Author : Princess Aysha Muhammad Saddiqa Category : Wattpad Hausa Novels
Compiled by Princess Aysha Muhammad
Copied by Umar Dalha
[10/29, 20:47] Saddiqa:
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
Zahra Muhammad Mahmud.
*wannan littafin kirkurars nayi,banyishi dan wani ko wataba,so in wani abu yayi kama da
rayuwarka arashine,a kiyaye juyamin shi ta kowacce siga*
*na sadaukar da wannan littafi ga kawata kuma aminiyata Amina Maman Gid'ad'o,Allah
yabarmu tare cikin aminci*
*Dedicated to Amina Maman Gidado*
*1-2*
Ɗakin tarone me kyan gaske,wanda ke dauke da kujeru na alfarma.zagaye da wani tebur.
Mutanene kimanin mutum hamsin zaune akan kujerun kowa rai abace,yayinda wasu yanmata
su uku ke tsugune agaban mutanen,daya cikinsu dauke da wani jariri se kuka yake tsalawa.
"Fatima Abubakar Radda,Hauwa'u Abubakar Imam,Amina,acikinku wlh idan baku fada mana
dan waye wannan jaririnba,se na koreku dukanku a makarantar nan,taya zaa haifi yaro acikinku
amman akasa gane wacce ta haifeshin"cewar chancellor na makarantar nasarawa state
university wacce akafi sani da suna Nsuk.
Gaba ɗaya hankalin yanmatan inyayi dubu ya tashi,sabida dukansu suna level four hundred ne
kuma final exam suke zanawa.
"Sir wlh ni ba dana bane,wlh banida wata alaka dashi,Fatima ce ta tsintoshi ta kawo mana shi
dakinmu jiya da daddare,bayan haka ni wlh bansan komai ba game da yaron"cewar hauwau
Abubakar imam tana share hawaye.
Amina ce ta tsananta kukanta,harda majina,inda tafara mgn.
"Taya mu da muke yanmata zaace wai mune kuma muka haifi yaro,nima wlh ba dana bane,sam
banida alaka dashi,sede atuhumi ita fatiman data kawo yaron,danni wlh a idona ma gani nake
tana kama da yaron"ta karasa maganar cikin kuka.
Allah sarki fatima baiwar Allah ware ido kawai takeyi,sabida ita tun farkonta bata iya magana
me tsayiba hasalima wuya take bata,shiyasa su hauwau suka fita baki,
Tsawa vice chancellor ya yimata gami da cewa.
"zaki mana bayanin inda kika samo yaron ko bazakiyi ba?"
A daburce tace.
"Sir wlh ba ɗana bane,wlh banida alaka dashi,kwatakwata nima tsintarshi nayi jiya na fito fitsari
zan koma daki naganshi cikin kwali ruwa na dukanshi yana kuka,shine na ɗaukeshi nakaishi
ɗakinmu,amman wlh ba ɗana bane"ta karasa maganar tana kuka gamida jijjiga yaron dake ta
faman kuka.
Shuru gurin yayi,kowa na nazari,inda su Amina da hauwau suka tubure sufa ba ɗansu
bane,inda amina kai tsaye ma ta alakanta yaron da fatima.
Fatima se kuka takeyi,Tana rantsuwa akan tsintar yaron tayi amman sam anki amincewa da
ita,sabida shaidar da aminanta suka bada kamar haka.
" sir watanni shida dasuka wuce fatima Abubakar Radda ta taba cemin watanninta uku rabonta
da ganin aladarta,wanda har na bata shawarar taje taga likita,bayan haka bata cemin tasamu
saukiba ko akasin hakan"cewar hauwau tana kallon fatiman.
"ke fatima anyi haka ko ba ayi ba?"cewar chancellor .
"eh anyi haka,sede na bari ne akayi hutu sannan naje asibiti dana koma gida aka bani magani
kuma nasamu daidaituwar abun"cewar fatima tana kuka.
"Nima ta fadamin hakan,bayan haka kuma tazo tana fama da yawan ciwon mara,wanda
lokacin,har cewa takeyi tanajin motsi acikinta,sannan lokacin tana yawan yin bacci dan so tari
ko aji bata iya zuwa"cewar Amina tana kallon fatiman.
"Fatima anyi haka ko baayi ba?"inji chancellor.
Cikin matsanancin kuka tace.
"Duka anyi,sede motsi da nakeji a cikina danaje asibiti cewa akayi infection ne ke haddasa
hakan,yawan bacci kuma lokacin banida lfy ne,ciwon mara ma danakeyi yanada alaka da
infection din,ku yard dani wlh ni ba dana bane"ta rushe da kuka.
Bayan angama muhawarane,aka maida hankali,dan sauraron hukuncin da shugaban ze yanke.
"Fatima Abubakar Radda bincike da shaidu na kusa dake damuka samu,mu mun gamsu
wannan yaron nakine,kuna sanda kika shigo makarantar,sunanki ajerin yanmata akasa,bakice
kinada aureba,so bazamu ci gaba barin barna na yawa acikin makarantar muba,dan haka abisa
dokar da aka tanadarwa budurwar da tayi ciki,hukumar makarantarnan ta koreki,daga
makarantar"cewar shugaban.sannan yayi signing a wata takarda,yamike yafice,kowa ma
ficewar yayi.
Ya rage daga fatima se kawayenta,da jaririn,fatima kuka takeyi kamar ranta ze fita,tama rasa
abinda zatayi,suko se rarrashinta sukeyi,
Miƙewa tayi dauke da yaron da ko zaa kasheta batasan daga inda yakeba,amman se gashi,an
maidashi danta,kuka take,sosai,a hankali take ɗaga kafarta har ta fito daga gurin,dalibai tasamu
birjik a waje suna mata tofin Ala tsine
Su hauwau ne sukazo suka tareta har ta fice daga inda ɗaliban suke,
Hauwau da Amina ne suka cemata.
"Fatima kiji tsoron Allah ki kula da yaron nan,kodan ladan hakan se kiga Allah ya yafemiki zinar
da kika aykata,kiyi hakuri da kaddarar data faɗa miki kinji"simuka faɗi suna kuka.
Bata ko waiwayesuba tasa kai ta wuce hostel,ta debo kayanta,tazo ta fice,tabarsu se kuka
sukeyi na rabuwa da ita.
Goye da yaron tafito,tanemi abun hawa zuwa tasha,tana zuwa motar garinsu katsina ta
nema,tahau tana kuka,
hmmmmmm.
Tofa,wannan lamari akwai daure kai,aciki,anya kuwa yaron ba dan fatiman bane?,inba hakaba
taya zata anshi dan da ba nata ba?
mudeje zuwa.
Surbajo for life
[10/29, 20:47] Saddiqa:
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
Zahra Muhammad Mahmud
*Don Allah kudena tambayar nanah aseeyah,wlh har rasa amsar baku nake,pls din girman Allah
kudena tambaya,duk randa Allah yasa zaa ci gaba zaku ganshi,so don Allah kudena tambayata
don girman Allah*
*Dedicated to Amina maman Gidado*
*3-4*
Haka mota ta cika suka kama hanyar katsina,fatima se kuka takeyi,
Zuwacan yaron yafara kuka,kowa na motar akamata ca akan ta bashi nono,dan da gani yunwa
yake ji.
Zuciyarta kamar zata tsinke,haka tasa yaron cikin hijab dinta tasa masa nonon a baki,carab ya
kama,ita kuma ta runtse ido,sabida azabar da takeji,
Yaron ganin ba ruwa a nonon ne yasa yaci gaba da tsala kukan shi,haka gankalin fatima yabi ya
tashi ta rasa yadda zatayi dashi,wata matace,ta amsheshi ta shiga jijjigashi har ya hakura yayi
bacci,sannan fatima ta ansheshi.
Da laasar suka isa katsina,mota ta hau da zata kaita unguwarsu,tana sauka tabi layin daze
sadata da gidan su.
Da sallamarta,ta shiga gidan,ummantace zaune tana gyaran alaiyahu,fatima na ganinta ta
rushe da kuka,ta nufeta,a rude ummanta ta rukota tana tambayarta.
"lafiya kuwa fatima kike kuka?"
"umma an koreni a makaranta akan laifin da ban aykata ba"ta faɗi sanda take sakko yaron daga
bayanta.
A firgice umman taja baya tana binta da kallon tuhuma.
"Umma wannan bawan Allah tsintarshi nayi a kofar dakinmu na makaranta,an yar dashi,ruwan
sama na dukanshi,sanadin taimakon da na mishine ni kuma aka koreni"daganan ta kwashe duk
abinda ya faru ta sanar da umman nata.
Fatima yace ta gari me tsananin biyayya ga mahaifiyarta,wacce kuma kullum bakinta cikin furta
gaskiya yake,shiyasa mahaifiyarta natsuwa da kalamin bakin fatiman.
Matsowa tayi kusa da ita,ta amshi yaron,hawaye na zuba afuskarta,tace.
"kowa da irin tashi kaddarar,kai taka a haka tazoma,Allah ya rayaka rayuwa me amfani duniya
da lahira,ke kuma fatima kiyi hakuri,bamu da karfin fahimtar da hukumar makarantar bakowane
ke yarda dame gaskiya a lokaci guda ba,ni musulmace fatima na yarda da kaddarar
Allah,wannan abu daya sameki ki rikeshi amatsayin kaddara kuma ki yarda da ita kamar yadda
nima nayi,da yardar ubangiji,wannan yaron zeyi rayuwa me amfani,sekinyi alfahari dashi
agaba,Allah ya shiryi mahaifiyarsa"ta karasa maganar hawaye na bin fuskarta.
Se a lokacin hankalin fatima ya kwanta,dan ita bata makomar karatunta takeyiba,ta makomar
rayuwar yaron takeyi idan mahaifiyarta bata amince da zaman yaron a tare dasu ba,yayanta
umar kawai takeji,tunda ko ummanta ta amince tasan shima zata shawo kanshi ya fahimta,dan
umar mutumne me tsatstsauran raayi,baya juyuwa ta daɗi.
Umman mikewa tayi,ta ɗauko zamzam da dabino ta tauna dabinon ta zuba acikin zamzam din
tafara ba yaron ayko carab ya amsa yana sha yana turo harshe waje gamida bude idanunshi
tar,seda ya koshi ya fara turoshi waje in an bashi.
Wanka umman tai masa,da ruwa me zafi ta gasheshi da kyau,ayko tun acikin ruwan yafara
bacci.
Haka ta gama ta masa kwalliya sannan ta nadeshi a zani ta kwantar dashi,bayan ta kwantar
dashine tacewa fatima.
"kije ki samu kiyi wanka kema,bari naje na anso masa kayan sawa gurin dije dillaliya ko kala
biyu ne,kamin Allah ya hore a siya masa da yawa"
Murmushi fatima tayi sannan tace.
"umma na kenan,me kyan zuciya,wlh ina godewa Allah daya bani ke a matsayin uwa,Allah ya
kara nisan kwana ummana"ta fadi tana dariya.
Murmushi umman tayi,sannan ta juya ta nufi hanyar fita daga gidan,har takai bakin kofa ta
waigo tacewa fatiman.
"Ki kula da yaron nan,duk wuya duk runtsi ki jure,wata rana se labari,jikina na bani wannan
yaron shi zeji kanki,ki rikeshi amana"ta fadi jiki a sanyaye.
Dariya Fatima tayi sannan tace.
"ummana kenan keda zaki ki dawo meye nabada sakon a hanyar kofar gida"tayi maganar cikin
nishadi.
Murmushi umman tayi tasa kai ta fice daga gidan,tanufi gidan dije dillaliya.
Ayko taje a saa dan ankawowa dijen kayan yara masu saukin kuɗi hakanne yasa ta zaɓo masa
kala hudu,gamida wanduna,da bulumboti,ta biya kudin ta amso kayan ta nufo gada.
Tana zuwa zata tsallaka titin da dagashi se gidansu kasancewar gidan abakin titi yake,kawai
sega wata mota aguje ta bigeta tabi ta kanta
jamaane akayo ca akanta,sede ina gaduk wanda yasan mutuwa yana kallon umnan fatima
yasan ta mutu,
me motar dama burkine ya tsinke masa yana bugetane yasamu motar ta tsaya,a gigice ya nufo
ta shima se salati yakeyi.
kan kace kwabo tuni gurin ya dinke da mutane,ganye aka samu aka rufa mata,kamin akawo
makara daga masallaci.
Fatima dake gidan bayan fitar ummanta ji take gabanta na faduwa,hakanne yasa ta kasa
wankan,duk ta rasa natsuwa.
Hayaniyar da ta jiyo a kofar gidanne yasa ta leka dan ganin abinda ke faruwa.
innalillahiwainnailaihirrajuun,ita kawai take maimaitawa sanda tai karo da gawar ummanta
kwance kan titi,da gudu tayi kanta tana kuka tana jijjigata,
wanda ya buge ummanne ya matso gurinta,matashine me cikar kamala da mutunci yace.
"don Allah ku gafartamin wlh bada sanina na buge ta ba,"
A hargitse fatima ta juyo ta kafeshi ta mari,sannan ta rufeshi da duka tana fadin.
"ka cuceni ka cuci rayuwata,ka kashemin uwata me tausayawa rayuwata,wlh bazan gafarta
makaba,mugu azzalumi"
Da kyar aka kwacr mutumin a hannunta,wanda zuwa lokacin gaba daya hawaye ya gama
wanke masa fuska,
haka aka shigar da gawar umnan cikin gidan,wanda hakan tayi daidai da dawowar,yayan
fatiman umar daga gurin ayki.
Tashin hankalin daya shiga baa mgn sabida umar ji yake ummansa itace rayuwarsa,yanasonta
yana kaunarta,yau gashi ta tafi ta barshi.
Haka aka hada umman aka sallaceta,aka kaita gidanta na gaskiya,kowa se yabon kyawawan
halayenta,yakeyi.
kayan data siyone,wani matashi yashigo gidan yamikawa fatima,ayko tana budewa taci gaba da
kukan se alokacin ta tuno da yaron dakecan dakinta yana bacci,mikewa tayi taje ta dubashi,har
lokacin baccinshi yakeyi.
Ranar fatima da yayanta ba wanda ya runtsa,duniyar ta musu zafi,dama gashi shekarar
mahaifinsu uku da rasuwa,mahaifiyarsu ce ke ci gaba da dawainita dasu to gashi yau itama ta
tafi ta barsu.
Haka aka cigaba da zaman makoki har zuwa ranar bakwai,umr yan ganin jariri a hannun fatima
amnan azatonshi dan daya daga cikin yan uwansune,shiyasa be taba kawo komaiba
aransa,suma jamaa kowa yaganta dashi dauka yake na watane acikinsua haka har kowa y
watse ranar sadakar bakwai da daddarw.
Umar ya shigo cikin gida ya leka dakin fatiman yasamu tana yiwa yaron wanka yana kukansa.
cike da tsananin mamako yace mata.
"wai yaron nan na waye?,ina uwarsa?"ya tambaya a bukace.
gaban fatimane yafara dukan uku uku,baki na rawa tace.
"Nima bansn wacece uwarshiba,tsinto shi nayi nima a makarantarmu,sanadin hakan aka
korenima a makarantar shine nazo na fadawa umma komai a ranar d zata rasu"ta karasa
maganar tana kuka.
tsigar jikin umar tuni ta jima da tashi,bacin rai na aynihine ya bayyana akan fuskarsa,afusace
yace.
"what!!!!!!"
muje zuwa
surbajo for life
[10/29, 20:47] Saddiqa:
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
Zahra Muhammad Mahmud
*Dedicated to Amina maman gidado*
*5-6*
"Ni zaki rainawa hankali?,su makarantar mahaukatane da zasu koreki hakannan batare dasun
tabbatar da nkin bane,?"cewar umar cikin matsnancin fushi.
"wlh yaya ba karya nake maka ba,ko umma ma ta fahimta dana mata bayani,don Allah kaima
ka fahimceni wlh. Ba dana bane"tayi mgnr cikin kuka.
"Se yanzu na gano musabbabin mutuwar mahaifiyata,ashe bakincikin kine yasa tafice agidan
batare data luraba ta fada mota ta taketa,to wlh bari kiji in faɗa miki,wlh kin gana zama tare
dani,kamin nima bakin cikin naki ya kar ni"
"yaya wlh ba haka bane gidan dije dillaliya taje siyowa yaron kaya,shine a hanyarta ta dawowa
tsutsayin ya rutsa da ita,don Allah yaya karka tozartani,banida kowa sekai"ta tsuguna
agabanshi tana kuka.
Ko ajikin umar,ranshi yagama baci ya yarda hundred percent ita tayi sanadin mutuwar
ummansa,dan haka bayajin ze iya gafarta mata.
Fincikota yayi ita da yaron,yana jansu hanyar kofar gida,kuka take tana rokonshi amman ko
ajikinshi haka ya cillasu kofar gidan,sannan yadawo yadauki jakar kayanta da ledar kayan yaran
daya gani a kai yazo ya cillo mata,sannan yafara mgn.
"koda wasa kika sake yunkurin kallon gidan nan a matsayin gidanku wlh sena halakaki,kamar
yadda kika halaka mahaifiyarmu,tur dake fatima,ki rasa sakamakon da zaki ba umma se kikawo
mata shege gida"
Tuni jamaa sun zagayesu sunajin abinda ke faruwa,ayko nan kowa yashiga tofin ala tsine.
mikewa tayi jikinta na bari,ta hoya yaron,sannan ta kwashi kayansu,tabar harabar gurin,dan tafi
kowa sanin waye umar,ze iya yimata abinda yafi haka ma,
Tafe take tana kuka tana tausayin rayuwarta data yaron bayanta,sam umar be musu adalciba,
Haka take ta tafiya da kafarta wanda ita kanta ko zaa kasheta batasan inda take sa kafarta
ba,kawaide tafiyar take.
Har dare yayi mata,gefen wata bishiya taje ta rakube rungume da yaron ,data rufe da hijabi,a
haka bacci yayi awaon gaba da ita.
Bata farkaba,seda garin Allah ya waye,shima kukan yaronne ya farkar da ita,a rude ta
tashi,tashiga jijjigashi.
Tafiya taci gaba dayi har tazo gurin wasu masu saida abinci,anan tanemi taimakonsu akan
tanaso ta dunga yi musu wanke wanke,dakyar suka amince nanfa ta duka tashiga yimusu
wanke wanke,harta gama suka biyata kuɗinta,
Shagon saida madarar yara taje,ta siyowa yaron,wanda sabida yunwa ko kuka bayayi,gurin
saida abincin ta koma tasamu ruwan dumi ta dama masa tasa a bulumboti,ta sa masa abaki,
Yadda yaron kejan madarar kadai abun tausayine,dan har kwarewa yakeyi sabida hanzari,tas
yashanye wanda ta hada masa,se gumi yakeyi,alamun yaji daidai.
Matar dake saida abincin ce,tacewa fatima.
"keko in banda abunki me ze hana kinemi maganin dake kawo ruwan nono,kidunga shayar da
danki,inaga hakan se yafi cacar kudin madara,"
Shuru fatima tayi tana sauraronta,tabbas da zata samu maganin zatayi amfani dashi Kodan
inganta lfyr yaronta.
dubanta takai gurin me abincin tace.
"hajiya kitaimakamin inkinsan masu saida maganin wlh banuda kudi amman innayi wanke
wanke se adunga cirewa a kudina,don Allah ki taimakamin"tayi zancen hawaye nabin fuskarta.
"karki damu kawata ce ke siyarwa,insha Allahu zan amsar miki,inyaso kya biya daga baya"
godiya sosai fatima ta dunga yiwa matar harda kukanta.
Dayake matar ita da maaikatanta agurin suke kwana shiyasa fatima ta shiga cikinsu itama
hankali kwance,da dare tayi matar ta kawomat maganin,ta nuna mata yadda ake amfani dashi,
Wanka tayiwa yaronta sannan t sauya masa kaya,ta wanke wanda ta cire masa,sannan taimasa
shinfida ta kwantar dashi taimasa rufar da sauro baze cijeshiba.
Haka rayuwar fatima ta kasance agidan abinci ita da yaronta,koda wasa bata sake waiwayar
gidansuba,hankalinta ya kwanta da inda take.
Suna nan suna sanaar abinci,madara take ci gaba da bashi sabida ruwan nonon yaki
zuwa,ayko ba laifi yaron gwanin shaawa yayi kubarsa abunsa,dan wata hudu kamar yakai
shida,sabida wayo.
Hajiya me abinci ce ta buɗe sabon gidan abincinta a garin Abuja,dan haka ta tara maaikatanta
ta sanar dasu,ayko kowa cikinsu yayi murna,sabida hajiya uwace tana kare musu hakkinsu da
mutuncinsu kamar kowacce uwa,ba kamar sauran yan tuwo tuwon ba.
Nanfa ta kawo motoci guda biyu suka kwashesu ita da maaikatanta zuwa garin Abuja,fatima
cike da kewar mahaifarta wato katsina.
*Wacece fatima?*
Fatima Abubakar Radda shine cikakken sunanta,
Anhaifeta agarin katsina,tana da yaya namiji guda daya,me suna umar,su biyu kawai Allah yaba
iyayensu.
Tayi makaranta tun daga primary zuwa secondry da islamiyya duk ajihar katsina,inda dakyar
mahaifinta yayi fafutukar samomata makarantar nsuk dake garin keffin ya musa,ta jihar
nasarawa.
Kasancewarsu masu karamin karfi,shiyasa ya wahala kan agama registration,nan aka shiryata
ta tafi karatun.
bata jimaba ta hadu da Amina da hauwau,wanda suka kulla kawance,Amina yace ga shugaban
nnpc ta jihar kaduna,yayinda hauwau ma mahaifinta hamshakin me kudine,fatimance kawai ba
yar kowaba.
Ta saki jiki dasu aminane sabida taga basu da wani hali mara kyau duk da suna yayan masu
kudi,amman basa nuna mata hakan.
Tunda ta hadu dasu suka dauki nauyin karatunta,musamman Amina ta taka muhimmiyar rawa a
rayuwarta dan Amina macece me matukar tausayin na kasa da ita.
So tari in anyi hutu,har kayan abinci take siyawa fatima takai gidansu,itama hauwau haka akwai
tausayi tana iya kokarinta wajen ganin sun inganta rayuwar fatima.
Tana tsaka da karatun Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa,wansa hakan sosai yadaga hankalinsu
dana mahaifiyarsu,haka dole suka fauwalawa Allah lamuransu suka rungumi kaddara.
kowa a gidansi yasan labarin kawayenta duk da basu taba zuwa gidan su fatimanba amman
alkhairinsu yasha zuwa.
Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin aminci har zuwa ranar da wannan tsautsayin ya rutsa
da ita,
*cigaban labarin*
muje zuwa
Surbajo for life.
[10/31, 14:03]