Author : Princess Aysha Muhammad Saddiqa Category : Wattpad Hausa Novels
+234 703 462 8375: í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
Zahra Muhammad Mahmud
*Dedicated to Amina Maman Gidado*
*7-8*
Sun sauka garin Abuja cike da farinciki game da sauyin da suka samu.
Tunda suka dawo Abuja fatima tafi sakin jikinta gurin gudanar da aykinta,zuwa yanzu an
sauyata daga wanke wanke zuwa me kai abinci.
Rayuwar ta mata daÉ—i,abu guda ke damunta rashin sunan da bata sawa yaron ta ba,abun na
damunta,matuka.
Yau jummaa,ranar na É—aya daga cikin ranakun da suka fi yin ciniki a gidan abincinsu,dan haka
da wuri fatima tai wanka ta shirya ta shirya danta,dan komai tasamu akanshi yake tafiya.
Fitowa tayi goye dashi abaya yana bacci,tafara aywatar da aykinta.
Wata motace kirar marcedez benz 4matic,fara me bakin glass ta wani manne akan kwalta,har ta
wuce restaurant din,sekuma motar tayo ribas ta dawo,daidai kofar shiga gurin.
Koda akayi parking su fatima duk sun kosa na cikin motar ya fito,suga ko waye,amman sam
yaki fitowa.
Hon aka dunga musu,da sauri hajiya me abinci ta tura fatima dan tafi sauran natsuwa.
Sannu a hankali take takawa har ta iso daidai window da direba yake,
Sannu a hankali glass din motar ya sauka,masha Allah,fatima ta furta azuciyarta.
yayin da tayi karo da wani matashi wanda shekarunsa zasu kai 29,kyakkyawa ajin farko,kallo
daya zaka masa ka fahimci,naira da hutu sun zauna ajikinshi,
Fuskarshi sanye cikin bakin glass,yayin da gefen fuskar zagaye yake da saje me kyau wanda
yadace da tsarin fuskar tasa,ga hanci me tsayi me kyan tsari,bakinshi dan karami kamar na
mace,kai gaskiya gayen karshen wankane.
Fadil Bukar Adam kenan, da ga Attajirin dan kasuwarnan,Alhaji Bukar Adam,wanda a fadin
Africa kaf babu me kudinshi.
Rusunawa fatima tayi ta gaisheshi muryarta se rawa takeyi,dan gaba daya gayen yagama
firgitata da kyanshi.
Waigowa yayi ya kare mata kallo,sannan ya yatsina fuska ya kauda kai,yace,cikin isa da
takama.
"Adana gaisuwarki,abinci nazo siya,ba komai ba"
Wayyo kunya,fatima ji tayi kamar ta tsaga kasa ta shige dan jin kunya,
Binshi tayi da ido,kawai,wayarshi ce tai kara,ya daga,ji tayi yace cikin fada.
"Haba mummy don Allah,shikenan ke duk abinda yaya gidado yazo ya fada miki seki hau kai ki
zauna,nide gaskiya ba inda zani,pls kiyiwa daddy bayani,abarni akasata in huta"
fatima batasan me akace masa dagacan bangaren ba se ji tayi yace.
"thanks you mummy"ya kashe wayar.
"Gidado,"shine sunan da fatima tashiga nanatawa a zuciyarta,tabbas sunan yamata daÉ—i,
"Roasted chicken nake bukata,guda biyu"yana gama fadi ya miko mata,bunch na yan 200 guda
daya.
jikin fatima se bari yake tasa hannu ta amshi kudin,tace.
"yallabai ay 2000 ne each"
ko kallonta beyiba,haka yasa ta juya cikin gurin ta hado masa komai kamar yadda ya bukata.
Ta dawo ta mika masa,kamar jira yake fuuuuuuuu yaja motar yabar gurin.
Jiki a sanyaye fatima ta koma cikin gurin,taba Hajiya duka kudin,kasancewar hajiya akwai
adalci,seta dauki dubu biyar ta barmata sauran,sosai fatima taji daÉ—in kudin.
Ranar fatima ta hada yar walima bayan sun tashi daga saida abinci ita dasu hajiya,tasawa
danta suna muhammad amman zaa dunga kiranshi Gid'ad'o.
Shiko fadil yana isa gida ya sa kanwarsa husna ta kawo masa plate da ruwa yafara cin kazarsa
danshi arayuwarshi ya tsani abincin me ayki,inyayi complain mummynsa tace yayi aure se
matarsa tai masa yadda yake so.
Hakane yasa ya gwammace yayi yawon gidajen abinci,danshi wacce yakeso karatu take,se ta
gama zasuyi aure.
Yana tsaka da cin abincin,wani matashi ya shigo falon yafi fadil kyau da komai,sede shi da gani
ze kai shekara 35 a duniya,gidado bukar Adam kenan.
kujera yaja ya zauna yana kallon yadda fadil din ke dibi dibi da naman kaza,murmushi yayi
yace.
"Fadil aduniya ban taba ganin mutum me shegen kwadayi irinka ba,yanzu shi kuma wannan ta
sunan gidan abincin da ka siyo shi?dan nasan garinnan daidai gidan abincin da basu sanka
ba".
Dariya fadil yayi,sannan yace.
"wlh bros ni nama.mance sunan gurin,amman wlh tunda nake siyan kaza bantaba cin me dadin
wannanba,".
Murmushi Gidado yayi sannan yace.
"hmmm nasanka fa fadil gobema kaji wani me dadin cewa zakayi baka taba cin me dadinsa ba"
"Allah bros ba wasa dandana kaji"
Ba musu yasa hannu yadauki yanka daya yasa a bakinsa,lumshe ido yayi sabida tsabar dadin
dayaji,tabbas fadil ya fadi gaskiya kazar tayi dadi sosai.
"fadil gaskiyarka kazar tayi dadi sosai,wataran zaka kaini nima naga gurin sabida in inaso naje
na siya"cewar gidado yana tauna naman.
Dariya,sosai fadil yakeyi yana tsokanar yayan nasa,
Shiko ko dariya bayayi dan beson raini.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[10/31, 14:04] +234 703 462 8375: í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
Zahra Muhammad Mahmud
*Dedicated to Amina Maman Gidado*
*9-10*
Tun daga lokacin Fadil ya maida gidan abincin su fatima gurin cin abincinshi,sabida shi mutum
ne meson abu me dadi.
Tare suke ci da danuwansa Gidado idan ya siyo,shiyasa shima gidadon yanzu inba abincin
gurinba baya cin na ko ina.
.Yauma kamar kullum zaune suke fadil da gidado suna cin abincin sunyi kaca kaca da
gurin,mahaifiyarsu ce tafito.
Macece kyakkyawa,ga aji sanye takecikin wani hadadden leshi,wanda yadace da jikinta yayin
da idonta ke sanye cikin farin glass siriri shima mekyau.
Koda ta shigo falon sam basu lura da ita ba abincinsu kawai sukeci.
Guri tasamu ta zauna tana musu kallon so da kauna,ba abinda hajiya maryam takeso sama da
yaran nan nata guda biyu,bata da wani buri daya wuce taga sunyi aure,amman kowa taiwa
batun auran,se yace be shiryaba.
"Ande ji kunya wlh,daga yayan har kanin anji bitir,yanzu fisabilillahi abunda kukeyi daidai
kenan,?ku kenan kullum fita siyan abinci waje,to wlh na dakatar da wannan iskancin,duk wanda
ya sake fita siyan abinci cikinku sena saba masa kunji na fada muku"cewar hajiya cikin hada rai.
Fadil ne ya turo baki gaba irin na shagwababbun yaran nan yace.
''haba mummy don Allah,kefa yan aykinki duk basu iya girkiba,yanzu kuma mun samo inda aka
iya kince mudena zuwa yanzu don Allah adalci kenan yaya?"ya karasa maganar yana kallon
gidado.
"ah sam baa mana adalciba,ina bayanka"cewar gidado yana dariya.
"nide na hana kuma dole ku hanu kunji na fada muku"cewar mummy.
"To inde hakane yaya muma muje gurin masu abincin su bamu me girka musu abincin
amatsayin me aykin girka mana agida tunda abun hakane"cewar fadil.
Dariya mummy takeyi dan tasan wawtar fadil tafi gaban haka ma.
"Wannan shawara taka tayi sosai haka kawai zamuyi,kuma komun kawo me girkin mu kadai
zaa dunga dafawa"cewar gidado.
"kude kuka sani,nide asiyo a waje ne akawomin gida ban aminceba"
Daga haka hira suka shigayi da mummyn tasu gwanin ban shaawa,
Da yamma suka shirya fadil da gidado,suka nufi gidan abincin,gidado kejan motar,suna
parking,fadil ya fita yashiga cikin gurin.
Fatima na ganinshi ta mike zumbur,dan be taba fitowa daga motar ba,hajiya ma da sauri tazo
inda yake.
"yalabai ay da base ka shigoba,inka tsaya acanma ay zaa kawomaka"cewar hajiya.
Murmushi atakaice fadil yayi,shima dan girmamawa yayi mata sannan yace.
"ba abinci nazo siyaba yau,alfarma nazo nema"
Ido hajiya ta ware tana kallinshi baki na rawa tace.
"alfarma kuma dannan?"
"Eh so nake ki taimaka kibani me girka abincin danake siya,zan kaita gidanmu tadunga girka
mana acan,"
Shuru hajiya tayi tana nazari,zuwacan tace.
"yaran dake ayki atare dani amanane a hannuna,taya zan baka daya cikinsu alhalin ban sanka
ba?"
"Fadil bukar Adam maliya,shine sunana,nasan ay may be kinsan mahaifina?"
itade hajiya bata yarda ba,ganin hakane yasa yaciro complementry card dinshi yabata,ta
karanta,sannan yaciro id card dinshi shima yabata ta duba.
Se a lokacin hajiya ta amince dashi dan tasan bukar Adam maliya bawan Allah ne me tsoron
Allah dagashi har matarshi.
"Fatima,shirya kizo"cewar hajiya tana kwalawa fatima kira.
jiki a sanyaye fatima tazo gurin,
"Gidansu zaki koma dayin ayki,insha Allahu na tabbatar da babu wata matsala,koda akwai
matsalar ki dawo nan kanki tsaye kinji"
Itade fatima ranta besoba hasalima gabanta bugawa yakeyi.
Haka ta dauko jakar kayansu ita da gidado,tazo tabi bayan fadil zuwa motar bayan sunyi
sallama da hajiya da sauran maaikatan.
Gidan baya ta bude ta shiga,shikuma yashiga gaban motar.
Wani sassanyan kamshine yabugi hancin fatima take ta lumshe ido sabida jin dadin kamshin.
"me ya zaunar dakai ne haka fadil?"inji gidado yana driving.
"wlh tambayoyine nasha kaga dole in tsaya in amsa kan abani"
"mtsssuu dan kawai zaka dauko yar ayki ake maka tambayoyin?"cewar gidado.
"eh wlh"inji fadil.
Itako hamshakiya mandiya fatima bata ma san sunayiba,dan har ga Allah kamshin da take
shaka,yasanyata cikin wani farinciki mara misaltuwa,hakanne yasa ta saki gidado dake ta
faman kiriniyarsa bata saniba.
Rarrafawa yayi yasauka akan kujerar,dan gidado rigimamme ne na ajin farko,ga kiriniya,shiyasa
tafi goyashi dan kar yayi barna.
Gidado da fadil se hirarsu sukeyi,sannu a hankali,gidado karami yayi nasarar dafa kujerar
direba yamike tsaye,hannunshi yake dagawa irin yadda yara keyi in suna jon nishadi.
Daga hannunshi keda wuya,se jikake fuf ya saukeshi da karfi abakin gidado babba da ke mgn
da fadil,
Akan idon fatima hakan ta faru,a gigice tace.
"Gidado me yasa bakajin maganane?"tafadi gamida fincikoshi.
Da sauri gidado babba ya waigo bayan motar rai a bace jin da ya yi an ambaci sunanshi,
muje zuwa
surbajo for life.
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
Zahra Muhammad Mahmud
*Dedicated to Amina maman Gidado*
*11-12*
"Uban waye baya jin maganar?"cewar gidado daya waigo a fusace.
Fatima rudewa tayi gaba daya dan ita batasan sunamshiba,jikinta se rawa yake.
A fusace yakara maimaita maganar.
"nace uban waye baya jin maganar?"
Cikin daburcewa da rawar murya tace.
"Uban gidado"í ¾í´£
Kuuuuu....
Yataka burki,dagashi har fadil ransu yayi masifar baci da zagin babansu dasuke tunanin tayi.
Yana parking,ya fito fadil shima ya fito,fincikota waje gidado yayi ita da sarkin barna wato gidado
karami.
Kafeta yayi da mari lafiyayyu guda biyu,yasake cewa.
"ubana ba saanki bane,dan haka ki kiyaye,wawiya kawai jakar kauye,jahila,"
Fatima ta rasa abunyi kuka kawai takeyi,fadi take.
"wlh ba da kai nake ba ranka ya dade da gidado nake gashinan baya jin mgn wlh don Allah kuyi
hakuri"ta fadi gamida nuna yaron.
Cikin rashin yarda da ita fadil ya gwada fadin.
"zo nan gidado"
Ayko da sauri yaron ya rarrafa gurinshi yana dariya.
"Oh my God"Gidado yace gami da shafa sumar kanshi,sosai yaji kunyar hukuncin da ya yanke
cikin fushi,mota ya koma yasha kunu,dan dabiarshi kenan baya laifi ya bada hakuri.
Fadil mika mata yaron yayi yana murmushi,yace.
"kiyi hakuri,sunane linzami yaja miki,shima sunan shi gidado,kasancewar beson raini ne yasa
kika sha tafi azatonshi dashi kike."
itade ba baka se kunne dan zuwa lokacin kumatunta kamar buredi dan girma,jiki asanyaye ta
bude bayan motar ta shiga.
tada motar yayi suka haura kan titi,lokaci zuwa lokaci,yana kallonta ta mirror yana ganin yadda
take share hawaye.
A haka har suka iso gidan,ba wanda yacewa wani kala.
Shide fadil se dariya yake a cikins,dan yasan kunyace ta hana gidado magana.
Tunda suka shiga gidan fatima ta koma yar kauye,sabida tsabar haduwar gidan,haka taita binsu
abaya har zuwa falon gidan daya gaji da haduwa.
cikin saa suka samu mummyn su zaune a falon ita da husna,wacce take ya ga kanwar
mummyn.
Da faraa a fuskar mummy ta tarbi fatima,dan daga ita har mijinta ba halinsu bane wuaƙanta
mutum komai kaskancinshi.
Gidado karami iyayen kiriniya,tuni ya jima da isa gurin mummy,ya dafa kafarta yanaso ya
mike,cike da kulawa tasa hannu ta daukeshi tana masa wasa,cikin ikon Allah itama yasa hannu
ya doke mata baki.
Sosai abun yabata mamaki,bin yaron kawai take da kallo na mmakin abinda ya aykata.
Haka su gidado suka fice suka bar fatima tare d hajiya da husna wacce se hrarar fatima takeyi
ke kyace uwarta ta kashe mata.
Tuni gidado ya yi bacci akan kujerar kusa da mummy,ba abinda ya kara daurewa mummy kai se
irin yadd yake baccin.
Itade shuru kawai tayi ta barwa cikinta amman yanayin dabiun yaron da kamanninsa sun
sanyata cikin wasi wasi.
Husna mummy tas ta nunawa fatima komai gameda gidan sannan ta nuna mata dakinta.
Sosai dakin ya burgeta,dan babu abinda babu a ciki najin dadin rayuwa,abun se godiyar Allah,
Suna shiga dakin ta kwantar da gidado dake ta faman bacci,ita kuma ta shiga wanka tana
futowa kimtsawa tayi ta nufi kitchen dan fara aykin daya kawota.
Tayi komai yadda ya dace kamin wani lokaci tuni gidan ya bude da kamshi,ita kanta mummy ta
kosa agama girkin,duk da tasan fatima me girkawa su fadil abinci ce,amman tabbas itam se taci
taji,dan kamshin ya shigeta.
Fatima n gamawa ta jere komai a dan karmin falon da su fadil ke cin abinci kamar yadda aka
nuna mata.
Sabida a tsarinsu basa cin abinci a dinning table sede a kasa.
Koda suka dawo kan abincin suka sauka,inda mummy da husna ma suka mara musu baya,su
fadil se tsiya suke musu.
muje zuwa
Surbajo for life.
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€í ¼í¾€
Zahra Muhammad Mahmud
Dedicated to Amina Maman Gidado.
*13-14*
Haka fatima taci gaba da zama agidan amatsayin me aykin dafa abinci.
Sosai take jin dadin zaman gidan,sede matsalarta dayace,itace ta rashin jin gidado,
Ya iya barna kamar dan bera,tanayin iya bakin kokarinta wajen ganin ta tsawatar masa amman
a banza,kullum kamar sake ingizashi takeyi.
Halin gidado na rashin jine yasa,gidado babba ya tsaneshi,haka itama husna,ko kadan basa
kaunarshi,shiko kamar ance ya nace musu,duk wani guri da suke zama yaron ya gama
haddace gurin,
Yauma kamar kullum,gidado babba ne kwance cikin garden din gidan yana karanta jarida,yayin
da gefe daya kuma juice ne yazuba a cup time to time yana dan kurba,sosai yake enjoying,din
yanayin.
Goga na umma sarkin barna ne ya karaso gurin cikin tafiyar shi ta yaran dake koyon tafiya.
Ko kadan gidado babba beji zuwan gidado karami ba,shi ko karasawa yayi gurin da ya ajiye cup
din juice din,be bata lokaci ba,ya dauka ya fara sha,yana cikin sha abunka da yaro se ya mayar
dana bakinshi ciki,
Gaba daya na cikin cup din se yayi wani iri,shiko gidado babba,hannu ya mika kawai ya dauki
cup din yakai bakinshi yafara sha ya kusa shanyewane yafahimci dandanon lemun ya
sauya,yanzu har wani yauki yakeyi.
Yana kai dubansa cikin kofin yaga abun mamaki,burtsatsin miyau ne gashinan birjik cikin lemun
sanz din da yake sha.
A gigice yafara waige waige,carab idonshi ya sauka kan gidado karami dake zaune yana masa
dariya.
a fusace yayi kan yaron,ba kunya ba tsoron Allah ya wankeshi da marin da se da yaron ya
tintsira,.
Ayko ya tsanyare da kuka,hakan yay daidai da zuwan fatima gurin,wacce ta jima tana neman
gidadon.
Da gudu tayi kanshi,ta daukeshi,zuciyarta ta gama hassala,dan a rayuwarta ta amince ay mata
komai,amman kar ayiwa dan amanarta,
"kai wanne irin jaki ne dabba mara tausayi?"cewar fatima cike da fushi me tsanani.
A duniya ran gidado be taba baci irin na yauba,
Yana waigowa kawai se ya rufeta da duka,yana fadin.
"ubankine jakin da ya barki kina yawon gantali har kika samo wannan shegen dan naki"
."wlh *GIDADO BA SHEGE BANE* sede in ubankane shegen"cewar fatima dake kasa bakinta
na zubar da jini.
wayyo zuciyar yan maza ta motsa,haka gidado yasaki kwanji yana bugun fatima,itama ko tasaki
baki se ihu takeyi,iya karfinta.
Gaba daya ahalin gidanne sukayo garden din dan ganin abinda ke faruwa,harda mahaifin su
wanda be jima da shigowa gidanba.
Da kyar fadil da daddynsu da masu gadi suka kwaci fatima a hannun gidado.
Rai a ɓace daddynsu yace.
"Gidado kanada hankali kuwa?,taya zaka kama yar mutane kaita duka kamae kasamu jaka,ko
baiwar kace ita?,me tayi maka?"
A kaida in ran gidado ya baci ko magana beson yi,dan haka koda daddynsa ke tambayarsa be
iya bashi amsa ba.
Maida tambayar daddyn yayi gurin fatima dake durkushe tana ta faman gunjin kuka.
"ke yarinya me kika masa?"
A ranta tace.
"wlh be daki banza ba sena koya masa hankali,ta yadda ko sunana aka kira agabanshi seya
firgita"
Amman a fili sake rushewa da kuka tayi inda cikin kukan ta fara cewa.
"Ni yar katsinace,nida gidado mun hadune a airport a Abuja,inda tundaga ranar muka kulla
soyayya me karfi,sannu a hankali gidado ya fara yaudarata,harde yayi nasarar kawar min da
mutuncina,wanda tun daga ranar ya maidani tamkar matarsa, koda nai korafi alkawarin aurena
yayimin,ana hakane Allah ya bani ciki,inda iyayena suka koreni sanadin hakan har a makaranta
ma seda aka koreni,koda nazo gurinshi shima guduna yayi,cikin ikon Allah na haihu lafiya inda
na haifi wannan yaron,nasa masa suna gidado ne sabida sunan mahaifinsane,kwatsam sega
fadil yazo gurin abincinmu siyan abinci,tunda naganshi nasan naga gidado,dan sometimes
lokacin muna tare da gidadon yana nunamin hotonshi,a hakade har sukaje da kansu suka
daukoni zuwa gidannan,shine nazo yau ina masa tuni,gameda makomar danmu,shine ya rufeni
da duka"ta Karasa maganar cikin matsanancin kuka.
Gurin gaba daya ya kaure da salati,mummy rushewa tayi da kuka,yayinda