Author : Saratu Musa Maman Umar Category : Romantic Hausa Novels
FAUZAAN yakira wayar mom yace duk abinda take yanxu tazo ga Feezah nan tadawo, haka yakira malam babansu fadeelah, duka kominti shabiyar basuyiba saigasu agidan.
Nan wannan akasake maimaita abunda yafaru mom kuka tasaka kamar ranta zaifita saboda jin yadda akaso rayuwar baiwar Allah tasalwanta amma dayake Allah ba'azzalumin sarki bane saiyajuyamusu mugun abunsu yakoma kansu.
Shikam malam baice komaiba tunda Allah yakaremishi yarsa, nan take FAUZAAN ya yanke igiyoyin aurensa da Feezah.
Hainal yaro mai hazaka zaune take yana sauraren malaminsu namakarantar islamiya yana koyardasu yadda. Yaron Allah yabashi hazaka sosai kodayaushe yabada aiki sai karatu.
Bayan hainal fadeelah tasake haifar yara biyu duka mata *Fairah* da *Feedah* yaran gwanin kyau dasu.
*Masha Allah anan nakawo karshen littafina mai FAUZAAN*.
*Kuskuren dayake ciki Allah ya yafemin*
*nagode*
Maman Umar CE.........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈
*FAUZAAN*
*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)
*86-90*
"Yana zuwa yagayawa mom halin da ake ciki game da ficewar Feezah dakuma yadda sukayi da mai gadi, ita kanta mom bakaramin tashi hankalinta yayiba, nan da nan tadauko wayarta domin takira Mom din Feezah tagayamata halin da ake ciki, wayar hartakare ringing ba'a daukaba har sau hudu tana kira amma ba'a daukaba, hankalinta kara tashi yayi tacewa Fauzaan yayi sauri yaje can gidansu yayimasu bayanin halin da ake ciki to mom amma kibari agayawa police tukunna, badamuwa Allah yabayyanata ameen cewar fauzaan.
Bayan yayi parking din motarsa shiga yayi cikin gidan yake tambayar mai gadi mom tana ciki kuwa? Domin awaje ya ajiye motarsa, a a Alhaji daman haka yake kiransa ai tun jiya datafita bata bata dawoba kuma batagayamin zatayi tafiyaba nima dai nayi tunanin ba lafia ba, to bakuyi waya bane ? A a bata kiraniba cewar mai gadi OK badamuwa idan tadawo kagayamata cewar taje gidan Mom dina tana son ganinta to to bamtsala insha Allah tana zuwa zangayamata.
Daganan police station yawuce domin yakai report din ko Allah zaisa aganta, yana zuwa yayimusu bayanin abinda yake faruwa suka rubuta statement tare dabashi tabbacin xa'aganta insha Allah, sannan yabaro wajen.
Can wani qauye mai suna dabo acikin karamar hukumar sokoto anan suka wayi gari da wani mummunan tashin hankali, garin yakasance kusa da rafine wasu matasa suna kamun kifi sukaga wata mahaukaciya tasheko dawani mugun gudu kamar zata tashi sama tana zuwa dai2 wadannan samarin taja burki tatsaya cekkk kamar gunki sai rabon ido take jajawur dasu kamar ansaka barkono, kalle2 takamayi can idonta yafada akan wadannan samarin dasuke kamun kifi nan da nan tayi cikinsu tana kokarin dangosu aikuwa damugun gudu suka dare kowa yayi takansa can tabi daya da gudu kamar walkiya saigashi ahannunta wata irin matsa da takaimasa saida idonshi sukafito waje saboda azaba kokari yake yakwaci kansa amma yakasa saboda bakaramin riko tayimasaba, inbanda dariya babu abinda take wanda dariyar kanta abintsorone , ganin haka 'yan uwansa suka ruga dagudu cikin gari domin asamo maza suzo suceceshi kar takasheshi, cen Allah yabashi sa'a yasami kufcewa yabi bayan abukansa da gudu suka shiga cikin gari itama dagudun tadafamusu baya sai tayi kusa da su sai surabu tabi wannan sai dayan yadawo kusa da ita wance yagudu haka sukayi tayi harsuka shigo cikin gari Mom din Feezah tana biye dasu dakyar suka samu suka bacewa ganinta.
Labarin Feezah anyi Neman duniya ba'a gantaba hargidajen rediyo anyi Neman amma ba'a gantaba dole akabarwa Allah domin lamarin yafi karfin tunaninsu babu Feezah babu mom dinta kuma duk lokaci daya,
Shidai malam haruna baice komaiba kuma baigayawa kowaba, shidai tunda 'yar shi takubuta ahikenan can sukarata daman idan zaka gina ramen mugunta kaginashi gajere.
Zaune take saman cinyarshi tana wasa da gaahin kirjinsa, takalleshi cikin alamun tausayawa tace bananata haryanzu babu wani labari game da maganar Aunty Feezah ne, yau tsawon wata biyu kenan babu wani labari hawaye tana zuba a idonta, sharemata hawayen yayi shikanshi dauriya kawai yakeyi amma bakamin damuwa yake cikiba game da lamarin, kinga natsuwata karki damu insha Allah za'asami labarisu banason kina saka damuwa aranki kinga edd dinki yatsaya karwata cutar dasameki don Allah kitausayamun kinji , shiru tayi tana share hawayen fuskarta tare dacemasa shikenan nadaina Allah yabayyanasu, ameen cewar fauzaan.
Yau fadeelah tatashi cikin yanayin rashin lafiya kuma gadukkan alamu nakuda ce, cikin bacci fauzaan yaji motsin ta yabude ido cen kasa yaganta tana dafe da mararta duk tahada wani uban gumi inbanda azaba babu abinda takeji, jitake kamar ranta zaifita, da sauri yasauko yanufi inda take cikin sauri yariketa duk yarude yarasa yadda zaiyi daukar wayanshi yayi yakira mom dasauri tashigo part dinsu tace maza yadauketa suwuce hospital haihuwace.
Bata dauki dogon lokaciba tahaifo yaronta jajir dashi kamar babansa, tubarkalla kato dashi, nan da nan akagyara uwar da danta suka dauko yaron suka mikawa Mom domin itace kusa da dakin, kallonshi mom tayi tace masha Allah wannan kamar antsaga kara da kai lokacin kana jariri mikamishi yaron tayi yayimasa huduba sannan yasake maidashi a hannun Mom yashige dakin da fadeelah take mom nabiye dashi, zaune take cikin goduwar Riga kamar baitace tahaihuba gwani banshawa kusa da ita yazauna yakamo hannunta yace sannun kinji nutsuwata Allah yasakamiki da alkhairi kinbani abinda duk duniya babu mai iya banishi nagode nagode, yanzu inayake miki ciwo, girgiza kanta tayi alamun babu inda yake mata ciwo sannan mom tamikamata yaron karbarshi tayi cikin jin nauyin mom tatauramishi ido kamarsu da Abbansa hartabace, nan dai doctor yashigo yakara dubata babu wata matsala yasallamesu su lokacin karfe shidda na safe.
Maman Umar CE.........