KAWAR KARUWAI Book Complete Hausa Novels by Fatima Abdullahi.txt

Author :  Fatima Abdullahi Category :  Hausa Novels 001

Chapter   7 / 7

18K to 19.7K   out of 19.7K words

BY



AUTAR MARUBUTA

_________________________________
Page 31&32





Alaji Mansur ya kalli Fadeela dake kuka yana cewa, "Kin yaudari kanki , kin kuma b'ata rayuwarki, yanzu ke nan ba daban wa'yannan Karuwanba shi ke nan idan na aure ki na fad'a cikin masifa Fadeela, kinga rayuwa ke nan ba ki da kowa yanzu duk sun guje ki ,harda al'umar gari ,kinga yadda KARUWAI💃💃💃
sukai wasa dake, daman idan ba ka iya kamun 'barawo ba to shi zai kama ka , yanzu kina cikin mummunan yanayi a cikin garinnan .

Sannan kuma har yanzu ina sonki ."

Fadeela ta d'ago kai tana kallonshi cikin kuka
"Amma bazan iya auren ki ba , yanzu ke abin gudu ce Fadeela."
Ta sake rushewa da kuka

ya cigaba da cewa ,"Ko kad'an bazan aure ki ba , amma ba zan so rayuwarki ta tagayyara ba , dan haka zan mai dake Kaduna ,zan kuma d'au nauyin yi miki aiki ki samu lafiya , wato a cire miki mahaifa".

Kuka ta sake rurucewa da shi tana kallon Alaji Mansur ta kasa cewa dashi komai .


Cike da fargaba su Ruma suke jiran sakamakon gwaje -gwajen da akai musu , hankali ya matukar tashi

bayan wani lokaci ne aka bayyana musu cewa babu wata babbar cuta a tare dasu , amma suna d'auke da cutar sanyi mai muni a tare dasu, nan likita ya rubuta musu magani da matakan kariya , suka koma gida .


Suna zuwa kofar gida suka sami Kalid yana tsaye , aiko suka gaisa cikin girmamawa, yake musu nasiha


Nan Ruma da Ummi baby suka rungume suja suna wani kuka mai gwanin ban tausayi,

"Wallahi tun rasuwar Farida jikina ya yi sanyi , sannan yanzu naga yadda rayuwar Fadeela take tagayyara, a halin yanzu bani da burin da ya wuce na koma mahaifata Nijer wajen iyayena."

Ummi baby tai maganar cikin tashin hankali da kuka , lokaci guda kuma tana sake rungume Ruma a jikinta,
ita ma Ruma cikin gawurtaccen kuka ta fara cewa , "Allah ne abin godiya Ummi, ki dubi yadda ya kare mu daga cutuka masu had'ari da muni, ko dan wannan ya ishe mu ishara mu koma ga Allah domin babbar da ma ce ya bamu."


Kalid jikinsa ya yi sanyi duk tausayinsu ya kamashi , ya yi godiya ga Allah tare da yiwa Farida addu'a .

A lokacin ya kallesu yana cewa, "Tunda yanzu Allah yasa kun gane komai , gobe idan Allah ya kaimu duk ku shirya ni zan mai daku gidan iyayenku insha Allah."

Sake rungume juna cikin farin ciki .


Kalid yace , "Insha Allah gobe kuna farin cikin ganin 'yan uwanku ."

Ruma ta kalleshi tana cewa, "To amma ita fa Ummi baby tana Nijer ne Kalid, koda yake idan ba zaka damu ba , sai duk mu kwana a gidan mu , idan yaso washe gari sai a tafi Nijer d'in domin nima zani ."

Kalid yace , "To shi ke nan Allah ya kaimu goben ."



A halin yanzu su Alaji Mansur sun isa Kaduna zuwansu ke nan 'kanwar Inna , wato baba Laure tace Allah wadai Fadeela ta zauna mata a gida , sakamakon ta sanadin Zakariyya sun sami labarin komai

baba Laure d'amara taci da gyalenta ta kare kofar gidansu, dake babban gida ne da duk 'yan uwa suke a ciki.

"Ai wallahi zaki ga ma sakamakonki yadda Allah zai wajugaki , haka kika ki auren Zakariyya ashe akwai abin da kika 'boye tsinanniyar banza , wallahi kin 'bata mana zuriya , kuma ba zamu yafe ba , kuma kika sake kika shigo gidannan yau kwanan lahira za ki ."


Baba Laure tana maganar kamar zata rufe Fadeela da duka

sai da kyer da sutin goshi tare da taimakon wasu manyan cikin gidan , baba Laure ta amince da Fadeela ta zauna a Kaduna

a karshe Alaji Mansur ya yi musu sallama tare da ba wa Fadeela d'imbin kud'ad'en da zasu ishe ta ai mata aiki har ta samu na kashewa , nan yace mata iyakar abin da zai mata ke nan , ya tafi sai wata rana .

Ta shiga sabon tashin hankali kuwa , a cikin Daren suka tafi asubitin sakamakon motsawar ciwon nata ,

Nan Fadeela ta ga ne duniya ba sa ar ta bace ,ta wuce tunaninta , yanzu abin dake yawan fad'o mata mutuwar Inna kalmar ta da tace bazata yafe mata ba , tabbas baba Laure idan taji labarin ta haka Inna ta rasu , Fadeela zata fuskanci sabuwar tsana a cikin family, hakan yasa tai shiru tana rokon Allah yafiya.




Washe Gari


Duk sun zuba kayansu a mota sun bawa mai gida mukullin gidansa ,

Ga Zainab ga Amina Salisu da Ambassador, duk bayan sun yi sallama , sai Ruma ta shige mota , Ambassador idanunsa cike da hawaye yake kallon Ummi baby,
ita ma da tausayinshi ya kamata tasha gabansa tana cewa, "Ambassador ka yafe mini duk wani abu da nai ma na rashin kautawa, ni 'ya mace ce , kuma tsohuwar rayuwata zan koma yanzu a gaban iyayena , abin da ya kamaceka ka tuba ka koma ga Allah tunkafin duniya tai maka zafi ."


Ambassador ya rike mayafin Ummi baby yana cewa, "Dan Allah karki tafi."


Ta fisge mayafinta tana cewa, "Ummi baby nake a karuwanci, amma a yanzu Zulaihat ce , ya rage naka shiryuwa ko sa'banin haka , Allah ya had'a kowa da rabonsa."

Ta shige ta hau mota , Kalid yaja mota suka tafi , yayin dasu Zainab suke musu bye bye , suma su Ummi baby suna d'aga musu hannu .


Kalid 'karamar hukumar bebeji suka nufa cikin wani gari mai suna cutar biki .

Zuwansu ke nan wani Farin ciki ya rufe Ruma , wani irin zumud'i take jikinta na rawa, kallo guda taiwa gidansu tasan kwarai arzikin babansu ya karu, sai dai Allah yasa wannan azzalumin yayan baban nasu ya mutu wanda ya yi sanadin shigarta wannan rayuwa,

Da gudu ta fad'a cikin gidan tana kuka , taci karo da wani dattijon mutum yana alwahar azahar , tabbas shekara shida ba wasa ba , dattijon da sauri ya mike yana kiran sunan Allah cikin mamaki yana kallon Ruma , da gudu ta rungume sa cikin kuka tana cewa , "Baba ni ce , ni ce baba ."

A lokacin su Ummi baby suka shigo suna kallon yadda duk mutanen gidan suke rungume Ruma cikin tsananin kewarta,

bayan komai ya lafa Ruma ta gabatar da su Kalid, nan babu 'boye-boye ta sanar musu irin rayuwar da tai ,
ita dai mahaifiyar Ruma farin ciki take sosai da ganin yarinyar ta , bayan Ruma ta tambayesu ina baba Salisu, suka tabbatar mata da yana gidan yari , sakamakon laifin da ya aikata na yiwa yara fyade a cikin kano , aka kaishi kotu,

Wani farin ciki ne ya sake lull'be Ruma , yau kwanan zaune sukai cirrr ana labarin abubuwan da suka faru .

Washe gari mahaifin Ruma wato Alaji muhd ya yi musu bizar zuwa Niger a jirgi , da Kalid da Ruma da Ummi baby suka tafi .

Matukar zumud'i ke tattare da Ummi baby kan taje ta ga nata a halin ,

aiko da wajen la'asar suka sauka a Nijer , a halin yanzu Ummi baby matukar shau'ki take sosai ta ga wani cikin a halinta ,
bayan su isa kofar gidan ta ga babu abin da ya canza kawai sabon fenti ne da bai jima ba , wasu hawaye taji sun zubo mata kawai cikin takun 'yanci ta 'bude kofar gidan wacce ke had'e da gate , suma su Kalid suka bi bayanta


ba tare da ta yi sallama ba ta shiga tsakar gidan , kawai wasu hawayene da kasala suke biye da ita, idanunta takai kofar d'akin falon su ,wanda ta ga ta kalma da kuma tashin sautin hayaniya , kawai tasa kai tana kuka ta shiga falon ,

wata tsohuwa ce mahaifiyar babanta ta mike tsaye , mahaifinta da mahaifiyarta da 'kanwarta Aisha da taji wani arnen kitso da kunshi da gyaran fata , duk suka tashi tsaye .

Ummi baby kawai fad'uwa tai ta sume , duk sukai kanta .

Bayan ta farka kuwa sai murna ,"me yasa za ki tafi ki barmu aunty Ummi. "

Aisha ta fad'a tana kuka , Ummi baby ta basu labarin rayuwarta da kuma sanadin tafiyarta , har yanzu mahaifin Ummi baby yana sonta matuka , ya yi farin ciki sosai ,

A lokacin ake tabbatar mata bikin Aisha ake domin sauran kwana biyu d'aurin aure .
murna dai kamar ta kashesu suma makota da abokan arziki suna samun labari suka ltaho , harda saurayin Ummi baby wanda ya yi mata ciki , yazo da matukar murnarsa.

Washe gari
Su Kalid suka shirya , mahaifinsu Ummi baby ya tabbatar wa Kalid da yase masa mota tana kano tana jiransa, ya ba wa Ruma kud'i kimanin..........,tare da basu hakuri wai sun zo a ga'bar bikin 'kanwar Ummi baby, aiko sun yi matukar godiya , da kuka su Ummi baby suka rabu yayin dasu Kalid suka dawo kano .

Kalid yana isowa ya sami gallelitar motarshi mai tsada da kyau ya yi matukar murna .





BAYAN SATI


Yau kwanan Zainab biyu a Kaduna gidan Zakariyya, abin ya yi armashi da tsari .


A halin yanzu babu abin dake damun zukatan Ruma da Ummi baby suna cikin farin ciki da kwanciyar hankali tare da ahalinsu .

Saurayin Ummi baby ya matukar nadama da neman gafara , hakan yasa yake sanar da ita har yanzu yana kaunarta kuma zai aure ya zauna da ita cikin soyayya.


A 'bangaren Fadeela kuwa tana samun sau'kin aikin da an kai mata , ta rame sosai tasa tunanin Inna a ranta ga rashin kulawa da bata samu , tana fad'a a ranta cewa tafi kowacce mace a sara a duniya , domin a halin yanzu mace juya ta fita amfani tunda ita akwai mahaifar a jikinta , ita kuwa fa .

Amma ta d'an sami sau'ki tunda Zainab tayi aure a kusa da ita , domin tasan tabbas Zainab ba zata gujeta ba .






Alhamdulillah Rabbil alamin .

Anan na kawo karshen labarina mai suna 'KAWAR KARUWAI,
Ina addu'ar kuskuren da nai Allah ya yafe mini , ya kuma ganar dani dan gudun sake aikatawa, abin da nai Daidai Allah ya haskaka mana .
Wanda kuma suka hango kuskuren ko matsala su sanar damu mu gyara ba a ringa zaginmu ba ko aibatamu .
Ina marhabin da duk shawar-shawarinku masoyana Allah ya bar zumunci da kauna .



Sannan kuma ina muku albishir da sabon labarina mai zuwa gare ku .

Wanda ya samu ingancin tsari
'kir'kira
Shiryawa

Mai suna MARUBUCIYA wanda wannan labarin sadaukarwa ne ga dukkan Marubutan kasata . Yana tafe gare ku masoya

FATIMA ABDALLAH KANO

( Autar marubuta).
Bissalam .


7 / 7