Author : Fatima Abdullahi Batul kamba Category : Romantic Hausa Novels
DSS , anbin cikeshi ya tabbatar musu danginmune suka turosu, tunda tun farko sun nuna babsa son aren kadija da Umar, shinefa wallahi mamee Dan adam abin tsoron ne."
Sun jimanta Al amarin kafin takai kallonta
Kallon Hajara tayi ita muma meya sameta?
Kasancewar tunda aka harbe doctor ta sume awajen
"Mamee firtatace kawai saikuma ɗan zazzaɓi "
Zazzabi?
Mamee ta maimaita tana kallon sa haryaso ruɗewa kodai wani nuna fikin yagaya mata komaine
"Eh Mamee"
Kyara zamansa yayi ya kalli mamee sosai yace
"Mamee dan Allah alfarma nake nema agunki"
Kallon mamaki tayi masa alfarma kuma Sani?
"Eh mamee"
"Kuma ina fatan samunta agunki dan Allah mamee "
Faɗi maganarka inajinka matuƙar baifi ƙarfinaba zanyi maka koma menene
"Mamee inason yau aɗaura min aure da Hajara dan Allah"
"Wannan ce alfarmar "?
"Inhar nina haifi Hajara sani nabaka aurenta kariƙeta amana kazamar mata uwa , uba, dangi, daduk wani abu data rasa "
"Kekuma takalli Hajara kiyi masa biyayya dan Allah kizamar masa mace ta gari abar alfahari ako ina "
Kasan batada dangin mahaifi kona mahai fiya dan haka kakiramin malam liman na gidannan yazo ayi muku jagora,
"Bansan dalilin ka nason auren Hajara ba kuma ayau bazan tambayekaba amma kasani kai marayane itama ahalin yanzu tazama marainiya kaine uba, yaya,Kani ,Kuma miji agareta, kaine bangonta ayanzu, kareeƙe alƙawari dan Allah sani karka canza da gayanda nasanka kaji "
"Namiki wannan alƙawarin insha Allah zakisameni mai cika alƙawari "
"Ya Sani dan Allah karka aureni baka sona Please indai ƙaddararda tasame nice yasa zaka aureni wallahi nayafe kuma nagode da kulawarka agaremu amma ni bazan aurekaba "
Hajara ce ke wannan maganae cikin kuka mai ban tausayi
Mamee ce ta kallesu cikin rashin fahimta, kantasamu damar magana Sani yarigata dacewa
"Ƙaddarar maraici ai bake kaɗai ce marai niyaba kawai inasonkine tunkafi zuwan wannan abin dan Allah karki sake cewa komai Hajara wallahi harcikin raina nake sonki..."
Ababban masallacin anguwar aka ɗaura auren Sani Muhammad Kebbi da amaryarsa hajara Abubakar Kamba akan sadaki naira dubu hamsin lakan ba ajalamba.
Bayan ɗaurin auren da kwana biyu sani yasamu kiran gaggawa daga London, hakan yasa yashirya yatafi yabar mamee da Hajara.
Tafiyar sa da kwana biyar Mai Hadi yaysin vci yar akofar gida tare da wasika,bansan me wasikar ta kunsaba Amma sun rike yarone ,suna kiranshi da Haroun
Aikin da sani yajeyi yasamu nasara hakan yasa suka riƙesa tunyana tunani nadan lokacine haeya gaji.
Nan yaƙira mamee yashaida mata garanar dawowa dan haka yaturo musu da komai su shirya zuwa jibi za'a kaisu Legos sushiga jiri suzo.
Mamee kan tace ita ba inda zataje matarsa dai nanan zuwa kasan cewar sun sanar masa da yaron hardashi zuwa
"Mamee Haroun fa dan Allah kibari suzo tare koya samu ingan taccen karatu ..."
Dakyar dai ta amince Haroun yabi hajara amma itakan ba inda zata..
Kamar yanda rayuwa ke gudu tana juyawa tamkar juyawar gudun agogo haka rayuwarsu tajuya Sani yasamu ƙarin girma a wajen aiki koda.
Yabiyawa mamee kujerar haji dashi kanshi .
Hakan baƙaramin daɗi yayiwa Mamee da Hajara ba yakoya mata sonshi da ƙaunarshi duk wani abu datake gudun faruwarsa akan rasa budurcinta datayi yakau domin tunranarda taje London sani ke bata wata riyar kulawa tamu samman wadda bata taɓa mafarkin samuba.. basu Wani jimaba yabiwawa mamee kujerar hajji
F🌹 A 🌹K BATOOOL KAMBA
✍️Alƙalami yafi takobi 🗡️
Typing 📲
https://chat.whatsapp.com/Gn6wOkxz4N6KBN3JbMkPiZ?mode=ems_copy_c
SON KI NE ƘADDARA TA
🌹Your love is My destiny 🌹
STORRY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI
BATOOL KAMBA
2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣
____________________________✍️
Sunje aikin haji sundawo lafiya sosai Mamee ta roƙawa Hajara samun ƴaƴa masu albarda , Dasamun ɗaukakar Sani.
Allah kuwa ya amshi addu'ar ta domin cikin ƙan ƙanin lokaci sani yazama masha hurin maikuɗi wanda duk faɗin Nigeria bawanda baisan daza mansaba...
Matsalar ɗayace haryau dasuke shekara uku da aure Hajara bata taɓa ko ɓatan wataba....
Tun abinna damunsu har suka fauwalawa Allah komai kullum Hajara nakukan rashin haihuwa, haka Sani zaita rarrashinta , yana kwantar mata da hankali,....
Yauma zaune take kan dining table ta tasa abinci agaba sai kuka take shigo warsa kenan yahangeta hakan ysa yanufeta cikin rarrashi yafara magana ...
"Please kidaina sawa ranki damuwa my hajar kinsan aure, arziƙi,mutuwa,haihuwa duk lokaci garesu kinmanta ko Mamee tadaɗe batasamu hai huwaba saidagabaya Allah yabata kisawa ranki salama mana uhmm ..."
Idonta ciketab da hawaye takalleshi harzatayi magana yagairgi zamata ka alamar tayi shiru nan yashiga ciyar daita dakansa harta ƙoshi yakalletà kokefa tawan, kinsanme? Yayi tambayar yana kallonta a'a kemafa inaganin wannan shekarar dake za'ayi aikin hajji.
Wani irin ihun murna tayi tareda ƙan ƙameshi tanazuba masa godiya, ɓata fuska yayi Kafin yace
"Mena godiya banason hakafa Please kidaina, komai nawa ai nakine "
Hakarayuwa tacigaba da gun gurawa akwana atashi bawuya awajen maiduka.
Barina leƙo muku ya Sani da Hajara suke
Zaune suke parlour yanayi mata matsar ƙafa , waro manyan idanuwana nayi waje ganin ta zaune kan two seater sani na durkushe agabanta yana mata tausa cikeda so dakuma ƙauna haɗida tsan tsar kulawa
Kallonta yayi cikeda so da ƙauna yace my hajara baki faɗamin wane suna ne za'a sanyawa baby ba.
Ɗago dakai tayi tasauke idanunta anasa kafin tace idan Mace Habibah nakeso
Dasauri yatari numfashinta dacewa "inkuwa namijine sunan baba doctor ko? "
"A'a marwan nakeso, cos inason sunan sosai." Murmushi yayi " kamar kimce wani abufa domin sunan yayi sweet sosaifa ririn sosai ɗinnan " yafadi yana kanne mata ido ɗaya.
" Yauwa kinsan zamuje Nigeria jibi cos mamee tadameni wainakawoki kihaihu gida to Allah ƙafata ƙafarki tare zamuje ko my hajar? " Ehmana my sani kosokake naje nakasa samun natsuwa, amma mufara bi ta kano muhuta ko yakagani?
"Waike menene haɗinki da kano?" "Kawai inason zuwane Please my Sani"
"Ok zamuje ammafa two days zamuyi saimuwuce kebbi "
"Bakomai saimubarshi gidan dady sadeeq koya kagani? "Eh hakanma za'ayi"
# Aminu kano International airport#
Tuda suka sauko hajara kecemasa yanema musu motar haya amma yaƙi datagaji dole taja bakinta tayi shiru
Wata dalleliyar motace tayi parking agabansu kafin hjara tace komai yabuɗemata gidan baya bamusu tàshige shima zagayawa yayi yashiga
Rigiyar lemo awani kata faren gida motar tayi parking kasancewar ba gateman agidan driver neyafito yaboɗe gate ɗin kana yakoma yashiga motar saida yayi parking kafin sufito mamaki takeyi
" wannan gidan waye kokasan wanine a kano ?" Murmushi yayi baice mata ƙalaba sanda suka ƙarasa tukun yace "kifara hutawa, kiwatsa ruwa, kici abinci zanmiki bayani yanakai nan yashiga wani ɗakin.
Saida tayi duk abinda yace tadawo perlou tazauna jim kaɗan shima yafito
"Tinkan tayi magana yace gidankine kenasiyama, kuma zakiga ƴan aiki zuwa gobe cos nasan kina son zama a kano bansan dalilinba shiyasa nasiya miki gida..
Cike da mamaki take kallonsa harta buɗe baki domin yimasa godiya yayi saurin katseta dacewa
" Banason godiya idan nayi miki abu tamkar nayiwa kainane so Please banaso .
Fashewa tayi da kuka "taya zanrama maka wannan alkairan dakake yimin"
Kuma fa sake katseta yayi nace miki banaso Please kidaina kinji kukan name nene uhumm
Rarrashinta yayi tukun suka fara fira cikin so daƙauna ...
*********Wayace a han nunta sai faman kiran layin sani takeya ama baiyi picking ba agala baice tamayar da akalar kiranta ga P.A ɗinsa shima saida tayi masa five miss call kafin yayi picking Assalamu alaikum yayi mata sallama, bata samu damar amsa masa sallamarba sabida gala baitarda tayi, saima ƙoƙarin magana take amma takasa buɗe bakinta, nishinda yaji tanayine yaɗansa yatsagaita, jinhar kusan minti Uku batayi maga naba saima salatinda yaji tanayi yaruɗashi "hello hello mada kina jina hello" dakyar tace Please dady help me zanmutu ina shi maigidan naka, dan Allah kuzo karna mutuuuu" dif yaji bataƙara maganaba ai awani irin ruɗe yafaɗa hool ɗin direct yanufi sani dake yin jawabi kasancewar shi baƙo aewan,
Tunda yahangi P.A ɗin sa afujajan yasan balafiya, tinkan yaƙaraso yanemi excuse .
Sir madance takirani tana nishi inajin balafiya saboda naji tanacewa natai maketa zata mu
Tinkan yaƙarasa yayi saurin barin waje direct motarsa yanufa securiti's ukune agefen motar suna hangosa suka buɗemasa yanashiga driver yaja suko sukashiga motarda kebayansu, dagudun gaske sukabar wajen, koda suka isagidan baijira angama parking ɗin motarba yaɓalle murfin yafito dagu yashiga gidan yana kwala mata kira tamkar maƙogaronsa zaiɓalle
"Hajar! Hajar !! Hajar!!! Kina inane? "
Dagudun gaske yake haura matattakalar benen cikin hatsamnacin tashin hankali yakebin jininda yagani da kallo rarraba idanuwansa yafarayi,canyahangota kwance sharkaf kamar gawa, dasauri yaƙarasa wajen baitsaya wani ɓata lokaciba yasa hannu ya cicciɓota yafito yana kwalawa P.A ɗinsa kira harya sakko yanufi compound ɗin gidan, securiti's naganinsa sukabuɗemasa gidan baya nasanyata shima yashiga a 360 sukabar gidan
Kyakkyawar hospital ce privet nan take akakarɓesu akawuce da'ita labour room.
dukyanda doctor's sukaso cetan rayuwarta abin yafaskara bayan tahaifi santalelen ɗanta kyakkawa jini ya ɓalle mata dasauri ɗaya daga cikin doctor's ɗin wani yafito yana neman Sani, jiki narawa sani yashiga ɗakin, ganin halinda takecikine yasa yafashe dawani matsanancin kuka kamar wani yaro ƙarami
Kallonsa takeyi agalabaice yace "Dan Allah kayafemin karoƙarmain mamee tayafemin nasan bazan rayuba kakulamin da abinda nahaifa .
Cikin kuka Mai hade da shash sheƙa yace "bazaki mutuba Please karkimanta namiki alƙawalin zanrayu dake nahar abada"
Murmushi tayi kafain tace "bazan rayuba naji hakan ajikina". fatana kasamawa abinda nahaifa uwa tagari wacece zata nashi tar biyyaaa
tanakainan tafarayin malmar shahada yanajin haka yashiga girgizamata kai hannunsa dake cikin natane yaji yasake alamar rai yayi halinsa sandarewa yayi kukanma yatsaya cak
Wata iriyar ƙara yasaki yana kiran doctor's gabaki ɗaya yafita hayyacin sa haƙuri doctor's ɗin suka shiga bashi P.A ne yayi ƙarfin halin kiran mamee yace tazo kano balafiya kasan cewar tasan suna kano nan tashiga kiran driver domin itama bata Kebbi tana kd wajen auren ƴar wata ƙawarta nan take sanar da ita P.A ɗin Sani yakira kuma dadukkan alamu balafiya
Nan hajiya nana tasanya driver yakaita kano , koda taisa har sunkoma gida sani natakuka kamar maxe duk yafice hayyacin sa tundaga bakin gare taga mutana sosai tacika da mamaki domin satinsu ɗaya ne a kano kodai hajara ce tahaihu tinda yaukusan kwana uku da wucewar edd ɗinta a compaund ɗin gidan motar tayi parking dasauri tafito tindaga shigarta parlour taga mutum an lulluɓe da fari ƙalle sosai tashiga firgici yayinda tahangi sani zaune gefen yana sharɓar kuka ga jinjiri riƙe ahannunsa shima sai callara ihu yake .....
Taku harkullum
F🌹 A🌹 K 🌹 BATOOL kamba
*SON KI NE ƘADDARA TA*
🌹Your love is my destiny 🌹
STORY & WRITING
BY
FATIMA ABDULLAHI
{Batool kamba}
_________________________________________________________________________________________________________✍️
25& 26
_________________________________________________________________________________________________________ Ƙarasawa tayi gaban gawar nanta durƙushe cikin matsa nancin tashin hankali take ƙoƙarin buɗe fuskar wasu siraran hawayene ke gangaro mata lokacinda tayi arbada Hajara matsayin gawa share hawayen tayi tanamai kwara rowa ƴar tata addu'o'i saida kamma yimata addu'a sanan wasu mutane suka shigo aka kamata akafita dan asallaceta.
Bayan ankaita makwancinta sundawo anan akashiga ƙarɓar gaisuwa gashi bawani jimawa sukayiba amma hajara tasami mutane sosai .
Ranar sadakar bakwai aranar akasawa yaro muna Marwan.
Bayan sadakar arba'in Sani yashirya don komawa London wajen aikinsa amma mamee tace saodai yaje shikaɗai bazata bashi jinjiriba yatafi uwa duniya dashi bayanda yaiya haka yakoma .
Bayan shekaru Uku
Haryau sani baisake yunƙurin wani aurenba yadai samu ya rarrashi mamee tabashi marwan suntafi London yasanyashi a school, shima Haroun yaji daɗin zuwan Marwan cos inhar sani yaje gun aiki sai magrib yake dawowa gida, shiko Haroun mutunne maison hayaniya, gashi dagashi sai nany dinda aka Samar masa
Marwan yarone marajin magana sosai kuma gashi da ɗanbabzan surutu hakan yasa suka ƙulle da Dan uwan nasaɗinnasa .
Mamee naƙoƙari wajen ganin sani yasake aure amma fur yace shi yagama aure .
Abin mamakin kosati ɗaya baiyi da maganarba marwan yafara takura masa ina momeensa .
Sometimes idan yadameshi saiyace tana Nigeria awane garinee dady a kano ko abuja hakazaita tambayarsa
Watarana sani bayanan shiko Haroun baidawo daga school ba marwan na dawowa nany ɗinsa tamai wanka yaci abinci, saida yabari takoma khiching yasuɗaɗa yafita securiti's sam basu lora dashiba harya fice daka gidan
Tashin hankali.
Lokacin da Haroun yadawo yake tambayar nany ɗin tasu ina marwan dan yaduba badroom ɗansa bayanan kuma yadoba toilet nanma baigan shiba
Wasa wasafa ba'aga Marwan ba nan akakira sani ana shaidamasa baimajira Haroun yaƙarasaba yakatse wayar yanufo gida yana kan hanyar ne doctor sadeeq yakirashi yana faɗamasa marwan na inane ," please doctor kodai yana hannunka? "
Kamarya daga tambayr yaro saikatuhu meni sani najin haka yajuya akaral matarsa zuwa gidan doctor sadeeq nan yatardda marwan zau ga kayan sweet nan agabansa saiwasa yake hankalinsa kwance
Doctor neyafito yana kallon yanda sani ke kallon Marwan .
"Dadyn boy yane" doctor sadeeq yatambayi sani cikin shaƙi yanci irin na abokai
Ƙaraso ciki mana kawani tsaya daga bakin ƙofa
Ƙarasa shiga cikin perloun yayi bakinsa ɗause da sallama
Follow this link to join my WhatApp group 👎
https://chat.whatsapp.com/CJPOk88Ckuw8zFUcXRbuoN
"Assalamu alaikum "
"Wa'alaikas salam "
Doctor sadeeq ya amsamasa
"Doctor please dan Allah a’ina kaga boy ? "
"Kabari kasha ruwamana doctor"
Saida yazauna shima doctor sadeeq yazauna kafin doctor yafara magana
"Doctor sani ksan meke damun boy harafito dakà gida? "
Girgiza kai sani yayi alamar A'a
Doctor sadeeq neyaɗaura dacew
Uhumm Sani wanna yaron nabuƙatar mahaifiya akusa dashi nany bakamar uwa bace musamman wadda baƴar Africa ba nahaɗuda boy anesa daginka kaɗa yazauna saikuka yake yana kiran momee, nayi rarrashinsa amma yaƙi shi adole akaishi Nigeria gun momeensa doctor kai kanka kana buƙatar mace akusa dakai , Hajara tarigada tatafi kuma bazata sake dawowaba , ldan da Allah bai kaini anguwar takuba harna boy mekake tunanin zaifaru?
Shiru yayi saican yace doctor banaƙi aure bane banason boy yatashi cikin tsan gwama kamar yanda muka tashi shiyasa kaga nahaƙura da Aure amma insha Allah zanyi tinda shi yanaso zaiyi masa momai danyasami farin ciki .
# Bayan wata shida
Doctor sani yashigo parlourn gidan hannunsa riƙeda na marwan, wata farar macece ke zaune a parlourn tinda tahangesu take zabga Murmushi .
Sam marwan bailura da idaba juyowarda zaiyi sukayi four eyes dagudun yaƙarasa yana faman zabga mur mushi, itama rungumeshi tayi tana cewa "oyoyo my boy" harkun dawo kyaɗamata kai yayi alamar eh shima sani ƙarasowa yayi nanacewa kinga boy ɗin ki koki kulani yayi maganar cike da zolaya ahaka rayuwa tacigaba da gun gurawa cikin farin ciki hajiya Ruƙayya matar sani wato mom ƴar asalin garin kano ce marainiyace ahannun kawunta tatashi dakawunta da baba doctor aminaine sosai sani yaje gaidashi lokacin dasuka je Nigeria shine yaganta anan dai suka daidaita harya aurota mamee tayi farin ciki sosai da sani yayi aure ,
Bayan shekara shida
itama mommy tashare shida zuwa bakwai haryau balabarin ciki bale haihuwar sutun suna damuwa har suka fwwa lawa Allah daga karshe suka yanke shawarar zuwa gidan marayu suyi addoting na ya mace tunda Allah ya bazu mazan har biyu Nigeria sukaxo gidan maratyu uka nemi Alfarma Kuma alhamdu lilah sun samu
Haka suka rika renon yayan su uku cikin so da kauna da kulawa da MUSAMMAN ..
# Dawowa labari💫💫
Cikin tashin hankali yake kaikawo , bayanda ba'a yida dady ba akan yzauna amma yakasa, kusan two hour sannan wani doctor yafito yana sharce gumin dake gishinsa .
Dasauri dady yanufesa yana
Tambayar ya jikin boy ɗin? Cikin kilawa doctor yace sir kabiyoni office yana.faɗin haka yayi gaba
Bayan sunshiga office ne doctor yace sir wai ita wannan yarinyar batarayene daharyau ankasa samun koda labarintane?
Yanzu duk bawannanba yajikin boy ɗin?
Coll down your mind Sir yasamu barci yanzuhaka amma maganar yarinyarfa?
"Bansaniba doctor nikaina abin yagirmi tuna nina boy bai iya sanya abu araiba tunda naɗauko yrinyae nan gidan marayu yaƙwallafa ransa akanta ada ina ɗaukar abin kamar wasa saida yatabbatarmin ita yakeson aura dafari, taƙiyarda bansan dalilin ta na amincewa dabayaba ashe danta haukatar min da yarone nakasa yarda guduwa tayi doctor duk irin nanda mukeyi mata sam bawandayazo mana dabayanin komai kama da ita abinda kebani mamaki doctor duk photunan tabakoɗaya abaya boy yace idan yazana photo ɗin fuskarta saiya goge to kwanaki yacemi wai kwaran kwalma photo yakoma , narasa samun solution nawannan ƙaddararren so
{sunan sabon book ɗina dazafito amma nakiɗine }
Nisawa dady yayi cikeda shakku yace sir koza'ayi malamarin nan duban tsanke , nisainake gani kamr da sihiri awannan lamarin ..
Nayi yunƙurin yin hakan amma nakasa narasa dalilin amma insha Allah zanyi iya ƙoƙarina ,,
# Maryam
Tunda suke tafiya amotar takasa sakin jikinta, sosai tsoro yakamata ganin sun ƙaraso wani ƙaya taccen hotel dama yariga dayayi boking ɗaki kaitsaye sukanufi ɗakin jikin ta ko'ina yayi sanyi gatsoronan yabayyana ƙarara atareda ita bayan sunshiga ɗakin yacemata tazauna shi zaishiga bathroom yawatsa ruwa yafito
Abin mamaki kusa 1 hour dashigarsa amma yaƙi fitowa gajiya tayida jira hakan yasa tanifi ledojinda yasa akayomusu odaring abinci harta kammala cin abincin baifitoba 1 hour tasake shuɗewa nufar bathroom ɗin tayi jikinta duk amace taɗan kwankwasa taji shiru kusan minyuna biyar tana bugun ƙofar bathroom ɗin amma