Author : Autar Manya Category : Romantic Hausa Novels
tabbatar ya dasa mata son sa acikin zuciyarta sannan ya barta aiko daren bata rintsa ba duk juyi shi take tunani abin ka da farin shiga.
Washe gari sai wajan taran safiya tayi sallar asubah sabida wayar da suka sha da Mahir ta makara ne tasha baccinta ta gode Allah wanka tayo ta shirya cikin Riga da skirt na Jar Atamfa Java bata ɗaura ɗankwaliba a haka ta fito Parlour tana kiran Maimuna da sauri maimuna ta ƙaraso ta rissuna tana cewa.
"Gani uwar ɗakina Barka da asubah"
Cikin halin ko in kula tace.
"Kije ki wanken toilet ki gyaran ɗakina ki kunnan turare akwai undies ɗina da zaki wanken washing machine ɗin toilet ɗina ya lalace"
Har lokacin maimuna bata ɗaga kanta ba har sai da Adaah taja aya sannan maimuna tace.
"An gama uwar ɗakina ga break ɗin ki can na haɗa komai kawai ci zaki yi"
A ya tsine ta amsa wa maimuna da.
"Ok"
Sannan ta wuce dining ta zauna ta haɗa tea ta ɗauki bread tana haɗawa da soyayyen ƙwai tana ci da yake Allah ya ɗora mata ci kamar gara ita Ko irin rashin cin nan ma na ƴaƴan masu kuɗi bata da shi.
Sai da ta share wannan bread da ƙwai tas sannan ta goge bakin ta da tissue ta ƙarasa cikin parlour ta kwanta tana canza channel.
Momi ce ta fito sai baza ƙamshi take.
Ta ƙaraso gaban Adaah tare da cewa.
"Tashin ki kenan na lalleƙa ki naga baki farka ba, Nima fita zanyi yanzun nan zan dawo"
Adaah tabi momi da kallo kafin ta kawar da kanta, ba tare da gaishe da mahaifiyar tata ba.
Momi tana ƙoƙarin fita daga Parlourn Sukai Kiciɓus da Abbah wanda shigowar sa gidan kenan hannun shi riƙe da ƙaramar jaka ta matafiya.
Momi zamewa tai a wayance ta zauna a saman kujera tana aje ƙaramar jakar hannunta dama lefen ƴar ƙawarta zata je gani sam bata kawo Abba zai dawo yau ba shiyasa zatai gaban kanta sabida ana faɗin irin dukiyar da aka laftawa ƴar ƙawar tasu.
"Sannu da shigowa Alhaji, amman dawowa babu sanarwa"
Ta faɗa tana sosa kai alamun rashin gaskiya.
Bai kulata ba sai Neman gurin zama da yayi da sauri Adaah ta diro tana sauka ƙasa har tana ƙwarewa wajan yiwa mahaifin nata barka da zuwa sabida shi tana shakkar shi ba kamar Momi ba.
Abbah ya bita da kallo ba tare daya amsa gaisuwar tata ba.
"Rabi'atu mai kike agida yau baki je makaranta ba?"
Sai ta hau kame kame sabida sarai tana da lecture ranar amman taƙi zuwa.
"Wato asarar kuɗina nake a banza ba karatun kike soba ko da yake ai magana ta ƙare dama abin da yasa na rabu dake na zaci zaki dage ki karatu ne, amman tinda baki son makaranta zan faɗawa Mijin naki ko bayan aure karya barki Fita ki haƙura haka abin da kika samu Allah yasa mai albarka"
Haɗe rai tayi nan da nan ruwan hawaye ya fara firfitowa daga idanunta ta jefa kallon ta ga Momi wadda ta kafe Abbah da ido tana jijjiga ƙafa.
"Wannan wace irin magana kake Alhaji wai shi wannan auren dole ne? haba yarinya bata so nida na haifeta bana so gaskiya ba zan lamunci a cusawa ƴata ƙatoton jahili ba, ce maka akai bata son karatu bayan ita kaɗai Allah ya bamu Tarin dukiyar da Allah ya baka in baka barta tai karatun ba waye zai riƙe mana ita nan gaba"
Abbah ya zubawa Momi ido cike da ɓacin rai, sam tinda lamarin auren nan ya tashi momi bata saurara mai bata masa ta sauƙi hatta ga kalamanta kawai yana kai zuciyar shi nesa ne yana duba wasu abubuwan jiba yanzu yadda take masa magana agaban ƴarta ba ladabin harshe ko tauna magana.
"Maryam sai fa Rabi'a ta auri Saadik koda gawarta ce wallahi zan kai gidan ƙarewar ƙiyayya in an aura masa ita tasa Ashana ta kunnawa kanta ta Ƙone ta mutu Ki sanar da ƴan uwanki anjima Za a kawo lefe"
Daga haka ya miƙe yabar Parlourn zamewa momi tayi daga saman Kujerar tana yarfe Zufa.
Da sauri ta ɗaga waya tana Kiran Hajiya Lubna.
Daga ɓarin Lubnah dake kwance domin har Lokacin bata tashi daga baccin safe ba.
Ta ɗaga wayar tana jan ƙaramin tsaki.
"Maryam yaya akai wannan wayar da farar safiya?"
Momi ta yarfe zufa a karo na barkatai kafin tace.
"Kinji wata sabuwa anjima zasu kawo lefen Adah ni kaina ma ya kulle"
Da sauri Lubna tace.
"Kamar yaya dama baki zuba masa magani a ruwan ya sha ba har ya sami zarafin maganar auren?"
Momi ta juya tana kallon hanyar da Abbah yabi taga ya ƙullewa ganinta sai tace.
"Yau fa ya dawo gari yanzun nan ya sauka yake wannan bayani wallahi bai ma bani fuskar na bashi ruwan ba bare akai ga na saka ke nifa gani nake suma aiki suke akan Alhaji duk yabi ya birkice min kamar ba shi ba"
Ƙaramin tsaki Lubna taja ido rufe da son biyan buƙatar kanta tace.
"Duk yadda za'ai karki yarda da wannan aure nima zanyi ƙoƙari na ta nan, Nifa ko ba Mahir ba wallahi nafi son Adaah ta auri Miji na kece sa'a irin yadda ƴaƴan ƙawayen mu suke aura haba ƙiri ƙiri za'a tauyeki ƴa ɗaya da Allah ya baki za'a cutar da ke a bata Ɗan jagaliya talaka faƙiri marar ilimi wanda ba lallai yasan darajar mace ba Niba burina Adaah ta auri ɗana ba Burina ta sami Mijin nuna sa'a mijin da zamu nunawa duniya cewa ƴarmu ta auri Namiji, wallahi inda ina da ƴa mace Budurwa Maryam kota halin ƙaƙa sai na shiga na fita na nemo mata wani ƙusa a ƙasar nan Ina zan yarda ƴata ta auri talaka"
Kalaman Lubna suka ƙara Raunana momi suka kuma ƙara bata ƙarfin gwiwar Tsanar auren da za'ai wa Adaah a raunane tace.
"Lubnah wallahi bada ban kar nai ƙarya ba sai nace kinfi kowa sona da damuwa dani, Tinda lamarin nan ya kunno ke kaɗai kike bani ƙarfin gwiwa duk da malam yace Adaah ta auri mahir amman ke ba burin ki ma ta aure shin ba ke burin ki ta tsallake ta sami miji na kere sa'a ya zanyi yanzu yau fa zasu kawo lefe?"
Ta faɗa tana kuka!
Lubnah ta cije baki ita kaɗai tasan meke ƙasan zuciyarta sai kuma Allah kafin tace.
"Karki musun zuwan su wannan ma wata dama ce da zaki ci musu mutunci karma ki gayyaci kowa daga dangin ki ke kaɗai zaki zauna su zo ki ci zarafin su tass kwaɗayayyun banza kinga daga nan suma in suka ji haushi zasu koma da ɓacin ranki nan ma wata damar ce da zaki wargaza auren"
Da sauri momi tace.
"Haka ne lubna dama wa zan faɗawa a dangina Allah na tuba Ai wallahi dama ni burina in Adaah ta sami miji ku zaku yi komai cikin girma ba tare da kun bani kunya ba"
Sai da suka gama tattauna komai sannan sukai sallama momi ba abin da take sai girgiza ƙafafu Adaah ta ja jiki ta ƙaraso wurin Momi.
Murya cikin rauni tace.
"Allah momi ina son ya Mahir ɗin Momy lubna yanzu bani jin zan iya rayuwa da wani idan ba shi ba momi kada ki bari Abba yayi mini auren dole"
Momi ta janyo Adaah jikinta tana rarrashinta
Har ta samu ta saki ranta.
Cikin shiri Abbah ya sakko sabida zai fita kasuwa zasu gana da wani mutum dake jiran shi duk da yana buƙatar hutu amman hakan ba zai samu ba.
Har lokacin bai da sukuni a fuskar shi ya ce.
"Maryam sai ki sanar da Ƴan uwanki nan da lokaci kaɗan zasu kawo kayan lefen akwai Lemuka da ruwa dana sa akawo sai ki sa masu aiki suyi musu Girki ki ɗauki kuɗi a ɗakina ki sallame su duk da ƴan gida ne amman yaba kyauta tukwici"
Idan kujerar data ke kai ta tanka to ta tanka wa Abbah har ya ƙare ya fita itama Adaah da ƙyar tai masa Adawo lafiya aiko yana fita tai ɗaki aguje tana kuka.
Momi da takaici ya hanata motsi a nan ta cigaba da zama koda mai kawo ruwa da lemuka ya turo mai gadi cewar ya ƙaraso cewa tai ace ya mayar dasu basa buƙata haka ya juya har akai azahar tana zaune sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe ta shiga ɗaki tayi sallah ta ƙara dawowa parlourn jira kawai take masu kawo lefen su zo.
Ƙarfe ukun yammaci daidai Maimuna tai wa su Ya minau Iso babban parlourn gidan ƙanin mahaifin nasu wanda in za a kashe su ba zasu iya cewa ga yanayin gidan kawun nasu ba sabida ba zuwa suke yi ba.
Ya minau ce, sai Aunty hajjo, da Faridah da Aunty Nafi ƙanwar Innah sabida innah tace karsu faɗawa kowa daga cikin danginta domin basu san kalar tarar da zasu samu ba gudun abin kunya, gwara Aunty nafi ƙanwar Innah ce cikinsu ɗaya bazzawara ce take zaman gida.
Su Ya minau suka nemi guri suka zauna Umar ne ya dinga shigo da akwati nan ya jere su reras a parlourn.
Momi tana kallon su batare data amsa sallamar su bare akai ga batun ta amsa gaisuwar da suke mata ba.
Aunty nafi ta ce.
"Ina mutan gidan ne muna ta sallama kamar babu kowa"
Tsaki mai ƙarfi Momi ta saka tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙaro Ƙarfin Tv.
Aunty Hajjo ce tace.
"Innah Maryam barka da rana ga abin arziƙi mun kawo kuma mun zo kamar baku shirya zuwan namu ba naga babu ƴan ɗaga kaya koda yake abune duk gida ina amaryar tamu?"
A fusace Momi ta ɗago tana watsa musu harara kafin ta taso har gabansu.
"Ku wasu irin mayu ne? wai ba'a faɗa muku bama ra'ayin haɗin auren nan ba kwaɗayi ne yasa Za'a ɗauki ƴata a bawa Ɗan uwanku to ni dana haifeta bana so Itama bata so don Allah ku ɗauki gayyar tsiyarku kuje kucewa Ubanku bama........
Da sauri Anty Nafi tace.
"Kai kai baiwar Allah ya kike abu irin na Mutane marasa kan gado Shin ba mijin kine ya kawowa Baba tallan ƴarki ba har kike kiran kayanmu da gayyar tsiya wallahi ke kam baki gaji arziƙi ba duk inda kika fito daga tsiya kika fito Yau inda ina da iko sai na hana Saadik ya auri ƴarki sai kace autar mata kije kiga yadda ƴammata suke tururuwa akan shi ke an samu an liƙa masa jarabar ƴarki har kina da bakin magana"
Anty nafi ta kai maganar cikin Ƙunar rai.
Tabbas yadda su Farida suke jin zuciyoyin su bada ban taci darajar Baba Amadu ba da babu abin da zai hana su gargasa mata baƙaƙen maganganu amman wata fuskar tafi gaban mari taci arziƙin auren ƙanin mahaifin su sabida haka da sauri suke ficewa daga parlourn.
Momi dan izzah da ƙasƙanci takan akwatinan ta dinga bi tana takawa tana tafiya zuciyar Aunty Nafi tai zafi ji take kamar Ranta zai fita dan ɓacin rai bata taɓa ganin mace mai izza da wulaƙanci da rashin sanin darajar mutum irin matar nan ba.
Sai a titi suka haɗu da junan su Ya minau mai rauni tuni ta soma kuka.
Umar ya samo musu ɗan sahu suka hau duk cikin su babu wanda ya iya magana, har suka ƙarasa Gida.
Yanayin da suka shigo gidan kaɗai shiya fahimtar da innah abin da ke zuciyoyin su.
Saadik yana zaune saman kujera ƴar tsugunno yana wanke takalmin training ɗinshi.
Farida randa ta nufa tana shan ruwa.
Su kuma suka zauna saman tabarma.
Kukan ya Minau ne ya cika kunnuwan su.
"Don Allah Innah ki cewa Baba yabar batun auren Saadik da Ƴar gidan Baba Amadu haba talauci hauka ne duk wahalar da muka sha ganin munyi komai cikin tsari abin ya kasa yiwuwa matar nan takan akwatinan da muka kai ta dinga bi tana takawa bayan cin mutunci da muzancin data mana.........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
*SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*15*
Idanunta yayi burɗun burɗun yayi wani irin ja, fuskarta ta kumbura sabida tsananin kuka wanda take yin sa cike da tsana da ƙiyayya.
Daga ita sai ɗaurin ƙirji daga dokin wiyanta zuwa cinyoyinta duk dilka ce Aunty Mariya ta sa wata mai gyaran jiki ta shafa mata gefe guda kuma ga haɗi na musamman a kofi wanda zuma ce da sauran ingantattun magunguna na gyaran jiki Aka zuba mata zata sha.
"Rabi ba zaki ɗauki kofin nan ki kafa a bakin ki ba sai ranki ya ɓaci?"
Cewar iyah wadda take zaune ta saka Adan a gaba.
Hawaye ta share babu damar musu ta ɗauki kofin tana sha tana yatsine fuska.
"Ina tausaya miki Rabi zaki je ki rayuwa wadda ba iri ɗaya data gidan ku ba, dama shiyasa ake son iyaye mata su horar da ƴaƴan su akan ayyukan gida da tarbiya sabida baka san ina ɗanka zai je yayi rayuwa ba, zaman aure zama ne na har abada sabida haka ki daure ki koyi tarbiyar zama da miji da kuma ƴan uwan shi sannan ki tina mijinki nada uwa nan ma sai kin koyi tarbiyar zama da ita"
Duk abin da iya take faɗa tana jinsa ne ta bayan kunnenta domin tabbas bata shirya zaman auren ba babu wanda zata bi babu abin da zatai musu tinda har ya kafe sai ya aure ta, to ta ɗaura ɗamarar gasa shi sai ya gwammace kiɗa da karatu tinda har ya nace sai ya aure ta.
Tana kuka tana komi ta shanye maganin aka kammala mata gyaran jikin Aunty Mariya tace ta shiga wanka ga ruwan ɗumi can a toilet yana jiranta.
Sai kallon banza take watsa wa dangin mahaifiyar tata waɗanda suka zo biki don wasu ma sai ranar ta sansu don ba shiga cikin su take yiba, ta tashi a wulaƙance ta shiga wankan.
Wai inda aka ci sa'a ma tana shakkar Iyah don tsohuwar batai mata da daɗi shiyasa har ta ke yin abun da Aunty mariyar ta sakata.
Koda tayi wankan ma zamanta tayi a ɗakin Iyah taƙi fitowa tana jin ƴan uwan iyah nata tsokanarta amman taƙi magana dama iyah ta kashe bakin kowa duk wanda ya tambayi bai ga Maryam ba sai tace maryam kam Kunya ta hanata zuwa wajan biki tana can gidanta tace gasu Mariya nan sune iyaye, tinda duk tsiya naka nakane baka bada fuska a wajan wani don ya ɓaci duk baƙin halin Maryam ƴarta ce, abin da yasa ma ta ɗauko Adaah tasan ba za'a wanye lafiya bane da Maryam shiyasa Abbah yace tayi taron a gidanta a ɗauki amarya agidanta dama ɗaurin aure a Ƙofar Gidan Baba za'a ɗaura tinda shine maɗaurin auren dama.
Wajan magariba wasu daga cikin Dangin su Iyah suka dawo daga gidan Amarya sai dai motar data ɗauki kayan ɗaki ta dawo da fin Rabin kayan ɗakin a cewar wata daga cikin ƴan uwan iya ai kujera ma guda ɗaya ce doguwa kaɗai ta shiga falon, Uwar ɗaka kuma sun saka katifa don gadon ma yaƙi shiga sai akwatinan da aka sa don su madubi ma duk sun ƙi shiga sabida kayan ba ƙananu bane.
Ataƙaice dai yadda suka sanar da Iyah falon ya sami carfet sai doguwar kujera guda ɗaya sai labulaye suma ba duka ba uwar ɗakan kuma katifa da akwatinan Adaah, Kitchen ma Gas yaƙi shiga sai tukwane da ƴan tarkacen ƙananun kaya ne suka sami zama sabida rashin wadataccen faɗi a gidan
Iyah ta maida ajiyar zuciya tace.
"Ai babu damuwa Allah ya sa albarka hakan, bari naiwa mahaifinta magana in yaso sai a maida kayan kawai"
Sabgar haɗa miyar taushen biki aka cigaba da yi.
Adaah na ɗaki tuni zazzaɓin takaici yayi awon gaba da ita
*****
"Yanzu saratu duk yadda Jiddah tayi wa Saadik halacci haka zai mata kawai sai ganin katin ɗaurin aure mukai ana rabo?"
Cewar wata maƙociyar su Jidda mai suna talatu.
Umma ta kama haɓa tayi tagumi
Cikin damuwa tace.
"Ni duk ba wannan ba, na samu wannan uwar nacin ta rabu da shi gaba ɗaya ta fitar da shi daga zuciyarta ta nuna da shi da babu duk ɗaya amman taƙi kullum kuka wallahi jiya daga ni har mahaifinta bamu rintsa ba ni yaya zanyi ne"
Ummah ta faɗa duk damuwa ta bayyana a saman fuskarta.
"Hmm saratu ai tashi tsaye zaki ki samawa ƴarki farin cikinta, wannan aure ai na kwaɗayi ne naji ance ƴar ƙanin mahaifin sace mai kuɗi kuma ita kaɗai ubanta ya haifa kinga da zarar ta haihu ai dukiya ta su ce sabida haka idan har kina buƙatar taimako akwai wani da zan haɗaki da shi a jawo hankalin Saadik ya birkice muku"
Umma tai jimm kafin tace.
"A iya ganin idanuna ai kamar soyayyar da yake wa Jiddah ma ta wadatar in muka ce zamu haɗa da bin malamai zamu shiga haƙƙin sa, Ni kin san talatu bana harkar biyar malaman nan nafi gane tsaiwar dare, Nidai barni in raina ya ɓaci zanyi faɗana sosai amman bana raba imanina biyu in har Allah yace jidda matar Saadik ce zasu yi aure amman in har Allah bai ƙaddara ba babu wanda ya isa ya basu junansu"
Cikin rashin samun nasara talatu tace.
"Haka ne saratu to Allah ya daidata lamarin bari na ƙarasa gida"
Ummah ta raka talatu har bakin ƙofa ta tafi.
Ɗakin jiddah umma ta shiga ta sameta kwance da rigar baccin jiya a jikinta, ummah ta sami guri ta zauna a gefenta tare da kamota zuwa jikinta.
"Kinga har yanzu jikin ki akwai zazzaɓi don Allah jiddah ki bar wannan damuwa nina fiki shiga tashin hankali amman yaya zamuyi mahaifin ki ya baki haƙuri nina baki haƙuri amman kinƙi daina kukan nan"
Muryarta sanyi ƙalau tace.
"Ummah kawu Saadik fa aure zaiyi gobe, duk yadda nake son shi ya kasa aure na a karon farko sai wata haba umma ta yaya zan sami Nutsuwa umma ki taɓa zuciyata kiji yadda take harbawa"
Cikin faɗa ummah tace.
"Zaki kashe kanki, ne a banza kinga sun kasa bikin su? ko kinga sun dena shirin su ina ba har lefe ya haɗa mata ba to in zaki gane karatun ɗa namiji ki gane, ni inda kinyi zuciyata da shi da babu duk ɗaya ki tattare su har mahaifiyar tashi ki watsar itama banda munafurci meye a auren da bakwa so harda gayawa maƙota su zo suga