JAMILA Completed book by Miss Green .txt

Author :  Rabi'atu Bashir Abdullahi Category :  True Life Story

Chapter   8 / 8

21K to 21.7K   out of 21.7K words

kuka tana neman yafiyar Jamey tare da gaya mata inda sauran dukiyar Mahaifinta suke.


Bashir ne ya tona asirinsu Suraj na kashe mahaifin Jamey da sukayi dpn haka nan da nan case ɗinsu ya ƙaru aka canza musu wuri wanda matuƙar kaje wannan wajen to sunanka sorry,kuka da na dama babu irin wanda Suraj da Mama Hasiya ba suyi ba ƙarshe dai suka haƙura.




A yanzu dukiyar Jamey ta koma hannunta gaba ki ɗaya dama dukiyar da su Mama Asiya basu taɓa ba duk an dawo mata dashi,yanzu komai ya zama tarihi sai dai fatan Allah ya bata haƙurin jure rashin mahaifinta don har yanzu matuƙar ta tuna mahaifinta da mahaifiyarta kuka tz ke sosai don ma Allah yasa Bashir yana matuƙar kula da ita sosai,baya son ɓacin ranta tattalinta ya ke tare da mayuƙar ƙaunarta,farin cikin da Jamey ta rasa acen baya a yanzu ta sameshi nin kin ba nin kin.






Rayuwa kenan juyi-juyi ce duk abinda ka aikata wataran shi zaka girba walau mai ƙyau ko mara ƙyau,har gida yaya deen yazo ya nemi yafiyar Jamcy yana kuka kamar zai shiɗe Allah ya taimaka ranar ma Ahmad baya nan da sai anyi ɓatacciya,ban sanda na yafe mishi ba ko babu komai ɗan uwa na ne.




A yanzu aurensa da Anty Safiya ya mutu,duk son Yaya Deen da ta ke yanzu sai dai ta kalleshi don ko kallon inda ta ke bayayi don gani ya ke duk matsalar da ya shiga ita ce sila,ɗan su ɗaya yana nan abin tausayi.


Ita kuwa Anty Safiyya yanzu ta yi aure kusan sa an Abbanmu matansa uku ita ce ta huɗu,ranar da na je gidan na ganta kamar zan mata kuka don ta zama abin tausayi,sosai na taimaka mata don d alhmdh mijina ya wadatao ni sosai, kishiyoyinta sun saka ta agaba sosai wai juya ce don tunda tazo gidan bata taɓa ɓatan wata ba.ina ji ina gani haka nabar anty safiya cikin wannan halin don daman ita duniya ta isa kowa riga da wando.








Tun safe Jamey ta ke ta kuka har da shagwaɓa wai sai taje gidan Jamcy babu yadda Bashir ya iya a haka ya ɗakko Jamey tana ja da ƙer don yanzu cikinta ya tsufa.




Ita ma Jamcy yanzu cikinta ya tsufa sosai haihuwa ko yau ko gobe,ranar a gidan Jamey ta yini suna zaune suna kallo aka nuno wata matashiyar mata wacce ba za ta wuce shekarunsu Jamcy ba,mutane suna ta mata kirari da Uwar marayu matar gwamna.






Da sauri Jamcy ta tashi duk da tsohon cikin da ya ke jikintanta ce"Daman zan ƙara ganin Fatima a rayuwata?".




Nan Jamcy ta ƙara faɗawa Jamey wannan itace Fatiman da ta ke nema,suka yanke washe gari zasu je govn hause don neman iso wajen Fatima.




Basu sha wahala ba wajen yardar mazajensu don da kansu suka kaisu wajen Fatima,Allah ya taimakesu da ranar Fatima tana gida bata fita ba,aka yi musu iso da ƙer suka ganta don ma Fatima macece mai son mutane ce.








Da gudu Fatima ta rungume Jamcy tana kuka sosai,dukansu kukan suke murnar ganin junansu ta cikasu sosai.


"Fatima yanzu muna gaei ɗaya ashe har kinyi Aure govn amman kika kasa nema na".


"Jamcy ba zaki gane halin da na ke ciki bane don wallahi babu yadda banyi ba in nemo inda kike amman abu ya faskara,yanzu Umma na ahekararta ɗaya da mutuwa sakamakon ciwon zuciya,anan nema governor ya aureni don har gidan radio naje daga nan yaji tausayi na ya aure ni,jamcy na yi baƘin cikin rashin dangi don ko babu komai idan na ganki nasan ina da dangi amman na nemeki Jamcy amman abu ya gagara.





Gaba ɗayansu suna cikin farin cikin ganin junansu kuma ko wannensu ya bada labarin bayan rabuwa,bayan sunsha kukan rashin Umma.




Ɗan Fatima ɗaya abdul ƘyaƘƘyawa irin asalin fulanin yola.












*After five years*




a yanzu Jamcy tana sa ƴaƴa uku twins duk maza da kuma mace,Jamey kuwa tana da ƴaƴa biyu duk maza.




Masha Allah yanzu ma auratan suna zaune cikin aminci da ƙaunar junansu.














Tammat bi hamdillah


Anan na kawo ƙarshen wannan book ɗin mai suna Jamila,dafatan zamu amfanu da abinda aka karanta.






Aƙwai mistake na wattpad user na


Rabiatu333


shine user na na wattpad.






Domin sharhi ko gyara
07068606171

8 / 8