa fans 1-12 nakune wannan kuyi yadda kukeso dashi nagode da comment dinku agareni Allah ya bar kauna ameen*




9-10



Haka suka karasa gidan sunata kowa nata sake sakensa a zuciya suka shiga sukai masa iso ya gaisa da umma da mama aka bude masa sitroom suka zauna da babansu sunata hira ya suna dakin umma sunata hira chan maryam ta mike tafito shiga dakin mamanta ta fada cinyarta mama gaskiya kisa baki ni bazan koma gidan nan ba nagaji badadi ke bana san iskanci kinsan halin mahaifinku jibi yadda kikai kyau kwana biyun nan dan kikai sannan kice ba dadi dan haka sawunki a likkafa tashi ku tafi Inda kuka fito bazaki jazan bala'I ba gun ubanku




Wallahi umma ba inda zani nan ne gidan ubana dan haka anan zan zauna rai bace ta koma wajen umman nafeesat tasa kuka ita batasan komawa gidan nafeesat gaskiya ita tagaji umma tace bazaki komaba yi zamanki yata bawanda ze takura miki Dama sangartace daga mura tawani kwasheki kwanta ki huta ki zamanki haba umma cewar nafeesat babane fa yace ya bar mana ita umma ta hade rai kebansan hauka yammata biyu muka aura masane Koko muma mahaukatanne irinku wuce ku tafi gida dare yafara nafeesat tana ta sharar kwalla ta fito taje dakin mama dan siyi sallama kafin taje dakin umma chan taje suka gaisa suka sha hira




Lafiya yata naga kina kuka cikin kuka tagaya mata umma ta hana maryam ta tashi su tafi ranta idan yai dubu ya baci jira ina zuwa taje takaraci fadanta basu tanka mata ba tunda kun maidani dutse bara naje na turo me iko da yar taki dan yata tana bukatar zamanta za'ai mata haka Ana wani wulakantata harda sata kuka me yar taki ta iya banda shagwaba da sangartata dakike A fusace tajuya taje sitroom takira babansu tagaya masa rai bace ya ce muje gidan dan sirikin nasa yaji meke faruwa bayan shiya rokeshi alfarma tun jiya ya kirashi yace yabarta a gidan saboda aikin dare yakeyi shiko wani nauyin aka rage masa shiyasa da suka Kira yace yabar musu ita tazauna danshi anrage masa wahala rai bace ya shiga gida




A fusace ke fito koni sa ankine bangaya miki kin koma gidan kenan ba fito nace jiki a sanyayeY umma tace haba Alhaji dakata bansa dakeba balle na kwashe dake bakuji takarar danai muku akan wannan maganarba ko jiki a sanyaye tace allah ya baka hakuri ke kuma maryam tashi ku tafi ta fashe da kuka ta rike umma dan ita harga allah tunda mutanen nan najiya suka gaya mata komai take tsoron arfan da gidansa dakyar umma ta bambareta ta fito tanata kuka nafeesat tace menai miki maryam kike guduna kike gudun zama dani ko ina cutar dbbake bansaniba ke yar uwatace karkimun wannan horon dan allah nasaba zama dake ke kike deban kewa kinsan shi bama zauni bane da daddare da yardarsa zaki zauna a gidan ai ki kwatar da hankalinki kanwata itama kwalla take tasan tsoron abunda ya faru jiyane a ranta



Itama maryam tarungume yar uwarta tana kuka bagudunki nake ba inada dalilina wanda ku bazaku ganeba tundaga jiya naji gidanki ya siremun rufe mata baki tayi dan karta Tona mata asiri kuwuce muje kwayi koke koken naku a hanya haka suka fice jiki a salube ko sallamar kirki basiyi da iyayensuba kowacce ranta cike da tausayin yayansu dakewa kawai sukai sunsan Alhaji akan kudi kuma yai musu takara indai maryam tadawo to kowacce ta tafi gidansu shiyasa umma tai haka badan ranta yaso ba Ita kanta tana kewar autar tata




Ya koma sitroom din jikinsa har rawa yake ai sun fita Kai suke jira allah ya tsare tashi kuje dare ya fara dubu Dari biyu ya bashi baba gashi ayi hidamar gida baba jiki na rawa ya karba sai zabga Addu'a yake godiya yake tamkar wani zautacce ko maroki sai haka ya isa haka dan allah baba nace banasan godiya kagamaimun komai tunda kaban auren nafeesat bara nashiga ciki miyi sallama dasu umma ya shiga ciki ya basu dubu Dari Dari dakyar suka karba dan su basu da kwadayi ga tsantseni kansu a hade yake tamkar tagwaye bazaka taba cewa kishiyoyi bane idan kagansu kansu a hade yake komai tare sukeyi allah Besa musu mugun kishin nan ba na hauka



Ko magani zasu sha tare suke sha kome zasi tare sukeyi baruwansu da hassada a tsakaninsu samun kishiyoyi kamarsu gaskiya ba karamin dace bane mama ce uwar gida umma amarya ya fice yaja motar suka tafi gida maryam nata kuka nafeesat na aikin rarrashi shiko gogan uffan yakasa cewa yarasa a wane hali yake bayasan kuka ko kadan ko cutarsa zaki a kwalta sa masa kuka kingama dashi gashi wani irin kuka take me kamar shagwaba har buga kafa take kamar ya janyota jikinsa ya rungume haka yakeji har suka isa gida tana kuka



Suna jan motar Alhaji yashigo kubani kudin daya baku marasa tausayi da imani duk wahalar danake bakwa gani Ga auren maryam gabana tana samun miji ya karbe ya basu dubu biyar biyar mama chatai sun gode ya rike umma ce ta karba har nata ya fita yanata sababi haka kawai za'a narkawa mata kudi mesuka sani banda hauka Kike bakwaso wallahi da badan tayi saurin karba ba kunrasa duka yafice rai fes shikansa yasan ya iya haihuwa yayansa suna hutawa yana fita yazarce gun me balagunku gaula guda ya siya a ka yanka masa nama him ya siyo Lemo me sanyi yabi takofar waje ya baje yanata dannawa




Nauwara takasama control din kanta Alhaji ghali ya tafi da imaninta Sam bata fuskantar meke faruwa maimuna tazo ta Kama hannunta kiyi hkr kawata idan na bata miki rai amma nasan hakan dakikai be kamataba bakisan mutum ba ki karbi kudinsa bakya tsoron ko dan shan jinine yai amfani da wannan damar ya aiwatar da mugun nufinsa akanmu nauwara takulu ganin yadda maimuna ke zagin masoyinta amma batace Kala ba Dan ta tsani maimuna indai sun fita sai ance anasanta




Kiyi hakuri kar mutane su fuskanci halin dakike ciki nasan maganganuna sun bata miki rai kiyi hakuri muje miyi abunda ya kawomu amma gaskiya dayace daga kinta sai bata haka taja hannunta duk da itama ranta ba dadi sukaje filin aka dinga raha Ana barkwanci ga nauwara da raha da kaudi amma tai shiru kowa yace lafiya nauwara yadda kikaci burin rawar nan amma ace kin kasa kowa yasan ke mazarice a class amma duk yadda kika ci burin wnn rana kin kasa komai Maimuna barin cikinsu tai ta koma wani click din




Kallon kowa take duk wanda yai mata mgn sai tace bata da lafiya ganin haka aka rabu da ita saida ta faki idon maimuna tuni ta nufi gida tana fita tasamu napep drop ta dauka direct kofar mazugal yakaita dubu guda ta bashi yana ga sanjin jeka tace ta fada lokonsu shiko mamaki yake kawai yai tafiyarsa da gudu ta karasa shiga gida tafada kan mahaifiyarta ta rungumeta umma yau nayi babban kamu umma zamu huta sai uwar ta toshe mata baki ta nuna mata bayi



Sai ga uban ya fito kamun uwar wa kikai batta ta fada mana muji kudai kunyi asara batayi sa'ar uwaba nikuma banyi sa'ar mataba ke kike sa yarki a hanyar banza haba malam mekaji tace kasan kamun datai yarinyace fa nauwara daga dawowarta aika tayata murnar gama makaranta Kasani ko makarantar dazata cigaba ta Kama haba kadinga fadin alheri mana mtswww kundauka bansan me kukeba aiba karatun takeba shiririta tasa a gaba da Tara samarin iska Danma suna tare da maimuna yarinyar arziki medora mata karatun duk abunda kuke akan idona kuke dan dai banga shedar tana yawo ba sai dai Tara samarin kuma alhamdulillah ta gama karatu lokaci yayi dazan cika alkawarin aurar da ita ga dan aminina Bello





~ANAN ZAN DAKATA SAI NAJI COMMENT DINKU NICE TAKU AKODA YAUSHE KU KARA HAKURI DAI~



*FEEDYN BASH*
[10/3, 4:46 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *👨🏻‍🎤DAN ISKAN NAMIJI👨🏻‍🎤*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*ASSALAMUALAIKUM MY FANS INA MIKA GODIYATA AGAREKU YADDA KUKE KOKARI WAJEN YIMUN DA ADDU'OIN KU GARENI NAGODE SOSAI ALLAH YA BIYA MANA BUKATUNMU GABA DAYANKU MASOYANA INA KAUNARKU KAMAR YADDA KUKE KAUNATA ALLAH YA BARMU TARE INTA SUBURBUDO MUKE KAYA TATTUN NOVELS*




~*DAN ALLAH INA ROKON KU MASOYANA DUK ME NEMAN BOOK DINA YA DAURE YANE MESHI A GROUP KUDENA BINA PRIVATE KUNA CEWA IN TURA MUKU ABUBUWA SUN MUN YAWA KU TAMBAYI FANS DINA TUNDA INA POSTING GROUP DAYAWA KUYI HAKURI DAN ALLAH ABUBUWA SUN SHA KAINANE*~




*😍😍WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GA ANTY HAUWA JINJINA AGAREKI GASKIYA INA YINKI IRIN SOSAI DINNAN WANNAN PAGE DIN NAKINE ANTYN MU👍🏻👍🏻*




11-12


Ihu ta zunduma ta rungume uwar wayyo Allah ummata na shiga uku wallahi dana auri wannan kazamin Bellon me tarin gemu gwara na mutu mutuwa zanyi wallahi sai dai ki mutu indai nizan daura Miki aure Bello zan bawa ba kazami ba komeye shi Dan bazan fasa ba alkawarin dana dauka zan cikashi ta zunduma ihu wallahi banasansa bazan aure Shiba malamin makaranta nefa makarantar ma ta islamiyya ta Kara rushewa da kuka




Haule Banda numfashi ba abinda take kwantar da hankalin ki yata na yarda za a daura wa nauwara aure Amma wallahi bada Bello kozanyi yawo tsirara cigaba da karatune baka so to na janye tafasa Amma wallahi kaima saika janye auren Bello akanta wallahi bazan janyeba wato bakyasan malamin makarantar islamiyya sai Dan iska irinki ko to kema haule idan Kika nemi ki rusa wannan auran tamkar kin rusa naki auren ne Kuma ninake da iko da yata na aura Mata Wanda nakeso haka addini ya bamu dama sai ki koma kauye kici gaba da Zama yasa Kai ya fice



Zuciyar haule tamkar zata fito kirjinta ita malam zewa wannan wulakancin da cin mutuncin wato ta koma kauye to wallahi be isaba bazata auri wani Bello ba Kuma Zama daram me nasama yaci bare ya bai na kasa akanem zata Kai yarta gidan wahala share hawayenki diyata bani labarin Wanda kuka hadu ta goge hawayenta ta bude jakar ta zaro farare bugun Abuja Rafa biyu ihu haule tasa taja Yar suka shiga daki harda rufe kofa diyar arziki me kashin arziki Ina Kika samo wannan kudin



Murmushi tayi umma kenan Wanda muka hadu ne ya bani me kudine na Bala'i umma zamu huta nake Gaya miki Amma fa akwai matsala ido ta zaro dama gasu kwala kwala matsala Allah ya rabamu da matsala bama fatan ta diyata meyake faruwa umma bafa Ni yakeso ba maimuna yake so maimuna maimuna take ta maimai tawa wallahi da sake be isa ya auri maimuna ba gaki tunda kudi sunzo Zama be ganni ba yanzu zan bazama gidan malamai a karkato da hankalinsa kanki wannan maimuna tazame Miki masifa shegiyar yarinya wata Kim da ita ba kyan gani sai farin jini wallahi Bata isaba ki janye jikinki daga nata dankar ta samu damar zuwa gidanki Dan yanzu zan bazama a raba ta da wani alhaji a cire Mata wannan farin jinin a a umma abar Mata tunda nasamu nawa mijin to diyata



Tana fita maimuna ta shigo tana kuka na nutsuwa kana ganinta kasan a cikin tashin hankali take Amma Sam Bata fita hayyacinta ba nauwara ta danne kishin daya taso Mata Dan ta tsaneta yanzu ta rike ta lafiya maimuna Usman ya rasu na rasa miji me nagarta me addini inafatan Allah ya bani madadinsa gabanta ita kanta ya Fadi mutuwar ta shigeta yaushe bashi da lafiyane lafiyarsa kalau motace tabi ta kansa kansa yai kwatsa kwatsa kirjinsa da gangar jikinsa sun rabe ai saita fara zunduma ihu kamar ubantane ya mutu maimuna tace haba nauwara koni banyi Masa ihu ba baya bukatar ihu addu a yafi bukata Dan Allah kidena



Dole nai kuka Dan Ina tausaya Miki kun shaku soyayyarku abar Sha awace da burgewa duk yadda muka Kai da shakuwa Wanda yafi mu sansa ya karbi abunsa ki tashi ki shirya na dauka umma tana Nan zamu tafi tare gidan Jana'iza babana yai gaba Inna tana gida tace nazo na kiraku haka suka shirya suka tafi da innar ta hawaye kawai take tana salati a zuciyarta tana rokon Allah ya Bata juriya da dangana na rashin masoyinta zuciyarta sai zafi take



Lawan Yana fita be zame ko inaba sai gidansu Laila yana zuwa ya aika a kirata tana fitowa ya kalleta ta cika Tai dam kamar zata fashe shiga mu tafi kawai yace ta shiga motar hotel din da suka Saba zuwa suka nufa suna zuwa hotel din ya Karbi key dinsa Dan shi permanent ne suka shiga Nan ya Fara shafata Yana Bata hakuri ganin haka ta Fara jaraba rashin mutunci harda zagin ummi har kiransa take da Dan iska Yana Jin tazagi ummi ya Mike ya zabga Mata Mari ya Fara dukanta sai dayai Mata lilis sannan ya nemi gu ya kwanta Allah ya Isa bazan yafeba Dan iska tsinanne be kulata ba Dan ze iya kasheta idan ya Mike



Haka ta zauna taci kukanta shi Kuma yaci baccinsa sai gab da magriba ya farka yaga itama baccin ya dauke ta yai murmushi Laila Ina sanki Amma hakan baze Hana idan kikai mun lefi na zanekiba Dan hukuncin ne haka idan ummi ta tabaki zan rama miki itama idan kin tabata zan rama Mata ya dinga shafata Dan ba lefi tanada da dadi duk da bashi ya Fara bulataba Amma bataji jiki sosai ba ta farka tana ture shi Ina yasan takan mace Nan ya gama gigita Mata tunani yadinga sarrafata San ransa kafin kace meye wannan ta bada Kai bori yahau



Sai da suka nutsu suka Gama komai gaskiya Laila adaura Mana aure haka Koda Baki tare ba daga baya Kya tare kafin na gyara Miki saman gidana auren mashayi kenan duk wannan dukan Tama manta da shi eh haka za ai saboda Yana side ta tas Kuma ba abunda yafi dadi irin mijinki ya gama lugwiy gwiy Taki kafin Yafara harka zanwa daddy na magana ni kaina nagaji nafiso a daura Mana aure nima na huta shikenan sweety Nan ya jawota suka Kara one round Allah ya shirya ameen lokacin da suka Gama dare yayi ya maidata gida ko tsoro Babu a fuskarta haka ta shiga gidan




Bayan sun shiga gida arfan ya fito yayi kyau kamar ka sace shi ka gudu ya Sanya manyan Kaya wandon pencil shaddar sai daukar ido take kamar Wanda zashi office da gaske Nan ko basaja yai dankar ta gane tunda baze yiwu kullum ya dinga cin zanzaro ba Yana fita Yana zuwa

3 / 7