Author : Fatima Abdullahi Category : Hausa Novels 001
tana cewa, "Wallahi Inna ban yi dan tozarta...."
Inna ta dakatar da ita tana cewa, "Yanzu ina kud'in gidan yake." Fuskar Inna cike da hawaye tai maganar
ita ma Fadeela fuskarta cike da kwalla ta fad'a mata yadda Alaji Sani ya yaudareta
Inna ta sake fashewa da kuka tana cewa, "Wallahi kin cuceni Fadeela, kin cuceni."
Fadeela na kokarin bawa Inna hakuri, amma Inna ta shige d'akinta cikin mummunan yanayi tana kuka .
Kamar tun d'azu dai Ruma da Ummi baby suna zaune , ita Ummi baby ta durkusar da kai kasa koma take tunani?
Ruma kuma tana danna wayarta , yayin da ta kalli Ummi baby tana cewa, "kinga Kalid yana fad'a mini Alaji Nuhu ya amsa laifinshi kotu kuma ta yanke masa hukunci , gaskiya Kalid yaron manya ne ya taimake mu ."
Ummi baby ko d'ago kai batai ba , hakan yasa Ruma shafa mata fuska tana cewa, "Magana fa nake Ummi."
Ummi baby ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye tana kallon Ruma
Ruma ta aje wayar dake hannunta tana cewa, "Me ke faruwa kuma ."
Murmushi Ummi baby ta yi tana cewa, "Wallahi kanwata Aisha na tuna yarinyar nan tana so na , haka Dady da momy , ban ta'bajin ina kewarsu ba kamar haka ,sai yau , ko wanne hali suke ciki oho , a gaskiya ahali sun yi a rayuwa."
ta share hawayen fuskarta tana murmushi
Ruma ita ma murmushi tai tana kallon Ummi baby da cewa , "Idan kuwa haka ne ,to lokaci ya yi da zamu tuba."
Da sauri Ummi baby ta kalli Ruma da idanunta da tasha kuka.
Fadeela ce kwance a kan gado tana takaicin irin halin da Alaji Sani ya jefata
amma taci alwashin dole taci gaba da neman kudinta don kada su rasa matsuguni
tashi tai taje ta rufe gida ta kwanta
Inna kuwa matukar tashin hankali take ciki da wannan hali da Fadeela ta jefasu
hakan yasa ta kasa bacci har zazza'bi ya sake rufeta duk da haka kuka take tana tunanin
tsawon lokacin da ta share a duniya da irin 'kalubalen da ta fuskanta na rashin 'ya'yanta
Inna kuka tai ta yi tana zubar da hawaye har wajen kimanin karfe 12:30 na dare
motsin Fadeela taji
babu jan lokaci taji ta 'bude gida ta fita ,
hankalin Inna tashi ya sake yi cikin tsananin fargabar Inna Fadeela zata a wannan daren, ta fito falo ta zauna cikin tashin hankali
Fadeela kuwa na fita gidan Ambassador ta wuce tana zuwa ya yi mata marhabun da zuwa suka shiga cikin d'aki
d'aki ne mai matukar hasken gaske tare da had'ad'd'en gado
tana shiga tai murmushi tana cewa, "Gaskiya wannan d'akin ya burgeni."
Ta karasa maganar tana cirea babban hijab d'in dake jikinta tana wata irin kwanciya a kan gadon , babu komai jikin Fadeela a halin yanzu take kwance a kan wannan gadon
Ambassador zama ya yi a kan kujera yana kallon Fadeela yana murmushi
yadda taso take juyi a kan gadon tana shashshafa jikinta tana kallon Ambassador
Ambassador ba tare da ya taso ba ya fara cewa, "Baby me yasa kika za'bi wannan rayuwar ko dan baki da kowa ne ko kuma kina neman kudi."?
Fadeela cikin shagwa'ba tana girgiza jikinta tace ," Ni ka taso , dare fa yayi Inna tana gida yanzu bata jin dad'i."
Ambassador yace , "Au kina nufin ba ta san kina fitowa ba."
Da sauri Fadeela ta kalleshi tana cewa, "Tabb to kafff duniya babu wanda yasan ni karuwa ce , kuma yanzu na kai shekaru da da ma domin duk taron legos ina zuwa baya wuce ni ,
zan cigaba da rayuwata a hakan ."
Ambassador ya mike tsaye ya matsa gabanta ,
kafin kace uffan Fadeela ta jawoshi kan gadon ya fad'a kanta .
Bayan ta gama duk shed'ancin da ta gadama Ambassador ya rakota ta dawo gida
cikin sand'a Fadeela ta fara taku dan gudun farkawar Inna a bacci
tana shiga falon ta ga Inna tana zaune tana kallonta ,
cikin firgici Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Inna jikin ne? me kika fito yi falo."?
Inna ta mi'ke cikin mummunan yanayi tana kallon Fadeela da cewa , " Ina kika je Fadeela, naga fitar ki tun d'azu sai yanzu kika dawo ."
Fadeela cikin tashin hankali ta matsa kusa da Inna , tana sosa 'keya zata fara magana
a wannan lokacin ne Inna ta hangi jikin Fadeela samm babu kaya a jikinta ,
"Inna da ma akwai wasu kud'i ne...."
Inna ta dakatar da ita cikin mugun yanayin yadda ta ga fadeela a wannan hali
wasu zafafan hawaye ne suka zu'bowa Inna , ta kalli Fadeela tana cewa, "Yanzu Fadeela fita kikai cikin daren nan ki ka je siyar da mutuncinki , tsirara kika fita Fadeela,
innalillahi wa innailaihir raji'un".
Inna tana gama fad'a ta fad'i kasa a karkace , da sauri Fadeela tai kanta , Inna ta dakatar da ita da hannunta tana wani irin haki tana cewa, " Bazan yafe miki ba Fadeela. "
Inna ta karasa kaiwa kasa cikin hawaye ko shurawa Inna ba ta sake yi ba ,
tafiyar ke nan , haka Fadeela ta ringa tsandara ihu cikin darennan har ma'kota sai da suka fito suka zo , suka sami gawarta.
Washe gari da safe sai ga Amina Salisu da Zainab da Ruma da Ummi baby sun had'u
matukar tashin hankali Zainab da Amina suka sake shiga ganin video da su Ummi baby suka nuna mata,
Ambassador ne da Fadeela,
abin ya zuzuta su matuka
hakan ya hassala Amina Salisu wai dole sai taje ta sami Fadeela
da 'kyer Zainab ta hana ta sakamakon rasuwar Inna ,
amma ita ma Ummi baby abin da taso ke nan kawai suje ayita a gama
saida Ruma taja hankalinsu kan wani shiri da tai hakan yasa duk suka sami sanyi cikin ransu
wayar Ummi baby ce ta fara ruri ta kalli wayar tana cewa, "Mene kuma Ambassador."
wayar ta kara a kunnenta tana cewa, "Ya akai."
Daga can Ambassador cikin tashin hankali ya fara cewa , "Karfa ki fitar da wannan videon ba a rufe fuskata ba ."
Ummi baby ta kwashe da dariya tana cewa, "Ambassador na fadeela, ai karma ka damu , har inda bai dace al'uma su gani ba wanda Fadeela ta bayyana a jikinta zamu rufe , duk da bataji kunyar Allah ba zan mata adalci ."
Ambassador yace , "To shi ke nan ."
ya kashe wayar
Amina Salisu tace , "To ita dabba jaka taya gar yay mata video bata sani ba."
Dariya Ruma tasa tana cewa, "Lallai ba zaki gane kan abinba , tana can tana jin dad'inta ai komai zai bazata gane ba."
Zainab dai da zancen ya matukar rud'ata tace , "Allah ya kyauta."
Amina Salisu tace, "kuma wallahi yau d'innan saina sanar da ita Zakariyya, Zainab zai aura kafin mu jefata cikin wani bala'in."
Ita dai Zainab shiru tai tana juyayin mutuwar Inna tare da tunanin da baba Aminu na duniya data jefashi cikin tashin hankali, sai Allah yasa yabar mata duniyar .
Bayansu Ruma sun koma gida ,suka sami Kalid yana jiransu
a yau suka ziyarci Gombe state suka nemi gidan su Farida, suna zuwa wata mahaukaciya suka gani a cikin gidan tare da wasu yarah kuma suna ta wasa , daga bisani bayansun sami mari'kin Farida suka sanar da shi duk irin rayuwar da Farida ta yi harta koma ga Allah,
yaci kuka sosaii yayi nadama duk da ba laifinsa ba ne , ya dad'e yana zuba idon shigowar Farida gida , amma a halin yanzu ya cire rai ,
haka shima ya basu labarin irin rayuwar wahalar da Farida tai a cikin gidansa , ga rasuwar 'kanwar mahaifiyarta wanda ita ce yake aure ta kuma d'auki Farida sanadin rasuwar iyayenta, su dai su Ruma sun san komai domin ta basu labarin
a lokacin mutumin yake nuna wannan mahaukaciya yake sanar musu ita ce azzalumar da tai sanadin komai da ba'kin halinta , domin ma ana zargin da hannunta wajen mutuwar'kanwar mahaifiyar Farida.
Da kuka suka rabu da juna Ummi baby kamar yarinya sai da ta d'auki dutse ta kwalawa wannan mahaukaciyar aiko ta fara ruwan ashar , Ummi ba ta sake bige Mata baki .
Sun yi matukar dare suka dawo cikin kano.
Amina kam kamar yadda ta fad'a
tasa Fadeela cikin mamaki a yanzu ta gane Zakariyya Zainab zai haura shi yasa ta ga da yazo gaisuwa ko sauraranta bai yi ba .
Washe gari da safe su Ruma suna karyawa sai Ruma take cewa , "Ummi ni a ganina a maimakon yiwa Fadeela hakan , me zai hana kar mu fitar da video, kawai mu mata bazaranar ta fito ta nunawa duniya ga irin halinta , domin kinga ita mace ce abin zai ta siri cikin rayuwarta sosai."
Cikin 'bacin rai Ummi baby ta kalli Ruma tana cewa, "ke kinma isa , kamar yadda nai alwashin tozartata to wallahi sai nayi, tana tare damu tana cin dunduniyarmu
kuma ke kinsan shekararta nawa a matsayin karuwar sirri , to wallahi ta rugamu farawa ,
kuma da kike maganar mu sata ta amsa , duk mutane sun san 'kawar mu ce , hakan yasa ake kiranta da 'kawar karuwai
to idan mukai haka kowa zai ce mu ne muka jawota ciki
gwanda kowa ya ganta 'kiri-'kiri ."
Ta aje maganar cikin huci tana kallon Ruma .
share and comment.......🙏
'KAWAR KARUWAI💃💃💃
BY
AUTAR MARUBUTA
_______________________________________
page 29&30
Fadeela bayan an sake kawo mata notice yasa cikin dare ta kwashe kayanta , har yanzu babu inda kanta ya kawo mata da zata je
domin ko 'yan uwan babanta na Kaduna sun ce ta shirya ta koma can , amma tace dasu idan sun tafi bayan tayi bankwana da mutane zata taho , hakan yasa suka tafi suka barta .
Gidan Sadiq ta wuce domin zama , aiko yayi murna sosai da ganinta a wannan lokacin,
shi kawai bukatarsa ayi abin da aka saba domin kwana biyu basu ha'du ba
duk da Fadeela na fama da zazzabi da ciwon ciki hakan bai hana Sadiq yin yadda yaso da ita ba ,
aiko ta ci wahala shi kam ko a jikinsa domin ya yi abin da yake so bayan ya fito daga wanka ya sameta shan'bar a kwance jikinnata ya yi tsafi sosai , a lokacin ne mahaifiyarshi ta kirashi a waya cikin murna take sanar da shi gobe yayansa zai dawo don haka ya shirya dawowa gida ya kuma gyara masa gidansa kafin ya sauka,
shi dai Sadiq damuwarshi rashin lafiyartaa a halin yanzu , hakan yasa ya nemi kaita asubiti.
Washe gari ma'kotan Fadeela suna shirin kai mata abincin rana suka ga gidan a kulle , babu jimawa suka ga anzo ana rushe gidan , bayan sun bincika aka tabbatar musu da ansiyar da gidan , hakan yasa suka fara tunanin ko ina Fadeelan yanzu,
wata mai kimanin shekaru iriin na fadeela ce ta fito daga d'aki tana cewa, "Umma !
Ai dole a nemi fadeela a rasa kinga videon ta."
Abin ya matukar basu mamaki sosai ji da ganin Fadeela a wannan yanayin.
Fadeela na cikin asubiti ita da Sadiq samm basu da labarin video da yake yawo na Fadeela, musamman cikin makarantarsu kowa malamai da d'alubai yasan halin da Fadeela ke ciki
Sadiq yana gabanta ri'ke da takardar da dactor ya basu tabbacin wata rashin lafiya dake tattare da Fadeela.
Kuka take sosai cikin tashin hankali tana kallon Sadiq tace , "Ka mai dani gidanka Sadiq ni tawa ta 'kare."
Sadiq ya kalleta cikin tashin hankali yana cewa , "To Fadeela ke da ba matata ba ni yanzu ina zan kai ki , sanin kanki ne gidan da nake gidan yayanmu ne kuma yanzu ya dawo , nima gidan mahaifiyarmu zan koma , kawai kiyi hakuri ni zan tafi ki nemi wani gun."Ya aje mata takardarta
Sauri Fadeela tai ta ri'ko masa riga cikin rurucewa da kuka tana cewa, " Haba Sadiq kar ka mini haka dan Allah ".
Sadiq ya fincike rigarshi yana cewa, " Sake ni dallah ni babban tashin hankali na ma wayasan tarin cutukan da kike dasu da likita bai gano ba ."
A lokacin Fadeela tai tunanin tun rasuwar Inna ,Alaji Mansur da Aliyyu basu sake waiwayarta ba , hakan yasa ta kalli Sadiq Sadiq tana cewa, "To ara mini wayarka nai kira."
Ya cilla mata wayar yana kauda kai , niko nace anci moriyar gan-gan...
Ta fara sa number taji an yi sallama hakan yasa ta aje wayar tana kallon masu shigowar cikin kuka
Ruma ce ta shigo da Ummi baby sai Alaji Mansur, Aliyyu, Ambassador, Zainab, Amina Salisu.
Fadeela ta rasa me zatai murna ko tashin hankali ne yake tunkarota domin tunda ta ga Ambassador a cikin su abin ya d'aure mata kai , kowa shiru ya yi
amma Ummi baby zuciyarta tafasa take sosai idan tana kallon Fadeela
"Nasan za ki mamakin ganinmu haka to ,sharrin da kika dad'e kina shukawa yau za ki kwashe".
Ruma tai maganar cikin jin haushinta.
A jiyar zuciya Fadeela ta yi , tasha jinin jikinta cikin kwalla ta kalli Ruma tana cewa, " Wanne sharri kuma Ruma , ni ce fa Ruma."
Ummi baby cikin fusata ta kalli Fadeela tana cewa, "Ai wallahi kin bamu kunya kin yi asara."
Cikin tashin hankali Fadeela ta sake cewa , "Wai mene yake faruwa ne dan Allah."
Amina Salisu da babu tausayin Fadeela a ranta ko kad'an ta fara cewa , "Ku fad'a mata mana shegiya mahaukaciya mun gano ke KARUWA CE".
Duk sai da sukaji maganar ta ratsasu duk da ba sabon abu bane .
" Wa iya zubillah Amina Salisu, karki mini 'kazafi saboda kin tsane ni."
Ta fashe da kuka ,
"Wato 'kazafi ko macucuya munafuka."
Amina Salisu ta sake fad'a
Fadeela ta daure ta tashi daga gadon asubiti ta ri'ke hannun Zainab tana cewa, "Yanzu ke Zainab kin yarda da wannan."
Zainab ta janye hannunta ta kau da kanta .
Fadeela tace , "Na shiga uku ni , Yanzu mutanen da nake son shiryay dasu su ne zasu tozartani .".
Aliyyu ya kwashe Fadeela da wani mari da sai da ya yi sanadin komawarta gado ta zauna ,
" Kin yaudare ni , kin cuci rayuwarki ."
Ya ciro wayarsa a aljihu ya nuna mata bidionta da wani gashinan an rufe masa fuska .
Sauri tai ta Kalli Ambassador ta rushe da kuka mai 'karfi .
Alaji Mansur bai ce komai ba , haka Zainab
"Innalillahi wa innailaihir raji'un, kin yi asara Fadeela."
Amina Salisu ta fad'a
cikin izza da kuka Fadeela ta mi'ke tana cewa, "EH nayi nayi karuwanci, amma ni sam banyi don neman kud'i ba , naji na yaudare ku amma idan na sanar daku mene hakan zai amfane ku."
Fadeela ta zauna cikin kuka ta durkusar da kai tana cewa, "Yanzu na tabbatar da nayi asarar duniyata ,
akwai wata rana wajen shekaru 7 da suka wuce , mun je biki Kaduna tun daga nan komai ya fara .
Wani daga cikin abokan angon ya nuna mini yana sona , hakan yasa na yarda , domin ni Allah ya sa mini saurin sabo da yarda da mutane,
Ranar da zamu dawo kano ina cikin motarsa , ya fara mini wasu irin maganganu na rashin tarbiya, hakan yasa kawai naji shed'an ya shiga zuciyata kawai na sumba ce shi , tun daga lokacin hankalinsa ya tashi ya tafi hotel dani ,
ya yi duk yadda ya gadama dani yayin da ni kuma na ba shi had'in kai , a ranar ban dawo ba saida na sake kwana biyu, na sake ne man wasu mazan."
Fadeela ta share hawayenta tana cewa, "Bayan na dawo naji bazan iya jure zama ba tare da maza ba , kuma a lokacin sam bana san aure , naci gaba da yi a nan , wanda nake fita duk lokacin da naso , sai baba Aminu ya sa mini ido, hakan yasa ya mai dani gidansa ,
nayi cuta sosai saboda bazan jure zaman gidansa ba domin bana fita , lokacin da Inna ta ga na rame sosai tace ya dawo dani
bayan na dawo na yi matukar farin ciki, hakan yasa na yanke shawarar fita da dad dare,
nake zuwa nai abin da naso babu wanda ya sani ,
bayan shekara biyu sai na had'u dasu Farida, da farko na yi tunanin fad'a musu nima irinsu ce , amma nai tunanin nai shiru kawai zai fi na samu kwanciyar hankali, gudun ace tunda ina tare dasu nima irinsu ce, yasa na farai musu nasiha."
Kuka Fadeela ta sake rurucewa da shi tana cigaba da magana, "Yanzu babu Inna babu baba Aminu, na yi zaton zan ci gaba da watayawata ashe ni ma na gama rayuwa, yau tsawon shekaru na 7 cikin wannan rayuwa, amma a yau gani ckin tozarci ."
Ta dauko takardar da dactor ya basu tana nuna musu , "Yanzu likita ya tabbatar mini da ciwon cancer ya kama mahaifata , yace ta kai matakin da dole za a cire ko kuma komai ya iya faruwa."
Ta sake fashewa da kuka , Aliyyu yaja dogon tsaki yana cewa, "Sam banji tausayinki ba , azzaluma mayaudariya ."
yasa kai ya bar asubitin baki d'aya
Sadiq ya kalleta yana d'aukar wayarsa a cikinta yana cewa, "Nima na tafi ."
Ya tafi tana kuka
Ambassador ya kalli Ruma yana cewa, "mu ma mu tafi ko."
Ummi baby ta kalli Fadeela tana cewa , "Zamu tafi saidai muce Allah ya sake shiryamu abin da yafi miki ki koma Kaduna wajen family d'inki."
Amina Salisu taja hannun Zainab tana cewa, "Taho mu bar nan."
Suka fice Fadeela na kallonsu da bakin cikin rayuwa ,
Ummi baby ta kalleta tana cewa, "Sannan kuma video wanda ki ka yi mun watsa shi a duniya, yanzu babu sauran biyo-boye kowa yasan wace ke ."
Kuka ta sake fashewa da shi tana kallon su cikin tashin hankali, yayin da sukai tafyarsu sai Alaji Mansur kawai a Cikin d'akin .
Su Ummi baby suna fita , Ambassador ya kalleta yana cewa, "Tom yanzu kuma sai ki cika alkawari , tun yanzu zamu tafi gidana ."
Ummi baby wani tashin hankali taji ya ziyartar mata zuciya, ta kalli Ambassador cikin masifa tana cewa, "Sai kace baka ji abin da yake faruwa da Fadeela ba , gaskiya muna cikin tashin hankali Ruma
ba za mu bar asubitinnan ba sai munje an yi mana gwaje-gwaje munsan cututtukan dake tare damu."
Ruma ita ma cikin tashin hankali ta amshi maganar
Ummi baby taja hannunta suka koma cikin asubitin.
Ambassador cikin ranshi yace, "To ni mene matsayin."?
Share_____
'KAWAR KARUWAI💃💃💃