Author : Fatima Abdullahi Category : Hausa Novels 001
ya fara cewa ," koki yarda Fadeela ko karki yadda ni ubanki ne , na gaji da zancen da mutanen gari suke kawowa a kan ki , ni wallahi sam bana yadda da duk wani motsinki, to wallahi na baki wata da`ya ki shirya Zakariyya ne zaki aura",
sai a lokacin Fadeela ta fashe da kuka
inda Inna ta titsiye baba Aminu da tambaya, "mene aka ce ta aikata haka Aminu",?
Inna tai tambayar tana rike da hab`a
cikin wannan huci baba Aminu ya fara cewa," Inna matukar na tuna Fadeela na gabana hankali tashi yake , ni yanzu ma wallahi na fara zarginta, kullum sai an kawo mini maganarta taya ne hankali zai kwanta , tunda ta fara mu'amala da wannan yaran duk hankalina atashe yake",
yay ajiyar zuciya yana cewa, "na dai fad`a miki ki shirya auren Zakariyya nan da wata d`aya kacal",
yana gama fad`a ya fice cikin huci ya tafi gidansa
Fadeela ta fad`a jikin Zainab tana wani rurucewa da kuka
", Zainab wannan wacce irin rayuwa ce , mene ne mutane suka gani ina aikatawa, yanzu shima baba Aminu yana mini kallon da wasu mutanen suke mini har ya furta yana zargina",
Zainab cikin karyayyar zuciya idanunta sun ciko da kwalla tace ", kiyi hakuri Fadeela, wallahi baba Aminu yana da gaskiya, ki daure ki auri Zakariyya zaki samu farin ciki",
Fadeela ta bar jikin Zainab ta doshi inda Inna take ta durkusa kasa tana cewa cikin gagarimin kuka mai gwanin ban tausayi," wallahii Inna ki hana baba Aminu aura mini Zakariyya, ya bani lokaci zan fito da wanda nake so,"
Inna tace ,"babu abin da zance Fadeela kibi umarninsa , ni barin duniya zan na barku tare duk yadda yay da rayuwarki cigaba yake nema maki",
Inna tana gama fad`a ta tashi ta shige dakinta,
kuka Fadeela ta sake rurucewa da shi tana kallon Zainab.
"lallai ma ambassador ya raina miki hankali, to wallahi idan zaki nemi wani namijin ma ki nema , zama dana miji d`aya asara ne",
Ruma tayi maganar tana kallon Ummi baby
jin Ummi baby bata ce komai ba yasa Ruma cewa," ni kinga ma anjuma wani sabon chairman nake da shi , zamu je muji irin nashi salon,"ta karasa maganar tana dariya๐.
baba Aminu cikin hucin ya koma gida zama ya yi a falo yana ajiyar zuciya
Jamila ce ta fito fuskarta cike da farin ciki da annushuwa,
ko tambayar halin da yake ciki batai ba ta kama hannayensa ta mik`ar da shi tsaye tana sumbatarshi
murmushin yak`e yay mata kawai yana cewa,"mene yake faruwa",
rungume shi tai ajikinta cikin wani rurucewa da kuka tana cewa.
kuna tare da Autar marubuta
share and comment.... my fans๐.
K`AWAR KARUWAI๐๐๐
BY
AUTAR MARUBUTA
_____________________________
page 11&12
,"ciki ne dani mijina ,
wallahi ciki ne dani "๐ญ
shima baisan lokacin da yaji idanunshi sun ciko da kwallaba
zameta yay a jikinsa yana kallon fuskarta
bai iya cewa da ita komai ba , kawai ya sake rungume matarshi yana zubar da hawaye.
Anan kofar gidansu Ruma kuwa ,wani saurayi ne tsaye wanda ga dukkan alamu yana jiran wani abun ne,
zuwa can Farida ta fito ta tsaya gabansa tana cewa," a she kai ne kake kirana",
saurayin yay murmushi yana cewa, "a she zaki gane ni ke nan ",
Farida tace ," me zai hana,to amma meke tafe da kai",
murmushi ya sa ke yi yana kallon fuskar Farida yana cewa, "kin barni cikin zulumi tun ranar da muka had`u",
murmushi tayi tana cewa," Hmmm, nifa malam karuwa ce na fad`a ma gaskiya dan haka ba wani mamaki ba ne",
cikin karyayyar zuciya yace ,"kina kama da mahaifiyata Farida, wallahi tun a daren dana ganki kwana nayi ina tunanin mahaifiyata, muna kaunarta sosai amma Allah ya raba mu da ita,"
Farida sake kallonshi tai tana murmushi sannan tace ,"mene sunanka",
cikin girmamawa yace ,"suna na Khalid ".
Yanzu misalin karfe 8na dare , Inna na zaune a falo, Fadeela tazo ta wuce ta rufe gida , inda Fadeela ta kalli Inna tana cewa", saida safe Inna",
sauri Inna tayi tana kallon Fadeela," yau kuma tun yanzu zaki kwanta",
Fadeela tace ,"eh Inna kaina yana ciwo",
Inna tace ,"nima kuwa zuwa zan yi na kwanta , domin kwana biyu ina yawan jin Ana hauro mana gida ina jin tsoro,"
murmushi fadeela tayi tana cewa, "ke dai kawai Inna ki ce matsoraciya ce ke," Fadeela ta shige dakinta tana dariya
Inna tace ",kin ji mini yarinya tsoron gidanku ",๐
Inna ta dauro alwala ta shige dakinta
Fadeela na shiga daki aiko kiran wayar Alaji Sani na shigowa nan suka sha wayarsu har yake tambayar yaushe zasu had`u,
bayan su gama wayar sai ga kiran Zakariyya, amma Fadeela kawai tayi blocking d`in shi ,
kawai ta kira Alaji mansur, suka sha soyayya
bayan duk ta gama abin da zatai wani matsanaicin ciwon mara ya riketa gamm, ta jima tana shan bakar wahala kafin ta samu sa'ida.
Ruma ce kwance kan wani had`ad``en gano tana shan ๐ฆ
babban hotel ne na masu abin๐ด
zuwa can saiga gogannaku ya fito daga bathroom ,
goge jikin shi yake da towel yana kallon Ruma , harararshi tai tana cewa," to mene kake kallona",
tsalle yay ya hau kan gadon yana cewa, "karki sake hararata ko kisha wahalar da tafima ta d`azu, domin ni chairman a kujerata ma ina basu wahala bare a gun mata",
tab`e baki Ruma tayi tana cewa," ku fa maza kuna bani mamaki , kawai wannan d`an abin da kamin shi ne shan wahala , to wallahi ko a jikina chairman",
haushin maganar yaji ya mike yana kokarin caf kota yana cewa, "to bari ki gani ",
da gudu ta tashi ta cillar da bargon dake jikinta tana dariya ,
shima dariya ya kwashe da ita katan banzan yana cewa," zo kisa kayanki Ruma",ya d`ebi kayan yana mika mata ,
fari tamai da idanu tana cewa, "mene amfaninka",
cewa yay "haka ne ta inda aka hau tanan ake sauka ",ya mike da kayan ya nufi inda take.๐
Zainab na shiga lungun gidansu Fadeela taji Ana kwala mata kira, tabbas idan ta gano muryar Zakariyya ce ,
aiko tana juyawa ta ga bawan Allah sanye da jakar goyo.
Fadeela ce kawai cikin gidan , sakamakon Inna tana gidan baba Aminu, tunda taji Jamila ta samu ciki bini-bini ta shirya ta je yanzu haka ma tana can
Fadeela tasa hijab tana shirin fita taji sallama
juyawa tai daidai lokacin da take amsa sallamar
had`e rai ta yi taja dogon tsaki tana kallonsu
Zakariyya da Zainab suka kalli juna cikin mamaki
Zainab ce ta karasa gabanta tana cewa", haba Fadeela mene haka ke nan",
Fadeela hankad`e Zainab ta yi gefe cikin mummunan bacin rai
su ma cikin gagarumin mamaki suke kallonta
", daman ke ce babbar munafukar da ki ke shiga kina fita kan dole baba Aminu ya auran Zakariyya, to wallahi kin bani kunya Zainab",
Fadeela ta juya ta kalli Zakariyya tana nunashi da yatsa๐
", tom ka ji ni da kyau kai kuma maye , na tsaneka Zakariyya bana kaunarka bana sanka , ku fi ce mana a gida",
tsananin mamaki ne ya kama Zainab saboda a iya zamanta da Fadeela tasan da cewa Fadeela ba ta da aljanu , to amma mene wannan abun da ta aikata,
tsananin fusata Zainab ta yi , amma ba tare da tace komai ba tasa kai ta fita , ganin hakan yasa Zakariyya bin bayanta da 'yar jakarshi da aka zo za'a kwana biyu๐๐
bayan sun fita Zainab tayi nannuyar ajiyar zuciya tana kallon Zakariyya," dan Allah ka yi hakuri Zakariyya ",
murmushi yay bawan Allah๐
yana cewa," babu komai Zainab ni yanzu zan koma",
sakin baki ta yi cikin tsananin jin tausayinshi
sa'ilin da tai ajiyar zuciya tana cewa ",zuwanka fa ke nan Zakariyya dan Allah kayi hakuri, kaje gidanmu ka huta ai kaduna ba wasa ba",
shi ma ajiyar zuciya yay yana cewa", da kin barni Zainab hankali duk ya yi gida wallahi",
cikin murtuke fuska tace ", to tunda gidan namu ne baka san zuwa , sai mu tsallaka mu je gidan baba Aminu",
a ajiyar zuciya Zakariyya ya kuma yi yana kallon Zainab cikin tausayin kanshi , sannan yace ," tom shi ke nan , mu je gidan naku",
sannan suka dauki hanya suna tafiya suna hira .
Ita kuwa Fadeela cikin b`acin rai ta fita waje , sakamakon Alaji mansur dake jiranta,
Farida ce da Kalid a kofar gidansu , suna cikin mota suna hira
Kalid ya kalli Farida yana cewa ",gaskiya ke Farida mutuniyar kirki ce, amma ban so kika jefa kanki a irin wannan yanayin ba",
kallon shi tai tana cewa," Kalid ke nan ",
fuskar shi babu wasa ya kalleta ", zan so ki bani da ma cikin rayuwarki , na zamto miki jigo na ma ye maki gurbin da kika rasa , ya zamto jinina yana yawo cikin jikinki Farida
wallahi Farida ina sanki",
shiru tayi tana kallonshi๐
ganin bata ce komai ba yasa Kalid cigaba da cewa ," zan nunawa dangina ke ce nake so , zan baki gudunmawar daidaita rayuwarki, wallahi har zuciyata nake kaunarki Farida ",
nannauyar a jiyar zuciya tayi jikinta duk a ma ce , wani kwarjini Kalid yake mata , hakan yasa ta kasa cewa komai
ta b`ude murfin motar ta fita
da sauri ya fito shima ya sha gabanta yana cewa", Farida",
juyawa sukai baki d`ayansu sakamakon k`arar mota da suka ji a bayansu",
motar Alaji mansur ce tai parking shi da Fadeela, suka fito
yayin da Alaji mansur ya jingina jikin motar tashi yana gyara babbar rigarshi,
share and comment.... .
K`AWAR KARUWAI๐๐๐
BY
FATIMA ABDALLAH KANO
(Autar marubuta)
_________________________________
page 13&14
Murmushi Fadeela tayiwa Farida tare kuma da d`aga musu hannu ta shige cikin gidan
tana shiga ta ga Ummi baby tana gyaran ganyen magarya
",Assalamu alaikum",
Ruma ce ta riga amsa sallamar daga fitowarta daga toilet
Ummi baby murmushi tayi tana cewa", ai na dauka shuka mu kikai ba zuwa za ku yi ba",
durkusa Fadeela tayi gabanta tana cewa", mene zaki da wannan",
ta nuna ganyen magarya
Ruma ce tai dariya tana cewa", wai maganin sanyi da kuma matsi , ni kam dai bazan amfani da shi ba",
Ummi baby harara ta dokawa Ruma tana cewa," rabu da waccen matar,
to wallahi wannan ganyen babban magani ne a gurin mata , idan kika bazashi ya bushe ki daka ,
kina tsarki ko shiga ciki , yana maganin budewar gaban mace",
Fadeela tace ",ikon Allah su Ummi baby masu gargajiya", tana dariya
ita ma Ummi baby dariyar tayi tana cewa", ke kuwa ba dole ba ,
ina san nake kashe ambassador da dadi",
Ummi baby had`e rai tayi tana cewa", a'a to barni haka",
ta mik`e tsaye tana cewa," ni wallahi ma maganin ciwon mara nake so , domin kwana biyu ina shan wahala kuma dah bana yi",
Ummi baby ta mik`e tsaye tana cewa ",zan baki wani sirri",
ta je kofa tana kokarin fita
tsayawa Fadeela tayi tana cewa", ina za ki ne",
" waje mana ke ce fa kika ce Alaji mansur yazo",
Fadeela tace ",haba sa hijab mana , ke ma Ruma ki fito ku gaisa",
ta karasa maganar tana fita .
Bayan Tsawon Lokaci
yau kimanin sati uku ke nan da mutuwar baba Aminu๐ญ๐ญ๐ญ
ya yi jinya ne Allah ya dauki ransa ba tare da ya ga matarshi ta haihu ba๐ญ๐ญ
tabbas wannan mutuwa ta girgiza mutane, Inna taci kuka sosai mara misali, haka ita ma Fadeela, uwa uba kuma Jamila๐ญ
wannan rayuwa haka take duk sanda lokacin ka ya yi babu jira ,
Allah yasa mu dace baba Aminu Allah ya yafe maka ๐ญ๐ญ๐ญ
bayan Fadeela ta fito daga wankanta na kaddara(Dare)
ta fad`a gado tana murk`ususu mararta kamar zata fita,
to banda abin Fadeela taje asubiti mana asan meke faruwa, niko nace waya sani ko wankan darenta ne yaja mata.๐
Wayar Zainab ce take Ring da sauri ta nufo wayar domin tunaninta kiran da take jira ne , tana isowa ta ga Zakariyya ne,
tai ajiyar zuciya ta zauna tana kara wayar a kunne,
", Assalamu alaikum ma a bociyar hankali da ilmi",
taji Zakariyya ya fad`a
wani d`an yammm taji haka , kafin ta amsa sallamar
bayan sun gaisa
Zakariyya ke cewa", Zainab na gode da dukkan gudun mawar da kika bani dan ganin na auri Fadeela, amma a yanzu ina tabbatar miki na fahimci Fadeela bata kaunata , dan haka na sake sabuwar rayuwa tare da wata , na mance da Fadeela",
Zainab tace ", Alhamdulillah, Allah yasa hakan ne yafi alheri, ita ma Fadeela Allah ya bata miji na gari",
dariya Zakariyya yay yana cewa", to Amin zainabata, amma bari na fad`a miki wata gaskiya,
Zainab yanzu ke nake so , kuma nake son aura, zuciyata ta kamu da sanki Zainab",
darau damm dumm Zainab taji a ranta , a take taji kanta ya sara,
" kasan dawa kake magana kuwa",Zainab ta fad`a cikin mamaki
murmushi Zakariyya yay yana cewa",na sa ni mana Zainab, dan Allah karki mini hali irin na Fadeela ki share mini hawayena da rad`ad`in da nake ciki, ki amshi soyayyata",
tsawon minti guda sukai shiru suna sauraran numfashin juna
daga bisani Zakariyya tace",dan Allah Zainab ki yarda dani ",
Zainab taja dogon numfashi mai zafi tana cewa", Fadeela fa Aminiyata ce kuma dan mu samu matsala da ita hakan ba yana nufin naci amanarta ba",
wayarshi ya sake daidaitawa a kunnenshi yana cewa," na nemi Fadeela da aure Zainab tace bata kaunata , to mene abin cin amana dan na soki",
a ajiyar zuciya tayi tana cewa",gaskiya bazan iya wannan abin ba kayi hakuri ",
ta kashe wayar yayin da Zakariyya ke kiran sunanta.
Yanzu misalin karfe 8na dare Ruma da Ummi baby sun gama cin abinci , yayin da Farida ke kwance tana kallonsu
", wai kwana biyu meke faruwa ne Farida?
duk kin canza mana fa lafiya kuwa",?
Ruma ta fad`a
murmushi farida tayi ma ta tana cewa ", kawai yanayi ne",
Ummi baby tace " tom ni dai gaskiya zan je taron karuwai na legos , idan zaku sai ku shirya",
Farida ce ta kalleta tana cewa ",au haka ne fa , ai nasan ambassador zashi sai ki bishi",
", auuuuu๐ kina nufin ba za ki ba farida",?
Ummi baby ta fad`a
tashi Farida tayi daga kwanciyar da tai jikinta duk a mace tare da wani yanayi na kasala tace ", a kwai abin da na keson sanar daku",
kallonta sukai a tare lokaci guda kuma suna kallon juna ,
kafin wani yace komai
suka ji hoonn d`in mota mai karfi daga kofar gida
dogon tsaki Farida taja tana cewa," kunji banza Alaji Nuhu ko, to wallahi ba inda zani tsinan ne",
dariya Ummi baby ta keece da ita tana cewa ",bari naje na ce masa ba kyenan",
Ummi baby ta ziri mayafi ta fice cikin rawar jiki,
tana fita ta karasa wajen motar
tunda Alaji Nuhu ya hangota ya fara sid`e baki๐
sauri yay yana fitowa daga motar daga shi sai singlet da gajeren wando, ga shi luk`uti bak`i
baki d`aya ita ma Ummi baby taji tsanarshi ta kamata
", Alaji Farida bata nan fa ",
ta fad`a ba tare data karasa inda yake ba sauri yay yana takowa inda Ummi baby ke tsaye yana cewa", toooooo,yanzu ya zan yi ke nan kuma wallahi a matse nake , baki d`aya K`AWAR taki ta kaurace mini
kuma naga kema ba lefi ko zaki fansheta ne yau kawai",
had`e rai Ummi baby tayi tana cewa", me kake nufi Alaji",
Alaji Nuhu yay dariya yana cewa", haba yarinya sai kace ba 'yar hannu ba",
ya karasa maganar yana aje hannu a kan kirjinta yana cewa", a taimaka mini",
mari ta falla masa tasa karfi ta wurgar da shi gefe kawai ta shige gida๐๐๐๐๐๐๐
tana shiga ta fara cewa", gaskiya Farida kina fama da wannan gardin mutumin",
dariya suka shek`e da ita yayin da ta basu labarin abin da ya faru ,
Ruma harda tintsirawa tana dariya cikin b`acin rai da haushi Ummi baby tace ," to dariyar ta isa haka Ruma ",
Ruma tana kokarin shanye dariyar tace", sorry na dena", lokaci guda kuma tana sake tintsirewa๐๐
Ummi baby duka ta kai mata yayin da Ruma tai saurin kaucewa,
bayan sun yi shiru ne Ruma ke cewa", to Farida mene ne zaki fad`a mana? muna ji Allah yasa cigaba ne",
cikin kasalalliyar murya Farida tace ", NA DENA KARUWANCI",
sauri sukai suka hada ido cikin tsananin mamaki da rashin gane inda maganar ta dosa,
duk ji sukai maganar na musu amsa kuuwa a kunnuwansu, Na dena karuwanci_na dena karuwanci.
...........comment and share my fans
K`AWAR KARUWAI๐๐๐
BY
AUTAR MARUBUTA
_________________________
page 15&16
",nifa ban gane me kike fad`a ba Farida",
Ruma tai maganar cikin tashin hankali,
kawai Farida ta tashi ta bar musu d`akin
yayin da suka bita da kallon mamaki da rashin fahimta.
Washe gari๐
Inna da Jamila ne zaune suna falo, sakamakon tunda Allah yay wa baba Aminu rasuwa Jamila ta dawo gidan ,
Fadeela kuma tana madafa tana had`a musu abin kari ๐ดโ๐ฒ taji wayarta na ringin , dubawar da zatai kawai ta fara murmushi ,
Alaji Sani ne ke kira ,
wayar ta d`aga tana karawa a kunne daga can Alajin yace", barka my sweet",
murmushi Fadeela tayi tana cewa", ina kwana fatan ka tashi lafiya",
", kin ganni nan tun asuba nake tunaninki da kewarki, kuma ina son na zo na gaida Inna , ko ya kika ce",
a jiyar zuciya Fadeela ta ja tana cewa," ban da abinka kai ne fa zab`ina kuma Inna zata so ganinka ai, kawai kasa rana",
murmushi yay yana cewa ",kwanannan zan se miki mota Fadeela, ke dai ki cigaba da mini addu'a",
", da gaske Alaji!,Gaskiya idan haka ne zanji dadi ka ga na koma 'yar bata",
Alaji Sani yay dariya yana cewa", to mene ? nawa motar take da bazan siya miki ba , a cikin watannan ma kuwa",
a jiyar zuciya mai sanyi ta sauke tana cewa", wallahi ka farantan rai, amma bari zami waya, yanzu ina son kaiwa Inna kayan Kari",
Alaji Sani yace"to shi ke nan",
tana aje wayar ta doshi inda su Inna suke da nufin tambayar Inna ina sugari yake domin zata zuba a cikin kunu๐บ
tana shiga falon Inna ta rufeta da fad`a
", gaskiya Fadeela kin bani mamaki, Zakariyya yazo har kano amma ki saka masa da wannan rashin mutuncin, duk a cikin samarin naki wayakai nagartarshi da ilminsa , daman da Allah bai jarabemu da rashin Aminu ba dah tuni kina d`akinki, to amma yanzu zan tsaya tsayin daka wallahi don ganin kin auri Zakariyya",
Inna cikin tsananin fusata ta ci gaba da cewa", uban mene ai bunsa? tom yanzu ni zan tsaya miki uwa uba don ganin kinyi aure ko dan shed`anun๐๐๐
zan je har kadunan zan yi magana da iyayen nashi na basu hakuri, ko kina so ko a'a Zakariyya ne mijinki, ana kokarin sama maki nagartacciyar rayuwa kina hauka",
kuka Fadeela ta fashe da shi mai gwanin ban tausayi, tabbas k`in Zakariyya ya ratsa zuciyar Fadeela
Jamila