JAMILA Completed book by Miss Green .txt

Author :  Rabi'atu Bashir Abdullahi Category :  True Life Story

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 21.7K words

gaba kud'aya ya canza.




Sun shaidawa Mlm MATAR tana da ciki,harma tayi b'ari sai dai har yanzu bata San inda kanta ya ke ba.




Dai dai nan Jamila ta fashe da wani irin kuka tana kallon namesake d'inta sannan ta ce in tak'aice miki sai da nayi kwana d'ai_d'ai har bakwai sannan nasan inda kaina ya ke.




Bayan na warke tsaf bisa kulawar likitoci da Matan Mlm don Mlm ya basu duka labarin abinda ya faru.




To tun daga nan na koma Gidan Mlm da zama,in tak'aice miki Jamila sai da nayi wata 1 agidan Mlm sannan na fara sakin jikina,don suna bani kulawa Sosai,don Amaryar Mlm macece mai matuk'ar kirki da Jan mutane ajiki.






"Kuma Jamila kin k'ara jin maganar gida kuwa?".




"Hmm".


"Tunda ganan ban k'ara jin labarin gidaba,sai dai har y'an gida ba,Amman ina matuk'ar jin tausayin halinda Masoyana zasu shiga musammam Mama,Baba,Fatima,da Ummanta".




Kuka sosai Jamila ta fashe da shi,Namesake d'inta na rarrashinta.








" Hmm Jamila kin gama naki labarin saura labarina domin idan kikaji nawa naki ba komai bane".










To sai Ku biyoni don jin labarin Jamila 2 itama.










*Miss green ce*
๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€
*_JรMร‰ร‰Lร‰R_*
๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€
*BOOK2*


Labarin Jamila2








~ Na ~


_*Ummu Maher(Miss green๐Ÿ’š๐ŸŒฑ*_






16<<>>17




*Jihar Bauchi*


.....Ni Y'ar asalin jihar Bauchi ce mahaifina mai kud'i ne sosai don yana 1 daga cikin mutane masu arzik'i wad'anda ake ji dasu a K'asarmu Nigeria kuma na kasance y'a d'aya tilo awajensa ya kuma d'auki son duniya ya d'oramin,Mahaifiyata ta rasu tun ina shekara5 ta sanadiyyar Haihuwa.






Sai ya zamanto duk wata k'auna da uwa zata bawa Y'ar ta ina samu gun Mahaifina,akwai watarana da bazan tab'a mantawa da ita ba.




Tun ina shekara 8 aka d'auramin Aure da K'anin Matar Mahaifina don bayan rasuwar Mahaifiyata Mahaifina ya yi Aure,sunanta Sakina su y'an asalin kano ne Amman a wani k'auye suke Fulani ne na asali.




Mahaifina yaje Neman Aurenta har garinsu Amman fir suka k'i,in har yana son Y'ar su sai sun gindaya mai wad'ansu sharud'a idan ya cinye sharad'an to zasu bawa Y'ar su Aurensa.




Hakan ce kuwa ta faru bayan ya nemi jin sharud'anne yaji abinda ya rud'a sa,wai indai yana son Sakina sai dai su Aura wa y'arsa suma d'ansu,wai don masu kud'i idan suka Auri y'ay'ansu mantawa suke dasu Amman indai har haka ta faru to dole su waiwayesu.




Allah ya Sani ba haka suka bar Mahaifin Jamila ba wato Alhaji Bashir,don su Wad'annan kalar fulanin akwai asirce mutum.




Yana ji yana gani suka d'auki Jamila suka bawa Harisu aka d'aura Aure,ita dai Jamila koda alokacin bata da wayo taji ana cewa ita aka d'aurawa Aure.




Shi kuwa Harisu da wayonsa don alokacin ya kai shekara 20 aikuwa awannan lokacin Alhaji ya biyawa Harisu Kud'in makaranta ya fara zuwa.






Kuma anbar cewa sai Jamila ta mallaki hankalin kanta sannan zata tare,su kuwa y'an uwan Sakinat musamman Mahaifiyar Harisu, don ita Y'ar uwace ga Babar Sakina don ita Sakina bata da k'annai Maza sai mata.






Mahaifina yana da sha'awar kaini waje inyi karatu,don haka bayan aurensu da Sakina sai ya fitar da ni waje don yin karatu,kuma har yanzu Y'anwansa Dana Mahaifiyata babu Wanda yasan ya aurar dani don yana tsoron sanar dasu shiyyasa ya bari har Jamila ta mallaki hankalinta.




Matar Babana kuwa ba k'aramin bak'in ciki ta shiga ba don jin Mahaifina zai kaini k'asar waje,nan ta fara sababi wai da Aure na za a kaini wata k'asar karatu.




Bak'aramin artabu aka shaba har dai aka samo kanta ta hak'ura,na tafi k'asar India karatu.













<>


After 5years
Bayan shekara biyar


Wata budurwa na hango wacce ba zata wuce shekara 16 ba kyakkyawar gaske don kyawunta ya yi matuk'ar bani tsoro kamar irin y'an matan Indian nan,sai da na k'arasa kusa da ita sannan na hango Ashe Jamila ce,tana zaune kan gras tana karatu don ayanzu Jarrabar fita daga Secondary suke.




Tayi nisa akaratunta sosai kawai sai ta jiyo wani k'amshin da bata tab'a jin k'amshi mai dad'in irin wannan ba,maze wa ta yi ta cigaba da karatunta Amman ina ji ta yi k'amshin yana k'ara kusanto ta.




Wata murya taji naji mai dad'in gaske tana yimin sallama da sauri na d'aga kaina don ganin mamallakin wannan zazzak'ar muryar gaba na ne ya yanke ya fad'i ban sanma na tashi ba tsabar daburce wa kallon2 muka shiga yi dashi irin kallon k'udannan.














_Mu had'u agaba don jin waye wannan_










*_MISS GREEN CEโœ๐Ÿป_*
๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€


_*Jร€MรˆรˆLรˆR*_


๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€




~ Na ~
*_Ummu Maher(Miss green)๐Ÿ’š๐ŸŒฑ_*




Wattpad Name
@Rabiatu222








18<<>>19




.......murmushi ya sakarmin sai da dimfil d'in shi ya lotsa,nima ban San lokacin da na sakarmai murmushi ba.






"How are u"


Cikin cool voice d'insa mai dad'in sauraro,amsa masa na yi da.




"I'am fine"


Sai da gabansa ya fad'i tsabar jin muryar da bai tab'a ji ba,muka zauna kan wasu kujeru na makarantar irin na simintin nan,Kallo ya ke yi sosai,sai na tsinci kaina a matsanancin jin kunyarsa don haka na sunkuyar da kaina,sai na tsinkayo muryarsa ya na cewa.




"Sunana Khalid"
"Ni haifaffan garin Kano ne a k'asar Nigeria mahaifiyata da Mahaifina suna k'asar England a yanzu inada k'annai uku duk mata ni ne d'an fari a gidanmu, ayanzu ina a matsayin lecture a awata makaranra mai suna Borney high college.






Kinji ta k'aitaccen tarihina,saura na ki nan nima na fara bashi ta k'aitaccen tarihina,a nan muka cigaba da hira.






To fa tunda ga wannan rana sai muka zama kamar wa da k'anwa, matuk'ar banga Khalid ba ko bacci bana iyayi, wata rana har fita bakin makarantar na ke yi bakin makarantarmu don inga tahowarsa,Ashe yana cikin makarantarmu harda gidansa guda a quarter's,tunda na gane b'angaren da ya ke kullum ta bakin tagar d'akinsa na kezuwa nida wata k'awata Khausar,muyi ta lek'ensa,harya gano hakan ya wata rana ya ke cemin indai na zuwa b'angaren malamai saboda gudun matsala,nan dai muka cigaba da hirarmu don yanzu munshak'u sosai yadda d'aya ba zai iya rayuwa babu d'aya ba.










Alhmdh yanzu mun gama jarrabawa sai shirye_shiryen tafiya gida,Dady na da Kansa yazo d'aukata,har mun shiga mota na ce"Dady banyi wa Malaminmu sallama ba yana da kirki sosai wallahi shine ya ke koyamin karatu",na fad'i hakan ina kallon fuskar Dady na,dariya ya yi sannan ya ce to je ki kirawomin shi".




Ina fitowa na nufi sashen Malamai sai dai ina tuno da maganar da ya fad'a ya ce indai na zuwa sashen Malamai,wani Malaminmu na gani mai suna Salim khan d'an asalin k'asar India ne,na tambayeshi Sir Khalid,ya ce min ai ya koma bakin aikinsa tun jiya da daddare ya tafi.




Kasa motsawa na yi,na fara tafiya har na shiga motar.




"Lafiya Jamila"?


" ina Sir d'in"?


Mahaifina ne ya ke yi min wannan tambayar,shiru na yi kamar ba zanyi magana ba sai na ce.




"Baya nan".


Na fad'i hakan kamar zanyi kuka," Jamila akwai wata matsalar ne?"naga kamar za kiyi kuka?k'ak'alo murmushi na yi sannan na CE"babu komai Dady,muna isa Airport jirginmu ya tashi sai Nigeria,muna isowa gaba na ya dinga fad'uwa don bansan wainar da ake toyawa ba don rabona da gida tun bayan da na gama primary na tafi India karatu,tuni na ji kewar k'asata ya kamani,duk da ina ganin Dady na duk wata yana zuwa min visiting, Amman na yi missing d'in y'an uwan mahaifiyata tare da childhood d'ina.








Tun daga nesa na hango matar Mahaifina fuskarta babu yabo babu fallasa,tare da wani saurayi suna kama sosai sai dai shi ya fita gogewa.






Da murna ya tareni ban Ankara ba naji ya rungumeni,sai da numfashina ya kusa d'aukewa,na juyo cikin fushi na b'anb'areshi kawai sai na ji ya CE"haba Jamila kefa matata ta CE".












Please kuyi hak'uri na yi tyip k'ad'an๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป.


Fans na Jamila INA gaisheku aduk Inda kuka na gode da k'aunarku za kuga na bar GRP to kuyi min uziri wani Abu ne daban ๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป.












เฆŠเฆŠเฆŠเฆŠเฆŠเฆŠ
Miss green ceโœ๏ธ
เฆžเฆžเฆžเฆžเฆžเฆž
๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€


_*Jร€MรˆรˆLรˆR*_

๐Ÿ€โœจ๐Ÿ€




~ Na ~
_*Ummu Maher(Miss green)๐Ÿ’š๐ŸŒฑ*_




Wattpad
@Rabiatu222






20<<>>21


....cikin fushi Na ce"ban gane Miji na ba? ta ina na zama matarka ni ban Sanka ban tab'a ganinka ba?sai kawai ka ce ni matarka ce?saboda ka rainamin wayo,na kalli Dadyna na ce"Dady wannan kuma waye Mara hankalin da ya samu damar rungumeni a gabanka kuma baka yi masa magana ba?sunkuyar da kai Abbana ya yi,baice komai ba ya bud'e murfin motar ya shiga,nima a zuciye na shiga gaba na zauna,sai da muka shiga motar sannan suma suka shigo,harararsa kawai na ke yi shi kuwa sai kallona ya ke yi kamar maye.










"Yanzu Alhaji wulak'ancin da y'arka ta yiwa k'anina Sooraj ya dace kenan?ko kuma so kake inyi magana kace na takurawa y'arka,shiyyasa ka d'ebeta ka kaita k'asar turai tunda ga Primary har secondary saboda kada in cinye maka y'arka,ni na tabba ta idan da ace kabar Baby a k'asar ta yi karatu to da sun saba da Sooraj,da bata yi mishi wulak'ancin da ta yi mishi ba,kuma kada ka manta Sooraj har yanzu yana nan amatsayin mijin Baby?" Don haka kajawa y'arka kunne ba'a wulak'anta min K'ani,shiru Dady ya yi har Matarshi tabar d'akin,yayi tagumi yanzu ta ina zai fara wannan abubuwan,daya San haka zai faru da bai aurawa y'arsa Sooraj ba,domin kuwa ayanzu Sooraj ya canza a yadda ya sanshi,don Sooraj yanzu shine shaye_shaye,bin mata,yawace yawace marasa dalili.






Da daddare muna lunch a dining, Abbana na ya kirawo sunana a hankali, na amsa ina kallon sa don bai fiya kiran sunana ba saboda sunan Mahaifiyarsa ne,Shiyyasa ya ke kirana da Baby,shiyyasa yanzu da ya kirawoni da Suna Jamila azahiri na ji gabana ya dad'i don bai tab'a kiran sunana haka ba sai yau.






"Baby ki kalli wannan na kusa da ke sosai?ya nuna min na kusa dani,na kau da kaina don tun ranar da ya rungume ni a airport ban sake yi mai magana ba,don na lura bashida mutunci ko kad'an ballantana wani Abu waishi kunya.




Na kalleshi na ya tsina fuskata na juya ba tare da na ce komai ba,hakan ba k'ara min bak'anta ran,matar mahaifina ya yi ba dama shi kansa Sooraj d'in.




" wannan yayanki ne sunanshi Sooraj,so you have to respect,kinji Baby na ki d'aukeshi a matsayin Brother na ki don haka na gama magana ta, yana fad'in haka ya haura sama ya barmu a wajen,nima kuwa ina ganin ya tashi na bi bayanshi don kwata_kwata bama shiri da Momi wato matar Abbana.






Hankali na a matuk'ar tashe na dube wayar tawa har yanzu number switch off,shin me yake faruwa da Sadiq ne,ya tafi babu Sallama sannan gashi haryanzu number bata shiga.kiran Hamida ne ya shigo wayata k'awata ce tun daga Jss1 har zuwa ss3 a India, na d'auka munsha hira sosai,kusan sai yanzu zuciyata ta yimin dad'i tun zuwa na,don Gidan namu gaba ki d'aya babu dad'i sam,Abbana ba zama ya ke yi agidaba daga ni sai Sooraj da Momi.








"Dady ina son zuwa Kano wajen Goggo yabi kakata ta wajen mahaifiya,Dady bai hana niba sannan ya bani kud'ad'e isassu ya ce gone za,a kaini Shopping in siyayya ta zuwa kano,na yi murna sosai don inason ganin dangin Mahaifiyata.




Tunda Dady ya fad'awa matarsa tafiyata ta kasa ta tsare tana ta faman masifa,ni kuwa ko kallo bata ishe niba,don nagama yarda Momi bata sona,tunda na je India bata tab'a nemana ba da zummar ziyarta na,sai yanzu don na ce zanje dangin Mamana za tayi fad'a.






**
" yanzu Adda abinda Mutuminnan suke yi acikin gidannan ya dace?haryanzu bai fad'awa y'arsa cewa ni Mijin ta bane,wai ita Y'ar so,to wallahi Adda darajarki kawai ya ke ci idan badon haka ba da na gama dashi wallahi,da shi da y'arsa don wallahi naga take_takensa so ya ke yi ya hanani Aurenta,to wallahi bai isa ba,yadda na keson yarinyar nan ko ke bana so haka?amatsayinki na Yayata,don yarinyar ta had'a komai na Y'a mace,don haka ki jawa mijinki kunne Donni bazan d'auki wulak'anci ba,yana fad'in hakan ya yi ficewarsa yana zuk'ar tsabar sigarinsa,yana busa ta sama sosai irin na y'an duniya.






Ranar litinin da sassafe na fito cikin shirina,na tafiya ina janye da troly na,babu kowa a farlon sai masu aiki suna sanye cikin uniforms d'insu suna aiki.




Sashen Dady na tafi ina zuwa shima Dadyn yana fito wa yana saka link d'in rigarshi,Momi na bayan shi rik'e da hularshi tana ganina ta had'e rai nima ban ce da ita komai ba,na gaishe da Dady sannan itama na gaisheta ko kallona ba ta yi ba,ballan tana in saka ran zata amsa Nima ban damu ba,na kalli Dady na da yake yimin dariya wai na tashi da sassafe duk zumud'in tafiyarne,sai nima nayi dariyar cikin shagwab'a ina b'oye fuska.




D'aga wa Dady na hannu na ke kamar zanyi kuka,driven ya ja muka tafi muna fito wa na hango motar Sooraj shima yana shigowa da Alama,kuma ba agidan ya kwana ba don tun jiya banji motsin sa ba,na turo bakina tare da yin tsaki na juyar da kaina don ya tsuramin idanu sosai kamar wani soko.


Sai k'arfe 12 muka isa kano,sai k'ofar Gidan kakannina na wajen Mahaifiyata,ban gane Gidan ba sai da driven gidanmu yace min Alhaji yana aikoshi nan Gidan sannan na gane,don Gidan ba ki d'aya an canza mishi fasali ya yi wani irin kyau,rabona da Gidan kusan shekara 7 kenan,bayan rasuwar Mahaifiyata, ina shiga Gidan na hau raba idanu don Gidan sashe uku ne yanzu,wata Y'ar tsuhuwa ce na gani ta fito daga wani new building me kyau,tana ta faman mita wai an fiya ajje mata takalmi k'ofar d'aki,koda ba'a gaya min ba nasan Goggo ce kakata,ta vayanta na je na rungumeta ina dariya.




"Na shiga uku ni Rabi wani gamon na yi kuma....maganarta CE ta sark'e ganin Jamila tana dariya, koda ba'a gaya maka tasan jikarta nan don har yau Jamila kama ta ke da dangin mamarta.






" Sadiq yau fito ka ganemin wai Jamila ce ko kuwa?"




Donni tunda ubanta ya kaita k'asar fararen fata ban sake ganinta ba Amman ai Jinin baya b'ata,ni kuwa har lokacin dariya kawai na keyi ina tsaye ajikin troly na,dariya ta ce ta sark'e ganin sahibina Sadiq sanye da jallabiya,hannunsa an nad'eshi da bendeji,shima numfashin shine ya kusa d'aukewa ganin Sahibarsa Jamila, da gudu na taho na tungumesa sosai,Inna kuwa ta hangame baki ta kasa rufewa.








*Miss green CE*
Don Allah idan kika karanta kiyi min share


Vote
Share
Comments.
*_๐Ÿ€JรMรˆรˆLรˆR๐Ÿ€_*







Ummu Maher(miss green)๐Ÿ€


_Wattpad@Rabiatu222_






_22/23_




Saurin juyowa na yi na ce"Inna rufe bakinki kada b'era ya shiga?"Shi kuwa Sadiq k'ank'ameni ya yi sosai ina mamakin ya ya akayi Sadiq yazo gidannan alhalin ban bansan shi acikin dangin mu duk da bana zuwa garin mahaifiyata amman muna chart da wasu daga cikinsu".






"Wai ni a ina kuka san junane Jameela?" don naga tunda kika shigo kuka rungume juna ni kuma kuka barni a tsaye,?Sadiq ne ya bata labarin komai da yadda muka k'ulla soyayya duk sai da ya bata labari.




Murna awajen Inna ba'acewa komai,don daman abinda ta dad'e tana jirane Allah ya kawo mata,na had'a jikokinta Aure,nan kuma Inna ta ke bani labarin dan ganta ka ta Da Sadiq,da Mahaifinsa da Mahaifiyata,uwa d'aya uba d'aya suke,Baban sadiq shine babba sai Mahaifiyata.








"Jameela nasan za kiyi zaton yaudararki zanyi a,ah tafiya ce ta kamani Allah ya yi banyi miki sallama ba saboda tashin hankalin da na ke ciki,mahaifiyata ce Allah ya yi mata rasuwa!"




"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yaushe ta rasu?"




"Wata 1 kenan yanzu sanadiyyar haihuwa, ta rasu da kwana7 ni kuma na yi hatsari to shine ya hana ki ji komai,don sanda na yi hatsarin bansan inda kai na ya ke ba,amman kiyi hak'uri da abinda na yi miki.....




"Don Allah kayi hak'uri wallahi ban san ma anyi rasuwa ba,amman ka yi hak'uri".






Daga nan Masoyan suka cigaba da hirarsu cikin so da k'aunar junansu.








***
Hutun Jameela a kano ya yi mata matuk'ar dad'i sosai,don tana samun kulawa so da k'auna awajen masoyinta harma da y'an uwanta,kulawar da bata samu a da ba yanzu ne ta ke samu,ga wata shak'uwa mai k'arfin gaske da ta shiga tsakaninsu.


Sai dai abinda bata sani ba shine mahaifinta har ya fad'awa Inna tasan komai,sai dai fa Inna ta buga tsalle tace babu wanda ya isa ya yi wa y'arta Auren dole,wannan munafukin Auren ma du kuncesa domin kuwa babu yadda za'ayi su yadda da wannan had'in,babu yadda mahaifin Jameela ya iya, don haka yaja bakinsa ya yi shiru bai ce komai ba.




Abinda bai sai ni shine?Matarsa tasan komai a game da abinda ya faru don duk wayar da ya ke yi tana lab'ewa ta ji me yake cewa,don haka ta shirya yadda zasu b'ullowa lamarin ita da k'aninta Sooraj.








" kin san Allah babu wanda ya isa ya hanani Auren Jameela matuk'ar kuwa aka hanani to komai ma zai faru,don ko kece kika hanani Auren Jameela to ki kuka da kanki"!ya juyo yana nuna yayar tashi da hannunsa.




Tana matuk'ar mamakin yadda aka yi Sooraj ya ke mugun son Jameela don ta yi imani Sooraj zai iya ki sa akan hanashi Auren Jameela.






"Ni shawarata kawai idan ta dawo ku gudu da Jameela don hakan shine zai kawo k'arshen komai,don na fuskanci Uban nata mata lallab'ata kawai ya ke yi bason Auren ya ke yi ba."




"Babu inda zan gudu da ita?ko su so?ko kada su so?bai dameni ba ya zama dole Jameela ta zama mallakina,haba shekara nawa ina dakon yawo da soyayyarta acikin zuciyata kuma na iya hak'ura da Aurena da ke kanta,to yanzu ya zama dole Jameela ta zama mallakina na gaya miki.




Sai da ya kusa buge Yayar tashi don tsabar b'acin ran da Sooraj ya ke ciki,don a rayuwarsa babu abinda ya keso Irin Jameela,ko uwar da ta haifeshi bai damu da ita ba kamar Jameela,donshi a ganinsa Jameela ita ce rayuwarsa,don ko yanzu Jameela ta mutu to shima ya zama gawa.




๐Ÿค”Ni kuwa Ummu Maher na ce,Son ma so wani k'oshin wahala.














***
Yaya Sadiq zan cen da nake gaya maka ba k'arya bane Mahaifina ya yi min Auren dole,a tunaninsa ban sani ba don na dad'e da sanin wannan labarin kawai sai bana nuna wa ne,kuma nasan kud'in mahaifina ne ya rud'esu,Amman mahaifina ya dad'e da Aurar dani........






" What Jameela kin san me ki ke cewa kuwa?"












Please kuyi hak'uri nayi tyiping kad'an rasuwa aka yimin ne.๐Ÿ™๐Ÿป








Ummu Maher ce๐Ÿคž๐Ÿป๐Ÿ’šโœ๏ธ
*_๐Ÿ€JรMรˆรˆLรˆR๐Ÿ€_*






By


_Ummu Maher(Miss

4 / 8