SO DA ALKAWARI HAUSA NOVELS BY AUTAR MANYA.txt

Author :  Autar Manya Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 12

18K to 21K   out of 35.4K words

Fa'izu suka sami gurin zama suna gaida ummah saɓanin Shi daya ƙarasa gaban gadon yana zubawa inda ta juya idanu.
Tsananin kunyar Umma tasa ya nemi gefe ya jingina kafin yaɗan rissuna ya shiga gaisheta.
Ba yabo ba fallasa umman take amsawa fuskarta ɗauke da damuwa.
Maganar fa'izu ce ta katse shurun ɗakin sabida tinda suka gaisa babu wanda ya kuma yin wata magana.
"Ummah wai me ya sameta har kuka zo asibiti?"
Shuru ummah tayi kafin ta furta.
"Shirme ne kawai irin na Jidda da yarinya yo Allah na tuba namiji goma uba goma ne ni wallahi tin kafin ayi auren nan lamarin nan ya fitar min da ga rai"
Saadik ya rintse ido ya shiga furzar da iska mai zafi, yaji ɗacin maganganun ummah domin tana Babba bai dace tana faɗin irin haka ba, in rai ya ɓaci zuciya ake dannewa bare ma shi bai ga wani abun zafi daya ma ƴarta ba.
"Umma wani abunne ya faru da Jiddan ni duk kin sakani a duhu na kasa fahimtar abin da kike nufi wallahi"
Ƙaramin tsaki taja.
"Wai dan mahaifan Abbakar sunce zasu aura masa ƴar uwarsa shikenan ta faɗi a soron gidansu ta suma yana kallon ƴar tawa ya tsallake ya tafi ya barta a haka ba da ban Allah yasa mutan gidan sun ganta ba da ko mutuwa zatai babu wanda ya sani ni wallahi Jiddah batai zuciyata ba sam danni inda nice da yanzu wata maganar ake ta daban banda abin ta menene na ɗaga hankali akan namiji"

Murmushi fa'izu yayi gaba ɗaya kunyar abin da mahaifiyar shi tayi yanzu ta gama kamashi inya fahimta ummah tana cikin zafin kishin ƴarta ne shiyasa take faɗin duk maganar data zo bakinta.

"Ummah bai kamata ki dinga faɗin irin haka ba shi aure nufin Allah ne karku bar shaiɗan ya raba alkairi don Allah ku dinga sauƙaƙa zuciyarku"
Ɗaga masa hannu tayi da sauri Saadik ya fita daga ɗakin yana jin ba zai iya jure cin fuskar da mahaifiyar Jiddah ke masa ba kuma baya jin zai iya tanka abin da take faɗa sabida yana ganin girmanta.

Nura da kansa ya kulle da lamarin shiya iya musu sallama ya baro ɗakin a titi ya hango Saadik yana tafiya sabida saurin da yake har yayi wa Nura nisan da bai tunani ba sai da Nura ya ƙarasa da gudu sannan ya cimmasa.

Tafe suke babu wani wanda yace wa ɗan uwan shi wani abun, sanin halin Saadik da Nura yayi in yana cikin damuwa baya magana har sai ya huce damuwar ta tafi sannan yake samun damar yin maganar.

Da ƙafa suka ƙarasa gida a ɗakin Saadik suka yada zango Nura ya zauna a gefen katifa shi kuma Saadik ya shiga banɗaki ya jima aciki sannan ya fito ya ɗauki Jallabiya ya koma banɗakin ya saka sannan ya dawo ya zauna.

"Wai Dagiya meya ke faruwa ne?, gaba ɗaya kaina ya kulle kaifa kana da matsala wato mu semu faɗa maka duk abin da yake damun mu amman kai zurfin cikin tsiya baka bari a tattauna damuwarka"

Yaja ajiyar zuciya mai ƙarfi saman hancinsa kamar kullum yayi jajir sabida ɓacin rai da damuwa idanunsa ya kaɗa yayi ja ya kalli Saiti tare da cewa.
"Aure baba zai mini, auren dole shine ita kuma take wannan shirmen har take kwanciya a asibiti"
Da mamaki saiti yace.
"Aure kuma kai ban fahimta ba aure da wa kuma?"
Ya lumshe ido kafin ya buɗe a wahalce yace.
"Wata yarinya ce ƴar ƙaninshi da sukai alƙawari zasu haɗa auren mu, to abin nima kaina da ka ya zo mini"

Saiti me zeyi in ba dariya ba harda kifawa ganin Yadda Saadik ya haɗe ranshi yana cewa auren dole baba zai mashi.
"To kai kam kaji daɗin ka ina ma nine aure a wannan ƙadamin ai sai ka shirya, Allah ya tabbatar da alheri inna fahimta Maman Tafisu taya ƴarta kishi take yi har taso tai abin kunya a gabanmu"

Jingina kanshi yayi da jikin bango ya rintse ido maganganun Ummah sun ƙona masa ranshi, inya fahimta Jiddah ce ta haɗa masa ƙarya da gaskiya a wurinta shine ita kuma ta hau ta zauna ta goyi bayan ƴarta in ko haka rayuwarsu zata tafi akwai matsala babba tabbas!

Nura ya tashi yana masa sallama tare da ce masa gobe zasu haɗu dasu Babu a tattauna akan bikin shidai bai cewa Saiti komi ba har ya bar masa ɗakin.

Dama ya ɗaura alwala a banɗaki sabida haka sallar isha'i yayi har ya cire jallabiyar jikinsa zai kwanta ya tina bai leƙa wajan innah ba yasan ko yayi bacci sai ta tashe shi yaci abincin dare, sabida haka rigar ya maida a jikinsa ya saka takalmi ya fita cikin gidan.

Da umar suka ci karo zai shiga cikin gidan shima, umar yaja baya yana bawa Saadik wuri don ya wuce, sai da ya shiga sannan umar yabi bayan shi yana cewa.
"Dama Kawu Saadik neman ka nake naje ɗakin ka na ganshi a kulle lissafin kuɗin ƙarfan motar nan ne"
A hankali yace.
"Umar kaje ka huta mu barwa safiya mana sai kace zaka gudu"
Dariya umar yayi yana cewa.
"Gobe ina da Exams a school zan fita da wuri sabida karatu"
Ya ɗan juyo yace.
"Ban gane sabida karatu ba, da me kake yi da baka yi karatun jarrabawar ba?"
Umar ya shafa kai tare da cewa.
"Kasan yanayin shagon yanzu anfi ciniki sabida masu cire rodin aikin titi, shiyasa bana son na motsa ko ina, kasan su Usman ba kamar niba in aka ga sune a shagon raina musu hankali ake su tsula kuɗi suyi tsada"
Saadik yaɗan ja ƙaramin tsaki.
"Wannan ba dalili bane, kada ka kuma sake jarrabawa tazo bakai karatu ba, ka miƙo makullin shagon ni sai na zauna kai kuma ka dinga zama a gida kana karatun ka har ku gama jarrabawar Allah ya bada nasara, in da wani abun da zasu siya kuma ka sanar dani koka ɗauka kawai"

Umar ya rissuna cikin ladabi yana masa godiya su kam tsakanin su da kawun nasu sai dai addu'a amman abin da yake musu a rayuwa na kyautatawa yafi gaban baki ya furta.

Shiga ɗakin Innah yayi shi kuma Umar ya shiga nasu ɗakin da yake kusa dana Baba.

Da sallama a bakin sa ya zauna a gefen gadon innah kafin ya jingina kansa ajikin gadon ya zuba mata ido tana lazumi ne carbi mai dubu a gabanta.

Har ya soma bacci sama sama yaji muryarta tana tashin sa.
"Sadauki! sadauki!! bawan Allah wato har yayi bacci"
Ya Mitsika idanun shi waɗanda suka ƙanƙance sabida bacci yana kallonta.
"Innah wai sai yanzu kika kammala kenan na dawo ne shine nace bara na zo muyi sallama sai da safe kuma"
Ya faɗa yana miƙewa yana saka hannu a baki yana hamma.

"A,a sadauki ka daure kaci tuwo mana kada ka kwana da yunwa"

Ya wani zaro ido ya saki ƙaramar dariya.
"Haba Innah so kike dole dai na zama ɗan gargajiya, tuwon darannan kumbura min cikina yake amman ke dole sai naci"
Dariyar itama ta saki.
"Dama kai tin kana yaro baka son cin abinci sosai to yanzu bara na dafa maka ruwan shayi kasha sai ka kwanta, Yaya jikin Jiddan?"
Ya lumshe ido ya buɗe tare da cewa.
"Da sauki tana ma gaishe ki"
Ya ɓoye mata zuwa asibitin da kuma maganganun ummah sabida su iyaye ba komi ake son faɗa musu na ɓacin rai ba.
"Innah kibar shayin nan zan fita na sayi kankana da lemo na sha na kwanta"
Ta zuba masa ido cikin so da kauna tace.
"To kadai kafe amman mai kankana zata maka maza jeka ka siyo ɗin kada dare yayi"
Ya fita yana dariya ƙasa ƙasa tin yana yaro innah ta saba masa da zaman gida in baya gida yana wajan neman kuɗi ko makaranta, bata son yawo ko kaɗan kuma bata son yawan abokai ko su Nurah ma don abokan shine tin na ƙuruciya shiyasa ta barsu tare amman innah macece mai saka ido sosai akan lamarin ƴaƴanta ta gwammace in yana gida ya zauna suyi hira ko girki tare, to hakama ƴan jikokin nan nata Motsi kaɗan tace a duba mata wane takan ce Allah shike da rayuwa dai amman kaima ka kula sosai ka kuma haɗa da yin addu'a.

Sai da ya je ya siyo kankanar ɗauri uku aka masa ya kai tasa ɗaki ya miƙawa Innah leda biyun aiko tana tsakar gida da fitila a hannunta.
"Yawwa dama kai nake jira ka shigo to sai da safe"
Ta karɓa ta juya ɗakinta.

Shima nashi ɗakin ya ƙarasa yayi duk abin da zai ya sha kankanar ya yi brush haɗi da ɗaura alwala sannan ya kwanta nan da nan bacci mai daɗi ya ɗebe shi.

***

Sai da Momi taga fitar Mahir sannan taja ajiyar zuciya ta shiga sintiri a falo kanta ya ɗau zafi gaba ɗaya lamarin Adaah nason bata matsala tana ganin kawo Mahir shine mafi sauƙi da kuma mafita a garesu amman Adaah zata ce beyi mata ba.

Da sauri ta koma cikin ɗakin Adaah wadda take zaune ta zabga tagumi Motsin Momi yasa ta ɗago ta zubawa momi idanu har momi ta ƙaraso bakin gadon ta zauna jiki a sanyaye.

Ta dubi Adaah kafin tace mata.
"Ki nutsu zamuyi magana"
Cikin sanyin jiki tace.
"Ina sauraron ki Momy"
Momi ta gyara zama tare da tattara hankalinta ga Adaah kafin tace.
"Ni ban gane miki ba fa Adawiyyah jiya kinsan wahalar dana sha kuma duk akanki, tafiya mukai tamkar zamu bar garin muka je wajan wani shahararren malami shiya ce mana dole auren ki da Mahir shine mafita sauran bayanan kanki bazai ɗauka ba, amman dai don Allah kada ki watsa min ƙasa a ido duk wannan wahalar dan wa nakeyin ta hatta mahaifiyata fushi take dani duk akanki"
Adaah ta nisa kafin tace.
"Momy nifa fahimtata ce baki ba, wallahi gaba ɗaya Mahir ɗinne bai yi mini ba kar nazo na aure shi ku sami matsala da aminiyarki"
Momi ta kwantar da murya ganin yadda jikin Adaah yayi sanyi tace.
"Ki haƙuri ki min biyayya, Adaah ki auri mahir kodan mu bawa marar ɗa kunya kinji ƴar albarkar momynta in sha Allah wannan haɗi namu alheri ne abin da nake so dake da zarar abbanki ya dawo ki kafe kice ke Mahir kike so kinga daya bamu dama mu dama a shirye muke"
Adaah cikin rashin madafa tace.
"To Momy zan yi yadda kike so ɗin amman nikam bai mini ba"
Momi tayi murmushin cin nasara kafin tace.
"Zai miki ne da zarar kun zauna waje ɗaya Allah dai ya maki albarka"
Kwanciya Adaah tayi a cinyar Momy idanunta suka cicciko da ruwan hawaye don dai kawai bata son ta zubawa momin ƙasa a ido ne sannan kuma ta bata tausayi na wahalar data ce mata ta sha shiyasa zata karɓi auren Mahir ɗin.

Sai dare sosai Momi tabaro ɗakin Adaah har sai da ta tabbatar ta saki jikinta damuwar da ke tattare da ita ta kau sannan tai mata sallama ta baro ɗakin ta koma nata waya tayi wa Hajiya Lubna akan gobe mahir ɗin zai iya dawowa su gana da Adaah dama ɗazu ciwon kaine ya saka bata fito ba.

Makirin murmushi lubnah tayi tare da cewa.
"Kai haba Maryam wajan jibi ya dawo abarta ta ƙara hutawa shima kin ganshi tinda ya dawo ya ɗagamin hankalina akan ciwon kan nata"
Daɗi ne ya rufe momi cikin farin ciki tace.
"Ga wanda ya dace ƴata ta aura wanda ya san darajarta yasan damuwarta harya ji ya damu da damuwarta ba wancan shegen baƙin mugun ba, daya zo ya gargasa mata baƙaƙen maganganu ba, ta mutu ko tai rai shi babu ruwan sa tinda su in da zata mutu ba so zasuyi domin suci gado"

Hajiya lubna mai zatai in ba dariya ba.
"Kai ƙawata baki da dama wallahi"
sallama sukai suka kashe wayar ranar Momi taji iska mai sanyi na shigarta domin tana jin ta gama da Kaso Hamsin cikin ɗari sauran yaƙin gabanta kuma na Abbah ne don tana jin sai dai duk abin da zeyi yayi amman bafa zata bar wannan aure ba muddin tana da numfashi! tinda har ta sami nasarar shawo kan Adaah sannan shima Mahir ya karɓi abin hannu biyu to fa tana jin sauran yaƙin gabanta ba komai bane.
**

Washe gari wajan ƙarfe goma na safiya Iyah na zaune a falonta gabanta kuma Alkur'ani ne mai girma ta karanta shi, ta shafa ta aje shi a gefe ɗaya, sannan ta juya ta kalli Abbas dake zaune a gefenta yana waya, bayan ya kammala tace masa.
"Abbas kira min Amadu Mijin maryam jiya nayi mafarki marar daɗi ina fatan Allah ya tsare Maryam daga sharrin dukkan abin ƙi"
Abbas ya shiga kiran Abban Adaah a waya wanda sai da wayar ta katse sannan Abbah ya kira.
Cikin girmamawa suka gaisa da Abbas sannan ya miƙawa Iyah.
Abbah ya shiga gaisar da iyah cikin mutunci da sanin ya kamata.
Iyah ta gyara murya kafin tace.
"Amadu yaya batun auren Rabi ne naji kwana biyu baka bugo munyi magana akai ba"
Daga wajan Abbah cikin farin ciki yace.
"Alhamdulillahi Iyah dama yaron namu ne ya nemi da a ƙara masa lokaci sabida ya gama shirye shiryensa, shiyasa ma maganar ta ɗan kwanta"
Cikin dattijantaka iya tace.
"Haba Amadu shifa irin wannan aikin alherin ba a jinkiri wajan aiwatar da shi sabida magauta wannan abu fa duk na cikin gida ne sabida haka, ni zan sa akira min Ɗan uwan naka ai da lambarshi a wayar Abbas, se muyi maganar data kamata ayi a ɗaura auren nan sabida ina gudun kar maganar ta lalace"
Abbah yayi murmushi cikin ƙarfin zuciya yace.
"Da ikon Allah maganar ba zata lalace ba iya"
Sallama sukai cikin mutunci kafin ta umarci Abbas daya kira mata lambar baba, wanda Lokacin yana kasuwa kiran ya shigo sama sama suka gaisa dan bai ɗauki murya ba, sai da ta masa bayani sannan ya gane nan suka kuma gaisawa a mutunce sannan ta shiga yi masa maganar data sa ta kira shi a wayar.
Baba ya nisa kafin yace.
"Ni bana gida ne, ina wajan nema amman bari na sa a sako miki lambar wayar sadaukin sai ki masa waya kuyi maganar, kinsan yaranmu sai haƙuri shi yace yafi son yayi komai kamar yadda ake yi a yayin aure to kuma abin ka da marar ƙarfi fafutukar ake yi"
Cikin Nutsuwa Iyah tace.
"Haba haba malam kamar ba gida ba nifa yadda na ɗaukaki wannan aure abin sai ya baka mamaki maza turon lambar mijin nawa muyi magana"
Baba ya sa dariya yana cewa.
"To to iya angode da karamci"
Ya kashe wayar tare da miƙawa wani yaro dake gefen shi yace ya turawa lambar data kirashi lambar wayar Sadauki.
Baba yana ta murmushin karamcin iyah wato albasa ce batai halin ruwa ba, inda tayo ruwan da batai yaji ba.
Minti kaɗan lambar ta shigo wayar Abbas shi kuma ya kira wa Iyah lambar wadda taita ringing ba a ɗauka ba.
Da yake fita zai yi sai ya aje mata wayar yace koda za a kira seta ɗauka suyi maganar.

Tai mashi fatan alheri ya fita.

******
An sallamo Jiddah daga asibiti sai dai har zuwa lokacin Ko waya Saadik bai sake yi mata ba, kuma dama bai faɗawa Innah suna asibitin ba bare suje dubiya, Gaba ɗaya ran ummah ya gama ɓaci mita take tana cewa ga baki ga hanci ai ko iyayensa ne sa zo dubiya bare shi.
Duk Jidda tabi ta damu ta ƙara komawa ƴar firit sabida Mitar umma da kuma damuwar rashin Jin Saadik.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *10*

Zaune yake a bakin rijiya hannun shi riƙe da kofin da Innah ta cika masa shi da koko gefen shi kuma ƙosai ne wanda yake dangwala da yaji yana ci yana korawa da kokon.
"Haba kokai fa nina fi son ka dinga cin abinci sosai koka yi ƙiba kaike nan sai tsayi babu kauri"
Saadik ya ƙunshe dariyar shi sabida gudun kada ya ƙware sai da ya kammala sannan ya ɗago idanun shi ya kalli innah tare da ce mata.
"Haba hajjaju kullum fa sai na fita filin ball na ɗan motsa sabida naga har tumbi ya fara zamarmin ni kuma bana son shi, ni banga rashin ƙibata ba"
Innah tayi murmushi.
"Sanda kana yaro kafi haka fa yanzu duk ka rame sai tsayi ma sha Allah, nidai Sadauki ka dinga zama kana cin abincin ka sosai"
Tashi yayi da kofin da plate ɗin Ƙosan daya kammale ya miƙa gaban kayan wanke wanke wanda Khadija ke zaune tana yi sannan ya ƙarasa wajan Innah ya mata sallama sabida shago zai fita addu'ar alkairi ta dinga yi masa har bakin ƙofa ta raka shi Ɗakin shi ya shiga ya ɗauki wayar shi da makullin shagon da Umar ya bashi ɗazu da Asubah da suka fita masallaci ya rufo ɗakin ya fita.

Yana fita suka haɗu da Baffa mahaifin Jidda shima da alamun fita zaiyi da ɗan sauri ya ƙarasa wurin Baffan suka gaisa ya ƙara masa ya mai jiki.

Saadik na durƙushe baffa yace.
"Malam Abubakar kafa yi haƙuri da halin mata naji duk abin da Saratu tayi maka a asibiti kuma nai mata faɗa ai wannan shashancine dama ina son ma na gana da mahaifinka gwara ko kuɗin auren ne ku kawo asan inda magana ta dosa in yaso ta na kammala karatun nata sai ayi biki ina ga abin da zamuyi kenan Amman kayi haƙuri don Allah"
Saadik ya shafa kai tare da cewa.
"Haba Baffa karka sa damuwa acikin ranka, Ni ban riƙe abun ba ina ga ita Ummah fahimta ce batai ba Allah dai ya shiga lamuranmu gaba ɗaya"
Baffa ya ansa da "Amin"
Saadik ya miƙe yayi hanyar fita daga lungun shi kuma Baffa ya ƙarasa wajan Babur ɗinshi da zai hau ya fita.

Sai da yaje shagon ya zauna sannan ya ga kira da sabuwar lamba a wayar shi, ya ɗan shiga mamaki sai da ya sallami matasan da suka kawo masa wani Fayif sannan yabi kiran.

Cikin kamilalliyar muryarshi Yayi sallama, daga ɓarin Iyah ma ta Amsa cikin Nutsuwa.

"Dama naga kira ne ɗazu"

Ya faɗa kafin yayi shuru yana sauraron abin da za'a faɗa.
"Eh nice nasa a kira min mijin da bai kawo min kayan faɗar kishiya ba"
Yadda ta faɗi maganar yasa yayi murmushi mai sauti duk da bai fahimci abin da take nufi ba.
"Kakar Rabi ce

7 / 12