JAMILA Completed book by Miss Green .txt

Author :  Rabi'atu Bashir Abdullahi Category :  True Life Story

Chapter   6 / 8

15K to 18K   out of 21.7K words

sun tsani surukar tasu,don babu abinda Mazajensu ba sa yiwa Mahaifiyarsu,wannan ne ya ke k'ara musu haushinta don sunyi su raba su Amman sun kasa,sai su kirawo inna Uwargida sau biyar ko Hajiya Ladi awaya ba su kirawo surukarsu sau 1 ba,don ma wani lokacin idan sunyi waya da mahaifiyarsu idan ta tambayi matan nasu su kirawo su su ba su wayar Shima ciki² suke amsawa don idan akwai wacce suka tsana to bai wuce Surukar tasu ba wato Mami, don haka sai suka k'ulla abota da su Inna Uwar gida,don daman duk wata gulma daga gurinsu ta ke fitowa shiyyasa suke zuwa wajensu.






Sosai Twins suka zage dantse suka ci Dinner da aka baje musu,ita kuwa Mami sai kallonsu ta ke cikin so da k'aunar y'ay'an Na ta.



Suna yi suna kallon y'an biyun Mlm Jamey da Jamcy Wanda har yanzu ba su saki jikinsu ba kasan cewar irin kallon da suke musu,don har yanzu les d'in nan lemon green d'inkin Riga da siket gashi ya d'an kama su,mussaman ma Jamcy ita CE me jiki.






Suna cikin cin abincin Hamida ta CE"Wai Ammi inasu Anty Amira suka shiga ne gashi ana cin abinci babu su."?




Rabiatu CE ta CE "Suna wajen Inna Uwargida kin San ita CE surukar ta su."


Ammi CE ta katsesu da cewa"wai ina ruwanku da inda suka shiga ne?kun bi kunsa ka yara a gaba da mitarku cen inda suka je ai za suci don da cen da nan duk 1 ne."


Tsit! sukayi ba su k'ara magana ba haushin matan yayyen nasu Na k'ona musu rai,don suna sane da yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu.





To su ma dai Twins d'in Na Ammi sunji haushi matuk'a ta yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu suna sane kawai ido suka saka musu don masu iya magana sunce shiru ma magana CE.








Muna gama cin abincin su Anty Maryam suka shigo suna jifanmu da mugun kallo,babu Wanda ya kulasu suka kalli Mazajen nasu sannan suka CE "Am: daman zamuje gidane muma mugana iyayenmu"?.




Banza suka yi musu sai da Mami ta CE" Ku yi tafiyarku ai dama dole kuma kuje gida".


Sun d'an ji dad'i kad'an don sun San indai ta mazajensu ne ko zasu kwana suna yi musu magana ba zasu amsa ba,Amman duk da haka Surukar tasu bata fita ba, suna fita suka fara gulmarta wai yanzu mazajensu sun zama remote control sai abinda uwarsu ta CE suyi shi su keyi.






Ko kafin dare mun share ko ina mun gyara tsaf har falo mun gyara harda b'angaren Twins d'in Mami tare mukayi aikin da su Anty Hamida yaransu tuni sunyi bacci.






"Jamcy kin kula da yadda wad'annan fitinannun Twins d'in suke bin mu da kallo Allah kamar Na yi fitsari a wando".






Dariya Jamcy ta yi sannan ta CE Ayya Jamey ni wallahi Na fiki tsorata dasu gasu da kyau kamar aljan......




Dariya sosai Anty Hamida ta ke sannan ta yi bud'a ta CE" ai insha Allah sai sun Aureku,Ku sharewa Mahaifiyarmu hawaye.






Kunya da nadamar maganar da mukayi suka hanamu d'ago idanu mu kalli Anty Hamidar da ke ta Smilling.












*Ummu Maher CE*
*_🍁☘️JAMILA☘️🍁_*








_True life story📗📙_






Na
_Rabi'atu B Abdullahi_
*Ummu Maher(Miss green)☘️*






Not edited......


🅿️36🟨37




Kallonmu kawai Mlm ya ke don yasan tunanin da muke yi bai wuce na had'uwa da danginmu ba sai ya CE"kuyi hak'uri Neman danginku a yanzu ya zama dole, saboda kuma ba zaku so Ku zauna haka ba tare da kunga y'an uwanku ba,don haka yana da kyau ayanzu kowaccenku ta shirya don yin wannan tafiyar".




" Ku tashi Ku tafi Allah ya yi muku albarka",jikin a sanyaye muka tashi zuciyoyinmu kamar zasu buga tsoro da fargaba ne suka had'u suka yi mana yawa,y'ar nutsuwar da muka samu kwana 2 duk ta tafi,muna shiga d'aki kowaccenmu ta shiga tunanin da zullumi".






"Jamcy bazan iya komawa gida a yanzu ba?ban shirya komawa rayuwar halaka ba don yadda suka Halaka Abbana babu makuwa nima sai sun halaka ni,don haka gaskiya ni dai bazan koma ba."




Hayawaye ne ya kwaran yowa Jamcy ta saka hannunta ta goge tana Jan zuciya ita ma ta fara magana,"Ban San me zance ba?bakina ya rufe hankali na ya gushe Jamey,ke kina ma da damar furta komai Amman ni na kasa furtawa,bana son abinda zai rabamu ni da ke Jamey".


Ga shi Mlm ya CE muyi shawara a game da Auran da zaiyi mana,na gwammace Mlm ya Auramin koma wanene?da in koma gida Yaya Safiyya da Yaya Deen su k'arasa min y'ar rayuwata wadda ta yi saura,a duniyata babu abinda n tsana irin mutum hud'u.




"Na farko shine Yaya Deen,Yaya Safiyya, sai Mama Asiya,da k'aninta Kamal,Sune wad'anda suka lala ta mana rayuwarmu Jamey" sune......






Bubbuga baya na Jamey ta yi tana rarrashi na ita ma tana hawayen Fuskarta,ina jin k'aunar Jamcy har cikin raina wato abinda ya faru dani tana jin shi a jikinta itama har ta kasa rik'ewa ta fad'amin,Lallai ya zama dole nima in tsani duk Wanda ya CE baya son Jamcy don yadda na ke jikinta ba'a fad'a.




Muna cikin wannan halin ne Mami ta shigo ta zauna tana me fuskartarmu ta CE "Yadda na kejin y'ay'an Dana Haifa acikina haka na ke jinku,zanfi kowa farin ciki idan aka CE kuma yau kun samu naku farin cikin, zan iya CE muku na fiku shiga wani hali a game da k'addarar Rayuwarku,Amman fa Ku Sani bazan tab'a goyon bayan abin da ba dai² ba".




Familynku sune Abu na farko da zaku ringa kalla a doron k'asa kuna jin dad'in Rayuwarku,Amman bai kamata Ku yanke alak'a da dasu ba tunda ba sune suka yanke alak'a daku ba wasu mutanane acikin su suka b'ata muku,don haka ni zan jagoranci tafiyar nan taku don asamu daidai to don haka daga yau zamu fara shiri ba sai gobe ba, don masu iya magana sunce da zafi² akan d'auki dutse".




Aranar mukaje kasuwa muka siyo kaya kamar zamu bud'e shago tsaraba da sauran abubuwa,Ammi ta yanke shawarar cewa Kano zamu fara zuwa gidansu Jamcy sannan Bauchi gidansu Jamey.






Muna zaune da daddare muna had'a kayayyakinmu Aunty Rabiatu na taya mu,don Aunty Hamida ta koma Sudan tun tuni sai Aunty Rabiatu ita kuma mijinta ne baya nan shiyyasa bata koma gida ba,sai ya dawo zata koma.




Wani almajiri ne ya shigo 1 daga cikin Almajiran Mlm ya CE wai Jamcy da Jamey Suzo?.




Kallon kallo muka shiga yi a tsakanin muka had'a baki wajen fad'i "inji waye"?.


" Mlm ne ya ce akirawo wai kuzo".


to muka CE sannan muka sanya hijabanmu har k'asa muka fito,Aunty Rabiatu ta cigaba da had'a mana kayan.






Muna shiga muka sunkuyar da kanmu,Ahmad da Bashir ne a zaune sunyi kyau cikin shadda ruwan dark Blue sai shek'i ta ke,ga Maryam da Amira sai cika suke suna batsewa haushin yaran na k'ara k'aruwa acikin ransu duk da basu San me za'a fad'a ba Amman sunji matuk'ar haushin ganin yaran a kusa dasu.














*Ummu Maher CE*
_*🍁JAMILA🍁_*






True life Story✍️




*_A story by🖊️_*


_Oum Maher(Miss green💚)_










_Dedicated to all my fans_






_*38to40*_




Guri muka Samu kusa da su Aunty Maryam da Amira da saurinsu suka matsa kamar dai sun ga wani abin k'i,a hankali Mlm ya kallesu sannan y kawar da kanshi yana mamakin matan y'ay'ansa yadda ko kad'an basa jin tsoron rashin kunya a gaban kowa.








"Ba wani abu ne ya tara mu ba illa son k'ulla aure tsakanin Ahmad da Jamcy,Bashir d Jamey Insha Allah a wannan wa......"




Wata irin ashar Amira t buga wato matar Ahmad don tsabar firgici ya yinda ita ma Maryam ta tashi tana sababi.




"Wallahi tallahi anyi kad'an kuma anyi k'arya a ce wai mu za'a had'a da wadannan tsintattun magen wa ya Sani ma ko y'ay'an karuwai.......






"Relax!abinda Ahmad da Bashir suka fad'a suma suna tashi tsaye suka nuna matan nasu cikin d'aga murya suka ce.




"Kuka k'ara wata magana a wajennan wallahi n lahira sai ya fiku jin dad'in duniya don muna aurenku ba wai yana nufin daku zamu mutu bane tunda ba don ku kad'ai aka Yi mu ba,kuma kada ku k'ara yiwa iyayenmu rashin d'a'a idan ba haka ba wallahi sai kun kwammace kid'a da makad'i,kuma Aure Babu fashi anyi shi an gama, kuma kada ku k'ara xagin yarannan d mummunar kalmominku kamar kunci naman kare,idan kuma ba haka ba wallahi ranku sai ya Yi mummunan b'aci,kuma ku fita daga d'akinnan kafin mu gama tattaunawa don bama buk'atar Marasa tarbiyya anan.




Suna fad'in haka suka zazzauna Mlm har lokacin bai ce musu komai ba,don ya Yi matukar mamakin rashin kunyar yaran basa tsoron,idon manya ko kad'an fatan shiriya ya Yi musu a cikin ranshi sannan ya cigaba da maganar da ya d'auko,da k'er Amira da Maryam suka zauna suna matsar kwalla tare da d'aukar alwashi akan wad'annan yaran Jamcy d Jamey,su kuwa bayin Allah wato Jamcy da Jamey sunyi tagumi kawai hawaye yana kwaranyowa daga idaniyarsu,na rashin mada fa da kukan rashin y'an uwansu a kusa dash,har yanzu Babu ko digon son Bashir da Ahmad a cikin zuk'atansu baron ba suyi musu ko wani abuba don Kyau,kud'i,ilimi,addini,duk sun had'a Amman zasu fi alak'anta hakan akan rayuwarda suka shiga a baya don har sun cire ran sake wata soyayya a gaba don su kan sun bar yin wata aba wai ita soyayya har abada.




*Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika*


Kamar yadda Ammi ta bukata haka kuwa a kayi don Kano muka fara zuwa wato garinsu Jamcy,munyi tafiya Sosai don daga Adamawa zuwa kano akwai nisa,Jamcy kuwa kuka kawai ta ke a mota don har yanzu zuciyarta ba ta k'aunar ganin wadannan mutun biyun,Yaya Deen,da kuma Yaya Safiyya wato Yaya ta wadda suka had'u da mijinta suka jefar dani a dokar daji saboda mijinta ya yimin fyede har ciki ya shiga suna tsoron tonuwar asirinsu.








Sai yamma muka shigo garin kano muna tafiya ina nunawa Yaya Ahmad hanya wanda tunda muka shigo motar ya ke ta kallona ta cikin glass ni kuwa sai kuka Na ke Mami na rarrashi na,daman ba mota d'aya muka shigo da su Jamey da Mlm da Yaya Bashir ba motarsu su uku daban ta mu daban.






Unguwar anyi gine² sosai wanda da k'er na gane gidanmu,an k'ara gyara gidanmu ya Yi wani irin kyau kamar gidan shugaban k'asa ko gwamna.




Sosai su Mlm suka yaba da kyawun gidanmu,har Mlm a fili ya ce "Allah sarki rayuwa ba kud'i ne jin dad'in rayuwar duniya ba,da kuwa Jamcy ta Samu farin ciki",ya goge kwallar da ta zubo Mishi n tausayin yaran guda biyu wad'anda ya ke jinsu kamar y'ay'ansa mafi soyuwa a arayuwarshi.




An canza duk security d'in gidanmu an saka sababbi wadannan har da bindigunsu sab'anin na da da Babu bindigo,a hankali na saka k'afafuna acikin gidan na shak'i iskar gidanmu wacce na ji ta har ruhina sai dai abinda ke cikin gidan yafi gaban wasanka,na kalli compound d'in gidanmu motoci sunfi goma kamar company sai da motoci.






Na kalli wajenda muke Shan iska ni da Yaya Deen d'ina, wasu hawaye ne suka wanke min fuska ta.






"Hajiya wajen wa kuka zo"?.




Tambayar da securities d'in suka Yi mana kenan,ba na kallesu da idanuwa da sukayi jawur Na ce "ni y'ar gidannan ce sunana Jamila na bar gidannan shekara uku baya",na fad'i hakan kamar zuciyata zata fito waje,wai yau ni ake tambaya wajen wa nazo?ni da gidanmu?wannan wacce irin rayuwa ce.




Da sauri securities d'in suka ce"are u sure?ke ce jamila da muka dad'e muna nemanki ?ke ce wadda muke nema shekara uku baya,koda ba'a gaya mana ba mun san ke ce Hajiya Jamila don kamar ku 1 da Hajiya Safiya don......




"Wait!" Na fad'i hakan cikin k'araji don ko sunan Aunty Safiya bana son ji a halin yanzu,da sauri na shiga cikin gidanmu har ina had'awa da gudu don na matsu inga, Mama na,Fatima,da Abbana.






Wani rantsatsan falo na iso mutane uku ne a farlon gidanmu umma na,da Abbana,sai K'anin Umma na Alhaji Adam.





"Jamila ta ke ce ko kuwa"?abinda Abbana ya fad'a kenan yana murza idanuwansa don gani ya ke kamar mafarkin da ya saba Yi ne.












More comments
More tyiping🖌️.




Ku tayani da addu'a n fara exam.








Vote
Share
And
Comments✍️.






UMMU MAHER ce
_*🍁 JAMILA🍁*_




By
_*Oum Maher(Miss green💚*_






_41&42_


....da gudu na rungume Mahaifina ina kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,sai a yanzu na k'ara tabbatarwa ba k'aramar cuta su Aunty Safiya suka Yi min ba,don da na rungume Mahaifina wata nutsuwa ce na ji tazomin wadda ada cen bani da ita.




Mama ma rungume ni ta Yi tana kuka shi kuwa K'anin Mahaifina yana gefe yana murmushi tare da kallonmu cikin so da k'auna,mun dau lokaci sosai a haka sannan muka saki junanmu,Amman har yanzu ina lafe a jikin Abbana,su ma su Mlm suka shigo suka zazzauna suna kallonmu gwanin sha'awa,Mlm kuwa wani dad'i ya ke hi yau ya had'a y'an biyunsa da iyayensu ya sauke nauyin da Allah ya d'ora Masa.





Jamey kuwa kallonmu kawai ta ke Yi cikin so da k'sunarmu,ta share hawayen da ya zame mata sana'a aduk sanda ta tuno da mahaifanta,yanzu shikkenan ita ba tada iyayen da zata fad'a musu damuwarta?ba ta da wanda za taji dumin jikinsa acikin iyayenta,wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin na saka gefen mayafi na ina gogewa,na tuno Mahaifina da yana raye bazai tab'a bari inyi kuka ba,Bashir ya zubomin idanu yana yimin alama da in dai na kuka,idan ba haka ba shima zaiyi kuka,ya Yi alamar yara idan zasuyi kuka,sosai abin ya bani dariya na manta sam agaban mutane na ke sai da Ammi ta ce"lfy y'a ta Jamey"?da sauri na ce Babu komai.




Bayani Mlm y Fara Yi musu sannan daga bisani ya fad'a musu abinda y kawo mu na son had'a Y'ay'ansa Aure dasu Jamcy,ba k'aramin murna iyaye na suka yi ba.




Sai alokacin Iyaye na suka tambayeni wad'anda suka d'auke ni daga inda,shiru na yi naki Basu labarin sai kuka da hawaye kawai na Fara,don bana don tonuwar asirin y'an uwana.




Ko da Mlm ya ga haka sai y Basu labarin abinda ya Sani sai dai bai bada k'ofar da zaisa a gane cewa y'an uwana sune suka yimin haka ba.




Sosai Mahaifana da Baba Auwalu sukayi mamaki Amman ba abin mamaki bane a wannan rayuwar da muke ciki,har lokacin kuka na ke Yi ina tuno ko Yaya su Aunty Safiyya za suyi idan sukaji na dawo?.




Sai alokacin na yiwa Iyayena bayanin Jamey da abinda ya faru da ita,sosai Mahaifana sukayi mamaki kuma sun dau aniyar sai sun kwatowa Jamey hakkinta a wajensu Mama Asiya da kaninta Suraj, sannan su maka su a kotu.




Abinsha da abinci kala² akawowa Su Mlm,Mama da Ammi kuwa tuni sun d'inke da Ammi sai hira suke yi kamar sun san juna da ma.




Rungume naji anyi da k'arfin gaske ana cewa"ga Aunty Jamila ga Aunty Jamila",ko da ba'a gaya min ba nasan Twins ne kanne na Raliya da Rayya,ni ma rungume su na yi ina kuka nima mai tsuma zuciya,mun dad'e kafin mu saki junanmu,na shiga kallonsu yadda na ga sun Zama y'an mata kyawawa,daman dukkansu dani suke kama,sai dai su Sirarane daman cen ni kuma yar duma² ce.




Sosai na yi murna da ganin Twins ko da ya ke daman cen munfi sabo da su akan Aunty Safiya,don daman ita ba mutun ce me sakin fuska ba ce,wai kada mu raina ta.






"Twins Ina Nasir da Fatima ta"don na ga Babu wanda ya Yi min maganarsu?".






Shiru suka yi fuskokinsu suka canza,Rayya ce ta Yi k'arfin halin cewa"Aunty tun da kika tafi bai fi kwana 1 ba ita da ummanta muka meme su muka rasa har yau Babu wani labarinsu,Sai dai mun lura wad'anda suka sace ki suna da alaka da wad'anda suka sace ki,shi kuma Nasir yana Maxico karatu tun bayan tafiyarki".






Shiru na yi ina wani tunani tsanar mutanen guda 2 tana k'ara ruruwa acikin zuciya ta,tabbas su Yaya Deen sune suka sacesu don sun san komai a game da fyed'en da Yaya Deen ya Yi min,cikin kuka na tashi na shiga wani d'aki da ke kusa da farlon,don gaba ki 1 an canza wa gidan fasali,Jamey ce ta biyo ni d'akin don matukar Jamey ta ganni acikin damuwa to ita ma yanzu zaka ga hankalinta ya tashi.




"Jamcy bai kamata ace har yanzu kina kuka ba,don ga ki acikin gatanki Na uwa da uba,kada ki manta Jamcy ni bani da irin wannan gatan na ki Amman babu yadda zanyi haka na karb'i k'addara ta don haka dole ne a yanzu muyi hakuri ni da ke don munga rayuwa sosai,ya kamata ace yanzu muyi karatun ta nutsu."




Share hawaye na nayi sannan na ce"Jamey dole na inyi hakuri,Amman ta taya Yaya Deen za suyi min haka? Why bayan sun b'atar dani bai Yi musu ba har sai sun b'atar da bayan Allah,me suka yi musu?".






"Wallahi Jamey a yanzu na yi matukar tsanar wadannan mutanen masu azabtar da rayukan mutane,su d'in Basu da zuciyar imani"?.


K'ara fashewa na yi da kukan tausayin k'auna,Jamey na rarrashi na.




Har yamma ban tambayi su Aunty Safiyya ba yan uwa da abokan arziki an cika gidanmu ana tayamu murna.




Safiyya & Deen




Kuka sosai Safiyya ta ke tana da na sanin abin da ta aikatawa y'ar uwarta,don yanzu Mama ta kirawo ta ta ke shaida mata cewa Jamila ta dawo.


Alokacin Deen ya fito daga band'aki yana goge jikinsa da ruwa,ya ce"ke kuma lfy kika sakani a gaba kina kuka kamar an aiko miki da mutuwar Abba ko Mama".




"Ba gwara mutuwa da abinda ya faru damu a baya ba,ka ingizani na aikata babban kuskure na aikata mummunan abu akan k'anwata,ka cuci k'anwata ka Yi mata fyed'e har ta haihu".




"Relax!"


Kada ki k'ara cewa ni na sakaki aikatawa k'anwarki abu,nima duk abinda na aikata abin yana damuna,tabbas daman ance ba,a sarki mugu sai an Samu mugun bafade,kuma kin san daman cen ba ke na ke so ba Amman kika san yadda za kiyi sai da kika Aure ni,Amman duk ina kallonki na k'eleki,to wallahi kada ki sake ki kaini k'arshe don saboda su Abba na ke zaune da ke da tuni na dad'e da mantawa da ke".




Sosai fad'a ya kaure a tsakanin Deen da Safiyya,don har sai da masu aikin gidan suka ji suka shigo,kowa yana Yi wa d'an uwansa tonon asiri.










*Miss green ce*
*_🍁 JAMILA🍁_*




By
*_Oum

6 / 8