Author : Autar Manya Category : Romantic Hausa Novels
furarki na sayo"
Sai da ta ɗaura alwalarta sannan tace.
"Ka kyauta ka bar ƴar mutane cikin wani hali kai tafiyarka"
Ya wani zaro ido waje.
"Inna itan ce tace nai mata wani abun nifa kawai biyoni tayi da kuka shiyasa na bar mata wurin"
"Oho ca nake kasan sanda ta faɗin, yanzu kayi sallah sai ka leƙa gidan nasu kaji yadda take nima danai sallar zan shiga"
Ya miƙa mata ledar furar tare da amsa mata da cewa.
"To"
Yana juyawa ya nufi ɗakin shi da fitilar ƙaramar wayarshi yayi amfani wajan haska banɗaki yayi uzirin gabanshi tare da ɗaura alwala, ya fita masallaci.
Bayan ya idar da sallar magariba, ya dawo ɗaki yayi wanka Nura saiti ya kira a waya yana tambayar shi akan koya dawo Nurah yace mishi yana bakin titi yanzu zai shigo lungun da sauri yace masa inya shigo ɗin ya biyo don Allah zai rakashi Gidansu Jiddah.
Zama yayi yana jiran Nuran bayan ya katse wayar jim kaɗan nurah ya shigo tashi kawai yayi suka fita.
A ƙofar gidan su Jiddah suka dakata yana tunanin ta yadda zai sami yaron da zai musu iso zuwa gidan dan shi yana jin nauyin kiran Umma a waya yace yazo.
Ana haka Fa'izu yayanta ya ƙaraso ƙofar gidan yana ƙoƙarin kashe babur ɗinsa ya ga su Saadik waɗanda suka ƙarasa gaban shi suna miƙa mai hannu.
Cikin mutuntawa suka gaisa yace.
"Kuma kunzo basa gidan kenan? nima sai da na zo bakin layin ummah ke faɗa min, suna asibiti Jikin Jidda babu daɗi"
Da sauri Saadik ya kalli fa'izun gabanshi ya faɗi tofa abin yayi zafi kenan harya kai da zuwa asibiti.
Cikin sanyi yace.
"Okay wane asibitin kenan bari mu ƙarasa"
Fa'izu yace.
"Nan asibitin Charity na bakin titi ko wani acikin ku zai hau bayan babur ɗin muje tare?"
Saadik ya kalli nurah wanda shima ya kalli saadik ɗin kafin Nuran yace.
"A,a bari mu tafi bibbiyun tafi daɗi"
Fa'izu yaja babur ɗin nashi ya tafi su kuma su nufi bakin titi.
Gaba ɗaya Saadik ji yayi garin yayi masa zafi fargaba ta cika zuciyarsa sai dai da yake akwai shi da dauriya yasa fargaban bata fito fili ba.
Duk Hirar da Saiti ke yi masa kawai jinsa yake a haka suka ƙarasa titi suka sami napep tafiyar kaɗan ce ta kaisu asibitin wanda yake ɗan ƙarami ne na kuɗi.
Suka sauka tare da bawa mai ɗan sahun kuɗin shi, suka shiga cikin asibitin.
Suna shiga shima fa'izu na ƙarasowa sabida haka a tare suka ƙarasa cikin ƙaramin ɗakin da aka kwantar da jiddan bakin su dauke da sallama.
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*007*
Kwantaccen murmushi ya saki yana shafa saman kanshi da hannun shi guda ɗaya, haka nan ya ƙarasa gefen data mayar da kanta ya zuba mata ido tamkar ranar ya fara ganinta, Har Lokacin murmushin kuma bai gushe daga saman fuskar shiba.
Turo baki tayi gaba tana ƙoƙarin sake juya masa baya yayi saurin jan gefen Hijabin ta ya wani marairaice kamar wanda yake roƙar ta gafara tare da cewa.
"Haba ƴar aljannah, ban sanki da fushi ba haba Hauwa'na mai jiddana"
Yadda yayi maganar ba ƙaramar dariya ya bata ba, Seta sa hannu ta rufe baki tana dariya ƙasa ƙasa, ya wani gyara tsaiwa ya ɗan tsira mata ido kaɗan sannan ya kauda idon nashi.
"Yanzu dai ki wuce muje cikin gida Innah tace bakya zuwa kwana biyu sabida kin zama surukarta tace ko kin ganta guduwa kike yi"
Zaro ido tayi kaɗan cikin sanyin halinta tace.
"Wallahi ina zuwa kawai kwana biyun nan ne, Bana zama kaima ai kasani sauka ta sakoni gaba sai munyi zan sami sukunin zama"
Yadda tai maganar ya kwaikwaiya sai ta kawo masa dukan wasa tana shura ƙafafunta da gudu yayi soron gidansu ta bi bayan shi da wayo ya jata har Rumfar Innah wadda duk suna zazzaune an kunna Fitila mai farin ƙwai sabida babu nepa.
Su kansu su Ummi zuba masa ido sukai ganin yadda ya faɗo Rumfar yana dariya wadda tai mugun yi masa kyau don shi ba ma'abocin yin ta bane.
Inna ce tace.
"Lafiyar ka kaikam ka faɗo min ɗaki kana faman dariya"
Muryar shi ce ta katse maganar Innah inda yake wa Jiddah magana yana waigowa wajan innah.
"Ki shigo mana kin wani raɓe to wai gidan baƙon kine?"
Sai lokacin Innah ta fahimci silar dariyar tashi wato tare da Jiddah suke.
Sai ta kada baki cike da Murnar Ganin Jiddan tace mata.
"Maza shigo Hauwa'u ni na rasa kwana biyu kunyar da kike ji tawa Ko a waje bana ganin ki ko wajan ƙawar taki bakya shigowa duk sabida Sadauki?"
Duk su Ummi dariya suka saka Banda Saadik daya ɗaure fuska aiko ba shiri su Ummi suka kama kansu kowacce ta yi ɗaki sim sim gudun Karsu jawa kansu masga.
Da sanyin ta tashigo ciki ta raɓe a gefe shiko ba kunya ya matsa wajanta Jug ɗin dake hannunta ya karɓa.
Yana ƙwalawa Khadija kira da sauri tazo gaban shi.
"Kawu gani?"
Umarni ya bata akan taje Kitchen ta ɗauko masa Kofi ƙarami ba jimawa ta kawo masa ya fara tsiyaya Kunun ayar aciki ya ɗagawa ya kurɓa ya wani Lumshe ido yana Murmushi.
Jiddah ta ɗan saci kallon shi tare da cewa.
"Nifa ba kai na zowa da shi ba"
Sannan ta kalli Innah tace.
"Innah kinga ya shamin abuna ko?"
Me Innah zatai In ba dariya ba kafin ta Miƙe tana cewa.
"Nikam babu ruwana da sha'anin ku kunfi Kusa ba ina jinki watarana Kina kawo masa ɗan Girke Girken kuba Ni wallahi gwarama anyi auren nan mun huta"
Ƙunshe fuska Jiddah tayi tana Murmushi shiko Saadik kallon Innah yayi yana cewa.
"Innah ko nayi aure ina tare dake babu mai rabani dake"
Innah data kai bakin Ƙofar fita tace.
"Kaji dashi dai ni ba za a min daɗin baki ba"
Innah tana fita ya matsa gabanta ya Miƙa mata Kofin Hannunshi.
"Kema ki shiga kiji gaskiya yayi daɗi nayi dacen mata komai fa Kin iya"
Juya fuska tayi tana ce masa.
"Dan Allah ka matsa baya kar Innah ta shigo"
Da taga yaƙi matsawar sai ta Miƙe tsaye ta fice daga ɗakin, Binta yayi da kallon So da ƙauna Tsananin kunyarta tana ƙara Jefa zuciyar shi a tafkin sonta da ƙaunarta.
Da sauri yabi bayanta kafin ya fita harta kai waje dama yasan ba zata tsaya ba.
Yaji daɗin Kunun Ayar sabida haka da shi ya wuce Ɗakin shi.
Yana shirin zama.
Nurah saiti da Abubakar Babu suka kutso cikin ɗakin nashi Saiti da Babu abokan shi ne tin na ƙuruciya da ihu suka faɗo ɗakin nashi suna rige rigen zama a saman katifa.
Aje Jug ɗin yayi tare da shiga Cikin banɗaki kafin ya fito har sun shanye Kunun ayar yayi tsaki tare da cewa.
"Ku dalla meye haka? daga ganin abun mutum kawai ku ɗauka Ku sha babu izini?"
Babu ne ya yi dariya tare da cewa.
"Dallah ware mu kaje wajan Hajiya Innah ka samo mana abinci yau ba kanta"
A fusace yace
"Ni ba maganar abinci nake muku ba ina ruwana da yunwarku ko gidan baƙon kune Kunun ayar da Kuka shamin zaku biyani"
Nura saiti me zeyi inba dariya ba.
"Haba Dagiya don Tafisu tayo maka kunu mun sha shine kake wannan masifar, Ko shima kunun nata Kishin sa kake tinda naga ƙiri Ƙiri ka hana Tafisu saka mayafi sai Hijabi"
Babu ne ya tare Numfashin saiti da cewa.
"In ma bita zaizai aka zubo maka to sai mu bita tare"
Juya musu baya yayi tare da kwanciya a can ƙarshen katifa bai Kuma yi musu magana ba.
Babu ya miƙe jim kaɗan ya kawo musu tuwon daya je Innah ta zubo musu suka ci suka Ƙoshi suka bar masa kwanukan a wajan sukai tafiyar su dama inda sabo sun riga sun saba da Halin shi abin masifa da ƙunci baya masa wahala.
Uban ƴan tsaftan suna fita ya share ɗakin ya kira salmanu ya fitar da kwanukan harda sawa a samo mai garwashi ya zuba turaren wuta nan da nan ɗakin ya cika da Ƙamshi.
Da yake babbar yaya Aunty Aminah Irin sana'arta kenan turaren wuta take tana aikawa gari gari. to shi kuma mayen ƙamshi ne duk sanda tayi sabo ta aikowa da Innah seta ware nashi daban tace a bawa Auta.
Cire kayan Jikin sa yayi ya ɗaura ƙaramin Tawul ya shiga wanka mayen wanka ne innah har faɗa take masa akan ya rage yawan watsawa Jikinsa ruwa, to da yake shi Mutum ne mai Jin zafi Bini bini ya yi wanka hakan yasa baya rabuwa da Mura wadda inta tayar masa kamar zai Mutu domin tana Matiƙar bashi wahala.
Seda ya kintsa komai sannan ya kwanta.
Yadda Momi ta sami Adaah Hankalinta yayi Mugun tashi kwance ta tarar da ita sai Nishi take sabida tana da matsalar Ciwon Ƙirji Muddin tai kuka Ko ranta ya ɓaci yanzu Ƙirjin nata zai sarƙe numfashinta yayi ta kaiwa da kawowa kamar mai Asma, yawan ciwon Ƙirjinta yasa Ba kasafai take sa kaya masu matse Jiki ba musamman riga domin in har zata sa rigar data Matseta yanzu zaki ganta tana Haƙi tana nishi.
Da sauri momi ta janyota Jikinta.
"Haba Shalelena meze sa ki ɗagawa kanki hankali kita Kuka so kike bayan matsalar Ciwon ki wata damuwar ta Kunno kai In maganar aure ce an gama rusa ta Nan da kwanaki kaɗan zakiji labari mai daɗi ai alƙawari nai miki wannan aure bamai tabbata bane"
Kwanciya tayi akan cinyar Momy hawaye na zuba kamar famfo a idanunta muryarta a dashe tace.
"Baki ga maganganun daya gaya min ɗazu daya zo ba, Mai yasa Abbah na zai kaini Gidan halaka yadda nake hango idanunshi Momy baya da imani Momy don Allah karki bar wannan auren ya tabbata"
Girgiza ƙafa Momy take Iya ɓacin rai Ranta ya ɓaci matiƙa Musamman yadda Adaah ke bata labarin har cikin falon su ya shigo ya gargasa mata magana son ranshi ya tafi.
Wata irin tsuma jikin Momi yake Ture Adaah tayi daga Jikinta tabar Ɗakin domin ba zata Iya zama ta cigaba da sauraron wannan Ɓacin ran ba.
Ranar sai ɓacci ɓarawo Amman Momi kwana tayi tana saƙa yadda zata kasance In burin su ya cika na Rusa batun auren Adaan
Washe gari wajan taran safiya Abbas ƙanin Momi ya kirata a waya bayan sun gaisa yace.
"Yaya maryam dama Iyah ce tace na kiraki gata zakuyi magana"
Jikin Momy a sanyaye ta fara gaishe da mahaifiyarta.
Cikin dattijantaka Iyah tace.
"Maryam ya shirye shiryen aurem Rabin?"
Momi ciki ciki ta amsa da Sai Godiya Innah bata jira cewar Momi ba ta cigaba da yi mata magana kamar haka
"Amadu yace daya dawo za'a ɗaura aure, sabida haka nake son Ki turo Min Rabi tunda Ni ban isa an kawota wajena a matsayina na kakarta ba, To nina na roƙa Ki kawon Ita ta Koyi wasu abubuwan Kona kwanaki Ne kafin tariyarta Kin san Dole sai Ƴarki ta sake halinta ta Koyi tarbiyar Gidan Miji sannan zamanta zai yi daidai"
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Momi ta sauke kafin tace.
"Iyah don Allah Kiyi haƙuri wallahi Nasan Adaah ba zata zo gidan kiba, kinga da nan da wajanki akwai bambanci sannan maganar Aure kuma Iyah babu Ita in sha Allahu Adaah ba zata Auri Wannan Baƙin Mugun ba"
Momy ta ƙarasa maganar tana Haɗe ranta, sabida tasan koda wasa Adaah ba zata zauna wajan Iyah ba duk da ta ƙere Gidan Iyah amman ba wani babba bane tasan ƴar tata akwai Tsurfa kwata kwata bata ma saba da Zuwa gidan Iyah ɗin ba tafi zuwa gidan Ƙawayen ta masu cewa tazo ta kwana haka zata haɗa kayanta taje can Shiyasa sai daga baya ta ganar da Adan cewar bafa ƴan uwanta bane waɗancan Ƙawayene.
To yanzu ma kwata kwata bata zuwa ko ina tinda ta ƙara Girma Daga makaranta sai Gida Ko sunce taje bata zuwa.
Ba tare da mamaki ba Iyah tace
"Nasan zaki faɗi fin haka Maryam tinda Allah ya ara miki dama har Kike ganin dan Ƴarki tazo wajena Ƙasƙanci ne, Nima ina ga bada ban albarkacin haihuwa ba da tuni Kin sakeni Kin ɗauki Duniya da ƴan duniya Kin maidasu dangi Ai shikenan Maryama duk yadda kika gani Kiyi duniya ce"
Iyah ta kashe wayar Jikin Momi na rawa take sake Kira amman ba'a ɗaga ba Inda dane da hankalinta baze kwanta ba har sai tabi Iyah gida ta bata haƙuri amman yanzu da yake hankalinta baya Tare da ita yana can wajan son cikar Burinta bata sake Bi takan Iyah ba ta shiga Kiran Lubnah.
Bayan Lubna ta ɗauka tattaunawa sukai akan zuwan Mahir wajan Adaah.Wanda suka bari akan yau zai shigo da Yammah tana gama wayar Kiran ƙawarta Hajiya Sa'a ya kuma shigowa akan yau ake kawo Lefen ƴar ta, wadda zata auri ɗan sarkin Yola.
Momi dabur cewa ta kuma yi a daddafe sukai sallama da wannan ƙawar tata ta shiga sintiri kai ai bama zata bari Adaah ta auri wannan yaro ba ina sam ai hakan babban Ci bayane a agare ta.
Cikin shirin Makaranta Adaah ta fito doguwar Rigar Material mai mayafi ce ajikinta har Lokacin Fuskarta bata saɓe daga Kumburin kuka ba ta ƙaraso ɗakin Momy domin tai mata sallama Momy ta zubawa Ƴar tata ido kafin tace.
"Kai Allah ya isa! wallahi duk wanda yayi silar Jefaki a damuwa Allah ya saka miki Jibi Yadda kika Koma don Allah Kije ki saka kwalli ki gyara anjima Maheer zaizo wajanki Ɗan Babarki Lubnah in kuka daidaita Kawai auren ki zeyi mu huta da wancan auren tsiyar"
Dafe gefen kanta tayi,tana rintsa ido tana so taiwa Momi magana amman ta kasa saboda yadda kan nata Ke faman sarawa
Se zama tai a bakin gado da tausayi momi tace mata In bata Jin daɗi ta haƙura da zuwa makarantar.
Kwanciya tayi a gefen gado tai lamo tana Tuna waye ma Mahir Ita yaushe rabonta da shi
Waya tayi wa ƙawarta Husnah akan yau ba zata iya shiga School ba bata jin daɗi Husnah tai mata ya jiki sukai sallama a ɗakin Momy taita Birgima har bacci yayi awon gaba da ita dama rashin baccine yasa mata ciwon kan.
Bayan sallar la'asar tayi wanka tayi sallah tana zaune Mahir ɗin ya faɗo falon yana faman Kiran Momi kallo ɗaya Adaah tai masa ta shaida shi kauda kanta tayi ko kaɗan bai mata ba, bama kalar Namijin data ke so bane.
Ita ko Momi Sai Murna take suruki yazo se sawa take ana kawo masa kayan Motsa baki shiko ya wani kafe Adaah da kallo tsaki taja ta bar Mishi falon kuma duk yadda Momi ta Bita ta rarrasheta akan tazo su gaisa da mahir taƙi daga ƙarshe ma seta sa kuka tana cewa.
"Yaya zanyi ne Abbah ya kawon ɗan jagaliya ke kin kawon mai kama da fefe tsakani da Allah wazan zaɓa wallahi Momy bai Yi min ba Koni fa na fisa tsayi Ga shegen rawar kan tsiya gaskiya Momy ki sake shawara Nidai abar min Habib yafi min su dukan su"
Ran Momi ya ɓaci tana gudun kar tirjiyar Adaah ya basu matsala da ƙawarta fita tayi ta bawa Mahir haƙuri akan Cewa Adan bata da lafiya ne ta kwanta.
Da rawar Jiki yace amata sannu zai dawo domin shi kam yaga waje dan baya jin zai iya haƙura da Neman aurenta koda in ya auren ta zata kashe kanta ne sabida wannan Dukiya daya hanga a gidan yasan in ya auri Adaah Kakarshi ta yanke saƙa ai shi du yadda Mamanshi ke kwaɗaita masa abin Bai tabbatar ba seda yazo dan shi bai taɓa shiga Cikin Gidan ba sai yau ko kawo mamarsu yayi to daga waje yake Juyawa.
Tare suka jero da Baba shi ya dawo daga shago baba kuma ya dawo daga kasuwa, Hannun Saadik riƙe da manyan ledojin daya yo musu siyayyar gida.
Har tsakar gida suka ƙarasa Innah tana daka daddawa Saadik ya mata sannu da aiki ya aje Ledojin yana ƙoƙarin ya juya Baba ya kira shi.
Ya dawo gaban baba ya tsugunna Baba yace.
"Sadauki nikam banji kana yin shirin bikin kaba, kaga jiya Amadu ya min waya yana ƙara tabbatar Min da ɗaurin auren ku bayan ya dawo"
Cije yatsa yayi sam ya manta da maganar gaba ɗaya Tunanin shi bama ya kan batun
"Baba akwai wasu kuɗaɗe dana aje akan fara ginina In sha Allah zan kaiwa Aunty Amina a fara haɗa lefe sannan batun wajan zama wannan Gidan da yake kallon mu naga masu gidan sun tashi zan wa mai gidan magana in babu wanda ya kama ni Ina so"
Baba ya faɗaɗa far'a tare da cewa.
"To Allah yayi jagora Ubangiji ya sawa abin albarka yanzu naji batu"
Innah kam dakanta ta cigaba dayi dan ba zata tabbatar da Murna ko takaicin auren ɗan nata ba tana dai yin addu'ar zaɓin alheri kawai.
Tashi yayi tare da nufar ɗakin shi.
Har ji yayi kansa na juyawa sabida Tada maganar da Baba yayi.
Ya zira Key a jikin Ƙofa Yaji alamun Kuka a bayan shi da sauri ya juya sukai idanu Huɗu da Jiddah Kwanon abinci ne ta kawo masa tazo Baya ɗaki zata Miƙawa Innah ta aje masa ta kuma gaida Innar wadda tace bata shigo wa kwana biyu tana shirin shiga Gidan taji maganar Baba wadda yake wa Saadik kuma tasan ba akan ta bane to wacece wannan wadda zata aure shi in ba ita ba inko itan ce ai ba shirin yanzu bane tinda taji Baffa yace seta gama makaranta.
Tana ƙara kallon shi sai taji zuciyarta ta karye wani Irin ƙaƙƙarfan kuka na ƙara tawo mata.......
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*009*
Yana sa ƙafafun sa a ɗakin sukai idanu huɗu da ita kallon juna suka shiga yi kafin da sauri ta janye idanunta daga cikin nashi tana mai juya kanta gefe bata sake kallon shiba.
Saiti da