JAMILA Completed book by Miss Green .txt

Author :  Rabi'atu Bashir Abdullahi Category :  True Life Story

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 21.7K words

Maher(Miss gree💚)_*












_*43&44*_




Sai da suka gama yiwa kansu Tonan asiri,sannan Suka hakura kowanne ya yi d'aki,Khalil d'ansu yana ta kuka acikin d'aki daman kullum idan sunayi sai dai ya Yi ta kuka,acikin d'aki babu me kulashi.






Safiyya na hango ta ciko akwatinta taf da kayanta tana jansa da k'er har ta fito waje ta shige motarta sai gida,daman ba wani nisa ne da gidansu ba.






Gabanta ne ya ke matukar fad'uwa har ta shigo cikin gidansu Hankalinta ba,a kwance ya ke ba,tunanin yadda zata had'u da k'anwarta ne fal acikin zuciyarta har ta gama shigowa farlon gidan nasu.






Jamila kuwa tana ganin Yayar ta sai da gabanta ya fad'i ta tashi ta yi shigewarta d'aki ta Samu Jamey tana ta baccinta abinta,ita ma ta matsa kusa da Jamey tana kallon fuskarta tana Raya irin son da ta ke yiwa Jamey don ayanzu tafi son Jamey Akan Safiyya yayarta don ita ba zata tab'a cutar da ita ba,yanzu rayuwa ta lalace sai kaga d'an uwanka yana neman cutar da kai,Amman wanda ba d'an uwanka ba yafi janka a jikinsa.








Ina cikin karanta Novels me suna A sanadin Abayar Sallah na UMMU MAHER,kawai sai naga Aunty Safiyya ta shigo d'akin da na ke,idanunta Fal da hawaye idanunta sunyi jawur abin tausayi,Amman fa ni banji ko da d'igon tausayinta ba don duk wanda ya sai rariya yasan zata zubar da ruwa.






Har k'asa ta tsugunna guiwowinta ta ce"Jamila bani da bakin da zan baki hakuri don nasan na cuceki......"




"Kin cuceni?ko kin cuci kanki?kada ki kuma cewa kin cuceni,na fad'i hakan cikin k'araji har sai da Jamey ta tashi ta k'ura mana Ido tana kallonmu,don duk ta ji abinda ya faru Tsakanin Jamcy da yayarta.






"Am!don Allah ki tashi ki fita na yi miki tsana mafi muni arayuwata na manta da ke kamar yadda kema kika so ki birne tawa rayuwar,ko a cikin yan uwana bana buk'atar a sakomin ke,don ke annoba ce a cikinmu,ki Sani duk abinda kika yi sai anyi miki",na fad'i hakan cikin bud'ewar murya yadda ko da kana kusa da d'akin namu zaka iya juyo tashin muryata,don Allah ya Sani na tsani ganin Aunty Safiyya.






Ina fadin hakan na tashi zan fita sai naji Jamey ta ruk'o hannuna sannan ta ce"Jamcy ashe mu bama yiwa Allah laifi ya yafe mana?,in dai kuwa muma baza mu yafewa wasu ba,to ba shakka muma Allah ya k'i yafe mana,kada ki manta a wata aya Allah shbhanahu wata'ala yana cewa _Innallaha Ma'assabirin_ wato Allah yana son bayinsa masu hakuri don haka kema ya kamata ki zamto me hakuri acikin bayinsa,hak'ik'a daga ni har ke an cuce mu an rugaza mana rayuwa,Amman haka gashi bai saka munk'i cigaba da rayuwarmu ba.




Jamey ta d'an fasali sannan ta cigaba"Jamcy kina da uwa kina da Una kina da y'an uwa a zagaye da ke,to ki godewa Allah don ni bani da iyayenma ballanta na in gansu ko don inji dad'i,Masoyina Sadiq ma sun kasheshi........sai na fashe da kuka a dai dai nan wajen.




Sosai jikin Jamcy ya yi sanyi da jin nasihar k'awarta ta rungume ta tsam a cikin jikinta tana jin wani abu acikin zuciyarta,tare da k'aunar Jamey har cikin zuciyarta.






"Jamey ke ba marainiya bace?kuma kin kasance kina da y'an uwa don ni kad'ai na isar miki Jamey".




kasak'e Safiyya ta Yi tana kallon su cike da so harda k'aunar yaran sun burgeta,lokaci 1 taji Jamey ta kwanta mata har a cikin zuciyarta taji ta kamar k'anwarta Jamcy.




Har Aunty Safiyya ta tashi zata fita Jamcy ta janyo hannunta tare da cewa,ko da kashi ne Jamey ta nuna min a matsayin inso shi to fa tabbas saina so shi,ballan tana ke Yaya ta,na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki 1.






Sai suka rungume junansu abin sha'awa,alokacin Ammi ta shigo ta samesu a haka ta ce su tashi su shirya za,a kaisu Gidan Kakannin Jamey.






Da saurinsu suka shirya harda Aunty Safiyya,mina fitowa naji an janyo ni cikin wani dan corridor da ke jikin d'akinmu,da sauri na waro idanu Ganin Yaya Ahmad ya rungumeni tsam acikin jikinsa,ina shirin kwace kaina naji ya rad'amin a kunne na,"yau kin Zama mallakina an d'aura mana Aure".




Da sauri na kalleshi kallon tuhuma,ya ce"yes".




Kuka ne ke shirin sakkomin ba wai ina tsanar Alhamd bane a,ah kawai dai abinne yazo min Baga tatan.






To ita ma Jamey acen Ido ya yi zuru² don ita ce ta Fara shiga cikin motar,bata san cewa Bashir yana ciki ba,kawai sai taji mutun ya rungume ta ya shiga aika mata da kiss ta ko ta ina.......






See Hajara har an waro idanu😅👏👏...






Ana zan tsaya saboda masu rashin comments idan kun Fara comments na k'ara yawan tyiping.










Share and comments👏
*_🍁JAMILA🍁_*








BY
*_Oum Maher(Miss green)💚_*








Not edited......






*45&46*






......da sauri Jamey ta ce"ikon Allah meye haka Yaya Bashir zaka wani rungumeni wannan ai iskan....."da sauri Bashir ya rufe mata bakinta Yana yi mata wani irin kallo me tab'a zuciya ce"ke ayanzu Mallaki na ce Jamila an Riga da an d'aura mana Aure,a yanzu duk abinda zanyi miki lada zamu Samu",kallonshi na ke kamar na Samu Tv na fashe da kuka alokacin su Jamcy ma suka fito ita ma daga ganin idanunta tasha kuka,ana cikin haka su Mlm suka shigo da Mahaifin Jamcy da goro harda ma Sweet,suna k'arasowa wajenmu Mlm ya umarcemu dukkanmu mu shigo cikin gidan akwai maganar da zamuyi idan an gama sai muyi tafiyar.




Duk jikinmu a Sanya ye muka shigo muka Samu waje muka zauna a babban farlon gidan Mlm ya yi gyaran Murya sannan ya ce"dukkanmu mun taru anan ne don kowa ya shaida d'aurin Aura da aka d'aura yanzu a masallaci a yau Ranar Asabar 25, ga watan Afrelu shekara ta 2020 an d'aura Auren Jamey da Bashir,Jamcy da Ahmad,duk Akan sadaki Naira dubu 50²".
Shiru farlon ya d'auka muka had'a baki wajen cewa to Allah ya bada zaman lfy,ni da Jamcy muka tashi muka shiga d'akinmu dukkanmu muka fad'a gadonmu sai kuka,ba wai bama son Auran bane a'ah?sai tunanin Auren da yadda zamu zauna da mazajen namu shine abinda ya sakamu kuka wanda aka san duk wata mace me kunya matukar za'ayi mata Aure sai ta Yi kuka.


Har d'aki Ammi da Umman Jamcy suka samemu suna ta Yi mana Nasiha me ratsa jikin duk wani me imani kuma nasihar tayi mana tasiri acikin zuk'atanmu,daga baya sai gamu muna ta dariya har Aunty Safiyya tana tsokanarmu,kuma an saka ranar tarewar mu nan da 2 masu zuwa kuma a satinnan za'ayi mana lefe,a satin kuma muka je gidan Kakar Jamey da ke Kano itama ta Yi murna harda sujjada don ganin Jikarta Jamey kuma tayi murna da aka ce Jikarta ta Yi Aurenta tayi ta shiwa Bashir albarka sannan ta ce ya kula mata da Jikarta don marainiya ce, Inna ta Yi ta tsinewa su Mama Asiya da kaninta Suraj Akan cutar da suka yiwa Jamila,kwananmu 3 a gidan Inna Kakar Jamey muka tafi Bauchi don kwatowa Jamey hakkinta wajensu Mama Asiya da kaninta Suraj.




Sosai hankalinmu ya tashi da muka je Bauchi aka ahaida mana cewa wai tun tafiyar Jamila su Mama Asiya suka yi tafiya har yau kuma ba'asan in da suke ba wannan abu ba k'aramin bata mana rai ya yi ba,daga k'arshe Mlm ya ce mu kyelesu duniya ce ta isa kowa Riga harda xanin d'aurawa.








Gaba dayanmu muka dawo kano muna gidanmu duk da Inna taso Jamey ta zauna a wajenta kafin buki Amman Umman Jamcy ta rok'i Innah Akan Jamey ta zauna wajenta akwai abubuwan da ta keso ta yiwa yayan nata ne,Amman ta ce idan ya Zama na saura kwana biyu bikin Jamey zata dawo nan gidansu ayi yinin buki,Inna taji dad'in yadda Umman Jamcy ta ke kula da Jikarta ta Yi musu fatan alkhairi suka koma gida,Su Mlm kuma washe gari zasu koma a cigaba da shirye².
Da daddare muna zaune a cikin d'akinmu bayan mun dawo daga yawon Shan ice cream da mazajenmu Umma ta shigo d'akin ta samemu mun zube Akan gado duk mun gaji,ta ce"oya ki tashi ki fito farlona yanzu zan hadaku da me gyaran jiki zaku tare a bangarena acen har lokacin buki".


D'an turo baki Jamcy ta Yi wanda ya yi ja saboda tsotsar da yasha yau wajen Yaya Ahmad na ce"Allah Mama mun gaji yau fa a bari sai gobe yanzu bacci mukeji"..."da kuka fita yawo da mazajenku baku gaji ba sai da kuka dawo gida?,maza ku tashi yanzu² ina jiranku a farlon,da sauri Jamey ta tashi don gaskiya tana matukar son Mama don ta dauketa kamar matsayin yar ta Jamcy don haka itama ta ke matukar son ta da k'aunarta,Jamcy cikin turo baki ta tashi gefe na zuciyarta yana Yi mata suya na tunowa da ta Yi ita fa yanzu bata a matsayin Virgina sai taji zuciyarta ta k'ara tsanar Yaya Deen,don ma Ahmad yasan komai na game da rayuwarta bata da matsala dashi Amman duk da haka Yaya Deen ya yiwa rayuwarta babban gib'e.




Sosai Mama ta yiwa me gyaran jikin bayani sosai na yadda za'a gyara mata yayanta,a Daren kuwa aka keb'e musu d'aki 1 har dame gyaran jiki.




Muna fitowa da ga wanka Jamcy ta ce "Wow Jamey Kinga yadda jikinmu ya yi kyau kuwa?".harara Jamey ta aikawa Jamcy sannan ta ce"kuma a haka Mama ta ce mutun ya tashi don a gyaramu yak'i tashi ba"?.Dariya Jamcy kawai ta Yi suka kwanta kowa yana kallon jikinsa don kusan yanayin fatar suma iri daya ce sai babbancin kiba don Jamey siririya ita kuma Jamcy y'ar duma².







*Washe gari*


Da Wuri su Ammi suka Fara shirin komawa gida,Su Jamcy kuwa kowacce tana d'akin mijinta ana Shan minti kafin a tafi Amman Basu yi musu komai ba iya kacinsu Romance ne kawai suka yi,ko da suka zo tafiya ba da k'er suka rabu saboda ad'an kwanakinnan bak'aramin sabo ne ya shiga tsakanin su ba,har da kukan shagwab'a ya yin da su kuma mazan Nasu suka so sakankancewa sai da Mlm ya yi Jan Ido sannan suka fito suka shiga motar matayen nasu na d'aga musu hannu.




Sai yamma su Mlm suka isa garin Adamawa(yola) kai tsaye Ahmad da Bashir gidajensu suka wuce bayan sun kai su Ammi da Mlm gida,inda Inna Uwargida ta ringa jefar da maganganu bayan Mlm ya fad'a musu D'aurin Auren Su Y'an biyu,nan da nan Inna ta shaidawa y'an uwa da kuma yayanta tana cewa wai yayan tsintuwa Mlm ya Aurawa y'ay'ansa.


Hajiya Ladi kuwa Har makota sai da ta fad'awa wai Ammi ta iya had'a munafinci daman tasan Auren yayan ta tafi tak'i shaidawa kowa,Ita dai Ammi ta toshe kunnuwanta sosai saboda bata son jin kalaman kowa Akan Auren yayanta duk wanda ba zaisa alkhairi ba to ya yi shiru,falyak'ul khairan auli yasmut,Mlm ma da yaji zancen ya yi musu Jan Ido Akan maganar nan da nan kuwa kowacce su ta Yi shiru Amman ta ciki na ciki,don Mlm mutun ne tsayayye a gidansa.








To fa can kuma gidansu Ahmad da Bashir ana cen ana kwasar rikici agidan Angwaye Wato Bashir da kuma Ahmad.










*😅To fa su Hajara marubuciyar Najmat Abiy a fito a raba fad'a tunda ku kuka had'a wannan Aure*.😅😅😅ni na gudu💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻insha Allah kafin azumi zan gama littattafaina duka saboda ayi bautar Allah sosai,sai bayan Sallah mu d'ora inda muka tsaya.










Miss 💚 green ce✍🏼
*Share and post*. .....
51&52






nayi mistake Ɗin page daga 47&48.


Amman a cigaba da karatu tunda pages ɗinne kawai.








Wata uwar ashar maryam ta buga jin wai mijinta ya yi aure,ta ɗauki waya ta kirawo Ameera wato Hafsat,abu ɗaya ta faɗa mata shine wallahi ba za ayi mata kishiya a zauna lfy ba,ta jira ta gobe zata zo.
Su kuwa mazajen nasu ko ajikinsu ƙarshe ma suka nuna musu ba ta su suke ba,,mlm mahaifinsu yasha zagi sosai wai duk shine munafukin da ya saka akai musu kishiya.




Sassafe HAFSAT tazo ta samu MARYAM sai kuka ta ke ta kalleta sheƙeƙe sannan ta ce yanzu zan zamuje wani waje da za ayi mana maganin ƴan banza,sai kallonta maryam ta ke jikinta duk ya yi sanyi suka tafi a motar hafsat Ɗin.




Wani daji suka shiga MARYAM sai ɗari-ɗari ta ke saboda tsoro,ita kuwa Hafsat sai kusa kai ta ke da alama ta saba zuwa wajen.




Wani kango sukaje duk sai haƙi ne ya ke tashi acikin kangon Hafsat ta shiga tana kallon ogan nasa,ogan ya jefar da tabar wiwin da ya ke sha ya ce"shegiyar ƙwana biyu kin manta dani".


dariya ta yi sannan ta ce buƙata nazo da ita jamble inaso a kashe min wasu mutane guda biyu.




Da sauri Marym ta kalleta idanunta a warwaje,bata san sanda suka gama maganarsu ba har suka fito daga cikin dajin,tsoro fal a zuciyar maryam.








Contact


Ummu maher
07068606171
*JAMILA*


Love&destiny story


wattapad user
name
*Rabiatu333*








49&50






,....Wani mugun tsoro ne ya kama Maryam don ita bata ɗauka iskancin hafsat ya kai haka ba,amman sai ta yi ta maza bata yi magana ba don Allah2 take ta samu su fito daga wannan baƙin wajen da suka je.


Kuɗi Hafsat ta
Basu sosai amman duk da haka sai suka biyota Bashin wani kuɗin don sunce kuɗin ba sunyi kaɗan sai ta daɗo,haka Hafsat ta yi musu alƙawarin cika musu kuɗin sannan suka fito daga cikin wajen,ai suna fitowa aka sai ta su da kan bindiga suka runtuma zasu gudu,dakarun sojin suka riƙe su cikin azama,suma mazan haka aka kamosu aka fito dasu,ƴan jarida sai ɗaukar hoto sukeyi.




Lbaran ƙarfe 4 alhaji Abbas ya ke gani mahaifin Maryam yana cikin kurɓar sanyayyan lemonsa ya hango ƴarsa cikin guggun pan daban da aka daɗe ana nemansu


Da hannu Alhaji Abbas ya ke nuna ƴarsa bakinsa yana ta kakkarwa,dai dai lokacin momin Maryam ta fito daga kitchen don kawowa Alhaji abinci,itama ta tararar da abin al'ajabin daya faru,a tsaye ta daskare itama tana nuna TV.




Tun ƙarfe 4 Ahmad yaga wannan labaran da farko ya kiɗima sosai don ganin matarsa da ƴan daba,ya ɗaga wayarsa ya kirawo Bashir ya shaida masa,a lokacin jamey tana kwance a jikinsa yana aikin rarrashinta,sai taji ya yi saurin tashi ta tambayeshi lafiya ya ce lafiya amman bari yaje wajen Ahmad yaji abinda ake ciki,kuka ta saka mishi wai don Allah ya tafi da ita tsoro ta ke ji,don dole ta tafi da ita gidan.


Suna zuwa suka rungume junansu amare wato Jamcy da Jamey suka fashe da kuka atare kamar an aiko musu da mutuwa,Twins ɗin Mlm suka kallesu sukayi murmushi tare da sha'awar matannasu.




Da sauri suka fito suka miƙi hanyar babbar headqouter




Ƴan sandan hankalinsu yana maruƙar a tashe,alokacin mahaifan Hafsat da Maryam suma sukazo hankalinsu duk a tashe.










fashewa da kuka Jamey ta yi tana cewa"wallahi Jamcy dama banyi auren nan ba,wahala nasha sosai kamar zan mutu".saurin toshe mata bakinta Jamcy ta yi tana ƴan dube2 kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya ta ce"haba Namesake kamar wata ƙaramar yarinya aishi aure ni'ima ne,kada ki faɗar haka kinji.


Ɗaga kai Jamey ta yi kamar ƙaramar yarinya ta ce"insha Allah bazan ƙara ba".nan suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa.










Mlm yana Bauchi shi da matansa sunje hutu da ta ke daman can usul acen suke suka dawo Adamawa.




Sosai hankalin mlm ya tashi,a tare suka taho da dukkanin matansa suma hankalinsu a tashe don duk da kishin da sukeyi da Ammi amman suna son ƴaƴanta don suna taimaka musu musamman ma Inna.












*** *** ***


Ba komai ne yasa su Maryam mamaki bai rin yadda su goje suka ce wai tare suke duk wani fashi da sukeyi,duk ƴan rantse2 su Maryam amman ƴan sanda basu yadda ba ƙarshe ma aka shiga gana musu azaba iri2.




Ahmad ya yadda da zancen Maryam don Maryam bata ƙarya sam, sai dai tun acen ya rubuta mata takaddar sakinta don bazai iya cigaba da zama da ita a haka ba.


To shima Basgir hakan ce ta faru don tun acen shi ya bawa Hafsat ta kaddarta don bazai iya zama da mugun iri a gidansa irin Hafsat ba don ya yadda shima da zancen matar ɗan uwansa Maryam da tace Hafsat bata gaya mata inda zasu ba kawai ta ja tane sai da sukaje taga inda Hafsat ta kaita.










*To koma dai menene duk wanda baiji bari ba,ba zaiji wohoho ba💃🏼*






don Allah kada a tura book ɗinnan jamila fans group don sun rage comments,,
*🍂JAMILA🍂*




by


UMMU MAHER(MISS GREEN💚🍀)






49&50


. . . .Sosai Maryam da Amira suka zama abin tausayi don ko a cen gidan ma ba daɗi suke ji ba,don babu wacce iyayenta suka ɗaure mata kai,ƙarshe ma sune suka zama boyi-boyin gidansu don hatta wankan ƙannensu da komai duk sune suke a satin biyunnan ba ƙaramin damunsu abin yayi ba,a hakanma don ba a kaisu gidan yari ba iyayensu sunyi tsayuwar daka sun tsaya akan maganar case ɗin fitowarsu da ƴaƴan ya ku bayi ne da baza a fito dasu ba.




Cen gidansu Ƴan biyun mlm kuwa soyayyace madararta ake sha don haka acikin sati biyunnan baƙaramin ƙiba suka ƙara ba gwanin sha'awa.




Yau ma ta kasance ranar asabar yau ake yinin ɗan gidan hajiya Inna kishiyar Ammi,komai na bikin ƴan biyu ne sukayi shi,duk wani kuɗi da Inna ke kashewa to daga aljihun ƴan biyu ya ke,ayanzu Inna ta ɗan fara sakin jiki da ƴaƴan mlm wato Jamcy da Jamey,saboda suna yi mata alkhairi sosai ba ita kaɗai ba duk matan mlm ma saboda haka yanzu duk gidan ake ganin girmansu mlm kuwa kullum godewa Allah da ƴaƴansa suka sami mata na gari.
Ƙwana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya a yau Allah ya yi aka kama Mama Asiya ita da ƙaninta Suraj sakamakon danfarar wani shahararren ɗan kasuwa da sukayi wa damfara kuma ɗansa soja ne da akayi bincike aka gano su.


A tv Jamey ta gansu ta dafe ƙirjinta tana kiran sunan Allah alokacin Bashir ya fito zai tafi unguwa sosai ya tausayawa Jamey kuma ya yi mata alƙawarin bari ya dawo daga aiki yanzu zai dawo sai suje inda aka tsaresu.




Ko da suka daƙer aka barsu suka gansu ko da suka gansu kuka sosai Mama Asiya ta fashe da

7 / 8