ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Love Story

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 37.3K words

ta tashi jiniya ta cika gidan mai nuni da Daddy ne ya dawo “ bari ma ga shi nan ya dawo bari na sauka na ji” ta faɗa tare da tashi ta sauko ƙasa.




Babu jimawa kuwa Daddyn ya shigo maƙarabansa na take masa baya,ya na ganin Granny ya sallame su duk suka fita daga falon.
“Barka da shiga dare Mama” ya faɗa da murmushi kan fuskar shi.
Ta ce “ yawwa! Ina ne ka tura Babana ya fita hankali tashe?”
“Babu inda na aike shi Mama,wani abu aka yi?”
“Maryama ta faɗa min ta ga ya fita cikin kakin soja”
“Ibraheem ne bai ji ko kaɗan Mama,ko na hana shi abu sai yayi” ya faɗa tare da nufar sashensa don ya matsu yayi tozali da abincin ruhinsa.Granny ta bisa da kallo kawai kafin ta je ɗauko wayarta,lambar Heemu ta kira amma ba ta shiga haka ma ta Ammy a doli ta koma can wurin Maryam.




“ Mi ya ce?” Maryam ta jefo mata tambaya, Granny ta ce “ lafiyarsa lau kin san halin Babana komai cikin sauri,abin da bai kai a ɗaga hankali ba shi wurinsa babba ne”
Maryam shiru ta yi kawai,ɗan salade ɗin da ta soma ci ta ture kafin ta tashi da gudu ta koma bedroom ta haye gado ta shiga raira kuka.




Hankalin Granny duk ya tashi ta rasa yadda za ta shawo kanta kawai sai ta zuba mata ido,har ƙarfe ɗaya na dare Maryam ba ta yi bacci ba ta na ta tsumayen zuwan Heemu amma shiru bai dawo ba.Zuwa wannan lokacin ƙarfin kukan ma ya ƙare sai hawaye kawai,farashin zazzaɓinta kuwa sai ƙara hauhawa yake.Bacci ne ɓarawo ya kwashe ta,yayin da Granny kuma ke kan sallaya ta na ta yin addu'o'in tsari wa jikanta don ita ma hankalin ta ba kwance ba.


DADDY


Yadda ya tarar da Zee cikin muguwar shigar nan,ya sallama kawai yau ba zai samu jam'in sallah ba.Abun nema ya samu sai wani shagwagwaɓe wa yake kamar wani ƙaramin yaro, Zee na basa abinci a baki bai san ta haɗa masa tarko iri-iri ba sai da suka shiga turaka Zee ta soma zayyano masa irin style ɗin da take so.
A matuƙar buƙace yake amma sam ba zai iya yin abin da take so ba,a shagwaɓe ta ce “ Baby ka na fa iyawa kawai tsoro kake ji ”
Ya ce “ ki duba shekaruna mana Baby,ki tausaya mini na yi aiki na gaji sosai”
Ran Zee yayi matuƙar ɓacewa don ita fa ta fi son style irin na turawa,dakyar ta danne zuciyarta ta basa haɗin kai amma fa sai ta nuna ta yi fushi ta barsa nan bedroom ta shige toilet ta na ta rusa kuka da ta gaji ta shige cikin bahon wanka a nan ta yi baccinta


#SOKOTO


Tsawon wannan wunin bisa kulawa ta Ammy ta yi shi,har ta shiga baccin dare ban bar gadinta ba.Wuraren biyu na dare na yi alwala sannan na kwanta kan doguwar kujerar da ke nan falo,kwanyata na buƙatar hutu amma sam na kasa bata shi shuɗaɗiyar rayuwarmu nake tuna wa ni da Abakar tun daga ranar da Daddy ya zo ya ɗauke ni.
Muna wasa ni da Abakar mun dawo daga makaranta,daidai ƙofar gidanmu Daddy na gani a tsaye ya na murmushi ya ce “na zo tafiya da kai IBRAHEEM zan tafi da kai babban birnin Abuja na mayar da kai SOLDIER MAN ”
Abakar na kalla yayin da shi kuma yayi saurin saka hannu ya riƙe ni gam alamun kar na barsa,kai na girgiza wa Daddy na ce “ a'a ni ba zan je na bar ƙanena ba” don haka nake kiransa zan girme masa da shekara biyu haka.
Daddy ya ɓata rai kafin ya je ya fizgo ni ya raba mu ni da abokina,ko Ammy ban yi wa sallama ba haka ya saka ni mota ya tafi da ni Abuja .Makarantar yara ya saka ni wacce tun nan ka zama soja sannan yayi tafiyarsa,duk wani horo da ake mini ina daurewa ne saboda yadda zuciyata ta dake su kuwa sosai suke jin daɗin haka ba su yi ƙasa da gwiwa ba suka sanar da Daddy a ranar da ya kawo min ziyara sai dai sun faɗa masa da matsala don ko bacci nake ina yawan kiran sunan Abakar.
Kimanin watana biyar kenan da zamana soja na koyi abubuwa da dama daga ciki akwai rashin tsoro,ido na tsura masa babu tsoro ko shakka na ce “ ina son Abakar shi ɗin ƙanena ne amma ka raba mu,muddin ka na son na ci gaba da zama a nan to shi ma ka kawo shi ”
“ Kar ka damu yarona in dai wannan ne babu matsala in dai iyayensa sun yarda” “na sani sam Umma ba za ta ƙin yarda ba Please Daddy ” sumba ya mini a goshi ya ce “ farin cikin ka shine nawa Heemu” jin haka yasa na saki raina na soma karɓar aikina yadda ya kamata ashe duk idonsu na kaina ko motsi na yi sai sun sanar wa Daddy.
A ranar da na cika shekara ɗaya ,a kuma wannan ranar aka kawo Abakar .Da murna muka rungume junanmu ya ce “ aboki duk ka yi baƙi ka ƙara tsayi”
Na sakar masa murmushi na ce “kai ma haka za ka koma” mun yi hira sosai kafin a ja shi izuwa sashen ƴan level ɗinsu.Duk yadda kuwa na so mu kasance tare doli aka raba mu don ba lokaci guda aka ɗauke mu ba,wuraren da muke haɗuwa su ne cin abinci,wanka da kuma training.
Abokan karatu waɗanda muke level guda tuni sun fara sabawa da Abakar,ko irin in muna hira in na yi fushi in su na son na sauka daga fushin sai su yi min hirar Abakar .Cikin soja muka ida wasarmu ta yarinta,haka cikin soja muka girma duk inda za mu je a tare muke zuwa Ammy da ummar Abakar sau ɗaya kawai suka taɓa kawo mana ziyara a shekaru biyar ɗin da muka kwashe a ciki.
Sai da muka mallaki hankalin kanmu ne sannan aka fara barin mu fita.


“Heemu ba ka kwanta ba?” muryar Ammy ta katse mini tunanina.Na ja ajiyar zuciya na ce “ Ammy har kin tashi wai?”
Hawayen fuskata ta goge kafin ta ce “ mine ne haka Heemu? Kamar wata mace shine kake hawaye?” na riƙo hannuwanta na ce “ na tuna abokina ne ”
“Ka yi masa addu'a ta fi wannan hawayen ”
Na ce “ Ammy Abakar ma ya na cikin waɗanda ba a samu gawarsu ba,sai nake ji a jikina tamkar zan iya ganinsa a kowanne lokaci ”


“Na dai fi son ka sa a ranka ya rasu,tun da akwai waɗanda boom ta tashi da su ƙila shi ma ya na ciki”


Na ja wani gwabron numfashi ina tunawa na ga agogon Abakar a ofishin Daddy.
“Ka je ka kwanta don gobe za ka yi sammako”
“Zuwa ina?” na yi saurin tambayarta.
“Ban son muso za ka koma ” daga haka ba ta ƙara cewa komai ba ta yi gaba.


Washegari kuwa tun da safe ta tirsasa mini doli na bar Sokoto zuwa Abuja,sai da na tsaya na sha mai sannan na ɗau hanya.Ko da na iso gida rana ta yi wantsar,ko da na shiga falo babu kowa direct kuma na wuce can sama.Ina tura ƙofar na soma jiyo shashekar ta,Granny ta juyo muka haɗa ido ta saki murmushi ta ce “ alhamdullah ga Babana ɗin nan ya dawo sai ki yi breakfast ɗin ai yanzu”
Maryam ta dubo ƙofa da sauri kuma ta tashi ta rugo kamar za ta faɗi ta yi wani tsalle ta riƙe ni gam.Na lumshe ido ina mai sa hannuwana na tallabo ta da kyau,wani siririn kuka ne take rerawa wanda yake samun wuri a zuciyata.
” Yi shiru mana ai gani na dawo” na faɗa ina mai bubuga bayanta,Granny ta tashi ta fice ni kuwa a hankali na soma takawa da Maryam tallabe a ƙirjina har na isa bedroom.Kan gado na kwantar da mu har yanzu kuma ta ƙi sakinazafin jikinta kuma na ratsa ni.Na ja ajiyar zuciya tare da ɗan jaye ta muna kallon juna da idonta da suka yi ja tsabar kuka,“ mine ne?”
“Tun jiya ka tafi ba ka dawo ba na ji tsoro sosai kar kai ma....” ban bari ta ida furicin nan ba da na san ba mai daɗi ba ne kawai na ɗora bakina kan nata.Shiru ta yi sai yanayin sheɗarta da ya sauya,sama da minti biyar ina kissing nata kafin na janye na miƙe tsaye kan ƙafafuna.Daga inda take kwance take kallona ta na murmushi,ni kuwa kayan jikina na rage na shiga toilet ina wanka ina tunanin sabon al'amarin nan da ke faruwa da ni.Tun da nake ban taɓa yin budurwa ba amma mugun son kasancewa nake yi da Maryam wacce ba soyayya muka yi ba ballantana na ce zumuɗin bege ne.Towel na jawo na ɗaura sannan na fito,inda take kwance na duba sai na ga har yanzu ta na nan a yadda na bar ta.Na taka zuwa bed ɗin,gefen wuyanta na taɓa na ji shi rau na kalle ta cikin ido da sauri ta lumshe su.Ƙwan lantarkin na kashe na haura gadon ina mai jawo ta jikina,ban wani sha wuya ba na raba ta da doguwar rigar jikinta na barta daga ita sai pant.
“ Kullum doguwar riga kamar aljana” na faɗa cikin kunnenta ina mai gyara mata kwanciya kan ƙirjina tare da jawo mana blanket.
“Na fi sonta ” ta faɗa a shagwaɓe,“ tun yaushe kike jin zazzaɓin nan?”
“Yau ne kawai” ta bani amsa ta na mai ɗan ja da baya ni kuma sam hakan bai yi mini ba sosai na ji daɗin yadda ƙirjinmu ya samu contact.
Ban ce komai ba sai rumfa da na yi mata da ƙirjina,na kai hannuna can ƙasan bayanta na tallabo.“ Ban so kar ka yi min” ta faɗa da sauri ta na mai kai hannunta kan haɓata,ta ɗan hasken da ya rage nake kallon fuskarta na ce “ mi a ba ki so?” shiru ta yi ba ta bani amsa ba ni kuma na janye hannun nata na cusa kaina gefen wuyanta,cikin muryar raɗa na ce mata “ wannan zafin da jikinki yayi nake son na rage miki babu abin da zan yi miki ki saki jikin ki” wata irin wawiyar runguma ta yi mini wacce ta kusa sa ƙusoshin kaina kwance har sai da na fitar da wani numfashi ban shirya ba.Sannu a hankali zafin jikin nata ke ratsa ni ya na saukar min da wata kasala,don jan magana Maryam bayana take shafawa kuma ta ce ba ta son na yi mata komai sam na kasa juriya na lalubo bakinta duk da kuwa ƙoƙarin hana wa da take sai da na ci gabala kanta ban barta ba sai da na samu ƴar nutsuwa, toilet na koma na tsabtace jikina sannan na fito.




Ina kunna lantarki na hange ta zaune daram ko kayan ba ta mayar ba,na kawar da kai gefe ina mai cewa “in kin jin ƙwarin jikin ki za mu je shopping ”
“Na fa warke,garas nake jin kaina dama rashin ka ne” da sauri na juya jin furucinta ta wani sa hannu ta na rufe ƙirji.Na taɓe baki ina zancen zuci ‘ Allah na tuba in ba dai don shi namiji da jaraba ba mi wancan abubuwan za su mini’ ina ganinta ta wutsiyar ido ta ruga ta shiga toilet ko kafin ta fito na shirya na wuce falonmu.
Abinci na gani kan table na haɗawa kaina tea na soma sha,zuwa can ta fito cikin wata pink ɗin doguwar riga.
“Zo ki zuba mana abinci” na faɗa ina danna wayata ina karanta saƙonni da suka shigo min,plate ta ɗauka ta zuba har za ta zauna na yi saurin jawo ta na ɗora kan cinya sai kuma na tuna na taɓa ganin Daddy ya yi wa amaryasa.Maryam ta faɗo jikina ta na jan gemuna da yake da yawa sosai,“ ina son wanga abun” ta faɗa kamar wata ƴar yarinya.
Na ce “ bai da suna ne?”
“ Ya nada” ta bani amsa ta na mai ci gaba da wasa da shi ni kuma hakan ba ƙaramin daɗi yake mini ba,kawai sai na zuba mata ido.Ta saka dukkan tafukanta ta na shafar sajena ta ce “ amma wannan ya fi kyau”
Na ja hancinta ina mai ci gaba da kallonta kafin na ce “ a bani abinci yunwa nake ji”
Ta yi dariya kafin mu soma ci a tare.






Littafin kuɗi ne 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[01/10 à 12:03] MRS SADAUKI 💫: *IBRAHEEM*
```soldier man```


© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*


#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓




11-12




Assalamu alaikum,ina ma'abotan karatun litattafan Hausa? To kakarku ta yanke saƙa.Mrs Sadauki ta yi muku bajin kolin littatanta duka tun daga na tsafi,soyayya za ta yi muku ragi mai rahusa,kai hatta ma waɗannan da take yi MAITAR IDO da shi kansa SOLDIER MAN za ta yi discount. Ga duk wanda yake ra'ayi ƙofa a buɗe take za ku iya tuntuɓarta kai tsaye ta WhatsApp+22795045822 Allah ya bada ikon biya Ameennnn!!!!!




Bayan mun gama cin abinci na ɗauki ATM ɗina,Maryam ta saka hijabi sannan muka sauko ƙasa ina mai rungume da ita.
Daddy na gani zaune shi ɗaya yayi uban tagumi kamar ba shi ne mai matsayi da ɗagawar nan ba.Cikin kunne na yi mata raɗa “ za mu je ki gaida mahaifina” sai ta jinjina min kai .
Tun kafin mu ida isa na yi gyaran murya,ya kuwa dube mu ni na fara gaishe shi kafin Maryam ta duƙa har ƙasa ta ce “ ina kwana Daddy ”
Sai da ya sake haɗe rai kafin ya amsa mata da “ lafiya lau” sai kuma ya kawar da kai gefe.Na sa hannu na ɗago ta ina mai janta jikina na riƙe ta gam,cikin Yaren mu na soja na ce “ ita ɗin ƙanwata ce kamar wancan ɗin dai ina sonta fiye da kalmar so saboda wancan ɗin dai sannan in sha Allah da sannu zan samo shi”
Wani irin firgici na gani a fuskar Daddy a lokacin da na kai ƙarshen maganata,na sakar masa murmushi kafin na ja Maryam mu fice ko Granny ba mu je mun gani ba.




Da kaina na buɗe mata mota ta shiga sannan na zagaya na hau mazaunin direba,tun kafin na fara tuƙi na kira Ammy na saka wayar a hand free na ce “ Ammy ce in ta ɗauka ki gaishe ta kuma ki yi mata ya jiki” ko bakina ban ida rufe wa ba Ammyn ta ɗauka.


Ina kallonta ta turo baki maimakon ta yi abin da na faɗa mata sai ta yi wanda take so,“ shine kika tafi kika bar ni,kuma...kuma ko sallama ba mu yi ba ”


Driving na fara aka buɗe min get, Ammy ta yi murmushi mai sauti ta ce “ Maryam Sarkin rigima, lokacin na bar gidan ai na san kin koma bacci.Faɗa mini ai dai bai matsa miki ko?”
Sai da ta dube ni kafin ta ce “ da dai sauƙi Ammy amma ...to shi kenan dai..” sai ta yi shiru.Da sauri na ɗauki wayar na kara a kunne ina cewa “ ina kwana Ammy ya ƙarfin jikin?”
“Alhamdullah Heemu ! Mi kake yi wa ƴar amanata?”
“Kin yarda zan iya yin wani abu da zai cutar da ƙanwarmu?”
“Na sani Heemu amma ita gani take kamar takura ce duk da na san ba zai wuce akan tashi sallar asubah ba don Maryama akwai nauyin bacci sai ka yi da gaske”


“Ammy ina driving in na sauka zan sake kiran ki”


“To yarona Allah ya tsare ku ya kai ku lafiya ya kuma maida ku gida lafiya”


“Amen Ammy ki kula da kan ki kuma ki sha maganin ki” na faɗa tare da kashe kiran.
Na ɗan haɗe rai na ce “ wato da na ce ki gaishe ta shine kika ƙi? Sannan kuma mine ne kike shirin faɗa mata?”


Ta ɓoye fuskarta tsakanin cinyoyinta ta na dariya ta ce “ laaa babu komai fa ya za a yi na sanar da ita abin da muke yi”


Wani haushi na ji ya kama ni,wato ɗan kiss ɗin da nake yi mata ya zama abin faɗa da alamu ma kamar zai kankaro mini raini tsakanina da ita.Wani haushin kaina na soma ji har muka isa ban ƙara ce mata komai ba,ina gama parking na fita ina jiran ta fito amma ta ƙi.Na zagaya na buɗe na ce “ a nan za ki zauna?”
Ta turo baki ta na mai cewa “ to ai kai ne ba ka yi saurin buɗe wa ba”
“Fito ni na rufe motata” kamar za ta yi kuka ta fito,na rufe sannan na kama hannunta.Muna shiga ciki ta soma zillewa wai na sake ta mutane na kallonmu,wani takaicin ya ƙara rufe ni na ce “ ke nan ba ƙauyen ku ba ne na Sokoto kowa harakar gabansa yake,ki nutsu ki zaɓi abin da kike so in kuma kika cika ni zan mayar da ke gida” sai a yanzu ta nutsu jin zan fasa yi mata sayayyar.




Muna shiga ɓangaren kayan mata ta tuntsire da dariya irin sosai ɗin nan har sai da ta jawo hankalin mutane gare mu,kunya da takaici suka luluɓe ni .Da hannu ta yi mini nuni da wani sket irin na ƴan gayu ta ce “ wa kuma ya kawo sket ɗin uwarsa nan terere” hannunta da ke cikin nawa na yi wa wata muguwar matsa a doli ta nutsu.
Ta na kumbure-kumbure na soma zaɓar mata kayan muna jefawa cikin kwando,dogayen ruguna kawai ta zaɓarwa kanta kayan bacci da ta ga ina ɗaukar mata ta kira sunana kamar abun ƙwarai “ Ya Heemu ?” na ce “ uhum ”
“Su kuma kayan ƴan iskan nan waye zai sa su?”
“Wane ƴan iska kuma?”
“ To irin na turawa ne fa,ni dai gaskiya ban so” ban kula ta ba har na ɗauki waɗanda na ga sun yi min muka wuce wani ɓangare kuma.Da sauri ta yi gaba ta soma jidar pant da bra,kallonta kawai nake yi kafin na tambayi kaina ‘ ko mi za ta yi da bra ’ kamar kuwa ta shiga tunanin nawa sai cewa ta yi “ to ai za su ƙara girma ba haka za su zauna ba ka ga kuwa ina da buƙatar abun tallabe su” wacce ke riƙe mana kwandon ta ce “ ki na da gaskiya Madam ko ma a

11 / 13