ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Love Story

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 37.3K words

haka za ki iya sa abarki ki yi kwalliya”


Mugun kallo na watsa mata ina cewa “ mine ne to na kallon ƙirjinta?”
Ta yi ƴar dariya ta ce “ haba kai kuwa mi zan kalla a nan Les nake ai wannan ta min ƙanƙa...” ba ta kai ga rufe bakinta ba na wanka mata mari da mugun sauri ta bar wurin dafe da kumci.
Na karɓe bra ɗin hannun Maryam na mayar ta sake ɗauko su ta rungume ta na cewa “ Allah ina so” ban ƙara cewa komai ba na yi gaba,ta ce “ kwandon kayan fa?”
“Sai ki ɗauki abin ki” na bata amsa,ta biyo bayana ɗauke da ƙaton kwandon yadda take nishi yasa na karɓa.
Sai da na saya mata takalmi da jaka sannan muka zo wurin biya,ana ta lissafin kaya bayan ya gama ya ce “ banda kayan kwalliya?”
“ Ba ta iya ba”na basa amsa ina miƙa masa ATM ,mai Mall ɗin na tsaye Dattijo ne sosai ya ce “ a'a yarona a saya mata sai ta koya ko ƴata?”
Maryam ta ce “ eh Daddy ina so” ta wutsiyar ido na dube ta kafin na ce “in akwai wacce za ku wakilta ta zaɓar mata a kira ta sai su tafi tare”
Ya ce “ mace ce mai kula da ɓangaren ku zo na kai ku” a tare muka je,da kanta ta zaɓarwa Maryam kalolin hodar da za su hau da fuskarta sannan sauran abubuwan shafe-shafe.
Da muka biya aka kawo mana har mota ,ina tsaka da tuƙi ta ce “ Allah kifi nake so”
“Sai ki bari har mu je gida” na bata amsa.
“ Babu inda ake kamo shi?” ban bata amsa ba har muka isa gida.
Ɗakin Granny muka yi tsinke ta soma baza surutu ni har mamakinta nake,wayata ce ta yi girrr alamun shigowar saƙo na ciro ta daga aljihu na duba ina gani da sauri na miƙe na fito.
Can sama na haura ina mai kiran Shamssudeen,ko damar magana ban basa ba na ce “ ka ce mi? Ya tsere? Ta yaya kenan?”
“Wallahi kowa mamaki yake yadda ya tsere don wuri mai tsaro muka ajiye shi amma muna tashi yau babu shi”
Na dafe kai na ce “ ku duk ku na aikin mi har ya tsere? Dagaci ɗan ta'adda ne mai laifi ban ma san dalilin da yasa ba ku harbe shi ba tun ranar da kuka kama shi ba” na faɗa ina jin allurar sojana na motsawa.


Daga can Shamssudeen ya ce “ Ibraheemu kamar dai ba ka san yadda mulkin ƙasar nan yake tafiya ba? Kawai ni na fi tunanin daga cikinmu ne wani ya fitar da shi amma babu wai zancen ya gudu”
Cike da masifa na ce “ ai ga irin ta nan shi yasa kullum ƙasarmu ke dawowa baya inda ya kamata a ɗauki mataki kai tsaye wai sai a tsaya sai an bayar da izini”


“Ni fa yanzu tsorona guda,kar a jingina laifin a kanmu ”


Na furzar da huci na ce “ yanzu ku na ina?”
“Muna hanyar Abuja cikin dare muna kawowa in sha Allah ”
“ Ya kamata mu yi wani abu ,doli mu yi fito na fito da jadawalin dokar ƙasar ya zama doli a canza su sam ba su yi ba”


“Allah dai ya kama mana,duk rashin tsaron da ake cewa babu laifin ya na wurin manya amma sai a dinga ganin laifinmu.Da zarar an kama ɗan ta'adda maimakon ayi yadda kace ɗin a kashe shi sai a tsaya ajiyar shi,ƙarshe sai ka ji an ce ya gudu”




“Shamssudeen Allah kawo ku lafiya sai dai kun zo,bari na je can compagnie na ji ya ake ciki” nan muka yi sallama sai da na sake yin wanka sannan na shirya cikin kakin soja ko hulla ban ɗora ba na sauko ƙasa.
Da sallama na shiga ɗakin Granny,ita kaɗai ce falon ta na ganina ta kafe ni da ido ko ƙyaftawa ba ta yi kafin ta tashi tsaye ta ce “ Ya Heemu ...” sai kuma ta zo ta rungume ni.




Kanta na dafa na ce “ zan je na dawo ne,ba zan jima ba” ta ɗago muna kallon juna ta ce “ ko mu tafi tare ”
Na girgiza kai “ a'a wurin aiki zan je,ina Granny?”
“ Ta shiga toilet ” ta bani amsa,na ɗan rage tsayi har zan sumbace ta kuma sai na tuna na yi alƙawarin ban sake yi kar ta raina ni.
“ Sai na dawo” na faɗa tare da janye ta daga jikina,ba tace komai ba sai ido da ta bi ni da su.




Motata na shiga na yi mata key na isa compagnie,ina gama parking na nufi ofishin Daddy yau ma sun so su hana ni amma yadda raina ke a ɓacen nan yasa ba su yi doguwar jayayya ba suka bar ni.
Ina shiga duk suka juyo su na kallona,DADDY ne da Joy da alamu wani abu mai muhimmanci suke tattaunawa.




“ Wa ya baka izinin shigowa?” Daddy ya tambaye ni,idona ya sauka kan screen ɗin system ɗin gabansa da sauri ya rufe ta na ƙara haɗe rai.
Joy na kalla na ce “ ina trollyna da ka shiga ɗakina ka ɗauko?” bai bani amsa ba sai cewa Daddy ma da yayi “ zuwa an jima zan sake dawowa na yi ma bayani” ya na shirin tafiya na damƙo rigarsa,a zafafe ya ture ni ya na cewa “ kar ka sake gigin kai hannu jikina ” na kuwa shaƙe shi ina cewa “ kai ɗin uban wane ne? Ka shiga ɗakina ka ɗauko kayana kuma na kasa magana?” shi ma tawa kwalar ya ci , Daddy sai faman cewa yake “ Heemu ka sake shi!” ni kuma na ƙi na buga wa Joy kai a fuska a nan take jini ya soma yi masa zuba ,ban damu ba na ci gaba da dukansa shi ma ya na ramawa.


Daddy ya shiga tsakaninmu ya na mai ɗauke ni da wani gigitacen mari,har sai da na ji kunnena yayi wani dummm.Ya danna wani abu sai ga jami'an da ke basa tsaro sun shigo,da hannu ya masu nuni da ni ya ce “ ku kai mini shi celle ” da mamaki nake kallon Daddy sai na ga ya na bai wa Joy haƙuri da rarrashinsa sai kace shi ne babba gare shi.




Muna fitowa waje na ƙwace daga riƙon da suka yi min na ce “ tun da hauka kuke sai ku kai ni can maƙargama” duk su na ƙasa gare ni doli suka bar ni.
Wani sashe na nufa inda muke bincike da kuma samun labaran da ƙasa ke ciki dama waɗanda aka gabata.Hotunan waɗan suka ƙone wurin yaƙi na nemo da duk waɗanda ba a ma san inda suke ba,sosai na yi mamaki ganin an canza sunan Abakar daga liste ɗin waɗanda ba a gani ba zuwa na wanda suka ƙone.Sam zuciyata ta ƙi yarda da hakan,don kuwa liste ɗin ta ƙwarai ta na ofishin Daddy kuma ita na soma ganin kafin wannan.
“ Tabbas a yau zan soma bincike ” na faɗa ina mai miƙewa na nufi ɓangaren asibitinmu, waɗanda suka ji ciwo a yayin fafatawar na kai wa ziyara.Sosai suka ji daɗin haka kuwa,su na samun kulawa mai kyau dakyar na samu wanda suka yi group guda da Abakar tun da in za a yi yaƙi group-group ake yi duk sai a rarabu to a cikin group ɗin su Abakar tun kafin a tafi na kalle su tsab kuma duk cikinsu wannan ɗin kawai yayi rai.
Kusa da kansa na zauna na ce “Ya jikin naka?”
“Da sauƙi alhamdullah!” ya bani amsa,cike da jimami na ce “ haka Allah ya rubuta ,ka ƙara haƙuri in sha Allah mune da nasara”
Ya ce “ Allah nuna mana ranar da ƙasarmu za ta fita daga cin hanci da rashawa duk da kuwa abu ne mai wahala”
A cikin idonsa ina hango wasu abubuwa,ƙunci,tauye haƙi akan gaskiya da kuma fargaba.“Haka ne ai ga shi na rasa abokin...” ban rufe baki ba na ga Joy shi da wasu sojojin a tsaye fuska a murtuƙe.


Ankwa suka sa mini kamar wani mai laifi,furgincin idon wanda nake hirar da shi ne na ga ya ƙaru suka tisa ƙeya ta zuwa gaba.Direct ofishin Daddy suka kai ni,sai a lokacin suka cire min ankwa ɗin suka fita suka bar ni da mahaifina.




Ya ja ajiyar zuciya ya ce “ Heemu ban san mi kake so da ni ba? Mi ya kai ka ɗakin bincike?”
Da mamaki na dube shi na ce “ haramun ne soja ya shiga ya bincika ya ga halin da ƙasarsa ke ciki?”
“ A'a ba haramun ba ne abu ne ma mai kyau amma ai ya kamata ka sanar da ni kafin ka tafi”


“Yi haƙuri shugaba ban san an canza dokar cewa in soja zai shiga ɗakin bincike sai ya nemi izinin ka ba amma zan kiyaye gaba yalaɓai” na faɗi haka ne don nuna wa Daddy nan kan aiki muke ba wai a gida ba.


Ya ja ajiyar zuciya kafin ya jefo min wata tambayar kuma “ to mi ya kai ka ɗakin maras lafiya?”
Na yi wani murmushi na ce “ shi ma an saka dokar shiga ne?” bai ce komai ba,sai aljihun table ɗinsa da ya buɗe ya miƙo min wata takarda ya ce “ Abakar na cikin waɗanda suka ƙone ko gawarsu ma ba a iya shaida wa ba,sai dai mun tsinci wannan agogon mai ɗauke da sunansa”


Takardar na karɓa,wacce tabbas ba ita ba ce na fara gani ba an canza ta yanzu kuma ya kawo min wata sabuwa tare da miƙo min agogon Abakar.Yi na yi kamar yanzu ne na gansu,na karɓa hannuna na rawa na kai ƙarfen agogon na ɗora daidai saitin zuciya na lumshe ido ina cewa “ Allah karɓi shahadarka abokina haƙiƙa na yi babban rashi” ta wutsiyar ido nake kallon Daddy fuskarsa sharrr babu fargabar nan da na tarar da shi da ita,har da sauke wani numfashi yayi kafin ya ce “ Amen! Allah nuna mini ka aje bindiga lafiya” ban ce komai ba na ajiye takardar kafin kuma na saka ƙarfen agogon cikin aljihu kuma sam Daddy bai yi ƙoƙarin hana ni ba har na yi masa sallama na fito.


Da na shiga motata kasa tuƙa wa na yi,tunani birjit ne ya soma ziyartar ƙwalwata,‘ mine ne dalilin Daddy na son mayar da Abakar cikin waɗanda suka mutu? Don na fitar da shi a rai ko me? ’ rasa amsa na yi kawai na daure na soma driving......








Book ɗin kuɗi ne 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[01/10 à 12:03] MRS SADAUKI 💫: *IBRAHEEM*
```soldier man```


© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*


#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a gare ka Yayana AbduRashid😓




Last free page
13-14




Raina duk a jagule na isa gida,benen na soma hawa ina haɗe bibbiyu har na kai sashena.Ina buɗe falon wani sihirtacen ƙamshi ya bugi hancina,ban gama shanye romonsa ba idona yayi tozali da Maryam cikin wasu arnan kaya riga da wando su yin bala'in yi mata kyau.
Duk sun matse ta tam ga su sharashara,ta rugo da guɗi ta yi tsalle ta kamo wuyana ta na yin wani murmushi mai tabbatar da tsantsar farin cikinta .Neman ƙuncina na yi na rasa kawai na rungume ta,cikin surutun nan nata ta ce “ albishirin ka na iya hawan bene ni ɗaya,yau Granny ta ce ba za ta mini rakiya ba ni kuma na ji haushi na hau da kaina.Ka ga kuma kayan da ka saya min irin na nasaru sun yi kyau? Na zama kamar ƴar tsanar roba”




Murmushi kawai nake ina kallonta,ta turo baki ta ce “ shine ka yi shiru? Ko ba su yi min kyau ba na cire dama ni sun dame ni ”
“Kin yi matuƙar kyau preety” na faɗa ina mai takawa da ita maƙale a ƙorjina har na isa ga kunera na zauna.Ta tuntsire da dariya ta ce “ ka ga ƙatuwa da ni amma na yi ɗare-ɗare kan cinyarka,ina da nauyi?” ta tambaye ni tare da ɗora dukkan tafukan hannuwanta kan fuskata ta na shafar sajena yayin da kuma ta tsurawa gemuna ido.
“Mary?” ta ɗago muka haɗa ido,a hankali na matsa fuskata na ɗora bakina kan lips ɗinta na mata kiss kafin na janye.


Murmushi na ga ta yi kafin ta ce “ bari na haɗa ma ruwan wanka” sai ta sauka daga cinyata,na bi bayanta da kallo har ta shige bedroom.Na dogon numfashi ina jin wani iri,ganin ta jima ba ta fito ba yasa na bi bayanta,sai da na rage kayan jikina kafin na shiga toilet ɗin a tsaye na tarar da ita ta na karanta dettol da duk abin da ke ciki na dangin wanka da kuma gyaran jiki.
“ Yaya mine ne wannan?” ta tambaye ni,na ce “ ki karanta mana ai kin yi makaranta”
“Ban gane ba ne,rubutun da French ne sai hoton gashi da aka yi,ko mai sa sulɓin gashi ne?” na karɓe na ce “ a'a ki barsa nan tun da ba ki san na mine ne ba” ta turo baki kafin kuma ta ce “ na yi ma wankan?” na girgiza mata,“ don mi? Ni fa matarka ce ”
“Ba ki jin tsorona?”
“Ina ji mana amma sai in ka murtuƙe fuska”
“Fita!” na faɗa cikin bayar da umarni kuma babu alamun wasa a fuskata, sumi-sumi ta wuce ta bar toilet ɗin.


Bahon wankan na shiga bayan na cire komai na jikina,na lumshe ido ina zancen zuci ‘ wannan ɗin ce zan nunawa sirrina ƙwaila da ita,sai ilimin faɗar kalmar mijin amma ba ta san mi take nufi ba.Wannan da ace ta san ana wata mu'amala ta aure da tuni ta min ƙorafi ban yi mata ba’ wani haushi ne ma ya rufe ni kawai na soma wankan da sauri-sauri .


Ina fitowa na shirya cikin jallabiya fara na fesa turare sannan na fita falo,a zaune na tarar da ita ta saka kwanonin abinci a gaba.


“Tun ɗazu nake jiran ka,yunwa nake ji kuma Granny tace kar na sake cin abinci ni ɗaya ba tare da kai ba muddin dai ka na gida” ta faɗa tare da soma buɗe kwanonin,na zauna tare da jawo ta jikina na ce “ki bar abincin nan zo ki ji tukuna”
“Ni ban so ka na ɗora ni kan cinya duk sai na takura na ga na sakar ma nauyi”
“Kin manta soja ne ni ?”
“Haka ne fa an ce wai har mota ku na iya cirawa da hannu shi yasa kuke da ƙaton ƙorji da kuma damatsa” ta yi furicin ta na mai dukan ƙirjina.Na riƙe hannun nata tare da kai yatsanta manuniya bakina na soma sha,ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “kar dai ka cije ni don alƙur'an sai na rama”


A zuci na ce ‘ai matsalar auren ƙwaila kenan kuma baƙauya sam ba ta san rayuwar romantic ba’
Sai kuma a hankali na fara ƙarewa surar jikinta kallo,na saki wani murmushi da na kalli ƙirjinta yadda ta saka uwar acuci maza.
“A bar kalle min abu,can da na ce ma ina son bra ɗin har cewa ka yi a'a ” ta faɗa a shagwaɓe ta na faɗo wa kan ƙirjina,na shafi gadon bayanta na ce “ in dai za ki fita ban yarda ki saka ta ba”
“ In fita in je ina ni da ban san kowa a nan ba”
“Da zarar hutu ya ida ai za ki koma makaranta ko kin haƙura ne?”
“A'a zan je mana ni da nake son zama nurse”
“Da wannan tsoron naki?” ta yi dariya kafin ta ce “ yunwa nake ji”


Na ce “ faɗa mini ba ki jin daɗin irin wannan yanayin da muke ciki?”
“ Ina ji amma in an ƙoshi ai ya fi” ta bani amsa.


Na ɗan janye ta daga ƙirjina kafin na ce “ to je ki ci”
“Kai ba ka ci”
“Eh ” na bata amsa tare da komawa bedroom, system na ɗauko na haye bed na ci gaba da yin bincikena ban fito ba sai kusan sallar magrib.Ban ganta ba falo,na sauka ƙasa su na zaune a babban falo ita da Granny ta na yi mata tausa.
Na je na gaishe da Granny kafin na wuce masjid ko da muka gama sallah ban fito ba sai da muka yi isha'i,sosai na yi ta mamakin mi ya tsayar da Daddy da har yanzu bai shigo ba.Da wannan tunani na koma gida,kafin na wuce part ɗina na ce “ Granny ina son Lipton a saka citta da lemun tsami dayawa” ina jin idonta a kaina har na haye step .






Granny ta dubi Maryam ta ce “ mi ya haɗa ku ke kuma?”
Maryam ta turo baki cike da ƙurciya ta ce “ to Granny kullum kowanne lokaci sai dai a yi ta yin abu guda kamar wasu tantabaru,kawai don na ce masa yunwa nake ji sai yayi fushi?”
Granny ta ɗan murmusa kafin ta ce “ Maryama ki yi wa mijin ki biyayya in ba haka ba wuta Allah zai saka ki ,ɗazu duk ba na faɗa miki ki cire kunyarsa ba?”
“Granny har fa kayan da kika ce na saka su ne a jikina yanzu haka,hijabi ne kawai na ɗora ko na nuna miki?”


“A'a ba sai kin nuna min ba shi mijin naki dai za ki nuna wa in kuma kika tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa.Wallahi ya auro wata ya bar ki nan sake da baki”


Maryam jin zance kishiya ta ce “ a'a wallahi ban so yanzu faɗa mini mi zan yi?”
“ Zan baki littatafan Hausa ki karanta don ni ma su suke ɗebe min kaɗaici”
Maryam ta yi dariya ta ce “ wai Granny dama tsofi na karatun litattafan dandalin soyayya?” ba ta bata amsa ba sai mai aiki da ta kira ta sanar da ita ta haɗa Lipton dayawa da kuma abubuwan da za a saka.
Granny ta je ta ɗauko wa Maryam littafai dayawa ta miƙo mata,ta karɓa ta na duba wa.Ana kawo Lipton ɗin Granny ta ce “tashi ki kai masa,da zarar kin shiga ɗaki ki cire wannan ƙaton hijabin”
Da “ to ” ta amsa kafin ta nufi sama,kamar yaro mai koyon tafiya haka take taka step ɗin har ta isa.




Ina kwance kan kujera abun duniya ya sha min kai ta shigo da sallama,ban amsa ba kawai na zuba mata ido duk da ta saka hijabi amma bai ɓiye tudun ƙatuwar bra ɗin da ta saka ba.
Kan table ta aje tray ɗin kafin ta cire

12 / 13