FAUZAN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY SARATU MUSA MAMAN UMAR.txt

Author :  Saratu Musa Maman Umar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 6

6K to 9K   out of 16K words

ya dan kwanta domin tasan halin mom dinta idan tace zatayi abu babu sai ta aikatashi, bata mantawa suna yara duk lokacin da Abbansu zaikara aure itace take lalata komai daga karshe matan suce basayi, dom haka yanzuma tasan komai zaizomata da saukine, sunjima suna tattaunawa sannan sukayi sallama hankalin Feezah ya kwanta domin ganin take tagama da wannan matsalar, wanka tayi tadauki motarta tabar gidan.





Wata irin soyayya Fauzaan yake nunawa Fadeela kamar yamaidata ciki saboda yadda yake jinta ajikinshi da zuciyarshi, bayasaon abinda zaisa tayi nesa dashi shiyasa itama take kokarin ganin tafarantamishi duk da irin yadda takejin kunya idan suna part din mom bata sakewa dashi sosai amma tana kokari sosai,
Bakaramin dadi mom take da irin kulawar da take ganin fadeela nayi da tilon dan taba domin bakaramin so take masaba, shiyasa take addu'ar Allah yasa kar fadeela tayi hali irin na Feezah duk da tayadda da yarinyar amma ba'a shaidar Dan yau.



Fauzaan ne zaune part din mom suna fira domin fadeela tayi bacci tana dakin mom, kallonshi mom tayi tace yakamata kafara hadawa Fadeela lefenta kafin ta koma gidanka tunda kaga bawasu kayane tazo dasuba tun wadanda kasiyomatane ranar da zakuzo, kuma tunda angama gyaran gidan bawani lokaci za'a daukaba inason kaje Dubai da ita kuyi siyayyar a can zaifi inyaso kuna dawowa sai kuwuce gidanku.

Murmuahi yayi yace badamuwa mom yadda kikace haka za'ayi saboda nikaina nafi son ina waje daya da matana, insha allahu jibi zamu tafi Dubai ahado lefen, abindama yasa bazamuje gobe ba saboda ita Fadeela batada Visa shiyasa , to babu komai Allah yayimuku albarka yabaku zuri'a dayyaiba ameen cewar Fauzaan, sannan karka manta da uwar gidanka kasan anayin kayan fadar kishiya don haka itam tanada hakki kahado mata nata lefen, yayi dariyarsa mai burgewa yace kai mom ai sai dukan yayi yawa cikin ahagwaba yayi maganar, itama dariya tayi tace yaro angayamaka auren mata biyu wasane shima dariyar yasakeyi yace inafa aigashi nagani sunjima suna fira sai da akayi kiran sallar azahar sannan yawuce masallaci.







Maman Umar CE.........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈




*FAUZAAN*

*NA*


*SARATU MUSA*(maman Umar)




*56-60*



"Wlh mom cikine da ita yanxu haka maganar danake miki daga hospital muke, cikin tsananin tashin hankali take maganar, kikwantarda hankalinki Feezah kinsan wannan bawani abun tashin hankali bane tunda kinadani, kuma kinsan sai inda karfina yakare indai akan matsalarkice, don haka inason kisanyawa ranki sunan wannan cikin matace.


Sai yanzu hankalina yakwanta my mom don Allah kiyi wani abu akai wlh jinake kamar inje inshaketa tamutu kowa yahuta, wlh bantabajin natsani wata halitta ba kamar wannan, kina haukane zakice kije kirufeta da duka aida kema kinsan makomar abinda zaki aikata bazaiyi kyauba.

Kawai kibar komai ahannuna kici gaba dayimusu biyayya har komai yazama namu, to mom nan sukayi sallama sannan suka ajiye wayar.



Zaune take saman bed dinta bayan tafito daga wanka tana tunanin irin son ta takeyiwa mijinta jinin jikinta, kamar ta hadiyeshi takeji aranta bakaramin kauda kai takeba aduk lokacin da zaije part din Feezah, hakuri kawai take tana danne kishin mijinta , duk da tare tagansu amma jitake tafi Feezah son shi, jintayi anrungumeta kamshin turarenshi tashaka batasan lokacin da talumshe idontaba, fuskarshi yamatsa dai2 tata hancinsu yana gugar juna yace mekike tunani natsuwata? Meye damuwarki wanda yasakaki acikin tunani mai zurfi har haka bayan kinsan nidin banason abinda zaishiga tsakaninki da farin cikinki, kigayamun mana kallonshi take kamar wani zai kwacemata shi, iska yahura mata cikin idonta yace wannan kallonfa kamar za'a rabamu, taji kunya sosai tasauke idonta kasa tana wasa da yatsun hannunta.



Ahankali tayi magana cikin natsuwa da sanyin muryarta, inason inje gida tun sanda kadaukoni bansake ganin yan gidanmuba.


Dariya yaiyi sosai sannan yace wannan shine yasa kike tunani? Shiru tayi domin dai tasan bashine ba amma dakunya tace masa tunaninshi take, can dabara tafadomata takaleshi tace kwana biyu ina tunanin mamana shiyasa, yanzunma murmushin yayi domin yagane kame 2 kawai take tunaninshine fal aranta wanda shikanshi bakaramin so yake mataba, har addu'ar yake Allah yabashi ikon yin adalci atsakanin su, kalonta yayi yana murmushi sannan yacemata zaki kiyiwa malam godeya ko? Tunda auren daya dauramiki kina kuka yayi dadi harda tsaraba zaki kaimasa, kukan shagwaba tafara tana dira kafafunta akasa nidai wlh a a tana sanya kanta acikin kirjinshi taboye.


kishirya insaukeki gida tund kinji sauki inyaso da dare inzo indaukoki, nan da nan tamike tsaye tamanta dabatun wata kunya domin gaskiya batayi tunanin zai amince da taje gida yanzuba kowata daya batayi da aureba, abinda batasaniba shine Fauzaan neman duk wani abinda zaisakata farin ciki yake domin itaba yasakamata duk da yasani bawai zai iya biyanta bane amma yanason shima yasanyata farin ciki kamar yadda take sanyashi.




'Boka aikinka yayi kyau sosai shiyasama kaga nazo yanxu domin ita yar tawa tagayamun jiya a can hospital suka kwana saboda suman da amaryar tayi, to amma sai wani sabon tashin hankali yatasomu gaba waton bullowar cikin da ita amaryar take dauke dashi wanda bakaramin barazana bane agaremu muddin mukayi sake tahaifi abinda yake cikinta,
Kallonta boka da'u yayi da kyau sannan yace bari muduba mugani, nan yafara sulkullenshi na tsafi can yadago idonshi dasukayi jajir yacemata gaskiya bakaramin tashin hankali bane taba wannan cikin domin naga taurarin wannan yaron dazata haifa masu tsananin haskene wanda baniba, duk duniya babu wani boka da zai 'iya yimuku aiki akansa yayi nasara, don haka ina maibaku shawara kurabuda wannan cikin tabbas sai anhaifeshi kuma zaitaka kasa intakaicemiki bayani wannan yaron dazata haifa shine zai zamo haske arayuwar mahaifansa kuma garkuwane agaresu, don haka nahaneku da taba wannan cikin idan kuma bakiji shawarar da nabakiba kina iyayin duk abinda kikeso amma nidai baburuwana.


Wata irin zufa mom tashare saboda tsabar tashin hankali datasami kanta aciki wanda atarihin rayuwarta bata taba saka abu agabantaba wanda bataci nasara akanshiba sai wannan, shiru kawai tayi ana sauraren tatsuniyar da boka yake gayamata wanda ita kanta batasan inda zata aza wannan soki burutsun ba balle kuma Feezah.

Nan dai tabarwajen boka tanufi wani qauye shima akwai wani tsohon boka dayayi yayin yimata aiki tun da jimawa wanda shi wannan bokan aikinshi kamar yankan wuka yake duk abinda kazomasa dashi bazaice a aba idanma sokake akashe maka mutum wannan karamin alhakine agurinsa domin bazaka bar wajenshiba mutumin zai mutu, amma shikuma sharadin aikinsa shine zaikwana da macce tsawon sati biyu idan bukatarta tabiya, idan kuma bukatarki tabiya baki dawoba asirinki zai tonu kowa yasan irin abinda kike aikatawa, sannan za'ayita firgitaki har sai kin mutu.

Abinda yasa tabar aiki agurinsa wancen lokacin shine,
Wata rana tazo wajenshi akan tanason akashe mata matar da mijinta zai aura domin tayi duk yadda takeyi domin tawargaza auren amma abu yaci tira shine tazo domin agama da matar kowa yahuta, bayan yagama jin bayaninta sai agayamata wannan ai maisaukine amma ga sharadinshi idan bukata tabiya zaiyi sati biyu yana amfani da ita idan har ta'amince shikenan aikinta zaitabbata yanxunnan, nan da nan ta amince da bukatar boka.

Bayan bukatar ta tabiya shima yace saura nashi biyan bukata, haka kuwa akayi kullum zatazo yayi jima'i da ita har lokacin da boka yadiba yayi wanda duk lokacin da boka yakwanta da ita bakaramin wahala takeba domin bakaramin mutum baneshi irin mazan nanne masu manyan kaya ga tsayi ga girma wanda inyana jima'i da kananan 'yan mata wash har suma sukeyi saboda azaba.
Wannan shine dalilin dayasa tabar aiki agurinsa , sai kuma yanxu zata koma wajensa.




Bakaramin murna Malam yayiba da yadda yaga Fadeela takomaba, alamun tana cikin kwanciyar hankali yaji dadin hakan sosai wanda har farin cikinshi sai da yakasa boyuwa, sunjima suma gaisawa da Fauzaan sannan sukayi sallama yawuce wanda tuni fadeela tashige cikin gidan.


Acen ma bakaramin mamakin canzawar tasukayiba wanda duk wanda yagamta yasan tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali, bayan sungaisa da mutanen gida bangarensu tanufa cike da dokin son ganin mamarta wadda kunya da kawaici yahanata fitowa tarbarta.

Dasalama tashiga zaune tasameta awajen dafa abinci tana aiki dafa abincin rana, bayan sungaisa akashiga firar yaushe gamo nan Fadeelah tafara mitar wai babu wanda yaje gidanta duk anmanta da ita tunda yanxu babu mai son ta, dariya mama Asmau tayi rin tasu ta manya tace to inbanda abinki fadeela taya dazuwanki gidan miji sai afara sintiri, yanxumma nayi mamaki danaji ana zancen zuwanki gidannan, sun jima suna fira irin ta da da mahaifi kallonta mama asmau tayi tayi murmushi domin tagane yar tata tanada shigar ciki don haka tace inafatan kina kulawa da kanki sosai domin kinga dai yanxu bake kadai bace, taji kunya sosai tace eh mama don takauda wannan zance tace mekike dafa mana ne mamana, haka tawuni cikin yan uwanta har dare sannan yazo daukanta suka wuce.






Maman Umar CE............
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈




*FAUZAAN*




*NA*

*SARATU MUSA*(maman Umar)




*46-50*




'Da sallama yashiga palon tana zaune taci kwalliya kamar mai shirin zuwa faty koda yake yasan Feezah game da kwalliya baya mamaki, shidai halintane kawai bayaso amma zaibimata yadda yakeso kodon azauna lafiya tunda yafahimci hakan atare da'ita.

Amsa masa sallamarshi tayi sannan tayimasa sannu da zuwa wanda ita kanta tamanta rabonta dayimasa sannu da zuwa, shima amamakance yake kallonta sannan yayi murmushi yauwa sannu da gida.
Wanka kawai yashiga abinda yakara bashi mamaki komai yasameshi yadda yakamata tahadamishi ruwan wanka da turaren wanka komai dai baisan sanda yayi dariyaba cikin ranshi yace yarinya wayagayamiki aida kitsaya har mutsadance inna biya sannan yasake wata dariyar sannan yafara wankanshi, bayan yafito zaune yasameta saman bed dinshi tafito masa da kayan shan iska tunda bafita zaiyiba, mai take shafamasa amma zuciyarta nacan tana yawo wato yadauka ko na hakura da cin amanar dayayimun shiyasa yawani saki jiki hummm zakazo ahannu wlh duk sai nafanshe wahata domin bazakaci bulus ba, katsemata tunani Fauzaan yayi dace inamaga kinyi shiru, murmushi tasakarmishi mai burgewa sannan tace kayi hakuri my baby nasan nasabamaka azamammu amma inason kabani dama akaro na biyu lallai zakayi alfahari da ni, duk maganar nan datakeyi cikin kuka takeyi domin takara nuna masa nadamarsa.


Rungumeta yayi ajikinshi domin bakamin tausayi tabashiba, kikwantarda hankalinki my dear na nidama banrikeki araiba saboda nasan daman wannan ba halinki bane shiyasa bansakashi arainaba, don haka kidaina kukan haka karkiyimun asarar hawayennan masu matukar tsada awajena, share mata hawayen yake yana kara lallashinta saboda tasaki ranta, tausayinta yakeji sosai domin baiyi tunanin zata kwantarda hankalinta hakaba lokacin da yayi aure amma gashi har yanxu bata yimasa maganar aurenshiba.



Zaunar da ita yayi sannan shima yazauna yafuskanceta domin yanason suyi magana mai mahimmamci, waton Feezah bakaramin mamaki kika baniba game da halin da kika nunamun wanda banyi tsammanin haka daga wajenkiba duba da irin rayuwar tashin hankalin da muka tsinci kammu aciki wanda haryanxu mamaki nakeyi, duk da ba abun mamaki bane amma kinshayar dani mamaki sosai narashin tankamin da bakiyiba alokacin da kikaga Fadeelah amatsayin kishiyarki sai ma wani tarin mamakin dakika bani shine lokacin da kika rungume fadeela afilin jirgi, sannan kikayi muna girki wanda nikaina rabona da inci girginki har namanta.




Wani shu'umin murmushi tayi wanda sai da Fauzaan yaji ajikinshi har jijiyarshi tana harbawa saboda tsabar shigarshi da murmushinta yayimasa, sannan tace haba mijina kai kanka kasan ina sonka wannancen lokacin ma danayimaka rashin kunya wlh sharrin shai danne, shiyasa nazauna nayiwa kaina fada, kamar yadda kace nice sanadin aurenka tabbas nidince domin dana karbi bukatarka daduk hakan bai faru daniba, nasan nice nacutar da kaina tomexaisa inkara tayar maka da hankali? Aikaga da banyiwa kaina adalciba, nagodewa Allah da ba mummunar hanya kafadaba dasai hakan yafi damuna bisa ga zargin kaina da laifin.


Matukar tausayi fauzaan yatausayamata domin yasan Feezah da zafin kishin tsiya amma tahakura, karki damu wannan kaddarace daga Allah koda bada laifin da kika aikatamunba in Allah yakaddaromun sai nayi kamar yadda kaddara tasa nayi ayanxu, don haka kikwantar da hankalinki komai yawuce, nidai fatana kuzauna lafia saboda shine cikar burina ayanxu banida wani farin ciki sama da naku don haka nake rokon kikara tausar zuciyarki duk danasan Fadeelah batada matsala amma sai kinyi hakuri da ita, babu komai ai munzama daya da'ita yanxu kuma insha allahu zakasameni mai biyayya agareka.



Washe gari Fadeelah takarbi girki yafita daga dakin Feezah, bayan yadawo kamar yadda yasaba part din Feezah yafara shiga sannan yawuce part din Fadeelah, bayan yayi wanka sunci abinci suna zaune suna kallon wani American film, film din bakaramin kyau yayimata shiyasa tamaida hankalinta akai gabadaya batason abinda yakatsemata kallon, jikawai tayi anjawota wanda tasan tunda yafara ba lallai yabarta tayi kallonba don haka takashe kallon inyaso dasafe sai taci gaba idan yafita aiki, meyasa kika kashe kallonki bayan naga gaba daya inmanta dani sai ta kallon kike murmushi tayi sannan tace aiduk mahimmancin kallon kafishi mahimmamanci agurina shiyasa nakashe domin inbaka lokacina yadda yakamata, kara jawota yayi jikinshi yana shafata, shiyasa yake masifar sonta domin duk wani abu nashi bata wasa dashi takan dauki al'amarinshi da mahimmanci sosai, wasa yakeyi da jikinta yana romance din jikinta sosai wanda ita kanta batafatan abinda zaishigo tsakaninsu dai2 irin wannan lokacin, bakinsu hade suna kissing din junansu kamar zasu tsinke harshen juna da tsotsa, hannuwansa ba'inda basa shiga ajikinta fitar da bakinsa yayi acikin nata yafa tsotsan boobs dinta masu shegen taushi wanda yana daya daga cikin abinda yake so ajikinta.

Ganin wajen bazai wadatar dasuba suka wuce bedroom dinta suna hawa gadon taji jikinta yakama rawa kamar tanajin sanyi shikuwa gogan baimasan halin datake cikiba tsabar nisan da yayi, wasa kawai yake da jikinta wanda dai2 wannan lokacin tayi nisa cikin wannan halin amma baimasa metakeyiba shifa atunaninshi takai lokacin da takeson yashigeta shiyasa jikinta yake bari haka.


Akwai matan da idan anawasa da jikinsu sai jikinsu yadauki rawa suna kugi kamar masu iska duk sufita hayyacinsu saboda yanayinsu bukatarsu mai karfice, wasu basa iya control din jin dadinsu alokacin romance.

Yayi minti asirin yana wasa da ita sannan yafara shirin sex da ita wanda haka yayi dai2 da daukewar nunfashinta, komai nata yatsaya cakkk shikanshi yalura da halin da ake ciki jijjigata yakeyi yana kiran sunanta amma ina batamasan anayiba, bakaramin tashi hankalinshi yayiba duk yarude yasara yadda zaiyi da ita sai faman jijjigarta yakeyi amma ko motsawa batayiba.







Maman Umar CE.......
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈



*FAUZAAN*


*NA*
*SARATU MUSA*( maman Umar)



*51-55*


"Duk yadda yadauki lamarin yawuce tunaninshi, jijjigarta yake da karfi amma ko motsi batayiba, can dubara kiran Feezah yafadomasa nan da nan yamayar mata rigarta yasaka jallabiyarshi yanufi part din feezah saboda shikam baisan yadda zaiyi da itaba, sauri2 gudu2 yashiga part din direct bedroom dinta yashiga kwance yasameta tana bacci duk da ba bacci takeyiba, domin kafin yazo tsaye take tana zullumin ko aikinsu yafara aiki tana cikin wannan tunanin sai taji anbude gambun palon anshigo shiyasa takoma takwanta azuwan bacci takeyi.



Cikin tsananin tashin hankali yake kiran sunanta da karfi zumbur tamike zaune tana zarar ido domin kiran bakaramin gigita tunaninta yayiba, lafia my dear meyafaru kakemun irin wannan kiran, ina Fadeelah, meyasameta , duk lokaci guda tajefamishi wadannan jerin tambayoyin, banda rawa babu abinda jikinshi yakeyi yamakasa yimata magana hannunta kawai yajawo suka baro part din sukayi part din Fadeelah.


Yadda yabarta haka yasameta kwance da hannu yanunawa Feezah ita bakinshi narawa maganarma takasa fitowa, cikin tsananin tashin hankali Feezah tayi kan Fadeelah tana jijjigata tana kuka kamar ranta zaifita, don Allah kitashi yar uwata kar kimutu kibarni wayyo ni nashiga ukku kuka takeyi bilhakki gwanin bantausayi, sai karantse batasan meyake faruwaba.
Can dai Fauzaan yayi karfin halin dafa Feezah tadago idanunta dasukayi jajir tsabar kukan da tasha abunka da farin mutum, cikin nuna jarumtakarsa yace da ita yakamata kibar kukan hakan kar kijawo wa kanki wani ciwon kema yanxu abinda za'ayi kawai mu dauketa muwuce hospital da ita nan da nan tashare hawayenta tace yauwa bari insanyo hijab dina dagudu tayi part dinta tana zuwa tafashe dawata mahaukaciyar dariya tanayiwa kanta kirari irin tayi nasara dinnan, daukar wayanta tayi takira mom dinta bugu biyu tadauka ko gaisawa basuyiba tashiga yiwa mom dinta bayanin abinda yake faruwa itama mom din bakaramin dadi tajiba aikinsu yayi kyau sosai don haka zata koma wajen boka domin afara aiki akan Fauzaan tunda wannan yayi kyau sosai.


Nan dai sukayi sallama sannan tasanya hijab dinta suka wuce hospital din da suke ganin doctor, dasauri aka shiga bata taimakon gaggawa sun jima akanta sannan tafarko cikin firgici allurar bacci aka yimata sannan aka canxa mata dakin hutu.


"Bata farkaba sai zuwa asba sannan tafarka cikin nutsuwarta lokacin Fauzaan yafita masallaci nan cikin harabar hospital din itakuma Feezah tana zaune kusa da gadon amma baccine yadauketa shiyasa koda Fadeelah tafarka batasaniba, sai da taji motsi sannan tafarka dasauri tanayima sannu kallonta Fadeelah tayi cikin mamakin sannun da tayimata domin ita dai tasan lafiyarta qalau tomeyasa takeyimata sannu?


Yunkurawa tayi domin tanason tashi tayi alwala saboda har hantayadda sallah taimakamata Feezah tayi tatashi sannan takaita toilet din dakin tafito zaune tayi tana jiranta, bayan tagama alwalar tafito tafara sallah.


Ahaka Fauzaan yasamesu zaune saman abin sallah, bakaramin dadi yajiba dayasamu nutsuwarsa tafarka harma tayi sallah alamun sauki yasamu kenan, bayan sungama ne suka gaidashi ya amsa tare da tablmbayar jikin Fadeelah murmushi kawai tayi domin yanzu tafahimci itace batada lafia saboda ganin gasu a cikin hospital naji sauki Allah yakara bada lafia ameen cewar Feezah.



Dasafe bayan doctor yashigo yaduba jikinta yacewa Fauzaan yasameshi office dinshi, haka kuwa akayi domin tare suka shiga office din bayan sun zauna doctor yakalleshi cikin fara'a yace azahirin gaskiya bamugano sanadin suman matarkaba amma abinciken damukayi mungano tana dauke da karamin ciki na sati biyu, don haka akiyaye kaga karamin cikine da ita gudun samun matsala.

Bakaramin murna Fauzaan yayiba jincewa yakusa zama daddy domin aduniya babu abinda Fauzaan yakeso sama da yara kodon shikadaine agurin iyayenshi ohooo, haka yafito daga office din bayan yakarbo takaddar sallama

3 / 6