Author : Autar Manya Category : Romantic Hausa Novels
faɗa maki karki ga kin sami daula dole sai kin Miƙe tsaye to gashi nan dai Kirsar da kike cewa kina da Ita bata hana Mijinki Botsare miki ba"
Momy ta ɓata rai.
"Keni kada ki faɗa min magana mafita kawai nake Nema Amman Ni nasan Kirsata tai Min maganin waɗancan tsinannun"
Taɓe baki Lubnah tayi tare da cewa.
"Yanzu dai turo min wani abun Da zan turawa malam ya fara Bincika mana Halin da ake ciki"
Da sauri Momy tace.
"Baki da matsala bari na sako Miki Kuɗin nan ƙawata Aminiyata ta duk duniya dan wallahi Kinfi min ƴan uwana don basa damuwa dani kamar Ke"
Lubnah tai dariya tare da cewa.
"Karki damu Komai nai miki kaina nayi wa Kin manta taren fa bata yanzu bace, Nima Kin min Komai a rayuwata duk da Mijinki yafi nawa arziƙi Amman baki taɓa yada ni ba Komai naki sai kin saka dani Allah dai yabar mu tare"
Bayan sun kashe wayar Momi ta rarrashi Adaah Ta nufi ɗaki domin sallah, Ita kuma Momi ta zauna tana turawa Hajiya Lubnah kuɗin data Buƙata Bayan Awa Biyu Hajiya Lubnah ta Kira Momi tare da ce mata Lamari fa ya wuce nan dole seta zo sunje tare dan bayani a waya ba zai yuwu ba.
Tashin hankalin ƙaryar da zatai wa Abbah ta shiga domin tasan Ba zai barta Ta fita cikin sauƙi ba Koda kuwa da Jikin Iyah tayi ƙarya A haka ta kwana tana Juyi tare da saƙe saƙen yanda zatai Cikin Ikon Allah ma washe gari da asubah Abbah ya zo mata sallama akan zashi lagos sati ɗaya zai yi wato rashin Jituwar da basa yine bai faɗa mata ba, Itama babu wata walwala tai masa fatan dawowa Lafiya ta Juya ta cigaba da uzirin gabanta.
Sai da taji fitar shi sannan ta kira Hajiya Lubnah Akan fitar tasu da magagin Bacci Lubnah ta miƙe se Lokacin ma tasan Asubah tayi Ta shiga Toilet dan ta kintsa domin a cewarta fitar wuri zasu yi.
Itama Momi Kintsawa ta shiga yi tasan Adaah inta farka taga bata nan ba damuwa zatai ba dan haka data kammala shirin sai ta zauna tana Jiran isowar Aminiyar tata.
Abbah Har ya nufi Airport Sai ya cewa driver ya koma da baya suje Chiranchi tinda akwai sauran Lokaci kafin tashin Jirginsu Suna tafe yana duba hanya don ya kwana Biyu bai zo wajan Ɗan uwan nashi ba sanda Motar su ta shiga Layin Baba yana Addu'ar fita daga gida sabida sammako zaiyi Abbatuwa wajan sarin nama domin Idan kana son Nama mai Arha sai kayi Asubanci.
Da sauri Abbah ya Ɓalle Murfin Motar ya fita ya ƙarasa gaban Baba ya tsugunna har ƙasa tare da cewa.
"Yaya barka da Asuba"
Baba ya miƙawa Abba Hannu cikin so da ƙauna irin ta Jini Abba ya kama Hannun Baba ya miƙe suka shiga Cikin Gidan.
Da Saadik suka ci karo wanda yake zaune a bakin Rijiya yana Brush cikin sakin fuska Abba yace.
"Malam Abubakar ashe yau zamu haɗu barka da asubah"
Sai da ya wanke baki sannan ya shiga gaida Abba wanda yaketa Kallon Saadik cike da son Ƙulla Alaƙar Aure tsakanin shi da Ƴarsa shiko Saadik ɗaki ya wuce ba wata cikakkiyar walwala a tare dashi domin shi Mutum ne mai gudun ƙasƙanci.
Abba yabi bayan ɗan uwanshi yana waigen Saadik aranshi yana Jin amintar bashi Ƴarshi domin Irin Yaron da wiya mace ta raina shi, Har Saadik ya shige Abba na waigen shi Tare da Jin rashin daɗin yanda baya sakewa dashi daga gaisuwa shikenan kwanakin baya babu yanda bai da shi ba akan ya dinga zuwa kasuwa wajan shi Amman fafur Yaƙi Yace shi Gwangwan ɗin shi ta fiye mishi zuwa kasuwa.
Innah dake fitowa daga Kitchen hannunta Riƙe da Ludayin Miya wanda take Juya Miyar da zatai Ɗumaman tuwon Ƴammakaranta ta saki fuska sosai tana amsa gaisuwar Abbah
"Dama Amadu kana duniya yaushe rabon duniya da ayyaraye rabon dana ganka har na mance fa"
Abbah ya sosa kai Zai bata amsa Baba ya ɗaga Murya yana cewa.
"Amadu Rabu da Hafsa yau wasan ƙanin Miji take maka zo mu gaisa Ina sauri"
Jiki a sanyaye Abbah ya shiga Rumfar da Baba ke zaune a nutse suka gaisa dan tsananin Kunya Abbah yama kasa ɗagowa ya kalli Baba shiko Baba sai jan Abba yake da Hira koda wasa bai masa maganar komai ba.
Tuwon dawa miyar kuka sai tashin ƙamshi daddawa yake Innah ta shigo masu da shi tare da Koko mai zafi.
"Wato Amadu yasa dole sena karya zan tafi kasuwa, Kin san Hafsatu fa da tuni nakai Titi Amadu wanke hannu a silba Muci tuwo".
Abbah ya ɗauki ruwa ya na wanke hannun shi tare da cewa.
"Wato na jima banci tuwon Innah ba kuma ina marmarin tuwon innah kasan Yaya yawanci matan yanzu ba ko wacce bace ta iya tuwon dawa kamar na Innah"
Aiko mai innah zatai In ba dariya ba ta fice tana cewa.
"Kai Amadu kodai zolaya ta kake yi nikam ba zan tsaya jin daɗin bakin kaba nayi nan"
Daga shi har Abba dariya suke Suka saka hannu tare da Bismillah suka fara cin tuwon Abbah ya zage yaci sosai yasha Kokon Shi kam Baba bai ma ci da yawa ba Ya tashi ya wanko Hannu Abbah ne yakai kwanukan bakin Rijiya ya wanko hannu shima ya dawo.
Bayan sun zauna Abbah yace.
"Dama Yayah batun auren yaran nanne Ina ganin idan na dawo daga wannan tafiyar sai a ɗaura musu Auren, Batun Hidimar Aure dama nace maka bana buƙatar Komai sai sadaki Zan basu gida sannan don Allah maganar Kasuwa har yanzu Ina Barar yazo wajena Ya nemi abincin shi na bawa wasu ma waje bare kuma nawa"
Baba ya nisa kana yace.
"Haƙiƙa Amadu a baya nayi Fushi dakai sabida yadda ka ƙaurace mini ka daina zuwa inda nake, Amman yanzu na huce sabida haka Bari na kira Sadauki! inya Aminta da tayin naka sai ayi komai a nutse dama bai fara Ginin Gidanshi ba kasan yadda lamarin yake yadai sayi fili anan bayan Gidannan"
Baba ya fita yasa Ummi tayi Kiran Saadik wadda tai shirin makaranta Cikin Blue Ɗin Uniform ɗinta.
"Ke Ummi in kika fita ki kira min kawun ku a ɗakin soro"
Ummi ta amsa wa Baba tana nufar soron sai dai ta ga Khadija a raɓe tana share hawaye Ummi tai saurin cewa.
"Ke kuma keda wa kike faman share hawaye?"
Cikin ƙasa da Murya Khadija tace.
"Kibi a hankali kayan kari Innah ta bani na kaiwa kawu Saadik wallahi bakiji ranƙwashin daya Min ba wai banyi sallama ba kuma nayi fa"
Dariya Ummi tayi tana cewa.
"Ba lallai Kinyi ba kuma kinsan halin Kawu su Ya Umar ma shakkarshi suke bare mu"
Ummi ta wuce A bakin Ƙofa tayi sallama sai da yaja aji kafin yace.
"Waye ne?"
Ummi tace.
"Kawu dama baba ne"
Bata ƙarasa ba jin yayi shuru sai can yace.
"Ni kike faɗawa ko ƴan Ƙofar Gida?"
Fahimtar mai yake Nufi yasa taja Labulan ɗakin nashi Ƙamshi da wani Irin sanyi ne suka bugeta daga Nesa dashi ta durƙusa duk Girmansa ya cika ɗakin.
Murya a hankali tace "Dama Baba ne yace kazo"
Ta faɗa tana Raba ido sabida yadda yayi mata masifar kwarjini.
Batare daya kalleta ba yace.
"Kice gani nan"
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa daga bakin katifar.
Da.
"To" Ummi ta amsa tana miƙewa ta fita daga ɗakin taje ta sanar da Baba Saƙon sannan suka tafi makaranta Lokacin ƙarfe bakwai da rabin safiya tayi.
09022260850
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*003*
Ita kuma tayi saurin taɓe baki tayi raurau da manyan idanunta waɗanda suka ciko da hawaye ta ƙura masa idanun nata duka tana kallon shi.
Murmushi yake yi har Lokacin hannunsa yana dafe da goshinsa.
"Ni da kika bugawa wannan ƙaton Goshin naki banyi hawaye ba sai ke?"
Hannu tasa ta kare fuskarta tana Murmushi ga hawaye kuma na ƙara zubowa.
Ya ƙara matsowa gabanta ya fita tsayi nesa ba kusa ba hakan ya sa ta ƙara komawa ƴar ƙarama a gabansa.
"To ni yaufa naga takaina Kinga dan Allah zoki rama Duk da nima dai naji zafi"
Dariya ta saki tana cewa.
"Kai kawu Saadik tsokanar kafa nake yi wai ina zaka je Sai ƙamshin turare kakeyi?"
Ta faɗa cikin sigar tsokana
Ya tsuke fuska kaɗan.
"Dama bana saka turare sai zan fita Hawwa'u?"
Saurin dafe baki tayi tana wara ido.
"Wasa nake maka fa"
Ya ɗan kalleta.
"Wai bana ce na soke kawun nan ba su in sun cemin kawu kema sai kice min kawu maza sai wata tazo tana cemin my love ke kina faɗin wani kawu"
Ƙafafu ta hau dirawa ta fara Kukan ƙarya Raɓeta yayi zai shiga ɗakin shi dake soro da sauri ta bishi
Ya tsaya a bakin ƙofar ya kare hanyar da zata shiga ɗakin ya tsareta da ido.
"Abinchi na kawo maka na miƙo maka?"
Ta faɗa tana Waigawa bayanta tare da ɗaukar Kular data zubo masa Abinchin.
Cikin tsananin so da tausayi ya dubeta.
"Bana hanaki kawo abincin nan ba yanzun nan muka kammala cin tuwon innah nida Baba"
Turo baki tayi kaɗan.
"Nima Gas ɗinmu ne ya ƙare seda ummah tayi wa Yayah Fa'izu waya ya kawo mana shiyasa ban kawo maka abincin da wuri ba"
Yadda take maganar Jiki a sanyaye ta ɗan bashi tausayi shikam ya rasa wani irin so yarinyar take mishi wanda yake ganin son da take mishi kamar yafi nashi duk da shima yana sonta.
Ya zira hannunshi ɗaya ajikin aljihun wandon shi.
"To ni yanzu yaya zanyi da wannan abincin tinda nidai cikina ya ƙoshi"
Yanda yayi maganar ta bata haushi sai kawai ta juya tare da ficewa daga soron.
Beyi gigin bin bayanta ba dan yasan rigima ce zata kaure musu ƙarshe inta saka mai rigima ya karɓi abincin ba iya ci zai yiba inya bayar kuma taji haushi.
Sai kawai ya shiga ɗaki cikin hukuncin Allah yana shiga ana kawo Nepa ya jona cajin ƙaramar wayarsa.
Yana ƙoƙarin cire shirt ɗin jikinsa ƙaramar wayar tasa ta shiga Ƙara alamun kira yana shigowa Bayan ya ɗaga Muryar Abokin shi Nura saiti ta cika masa cikin kunnen shi.
"Wai dan Allah dagiya ina ka shiga ne?"
Saadik ya ɗan ja tsaki kaɗan.
"Yanzu dai meke tafe dakai ko tambayata ka kirani kayi? kaje shagona baka ganni bane koka zo gida bani nan?"
Saiti yayi dariya tare da cewa.
"To sarkin fushi nai maka magana ne naji shuru, ko baka kunna Data bane yau?"
Takaicin ɗazu ne ya faɗo masa ya fesar da huci mai zafi.
"Bari kawai Nura wayar ma bata wurina Allah yasa sim ɗin yana wannan wayar"
Da sauri Nurah yace.
"Garin yaya matsala ta samu?"
Cikin son kauda zancen sabida shi gwanin zurfin ciki ne yace.
"Ya ake ciki ne kana shagone koka shigo?"
Nura yace.
"Yau na sami cinkoso ne a wajan IBB Road kasan hanyar tamu sai a hankali, Amman gani nan dama Najika shuru ne nace bari na taɓaka kako san yau Za'a Buga wani zazzafan wasa?"
Duk yanda Saadik ke son kallon Boll sam yau ya mance zasu je kallo kwata kwata sabida haka tsaki yaja dan baida karsashin fitar ma gaba ɗaya Nafila zai yi kawai ya kwanta yasan Baba zai fita waje shan iska bayan ya gama jin Labaran sha ɗayan dare ya rufo gida shiyasa zeyi kwanciyar sa.
"Nura Kuje kawai kaida su Babu danni gaskiya yau ɗinnan ba zan iya zuwa gidan kallo ba"
Daga haka ya kashe wayarsa gaba ɗaya ya mayar chaging ya koma ya kwanta ya zurfafa acikin tunanin wannan lamari mai girma daya faɗo masa ko a kanshi bai taɓa tunanin Baba zai masa auren dole ba, dan shi kam wannan aure na dole ne yana zaman shi lafiya Baba ya bashi Umarnin zuwa inda za a ɓata mishi rai.
Maganganun Baba na jiya da daddare ne suka soma dawo masa cikin kansa.
"Sadauki!Waye mahaifinka?"
A lokacin sun kammala cin abincin dare ne duk suna zaune a Rumfar Baba shida Baban da Innah wadda take cin Gyaɗa marau marau.
Ya Nutsu sosai tare da cewa.
"Baba duk duniya ban san wani a wannan matsayin na uba ba face kai"
Baba yaji daɗin kalamin shi duba da yanda yayi Murmushi a lokacin haɗi da samai albarka kafin ya fara dirar mashi da maganar data haifa masa ɗaukewar Numfashin wucin gadi.
"Sadauki jiya mahaifin Wannan yarinya Hauwa'u mai haƙuri da kawaici ya kirani akan maganar auren ku sabida karatunta daya kusan zuwa ƙarshe, Bayan nai masa na'amm da maganar sai na ɗauki wayata na Kira ɗan uwana wanda duk duniya bani da kamarshi Amadu uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya nina saki Nono ya kama na shaida masa batun Auren ka"
Baba yaja fasali.
Saadik yaji wani irin farin ciki a zuciyarshi.
Innah ma sai ta hau murmushi sabida Jiddah ta cancanta ta zama surukarta duba da yanda yarinyar ke son ɗan nata tilo tal namiji aduniya kuma auta acikin ƴaƴanta waɗanda dukka mata ne Allah ya bata shi kaɗai ne namiji acikin su kuma shine auta.
Maganar baba wadda ta katse Murnar Innah da Saadik ita ce ta cika Kunnuwan su.
"Sai dai Amadu ya katsen hanzari, ya mini kyauta kuma na amsa tinda bahaushe yace yaba kyauta tukwici dik da kyautar dama bata yanzu bace amman Lamarin daya zo ya cuɗe a tsakanina da shi yasa na fidda rai akan kyautar ta shi Sadauki Amadu yace kaje ka Nemi auren ƴarsa RABI'AH duk da maganar ba sabuwa bace a wajena nida Hafsatu mahaifiyarka Tin ranar da Aka haifeka da Amadu ya ɗaga ka yace In har Matar sa ta haifi ƴa mace yayi ALƘAWARIN ba tada Miji sai kai to yanayin yadda Zumuncin mu ya lalace da shine yasa Ban ɗauka zai cika wannan Alƙawarin ba sai kuma gashi ya cika don yace sadaki kaɗai zaka bada Rabi'atu dai ƙanwarka ce da ubanta dani cikinmu guda dan haka In har ni na haifeka kamin alfarma kaje ku sasanta In yaso ita Hauwa'u sai ka aure ta inta kammala karatunta ba zan hanaka auren wadda kake so ba Amman Nima ka auri wadda Mukai Alƙawari Nida ɗan uwana ko Allah yasa silar auren ku zumuncin mu ya daidaita"
A lokacin jikin Saadik babu abin da yake sai rawa hatta bakin shi Gumi ya jiƙa masa rigar shi, Dama ga zafin ɗaki dan lokacin babu wutar Lantarki.
Inna zatai magana Baba ya ɗaga mata hannu alamun baya buƙatar cewarta, Sai taja baki tayi shuru.
Numfashi ya dinga ja yana ambaton sunan Allah kafin ya samu Nutsuwar Furtawa Baba Kalmar.
"Amman Baba hakan ba zai jawo mana ƙasƙanci ba, Mutumin da baya neman ka Yana matsayin ƙaninka amman ya nuna yanzu Shi mai Kuɗi ne ya janye zumuncin dake tsakanin ku, Baba ka rabu da shi Ka Nema min Auren Hawwa'u ita ce wadda take matiƙar sona domin Allah Nima Kuma nake sonta Amman ita waccan da ban santa ba bata sanni ba Ko sunanta ban sani ba tayaya zan aureta Baba?"
Baba yayi murmushi irin nasu na manya kana yace.
"Ka bar batun Amadu Yaro ne ɗan halak Shu'umar macce kawai Ya haɗu da ita Ina son ka auri Rabi'ah ne Ko ta sanadin auren ku Allah zai sa Zumuncin mu yayi ƙarfi nida ɗan uwana, Fanni zamantakewa kuwa nasan Autana Ba ragon namiji bane in mace Huɗu ya aura zai iya ɗaukar Nauyi ci da shanta Hauwa'u Kuma In Allah ya yarda bata da Miji Sai Kai Kodan karamcin Mahaifanta garemu"
Yayi Biyayyar Amsawa Baba tare da amsar Auren ne badan komai ba sai dan tsan
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*005*
Da sassarfa yake tafiya cikin gidan nasu harya ƙarasa cikin rumfar da mahaifin nashi tare da ɗan uwan shi, suke zaune da sallama a bakin shi Ya Nemi Gurin zama daga Nesa dasu yaɗan Sunkuyar da kanshi a ƙasa.
"Sadauki! dama Babanka Amadu ne yazo min da magana shi ne nace a kira ka Amadu ga ɗan naka nan sai kuyi maganar"
Har Lokacin bai ɗago kanshi ba Abbah ya gyara Murya tare da cewa.
"Kwanakin baya na taɓa zuwa da maganar ka fara zuwa Inda nake a kasuwa amman ka nuna baka ra'ayi shine nace yanzu meze hana kazo wajan nawa Kodan Iyalin da zaka fara riƙewa kasan yadda rayuwar ta koma, Batun auren ka da ƴar uwarka Ina son daga na dawo ai maganar auren ku sadaki kaɗai nake buƙata zan baka Gidan zama da Mota sannan kuma ga kasuwa duka Allah ubangiji yasa wa auren ku albarka Amin"
Baba ne kaɗai ya taya Abbah amsawa da Amin amman gogan naku ko gezau bai yi ba sai da Baba ya kuma cewa.
"Wai Sadauki! ba kaji maganar Kawun naka bane?"
A hankali ya ɗago fuskar shi wadda tai jajir abin ka da fari yawanci in yana cikin damuwa Fuskarshi ja take Musamman saman Hancin shi.
Murya a shaƙe kamar an masa dole yace.
"Abba nagode da karamcin auren da kabani ma kaɗai ya wadatar sauran duk na yafe, da farko ina da sana'ata duk da a wajan wasu kamar ta ƙasƙanci ce amman ni a wajena sana'ata tana da Muhimmanci a gareni domin da ita na dogara har na tsaya da ƙafafuna, Gwangwan nake kamar yanda ka sani ina Auna ƙarafa ina siya nima na siyar na sami abinci, Sannan Batun Auren gaggawa dan Allah Abbah ayi min uziri kaɗan zan ƙarasa shirina sabida Kutsen da aka min son samu na zauna agidan kaina amman hakan baze samu ba dan haka zan kama haya Kuma zan mata lefe daidai ƙarfina son samu ta saka kayan Da Mijinta ya ɗinka mata sabida haka ayi min uziri har na kammala komai sena yi magana"
Gaba ɗaya Abbah shagala yayi da kallon Saadik a ranshi kuma yana jin wannan shine Mijin da ya cancata Ƴarsa ta aura sabida ta Ko'ina jarumi ne, Baba kuwa baiji mamakin furucin ɗan nasa ba Yasan shi sarai shiyasa yaƙi amsawa Abbah tayin daya masa Sabida yasan da wiya Saadik ya amsa aikuwa gashi nan ba'a je ko ina ba yaƙi.
"Shikenan Abubakar! Allah yasa albarka a lamarin Na gamsu da bayananka, Kuma Ina fatan Zaka riƙe ƴar uwarka da amana"
Bai Motsa ba, bai kuma tankawa ƙanin mahaifin na shiba.
"Zaka iya tafiya"
Cewar Baba.
Da sauri Abba yace.
"A,a dan Allah Abubakar, ka ƙara komawa wajanta Ku sake tattaunawa sabida Ku fahimci Juna don zaman lafiyar auren ku shine kwanciyar hankalin mu"
Tausayi Abba ya bawa Saadik da ɗan sassauci yace.
"In sha Allah"
Yana danne takaicin ta na jiya dan shi ba soko bane baya jin zai iya kai ƙarar mace bada ban haka ba da yace