ZAWARCI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Love Story

Chapter   13 / 13

36K to 37.3K   out of 37.3K words

hijabinta wanda ban san dalilinta na yin haka ba,ƙila don ta ƙara cutar da ni wani sashen zuciyata ya faɗa ban ida yarda da haka ba ma sai da ta duƙa don zuba mini Lipton ɗin a kofi .Na maida kaina gefe zuciyata na matsanancin bugawa na ce “ ki saka hijabin ki, sannan ki je ki yi sallolin ki”
“ Toh” ta faɗa ba tare da ta bani kofin Lipton ɗin ba ta yi gaba ,wani haushi ya rufe ni na tashi na ɗauka na soma sha sosai na ji daɗinsa lemun tsami ya kama da kyau cittar kuwa sai ƙamshi take.Da na sha Lipton ɗin na soma jin dama kafin kuma madubin idona yayi ta hasko min surar Maryam yayin da zuciyata ke tirza ni akan na je na kawar da damuwata ai da igiyoyin aure na kanta.Na cije leɓena na ƙasa,kafin dakyar na miƙe na shiga bedroom a tsaye na ganta ta cire rigar kayan ta tsaya daga ita sai bra rabin ƙirjinta duk a waje.A yanayin da nake kawai da ace ta na da hankali ta san abin da na fi buƙata,amma ta yi saurin juyawa ta na ɓoye ƙirjinta tare da saka doguwar riga ta sallah ta zumbula uban hijabi kamar matar liman ta ƙabarta sallah.
Dakyar na iya saita kaina ta hanyar yin wani wanka,sannan na ɗauki key na fice na bar gidan.Compagnie na nufa inda sojawa ke kwana,ɗakinmu na wuce wanda a yanzu ya zama ni kaɗai ke da shi.Na yi kwance kan ɗan gadona na ƙarfe,a hankali na soma ware idona kan ƙananun rubutun da aka yi a jikin gadon da ke can saman nawa wanda dama can Abakar ke da na sama ni na ƙasa ban ganinsa da kyau wannan ya saka na kunna fitilar wayata na soma karantawa.






```Na san za ka karanta wannan rubutun abokina a lokacin da na yi ma nisa,kake cikin kewata.Ana bibiyar rayuwata ,ina takaicin sanar da kai cewa Daddy na cikin wata ƙungiya ta maras gaskiyan ƙasarmu ,ban san komai akai ba amma don Allah ko bayan raina ka lalubo gaskiyar nan domin ƙasarmu ta zauna lafiya ka ji IB```




Na karanta rubutun nan ya fi cikon casbi,sam hankalina ya kasa ɗaukar wannan lamari wanda na tabbatar Abakar ne ya rubuta shi,domin rubutunsa ne.Sannan shi kaɗai ne ya san in ina cikin damuwa kawai nake hawa gadon nan na yi kwance,hasalima ko a nan zan kwana na fi son na yi shimfiɗa ƙasa saboda in ina bacci ina yawan juyi.Ƙarshen zance kuma shi ne kawai yake kirana da sunan IB.
Wani abu ne ya tsargar min na zargi ‘tabbas mutuwar Abakar an shirya ta ne saboda sun gano ya san sirrinsu ’ na miƙe tsaye ina jin a yau ba sai gobe ba sai na yi fito na fito da Daddy ko da zai kashe ni ne.Ina tuƙi ina tunanin yadda Daddy ke ta fafutukar ganin ya kawo zaman lafiya da tsaro a Nijeriya,ni shaida ne akan hakan amma ta ya kuma za a same shi da hannu a cikin ƴan tafa zaune tsaye? Ina cikin gudu ne motata ta samu matsala,an yi sa'a banda nisa da masu gyara.Na fito na yi musu magana aka zo aka fara duba mini,kafin nan sai na yi zaune kan banci ina sauraren hirar abokin ɗan garejin.


“Kai amma Komanda Isah ba ƙaramin ƙwaro ba ne,in ba shi ba ina aka taɓa ganin shugaba ya tafi yaƙi shi da ya yaransa ”


“Ai in faɗa ma yau an yi ɓarin wuta,yadda ma na ji an ce wai ya samu harbin bindiga a ƙirji amma sun ɓoye abun kawai suka ce ya ɗan ji rauni ne”


Ban san lokacin da na ce “Shi Komandan sojojin?”
“Eh wallahi! Halan ba ka kallon tv? Yanzu nan aka gama nunawa a labarai”
Ban sake cewa komai ba har aka ida min gyaran na biya shi sannan na shiga motata,a tsiyace nake gudu har na isa gida tun yanayin da na tarar da Granny na fahimci abin da na ji ɗin dai gaskiya ne to amma na rasa ta yaya hakan ta faru sunan ina soja kuma ɗansa amma ban san da zancen tafiyar ba.


“Zo ka kai ni an ce ya na babbar asibitin nan” Granny ta faɗa ta na hawaye ,ban musa ba na ja hannunta muka shiga mota.Tun da na karyo kwanar asibitin na ga ko ta ina sojawa ne sannan ga ƴan jaridu nan birjit,motata ma dakyar aka bari ta wuce shi ma saboda Granny ne.
Sojawa biyu suka yi mana rakiya har ɗakin da Daddy ke kwance an saka masa oxygene yayin da na'urori ke jone a jikinsa.Yanayin sheɗar tasa kawai in mutum ya kalla doli ya firgita don sai tiii!tiii! Ƴar ƙaramar system ɗin ke yi.Daga inda yake kwance yake kallonmu,ko magana bai iya yi ga wurin da aka fasa aka cire alburushin nan an naɗe da bandeji.
Granny ta je kusan kansa ta yi zaune ta na shafar sumar kansa tare da soma yi masa addu'a idonta na ɗigar da hawaye,shiru kawai na yi na ƙurawa system ɗin ido yadda ka san addu'ar Granny ita ce magani haka numfashin Daddy ya soma komowa daidai har ya dawo normal.Na lumshe ido ina jinjina girman addu'ar uwa ga ƴaƴanta,wacce Allah da kansa ya ce babu hijabi a tsakaninsa da ita bakin uwa mahaifiya na da matuƙar ƙarfi.




“Ibraheemu?” na ji muryar Daddy cikin wani sauti,na matsar da kai ina cewa “na'am Daddy ya jikin naka?”
“Da sauƙi alhamdullah! Gobe in Allah ya kai mu ka je ofis ɗina duk wani jadawalin aikin da za a yi ka gabatar da shi a matsayina zan yi wa Sergent Yakubu magana,PIN ɗin system ɗin sunanka za ka saka,don Allah kar ka yi wasa ya kamata a yi komai kan tsari”
Na kamo hannunsa ina cewa “in sha Allah Daddy” mun ɗan jima nan kafin mu dawo gida cike da ƙwarin gwiwa akan hanya ina tuƙi ina tunani ‘mutumen da ke da hannu da ta'addanci ta ya zai iya bari a duba system ɗinsa? Ina ganin dai Abakar bai fahimci Daddy ba’ da wannan tunanin na tunkuɗe zargina akan Daddy muka isa gida.


Na yi wa Granny rakiya ɗakinta har zan wuce sama ta ce “ka je ka sanar da matar Mahaifin ka halin da ake ciki ita ma ta na da haƙin sanin halin da mijinta yake ciki,kar ka yi min muso in dai na isa da kai”


Cike da jin haushi na fita daga nan na wuce sashen Daddy,ko sallama ban yi ba na tura ƙofar kunnuwa ne da idona suka yi min mugun ji da mugun gani.Ƙatuwar tv ɗin da ke manne ga bango ce ke ta wano BF ga sautin duk ya cika ɗakin ,duk tsiyar ka in dai kai lafiyayye ne doli ka ji wani abu.Da sauri na baro ɗakin ina da na sanin shiga,ina haurawa can sama na tarar da Maryam a zaune an ci wani sabon adon na kayan bacci .Lipstick ɗin da ta saka yasa laɓanta suke sheƙi,idona har wani dishi-dishi suke yi na isa gare ta dama na ɗau caji,“kin yi kyau ina son wannan ”na faɗa ina nuna laɓanta da suka sha man leɓe,da na soma sumbatarsu kuwa har wani gajimare nake gani.
Ta ƙwace bakinta dakyar ta na numfashi da sauri da sauri ,ta na mai ƙure ni da ido murya na ɗan rawa ta ce “kakkaaa”
“Shuuut!” na katse ta tare jawo jikina na yi mata raɗa a kunne ,na ce “duk bayanan da Ammy ta yi miki ba ta sanar da ke haƙin miji ba?”
“Ta faɗa mini” ta faɗa cikin rawa murya.
Na ce “to yau zan fanshe sadakina wallahi ki nutsu ban son shirmen nan” damatsana ta riƙe ƙwairai tare da fashewa da kuka,wanda sosai yau ya yi min daɗi sai na ji shi cakwai kamar zuma wannan yasa ban kula ta ba na kai ta kan bed.


Nan na kawo ƙarshen free page,na kyauta ya ida mai son ci gaba sai ya biya
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

13 / 13