Chapter 6 Reading Gidado ba shege bane (Complete)by Princess Aysha Muhammad Saddiqa .pdf Arewa Novels

Gidado ba shege bane (Complete)by Princess Aysha Muhammad Saddiqa .pdf

Author :  Princess Aysha Muhammad Saddiqa Category :  Wattpad Hausa Novels

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 33.7K words


Da sauri ya isa gurinta,ya cafko ta.

cikin tsoro take ta yunkurin kwatar kanta,sede yaki sakinta,hakanne yasa ta dokeshi a gabanshi
wanda da sauri ya saketa,ya rike gurin.

ita kuma da gudu tayo gurina,ta rungumeni tana kuka.

Mikewa mutumin yayi yazo ya fincikota yana fadin.

"Tunda kika daki sandar girma dole kema sandar girma ta dake ki"yana kaiw nan yafara rabata
da suturar jikinta,itako se ihu take tana fadin,

"ni ku kyaleni don Allah kar ku ci mutuncina,bawan Allah ka hanasu don Allah"ta karasa
maganar tana kallona tana kuka.

Ta maza nayi na kwace yarinyar na boyeta bayana,

Ayko hakanne ya fusata su,se gani nayi sun saka rigar saukar lema,sannan sukace.

"Tunda mu ka hanamu mu kwashi gara,to kai yazama wajibi ka kwasa,in ba haka ba,zamu
kashe suran direbobin da kai da kuma ita,mu kuma mu sauka,kaga daga jirgin har mutanen ciki
sunansu konannu"

Kabir hamza ne ya shigo first class din,dan duba lafiyata,dan tuni sun buga waya,sun sanar da
cewa cikin jirgi akwai matsala.

Yana shigowa aka rutsa dashi,jikinshi se bari yake,

Gaba daya fasinjan dake cikin first class din mutum biyar ne.se ni da kuma kabeer da tsautsayi
ya shigo dashi.

Duk wata magiya babu wacce ba muyi musu ba amman sunki yarda,sunce dole sena kwanta
da wannan yarinya.

Ganin bazasu yarda bane yasa nace.

"zanyi abunda kuka bukata amman don Allah kubari a daura mana aure nida ita in yaso se inyi
abinda kuka bukata"

Da har sunki amincewa,sekuma daya daga cikinsu yace,

"mun amince,dan burinmu kawai,ashigi babynnan tunda bata da kunya"

cikin first class din akwai mutane biyu maza musulmai,da kabir na uku,jikina na bari na ciro kudi
a aljihuna wanda bansan ko nawa bane,na mikawa yarinyar amamsa tayi tana kuka,jikinta se
rawa yake.

Take kabir yay min wakilci,daya acikin musulman guda biyu na cikin gurin yayiwa yarinyar
waliyyi,dayan kuma ya daura auran,acikin abunda be wuce mintuna goma ba.

Haka suka sa na afkawa yarinyar mutane,wanda kuma nine mutum na farko daya fara tarawa
da ita,nayi kuka nayi bakin ciki,har Alƙah wadai nayi da kasancewata acikin jirgin.

Akan idonsu komai ya wakana sun rutsamu da bindigogi,se dariya sukeyi,itako yarinyar,tuni ta
sume.

A tsorace na É—agata,sede sam bata numfashi.

Suko ficewa sukayi suka barmu,hatta kabir shi kanshi kuka yakeyi.

suna fira,suka bi duk wata camera ta cikin jirgin suka kashe,sannan suka kashe fitilun cikin jirgin
duhu ya bayyana ciki sabida tafiyar dare ne.

Cikin hikima suka cire marsk din da sukasa a buskarsu da safar hannun suka kuma zubar da
bindigogin akasa,suka nemi guri suka zauna.

Cikin yardr ubangiji umar ya saukar da jirgin lafiya,a airport a uk.

Sede tuni jamian tsaro sun yiwa jirgin kawanya.

haka akai ta checking,na fasinjojin,wanda cikin yardar Ubangiji aka kama mutanen,ta hanyar
camerar da ta daukesu sanda suke saka marsk a fuskarsu a toilet na cikin jirgin.

Nide ban bi takansu ba dan sun riga da sun gama cutata,haka yan jarida sukazo kanmu nida
yarinyar da aka gunguro agadon daukar marasa lafiya,take na tsaya rai abace nace musu.

"Bana bukatar ku yada abunda ya faru dani a media,in kuma daya daga cikinku yayi yunkurin
aykata hakan wlh kotu ce zata rabamu"

ina kaiwa nan nabar gurin,da yake kasace datasan hakkin dan adam,take suka gige rohoto
akaina da matata ta cikin jirgi.

Asibiti aka kaita,duk wani taimako daya dace su bata shi suka bata.

Ta farfado inda na taimaka mata tayi wanka,se kuka takeyi,tana share hawaye.

Wasa wasa seda mukayi kwana uku a sibitin ni nake kulawa da ita, a rana ta ukunne ta warke
sosai.

inda na bukaci ta sanar dani sunanta da kasar data fito.

Murmushi kawai tayi tace min.

"Kai ya sunanka daga wacce kasa ka fito?"

"Gidado sunana daga nigeria"

"Gidado"ta maimaita sunan,se kuma tayi shuru.

Duk yadda naso nasan wacece ita fafur taki yarda,daga karshe kuka tasamin dole na kyaleta.

Washe gari likita ya sallameta,dakaina na daukota a mota,inda nakaita gidanmu nida fadil,na
gabatar wa fadil ita amatsayin sabuwar maaikaciyarmu ce a kamfanin etihad,zata kwanane
gobe zata wuce masaukinta.

Sosai fadil ya karramata,har zuwa washegari dana É—auketa zan kaita masaukinta,sede fafur taki
amincewa wai sede na ajiyeta a bus stop ta hau bus.

Bayan na kaita bus stop dinne harta bude murfin motar seta juyo gareni tana murmushi ta kama
hannuna tasamin wani zobe tace.

"na bakane dan wata rana ka tuno kataba yin aure na tsawon kwanaki hudu a rayuwarka,"

Shuru nayi kawai ina kallonta,sam na kasa mgn.

wayarta ta ciro ta dora kanta akan kafadata ta daukemu hoto kala kala.

sannan tace.

"To gidado muna shirin rabuwa amman baka sake niba ko so kake naita yawo da auranka?"

Haka kawai naji banson rabuwa da ita,amman tunda ta matsa haka na saketa saki daya,na bata
kudi masu yawa,sannan mukai sallama nida uta muka rabu wanda har yanzu ban sake ganin ta
ba.

To se yanzu na lura da kyau da kamannin gidado karami wlh murmushinshi irin natane haka ma
kukansa,duk irin natane.

Tunda haka ta faru nakasa samun natsuwa a zuciyata hakanne yasa nadunga sadaka da rokon
Allah akan ya mantar dani duk abin da ya faru domin na zauna lafiya,

Allah ya amshi addua ta inda koda wasa ban taba tuno abun ba,
Bayyanar gida
do a matsayin danane yasa naci gaba da rokon Allah ya bayyana min gaskiya,to shine jiya nayi
mafarkin yarinya wanda hakanne yasa na tuno komai da ya faru.

ya karasa basu labarin cikin kuka.

Kowa na É—alon kukan yakeyi,dan tsananin tausayin su.

Sede kuma kowa yashiga mamaki gami da rudu,tun da gidado yace gidado karami na kama da
matarsa ta jirgi to ita kuma fatima ya take da yaron?

muje zuwa.

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*GIDADO BA SHEGE*
*BANE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra muhammad mahmud

*i really sorry masoyana don Allah kuyi hakuri da barinku da nayi jiya idonane ya fara ciwo
shiyasa*

*Dedicated to Amina Maman Gidado*

*33-34*

Falon ne yayi tsit sabida kowa ya tafi tunani,se zuwa can daddy yace.

"munji bayaninka kuma mun gamsu,dashi,Allah ya bayyana wannan yarinya dan musan abinda
ya shige mana duhu"

Kowa haka ya dunga jajantawa gidado.

"muna so fatima tai mana bayanin inda tasamu wannan yaro"cewar mummy.

Ayko ba musu,cikin kuka fatima ta kwashe komai da ya faru ta shaida musu.

Sosai suka tausaya mata,gamida yimata jajen rasuwar mahaifiyarta.

"Ya kamata Ka shirya ka koma gurin aykinka da iyalinka,hutun ya isa haka"cewar daddy yana
kallon gidado.

Kukan husnane ya maida hankalinsu kanta,inda cikin kukan taje ta kama kafar daddy tana
fadin.

"Daddy son bross ze kasheni,don Allah kasa gidado ya aureni,wlh ina sonshi,kuma na fada
masa yaki amincewa dani,don Allah kataimakamin wlh zan kashe kaina in be aureni ba"ta

karasa maganar cikin matsanancin kuka.

Kowa mamakin maganar yakeyi,su fatima ko iyayen kishi,tuni maganar ta kawo mata wuyanta,

gidado ranshi ne ya baci da abinda husnar tai mishi agaban mahaifansa.

murmushi daddy yayi,sannan yasa hannu ya dago husnar yana dariya yace.

"yanzu ke akan yayan naki kike kuka?to share hawayenki,tunda kin tabbatar da kina sonshi,zan
aura miki shi"

A razane gidado ya É—ago yana duban daddy,bakinshi har rawa yake yace.

"daddy.."dakatar dashi daddyn yayi sannan yaci gaba da cewa.

"Sati me zuwa zaa daura auranku,in yaso sati na sama se ku tafi uk din duka na gama magana"

"Alhaji bafa a yiwa namiji auran dole,taya zaka aura masa abinda baya so,don Allah kabar
maganar nan,don Allah"cewar mummy cikin damuwa.

"na gama magana nace"cewar daddy,daya mike yabar gurin,dauke da jikansa.

Hannu gidado ya dora akai kamar zeyi kuka,dan bakin ciki,itako husna harda rawarta ta mike
tabar gurin.

Fatima tafi kowa shiga damuwa cikin lamarin,da kyar ta iya mikewa ta nufi dakinta.

Tana shiga ta fada kan gadonta tana kuka.

"Wanne iein son kai ne wannan,aure ko tarewa ban yiba acw anmin kishiya,na shiga uku ni
fati,wlh bazan iya zama da kishiyaba,musamman husna da bata kaunata"

Sune zantikan dake fitowa daga bakin fatima tana kuka.

A falo ko mummy da fadil ne suka sa gidado a gaba suna bashi hakuri,dan zuwa lokacin tuni ya
fara kuka,dan yasan mahaifinsa kaifi dayane,baya sauya magana.

Dakyar suka samu yayi shuru,mikewa yayi yabi bayan fatima,yana shiga dakin ya jingina da
kofar yana kallon yadda take kuka,abun na taba zuciyarshi,dan yasan tabbas baa mata adalci
ba.

Takawa yayi a hankali ya isa inda take,kamota yayi ya rungume,a jikinshi,cike da masifa fatima
ta shiga kwace jikinta,tana fadin.

"sake ni mayaudari kawai,ay dama na jima da sanin baka sona,jikina kakeso,dama can husna
kakeso shiyasa ka kasa yiwa daddy bayani akan baka sonta"taci gaba da yin kukanta.

Dafe kai gidado yayi,zuciyarshi na mishi kuna,se yanzu ya yarda tabbas mata nada kishi,dan
maganganun fatima sun sosa ranshi.

"princess don Allah ki saurareni,wlh babu soyayya tsakanina da husna,ko kadan bana sonta pls
karkimin haka don Allah,"

"baka da abun fadamin na yarda,dama tashi kayi ka ficemin daga daki,tun kamin arubuta
sunanka ajerin makaryata,dan komai ze fito daga bakinka karya ce"cewar fatima tana kuka.

Ganin bazata saurareshi bane yasa ya mike ya fice daga É—akin.

kifewa tayi taci gaba da kukanta,dan fatima macece me kishi me zafi,har addua take akan Allah
ya yaye mata.

Gidado ya rasa inda zesa rayuwarsa ga auran dole gashi fatima na fushi dashi,

a haka har lokacin da majaufinsa ya diba yayi aka daura auransa da husna,auran daya samu
hallarta mutane da dama.

inda shagali sosai akayi,na auran,fatima a É—aki ta rufe kanta dan gani take wani abunma da
biyu ake mata shi.

Bayan angama taro kowa ya watse, ne ta bude kofar,zuwa lokacin kowa ya ganta ze dauka ta
shekara ne tana ciwo sabida fita hayyacinta da tayi.

Mummy sosai take tausayawa fatima,sede duk son da take mata bekai wanda takewa husna
ba,dan husna jininta ce.

gidado ko ba baka se kunne,duk yabi ya susuce sekace ba ango ba,damuwarshi kawai fatima
da taki yarda su hadu.

Husna farincikin da take ciki abun be misaltuwa,dan ta cika burinta,na mallakae gidado,saura ta
rabashi da fatima.

Daddy ne ya tarasu yay musu waazi dukansu akan su zauna lafiya,

inda yaja kunnen gidado akan yayi adalci a tsakanin matanshi.

A haka akayimusu visa dukansu,harda gidado karami,inda mummy ta basu daya daga cikin

masu aykinta,dan ta dunga kula da gidado karami,me suna *Ligido*

Ligido sanda taji da ita amasu tafiya uk,har kusan suma tayi,dan farin ciki,

Kamin su tafi daddy yasa angyara daya daga cikin sauran gidajensa na uk,an zubawa kowacce
kayan daki na gani na fada,abun se wanda ya gani.

Ranar tafiya,haka suka rankaya,zuwa airport,jirginsu ya daga se uk.

Kuyi hakuri da wannan pls.

muje zuwa

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*GIDADO BA SHEGE*
*BANE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


Zahra muhammad mahmud


*Dedicated to Amina Maman Gidado*


*35-36*


*UK*


Sun isa da safe,kowa cikinsu ya gaji,gidado karami,tuni yayi bacci.

Husna se wani langabewa take acikin gidado,ita ga me miji.

A haka suka nufi motar da tazo daukarsu,da sauri fatima ta bude gaba ta shiga.

Husna da ligido da gidado suka shiga baya,sam gidado beji daÉ—in abinda tai masa ba,amman
ya cinye be nuna mata ba.

Koda suka isa gidama haka,inda yace fatima ta zabi bangarenta,ta tsaya bakin kishinta wai se
ta ja aji ta zaba.

Ganin haka ne yasa husna cewa.


"Bross nide fitsari nakeji,dan haka ni nazabi cancan dan bazan iya jiraba"tana kaiwa nan ta nufi
wanda yafi kusa dana gidadon,wanda a zuciyar fatima shi take da burin zaba,amman bakin
kishi yasa tai nauyin baki.

Gidado be hana husna ba,sabida ta fisu gaskiya,bakin ciki ne yasa fatima ta samu guri a falon
ta zauna,rai a bace.

Ligido ma tuni ta nemi dakin ta ta shige,rike da gidado karami.

Gidado bin fatima yayi da kallo,wacce bata ma san yana yiba,ta cika ta tumbatsa,kawai.

Wucewa yayi shima dakinshi,dan ya lura fushi take sosai.

Tsawon awanni kowa yayi a dakinsa yana hutawa,amman banda fatima da kishi ya
dabaibayeta,ya hanata motsawa.

Tana nan zaune a falon har yamma tayi bata tashi ba,gidado ne ya fito,da nufin zuwa ya dubota.

turus yayi yana binta da ido sanda ya sameta zaune a falon kamar yadda ya barta.

Karasawa yayi gurinta ya tsuguna,ya dora hannayensa akan cinyarta,ya langabar dakai,kamar
me shirin yin kuka yace a tausashe.

"princess nine fa,meyasa kike azabtar dani da fushinki,akan laifin da ba nawa ba?don Allah kiyi
hakuri,ki taso muje daki,pls"yayi maganar kamar zeyi kuka.

Harara fatima ta watsa masa,sannan ta ture hannunsa akan cinyarta,tace rai abace

"a kanka nake zaune da zaka zo ka sani a gaba akan se na tashi,?to babu inda zani"ta karasa
maganar cikin murguda masa baki.

Murmushi yayi ya mike,ya tattare hannun rigarshi.tuni tsoro ya bayyana akan fuskar fatima ta
fara ja da baya,tana fadin.

"To me nayi maka kuma da zaka dakeni?"É—mdan ita duk zatonta dukanta zeyi.

Dariya yayi mara sauti sannan ya karasa inda ta rakube,yasa hannu ya dauketa cak,ya nufi
dakin ta da ita.

Suna shiga ya sauketa ya janyota jikinshi yace.

"Kina abu se kace yarinya,bakisan kina da kishiya bane a gidan,mata fa basaso kishiyarsu
tasan tsakaninsu da mijinsu,amman ke kin zauna a falo se zuba kikeyi"ya fadi yana jan
hancinta.

Kuka tasa mishi,gamida doke hannun shi daya ja mata hancin,tace cikin kukan.

"Ay dole kacemin hakan,tunda yanzu kayi amarya,kuma yar uwarka,ba dole kaita rawar kafa
ba,nide wlh bazan zauna adakin nan ba,ko de ka bani naka ko kuma ka maidani nigeria,inci
gaba da sanaata ta saida abinci"

Dariya ce ta kubcewa gidado,ayko yashiga kyalkyalata harda kwanciya a kasa.

Fatima tsayawa tayi tana duban jikinta dan taga abinda yakewa dariyar amman bata gani
ba,nufarshi tayi tana duka tana fadin.

"wato ga mahaukaciya ko,wlh da gaske nake yi,sena koma seda abinci abakin titi wlh"

Janta yayi ta fada jikinshi,zatayi magana ya hade bakinsu guri guda ya shiga ayka mata
sako,tuni ta mance da bacin ranta,seda taji ze zarce ne ta kwace kanta tana haki.

Bin ta da ido gidado yayi,dan amatse yake,sosai amman alkawari ya dauka baze kusanceta ba
se lokacin da taso dan kanta.

"wlh bazan zauna a dakin nan ba"muryar fatima ta doki kunnenshi.

Mikewa yayi da kyar,yace mata.

"duk yadda kikeso hakan zaayi gimbiyata,muje na rakaki dakin nawa"ya fadi gamida ruko
hannunta,ba musu ta bishi zuwa dakin nashi.

Dakin har yagaji da haduwa,dan yafi nasu kyau nesa ba kusa ba,duk wani abun more rayuwa
yana ciki.

Tunda suka shiga dakin fatima take dariya,dan tasan ta cutawa husna,kuma tana da tabbacin
ranta se ya baci in taga gidado ya bar mata dakinshi.

Gidado ganin fatima na dariya ne yasa yaji sanyi a ranshi,dan ya lura tayi farinciki da bata dakin
da yayi.

Ficewa yayi,da jakar kayanshi,zuwa wancan dayan dakin,sannan ita kuma yakai mata nata
dakinta.

Wanka ta shiga,wanda ta jima tana kyalkyale jikinta,bayan ta fitone,ta zauna gaban mirror ta
fara tsara kwalliyar da tunda take bata taba yin irinra ba.

"Masha Allah",ta furta a hankali,sanda ta kalli kanta a mudubi taga yadda tayi kyau.


Gurin zabar kayan da zata sakane,ta tsaya ruwan ido,harde idonta ya sauka akan wasu riga da
wando pink da fari,wandon three Quater,yayinda rigar ko cibiyarta bata gama rufewa ba,gashin
kanta,raba shi tayi gida biyu,ta kama da farin ribon,se ta koma kamar wata yar baby,

bin jikinta tayi da kallo.

Fatima farace amman ta sirka da ja,hakan yabata damar yin kyau dan gaske,ita ba doguwa
bace sannan ba gajera bace,wato medium size,tana da shafaffen ciki kuma tsukakke,yayinda
kugunta kuma yake da fadi wato tana da hips masu kyan tsari,wanda koya ta motsa suma
sesun motsa,kirjinta cike yake da na shanu,fuskarta cycle ce me dauke da dogon ganci me
kyan tsari,tana da dan karamin baki,da labba masu dan tudu,ga sexy eyes da Allah ya
bata,koya ta motsa bakinta dimple dinta se ya bayyana,ga yar siririyar hushiryar dake tsakanin
kyawawan hakoranta,tana da bakin gashi,me santsi da sheki,gashi me tsayi har gadon bayanta.
Kai abunde se wanda ya gani.nana fatima Abubakar Radda kenan jinin katsinawa yarinya me
jini acika bafulatanar usuli.

tsaya tayi gaban mirror tana ci gaba da kallon kanta tana godewa Allah.

Anata bangaren husna ma nacan tana kure adaka,ansha wankan riga da siket
matsatstsu,masu kyan gaske,baki da fari,ba laifi husna ma akwai kyau,sede koda wasa bazaa
hadata da fatima ba,da diri da komai fatima ta fita.

feshe jikinta tayi da turaruka kalakala,sannan tasa takalmi,ta fito zuwa,dakin gidado,wanda
batasan yanzu ya koma na princess dinsa ba.



muje zuwa


Surbajo for life.
[11/18, 07:57] Jamiela D Ilyasu: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*GID'AD'O BA SHEGE*
*BANE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

*Dedicated to Amina maman gidado*


*37-38*


Cikin takun daukar hankali,husna ta isa bakin kofar dakin,

Nucking tayi,wanda yasa fatima dake ciki,takowa,cikin izza da isa,tazo bude kofar dakin.

Kallon kallo suke yiwa juna,kuma kowaccen su ranta ya baci da ganin yar uwarta.

Tun kan fatima tai magana,husna ta rabe ta jikinta ta shige cikin dakin tana tsaki,fatima harde
hannu tayi a kirji tabi bayanta da kallo.

Ko ina a falon babu inda husna bata leka neman gidado ba,amman bata ganshi ba,dan haka
hanyar bedroom ta nufa.

Da sauri fatima tasha gabanta ta hanata shigar mata daki gami da cewa.

"Rainin wayon naki naso

6 / 12