Author : Fatima Abdullahi Category : Hausa Novels 001
sami Fadeela a matsayin K`AWAR SU
suka yaba da kokarinta amma daga karshe suka dena makarantar suka kama harkarsu yayin da kuma suka sami Ruma wanda tun asali Karuwa ce
ta taso cikin wata karamar hukuma dake jahar kano ta bayyana musu mahaifinta yana raye , amma yayan mahaifinta shi ke juya komai nashi , ya hanata karatu azzalumi ne shi kuma babansu yana masa biyayya saboda hakurinshi ,
a karshe yayan babanta ya tilasta mata kan sai ya yi amfani da ita ,
Ruma tace ga garinku nan ta baro masa garin ta tsinci kanta a wannan hali .
Nan suka saba komai nasu tare , ita kuma Fadeela ta kasa rabuwa dasu πππ
tana ganin nasiharta zata tai make su a rayuwa , ta yi dasu ma su koma gidajen iyayensu amma sun ki , haka dai suka ji suka gani zasi rayuwarsu.
DA Aminu da Inna ne cikin gidansu Fadeela bayansun gama gaisawa Aminu ya mik`a wa Inna takardun gidan da suke zaune mallakin Fadeela suna cikin hirarsu Fadeela ta shigo cikin babban shigabi
har kasa ta kai ta gaida baba Aminu ya amsa cikin girmamawa
"to Fadeela ga takardun gidan " Inna ta fad`a tana mik`a mata
Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Inna ki aje a gun ki",
Inna ta maida takardun jikinta tana adanawa.
Baba Aminu ne yace ," yawwa Inna ,
ya maganar Zakariyya da Fadeela
domin yaron nan jininmu ne kuma yana san Fadeela ",
Fadeela ta murtike fuska tana kallon Inna
Inna ba tare data kula da yanayin Fadeela ba ta fara magana ," to Aminu yanzu dai Fadeela tana karatu a bari idan ta kammala sai ai maganar domin shi ne burin mahaifinta, Allah ya jik`anshi",
"amma ni Inna bana san Zakariyya fa ",
Fadeela ta yi maganar tana durkusar da kai
", to wa kike so ba za ki samu sama da Zakariyya ba , bazan zauna na zuba miki ido ba kina girma kina yawo da Karuwai har ki ja mana abin kunya ", Inna ta aje maganar cikin haushi tare da sake fad`in
," zamu zauna a kan wannan maganar Aminu in yaso tayi auren taci gaba da karatun",
wani bakin ciki Fadeela taji ya tokare mata zuciya.π
Yanzu dare ne wajen karfe goma Ruma da Fadeela ne tsaye bakin titi ga dukkan alamu abin hawa suke jira
babu jimawa wasu motoci fara da blue sukai parking a gabansu,
Farida tsaki tai kawai tana kallon mai tuk`a blue mota tana haraararshi tare kuma da bud`e kofar ta shige suka tafi
Ruma ma farar motar ta nufa tana dariya mai motar ne shi ma cikin murmushi yace ,"yau dai wannan murmushin ya tabbatar mini zan huta akwai tanadin da akai mini",
ba tare da tace komai ba ta shige motar tana masa wani kallon bariki ,"yau hotel nake san zuwa",
murmushi ya sake yi yana cewa, "yanzu kuwa hajjiyata",
ya tuk`a motar suka nufi hotel nan daga zuwansu suka ringa tanbad`arsu da iskancinsu niko nace ba a yi a gabanmu ba ππππ.
" wai dan Allah Fadeela me yasa kike yiwa Zakariyya haka ne",? Zainab ta fad`a ranta a b`ace
ita ma Fadeela kallonta ta yi rik`e da wayarta a hannu tana cewa, "wallahi Zainab na tsani Zakariyya, bana san shi fiye da tunaninki",
Zainab ta rik`e hab`a tana cewa," ikon Allah!
Yanzu mene ne abin gudu wajensa Fadeela ",?Fadeela wani murmushi tayi tana cewa," duk abin da zai rabani da su Ummi baby bana kaunarshi, amma shi Zakariyya yana kiran kanshi ustaz amma ya kasa gane wannan irin jahadin da nake , kullum sai wa'azi Allah ya ce, malam wa ne ya ce , gaskiya ni bazan iya auren Zakariyya ba",
da babbar murya mai cike da mamaki Zainab tace ,"tab!
Yaushe kika koma haka Fadeela? gaskiya zamanki da karuwai bai amfane ki da komai ba , kin bani mamaki",
Fadeela na kokarin maida mata da martani taji wayarta ta fara ruri ,
ganin wanda ke kiran wayar yasa murmushi da far'a suka bayyana a fuskarta,
"wannan kai ne babban burin da nake so mallaka a rayuwa", Fadeela ta fad`a cikin shauk`i
dajin zanen Zainab tasan cewa Aliyyu ne ke kiranta .
Bayan wasu kwanaki
Zainab da Fadeela ne zaune cikin ajinsu fuskar Zainab murtike
ita kuwa Fadeela sumul sai shauk`i take domin tana sauraran zuwansu Ummi baby zasu kawo mata ziyara
ganin kiran wayar Ruma ne ya tabbatar wa Fadeela sun iso , hakan yasa ta kalli Zainab tana cewa," mu je mana Zainab ",
ba tare da Zainab ta kalli inda Fadeela take ba tace da ita ," ba inda zani , a dawo lafiya kije ki tsaya dasu students suna muki wani kallo", kawai Zainab ta yi tsaki ta fice
Fadeela ta fice ita ma tare da nufar inda take da tabbacin za ta ga su Ruma , tana isa suka rungume juna suna murna
"Aliyyu yace duk yana gashsheku ", Fadeela ta fad`a musu cikin girmamawa
" a'a gaskiya ba ma amsawa , kullum sai gaisuwa ya kasa zuwa a gaisa",Farida tayi maganar cikin ya tsine fuska ,
yayin da Ruma ta ce,"ai kuwa dai",
Fadeela tayi murmushi tana kallon hagu da damanta yayin data kula idanun wasu d`aluban a kansu yake, ba tare da yanayinta ya canza ba ta sake kallonsu tana cewa, "to naji insha Allah zaku gaisa da shi ,
amma ni bama wannan ba , yau idan na koma gida zan yi tafiya",
" toooooooo"π― Ummi baby ta fad`a
ba tare da Fadeela ta jira sun tambayi k`arin bayani ba ta sake cewa,"zani biki kwana biyu zan yi na dawo",
jin wayarta ta fara ringin yasa ta saurin cirowa wayar a rigarta mai tafe da aljihu , kallon fuskar wayar tayi ta saki dogon tsaki π
yayin dasu Ruma suka kalli juna lokaci guda kuma suna shirin jefa mata tambaya.
share and commentπK`AWAR KARUWAI πππ
BY
AUTAR MARUBUTA
_____________________________________
page 7&8
"mene ne hakan kuma, wake kira ",?
Ruma ta tambaya , Fadeela cikin yatsine fuska tace ," wallahi Zakariyya ne ",ta aje maganar tana ajiyar zuciya sake kallonsu tai tana cewa," bari nai shirin komawa gida domin kar nai dare",
Farida tace, "eh haka ne , mu ma bari mu koma",
a lokacin Amina Umar tazo wuce wa ita da wasu k`awayenta
yayin da take kallonsu Fadeela tana cewa," abokin b`arawo dai b`arawo ne , ato a fito kawai a ce anason karuwanci ", tana aje maganar sauran k`awayenta suka shek`e da dariya , suka wuce abin su
ajiyar zuciya Fadeela ta sake yi tana kallonsu cikin rashin jin dad`
yayin da wayar Ruma ta fara ringin , hakan yasa kowannensu bai ce komai ba ya maida hankali kan Ruma ,
Ruma murmushi tayi tana kallon fuskar wayar lokaci guda kuma tana cewa dasu ," Mubarak ne nasan akwai harka yau ",
wayar ta kara a kunne tana cewa," bani nasha mutumin ",π
daga can bangaren aka ce ," Ruma akwai wani Alaji yana hanyar zuwa kano yau , kuma zaki debe masa kewa , amma bari zami magana anjuma ",
tace ," ok ",
yayin da ya kashe wayar
" harka tazo ko",?Ummi baby ta jefa mata tambayar
d`aga mata gira Ruma tayi alamun eh,
Fadeela kawai ta zuba musu idanu .
Bayan Fadeela ta koma gida sukai sallama da Inna , nan Inna ta bawa Fadeela sak`o wanda zata kaiwa k`awar Fadeela da zata bikinta , bayan Fadeela tasa k`afa ta fice duk jikin Inna ya yi sanyi ya mutu .π
daga cikin adai-daita Ruma ta fito yayin da ta dubi babban gidan da akai parking d`in ta a kofar, taku ta farayi tana dosar gidan tare da duban girmanshi , harta shiga cikin falo ,
tsayawa ta kuma yi tana duban falon tana murmushi da jin dad`in yadda iska mai sanyi ke ratsata ,
ba tare da ta ankara ba taji ana kokarin kissing d`in ta,
da sauri ta juya tana kallon waye ,
gajeren wando kawai yasa , ba bak`i ba ne can yana da suma a kanshi mai kimanin shekaru 40
ajiyar zuciya tai tana cewa, "haba Alaji! Ai saika sa na tsorata , ko ciniki ba ai ba kake kokarin cin gyara",
murmushi yayi yana kallon ta sama da kasa ," haba baby nifa cikakken d`an bariki ne , kuma nasan farashinki, shi yasa na fara abin da ya kawoni",
ya matsa kusa da Ruma ya rik`e hab`arta yana cewa, "karki nunamin kin fini bariki domin zaki sha wahala , ba a maneji dani kad`an daga cikin mata ne ke dawowa gare ni bayan munsan juna",
duk Farida jin shi take domin ko tsoro bata ji ba a cikin ranta tace," baka san wace Ruma ba ",
Zainab ce zaune a falon gidansu ta kara waya a kunne
ga dukkan alamu waya take , daga can bangaren aka ce,
" wallahi Zainab, sam Fadeela bata sona , amma ni ina tausayin Fadeela, domin nayi alwashin share mata hawayenta na rashin iyaye amma sam tak`i bani had`in kai ",
ajiyar zuciya Zainab tayi cikin muryar tausasawa tana cewa," ka yi hakuri Zakariyya, wallahi kullum ina fad`a mata wannan, amma insha Allah wata rana zata gane ",
Zakariyya yace ," to Allah yasa Zainab, yasu umma da yaran",
Zainab ta bashi amsa tana cewa, "wallahi lafyar kalau,"
yace "to Masha Allah aunty Zainab a gashshe mini dasu sosai",
Zainab ta d`anyi jimm sannan tace ,
" uhumm aunty kuma "?
Zakariyya yace ," eh mana bama wannan ba bani labari",
abin ya sake ba Zainab mamaki tunani tai to kodai ya zata da Fadeela yake magana ne , domin ya tab`a fad`a cewa muryarsu iri d`aya ce .
Ni kam nace ohoπ
a rungume take jikinshi yana bin laushin fatarta yana shafawa da gani babu tambaya wanka sukai , yadda yake jin laushin fatarta yasa yake yawo da hannunshi ko'ina cikin jikinta
,"I love you Ummi baby ", ambassador ya fad`a yana murmushi
" gaskiya babu ta biyunki cikin mata , ban ga wacce ta kama farcen ki ba",
Ummi baby tai tsaki ta mike tare da sake tamke towel din dake jikinta ,
kallonta ya yi yana cewa, "mene hakan",
fari tayi da ido tana cewa," dad`in baki ambassador, duk matan da kake nema haka kake fad`a musu , sannan kuma karka mance akwai alkawarin aure da kai mini",
murmushi ya yi yana mikewa ya sake kanannad`ota jikinsa yana cewa, "haba baby a kan wannan zaki b`ata ranki, to yi hakuri ki murmushi",
baki ta sake tab`emai tana cewa," to idan da gaske ne ka fito mi auren",
"haba Ummi kinsan yanzu abubuwa sun cakud`e, amma komai yana daidaita zami aure",
cikin shagwaba tana girgiza jikinta tace ", to shi ke nan",
ambassador ya fara bin kamshin jikinta yana shaka tare da ajiyar zuciya,
kai ambassador ko maye ko kadan baya gajiya da kusantar Ummi baby.π
Yanzu wajen karfe 11:20 na dare , amma Farida tana tsaye bakin titi tana neman abin hawa , har da 40 tayi amma babu wani abun hawa da ya tsaya da nufin d`aukarta .
Daidai da lokacin da tai ajiyar zuciya wata farar mota tai parking a gefenta
ko kallan motar bata yi ba sakamakon wani huci da take , sanadi kuwa Alaji Nuhu ne ya b`ata mata rai tunda ta baro gidanshi yake ta kiranta a waya harta gaji ta kashe wayar, wani mahaukacin mutum ne Alaji Nuhu da sam ba ya da hakuri a kan abin da ya keso.
" yan mata lafiya kuwa",
saurayin dake cikin motar ya zuro kanshi yana fad`a
dogon tsaki taja tana sake kau da kanta
"yan mata bai dace ba kina mace ,amma kina waje a irin wannan lokacin , ki shigo na rage muki hanya",
Farida ta kalli saurayin wanda lokaci guda taji ya kwanta mata tayi murmushin takaici tana cewa," a'a na gode",
rufe bakinta ke nan motar Alaji Nuhu tayi parking
duk hankalinsu ya karkata wajen , da sauri ya fito yana cewa, "ni zakiwa haka farida? to wallahi baki isa ba,
yau ina san kwana dake kuma ina yunwarki dole ki bani hak`k`ina",π
saurayin dake cikin motar ya saki baki cikin ranshi yake cewa", a she matar aure ce , amma wannan mijin nata ba shi da hankali",
Farida ta sake kicin-kicin da fuska cikin isa ta fara cewa.
share and comment.... my fans
K`AWAR KARUWAIπππ
BY
FATIMA ABDALLAH KANO
(Autar marubuta)
____________________________________
Page 9&10
"wallahi Alaji Nuhu ka kiyaye ni , dube ka shirgege da kai amma neman mata kamar jaraba , to wallahi ko mutuwa zakai saidai ka mutu amma ni bazan sake mu'amala da kai ba",
Alaji Nuhu cikin rad`adin abin yace ," wallahi kin yi karya farida kizo mu wuce kije ki sauke nauyin dake kanki tunkan raina ya b`aci wallahi ",
Farida kawai ta bud`e kofar motar wannan saurayin ta shige , shi kuwa saurayin ganin yadda Alaji Nuhu yake zak`ewa yasa shi saurin jan motarshi ya tafi , Alaji Nuhu yabi motar da magana yana cewa," zama ki dawo ki sameni tunda kike mini shocking d`in da ba macen da ta iya wallahi sai kin dawo , ai ba hauka ake ba",
ya koma motarshi cikin huci .
saurayin tuk`a motar yake yana satar kallon farida a fakaice , zuwa can ne kuma ya fara cewa ,"ki yi hakuri ke irin kaddararki ke nan",
Farida tayi shiru
jin hakan yasa saurayin sake fad`in, "mijinki ne ko",?
Lokaci guda Farida ta kece da dariya π
murmushi ya yi yana sake kallonta ," haba mene ne abin dariya",
Farida tace ,"Hmmm
amma ka bani dariya in rasa wanda zan aura sai wancan bagidajen mutumin, to ka b`ude kunnuwanka da kyau kaji , suna na Farida kuma ni Karuwai ce , abin dana fito yi ke nan ",
cak ya tsayar da motar ya tsaya yana kallonta,
" karuwa kuma",ya fad`a cikin mamaki
Farida had`e rai tayi tana cewa, "oho kana shakka ke nan to wacce macen tarbiya ce zaka ganta a titi yanzu? ai sai mu ",
ba tare da ta jira abin da zaice ba ta bud`e kofar zata fita ," tom ni zan wuce na gode da taimako",
mutuwar zaune yayi yana binta da kallo harta tsallaka titin ta shiga gidansu,
yay ajiyar zuciya.
Anan gidan Inna kuwa baba Aminu ne da matarshi suka kawowa Inna ziyara nan suka sha hira sosai .
tafiya suke cikin mota yana mata wani kallo
Fadeela saidai kawai ta kalleshi tace "uhum",
magidanci ne sanye da shadda jaah yake tuk`a motar ," zan yi kewarki Fadeela dan ma Allah yasa nima zan kwana biyu a kanon da bansan ya zan yi ba",
Fadeela cikin kunya ta kalleshi tace "haba Alaji sani ai naga ba wani shakuwa mukai ba",
" keeeeeeeeh",Alaji Sani ya fad`a
"soyayya ke nan , cikin kwana biyu kin mamaye zuciya, gaskiya Fadeela ina sanki",
kallon shi tai ta rufe fuska tana cewa," har kasa naji kunya",
Alaji Sani ya yi murmushi yayin da ya yi parking kofar gidansu Fadeela
"har naji wata kasala da mutuwar jiki ya kamani , bana san na barki Fadeela",
ya fad`a yana kallonta
ajiyar zuciya tayi lokaci guda tana kallon kofar gidansu tana cewa," to ni dai bari na shiga domin na gaji sosai",
yace ,"to shi ke nan sarauniyata ki gashshe mini da Inna kafin nazo",
Fadeela ta fice tana masa bye -bye yayin da ya murza kan motarshi yay gaba
to ni ko nace zan ga yadda Fadeela zata kai Aliyyu da Zakariyya da Alaji mansur ga kuma Alaji Saniπ
Inna tayi murnan dawowar Fadeela sosai musamman yadda take korafin gida ita 1
"kai duniya ambassador jarababbe ne", Ummi baby ta fad`a tana rike da kugunta tana kallon madubi
dariya Farida ta kwashe da ita tana cewa", hhhh dan Allah Ummi baby kije wajen Alaji Nuhu nan ne zakiga masifar jaraba , wallahi Ummi baby ko Alaji Nuhu zai mutu ya dena kusantata",
" wai ke farida ba kye yafiya ne tun da ya fad`a miki wannan maganar fa kika tsane shi",
Ruma ta kwashe da dariya tana cewa...
yanzu wajen karfe ukun asuba Fadeela ta fito daga wanka , b`urun-b`urun din ta ne ya tada Inna zaune tana tsaki
"Allah ya yaye miki wannan wankan daren, ace kullum ta Allah saikin tashi irin wannan lokacin kina wanka",π
Fadeela tai ajiyar zuciya wanda jikinta duk a ma ce ta kalli Inna tana cewa," ki yi hakuri Inna wallahi na saba idan ban yi ba jikina ciwo yake",
"to shi ne kuma sai dare abin ya fara damuna kuma na fara jin tsoro ,
haka mahaifinki fa ya ringa yi kullum wanka a rana sai yay wanka sau nawa , a karshe likita yace mana yana da kansa haka ya mutu muna gani",
Fadeela ta fad`i jikin Inna tana kukaπ
" Inna na tuna Abbana , yana fadan kullum cewa yanzu ake yi anjuma sai labari,
duk lokacin da ya fad`a dariya nake mai ",
Inna ta fara rarrashin Fadeela cikin karyayyar zuciyaπ
DA sauri baba Aminu ya farka a bacci yana cewa," Jamila ina jaririn yana ina , bani shi bani shi Jamila",
hakan yasa matar shi Jamila saurin tashi tana cewa, "lafiya Aminu ?wanne jariri",?
baba Aminu yay ajiyar zuciya yana cewa ," yi hakuri Jamila wallahi mafarki nayi mun haifi jariri",
Jamila tace ,"Hmmm "
Fadeela ce tsaye kofar gidansu Ummi baby ita da muradinta Aliyyu
wayarta ta dauka ta kira Ruma "Hello Ruma muna waje fa",
Ruma tace ," to ki shigo da shi mana ai kinsan bama shakkar maza ko",
"ke dallah dakata mini , aka ce miki shi kwarto ne ko me? idan zaku fito ku fito ko mu tafi",
Ruma tai ajiyar zuciya ta kashe wayar
Aliyyu yay murmushi yana cewa," Fadeela ta ke nan , sai kin yi hakuri kuma duk gudun mawar da kike so daga guri da ya shafi shiryuwarsu zan baki",
murmushi tayi tana cewa, "na gode",
Farida ce ta fara fitowa, sa'ilin da Ummi baby ta biyo bayanta sannan Ruma
Aliyyu bin su yake da kallo cikin ranshi yake mamaki wai Karuwai neππππ
" Aliyyun Fadeela ya kake ya shagali",
Farida ta fad`a
murmushi yay yana cewa, "Alhamdulillah fatan kuna lafiya",
Ruma tace", lafiya kalau mu ke",
nan suka ringa hira ana wasa da dariya har cikin hikima Aliyyu ke sake Jan hankalinsu a kan kudirin Fadeela, inda su kuwa suke shek`e mai da dariya.
su Ruma manyan 'yan duniya ne , niko zanga yadda zasu dawo kan hanyaπ
Bayan Fadeela ta dawo gida ta tadda Zainab zaune tana zaman jiranta
Inna ce ta fara cewa", kin tafi shiru dake Fadeela, sai kace anyi biyan bashi dake",
murmushi Fadeela tayi kafin tace uffan ", taji an kwasheta da wani gigitaccen mari, fad`awa tai kan kujera cikin tashin hankali
", Aminu! Mene ne haka", Inna ta fad`a tana mikewa, yayin da ita ma Zainab ta mike tsaye
cikin huci da tsananin b'acin rai baba Aminu