WATA UWA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 9

3K to 6K   out of 26.7K words

bugunki shine nizzo in taimakeki "

Kallon junansu sukayi,atare sannan suka kalleta"a gidan ubanwa kikaga yana dukan nawa,muda tun Wazu wasa muke a harabar gidanmu,ke wlh koda ubanki kike yawa,se kin biyamu ?wan mu"cewar matar lokacin data dan?o kwalar rigarta ta cukuikuyeta.

Mijin shima maimaita mata ta biyasun yayi,dan bazasu ?yaletaba.

kuka ta fara tana basu ha?uri amma ina sun dage seta kaisu gidansu anbiyasu.

"muje to abiyaku,amman da nisa ne gurin"ta faWi tana share gumin da ya tsatstsafo mata.

ba musu suka sata amota,matar tasako hijabinta suka kama hanya tiryan tiryan har office Win Naim.

tasan gurinne da jimawa,kallo suka bita dashi,mijin yace"me mukazo yi a maaikatar manyan sojoji?"

"kuWin zaumu amsa,"ta bashi amsa gamida yin ciki su kuma suka tsaya suna kallon ikon Allah.

Kusan kowa na gurin yasan sajeeda tare da naim amma saninta amazaunin matarshi farouk ne kawai yasani.

Shiyasa basu hanata shiga office Winba,zaune yake yana ganawa da wasu sojoji yaga shigowarta,a zabure ya mi?e,yana binta da kallo,duk Wanyan ?waine ajikinta dayafashe,ga ido taci kuka ta ?oshi.

"kuWan bani guri,zan nemeku pls"ya faWiwa sojojin.ba musu suka fita bayan sun sara masa.

"Sajeeda meya faru naganki anan meye wannan ajikinki?"cewar naim yana binta da ido.

Cike da shagwaSa ta kwashe komai dayafaru ta faWa mishi hawaye na biyo idonta.

Runtse ido naim yayi yana karanto duk adduar da tazo bakinshi,dan zuciyarshi tai sanyi.

Numfasawa yayi sannan ya dubeta cike da takaici,yace"suna ina masu kwan?"

"Suna waje"ta bashi amsa.

ficewa yayi ta bishi abaya,har zuwa gun masu kayan,motarshi ya buWe ya Wauko kuWin dashi kanshi besan nawa bane ya mi?a musu sannan ya finciketa yasata a mota yaja suka fice a gurin.

tu?i kawai yake batare daya kulataba,tana ganin anfara barin garine takai dubanta gunshi tace "zaki ina ne zamuje?"

"?auyanku zan maidaki sajeeda nagaji,tunda kin?i ki kama kanki ki natsu to yazama dole na maidaki gida."

wata uwar ?ara ta saki tana faWin"wallahi na dena ni banason ?auye karka maidani dan Allah zakina,nashiga uku"ta faWi tana tirjewa acikin motar

Faka motar yayi,agefen titi,ya kwantar da kujerarshi,yana tunano ?addarar data jefo sajeeda cikin Rayuwarshi.

FARKON LABAR


Na'im Hassan Chalawa sunanshi,?ane ga Alhaji Hassan chalawa,me kamfanin chalawa investimen.

Mahaifinshi,fitaccen Wan kasuwane,afaWin ?asar nigeria,da WaiWaikun mutanene basu sanshiba.

Gidansu gidane na arzii?i da wata,dan inde kuWine to su ruwane agurinsu.

Naim su biyune iyayensu suka akwai yayarshi,Amina se shi auta.faWin gatan da naim yataso aciki Sata lokacine,dan mevkaratu ko baa faWiba kasan anmori gata.

Mahaifiyarsu,hajiya zainab,macece mejin kanta ko kaWan batason harka da talaka,shiyasa tun su naim na yara take nuna musu talaka abun ?yamane,amman su ?a?an basu Wauki hakanba.

Ankai ruwa rana tsakaninshi da iyayenshi lokacin daya zaSi aykin soja yakeso,sun nace shima ya kafe,dole tasa suka barshi suka bishi da fatan alkhairi.

ita kuma aunty Amina,fannin lafiya ta karanta,inda mahaifinta ya buWe mata katafaren asibiti wanda babu kamarsa ajihar kaduna inde private ne.


Naim da dukkan zuciya da jikinshi yake ayki agidan soja,shiyasa yadinga samun ?arin girma duk da ?ananun shekarunshi,

*********

LAKURAWA, ?ungiyace ta ?an ta'adda masu da'awar jihadi,da suka fito daga yankin Sokkoto/Birnin kebbi,dasuke kisa kan me uwa da wabi,ba yara ba manya.

A yun?urin gomnatin tarayyar nigeria nason ganin ta kawo ?arshensu,wajan mur?ushe duk wani hari nasune,aka ayka da zaratan sojoji yankin dan ganin an tsabtace Sangaran,jama'ar yankin su samu zaman lfy da kwanciyar hankali.

Naim hassan chalawa,na Waya daga cikin tawagar ta sojojin da aka tura domn kawo Wauki wa a'lumar yankin.

Sun isa lafiya,inda aka rarrabasu sashi sashin da abun yafi tsamari.

SOKKOTO STATE

SILAME LGA,

Anan aka ajiye su na'im,inda aka musu sansani aciki dajin dake kusa da ?AUYEN GANDE.

Dare ya raba,?an taaddan sun kawo musu hari,inda aka shiga musayar wuta ba ?a??autawa,cikin salo da dabarun ya?i da nuna ?warewa ta sojan nigeria,su Naim sukai nasarar tarwatsa su,suka kashe wasu,wasu kuma suka kamasu,yayinda wasu kuma suka ranta ana kare,sakamakon binsu da sojojin sukayi..

Naim yankewa yayi cikin dajin dan yasamu ya rage mararsa,dan mutum ne shi marar tsoro,kukan jaririne,ya cika kunnuwansa alokacin dayake tsugune yana fitsarin.

cike da mamaki ya mi?e yana bin inda yake jiyo sautin kukan,ayko kwatsam se gashi agun.

kwance a ?asa,kan tantagayyar ?asa,jaririyace sabuwar haihuwa dake da faman tsala ihu,na neman agaji,

gefenta,wata jakar matace,?ar ?arama,da sauri naim ya tuSe rigar kakinshi,yasa hannu ya Wago yarinyar ya naWeta aciki,se kuka take,amma jin an Wauketa yasa tai shuru tana tsotson hannunta.

Rungumeta yayi,hawaye masu zafi na biyo idonshi,na zallar tausayin jinjirar.

tunaninshi,da be zo gurinba haka ?ar zata kwana agurin tana kuka harta mutu,ko maciji kode wani abun cutarwar ya sameta.

Haska kewayen gurin yake,bega kowaba,hakanne yasa ya Wauki jakar,ya buWe,ba komai aciki,se hoton wata ?ar matashiyar budurwa me kyan gaske,abayan hoton akwai address na wme hoton kamar de yadda masu hoto kesawa.

maida hoton yayi ciki,sannan yasa jakar cikin rigar daya naWe yarinyar,yabi wata siririyar hanya,da yake,da tabbacin hanyace ta zuwa wani gurin.

yayi tafiya me tsayi,kamin ya iso,cikin wani ?aramin ?auye. me suna MALE,lokacin asuba tayi dan haka kai tsaye masallaci ya nufa,yana zuwa ko yasamu ladan na kiran sallah,jira yayi ya idar sannan yamasa sallama,

ganin sojane yasa ya tsaya batare dayaji tsoroba.

bayanin abinda ya fa faru,Naim ya masa inda ya mi?a masa ?ar,gamida bashi kuWin da zasu kai dubu Wari,a,aljihun wandonshi,yace.

"Baba yanayin aykina baze bari inkai ?arnan ga jamian dasuka dace dasu karSeta ba,amma ga wannan kuWin in gari ya waye,ka tambaya ka kaita don Allah"

hannun ladan har rawa yake yasa hannu ya karSi ?ar hawaye na biyo idonshi,ya rungumeta,ya amshi kuWin.

da sauri naim ya juya yabar gurin yabi hanyar daya biyo,har,ya dawo sansaninsu,zuciyarshi cike da tausayin jinjirar.


Ladan me suna malam yakubu,mutumne me tsoron Allah,haka matarshi,inna jamila,mutanene masu takatsantsan da duniya,sede tun auransu Allah be basu haihuwaba.

Lokacin daya isa gidanshi da jinjirar,inna ta kaWu da ganinta,hannu tasa ta amsheta ta rungumeta tana kuka.

"Tsintota wani jamii yayi yace inkaita gun maaikata dan aturata gidan marayu ko ay cigiya,jamila"cewar malam muryarsa na rawa.

Share hawayenta tayi,tace"malam daga yau kukan rashin haihuwa nide Allah ya sharemin,wlh kan inbada jinjirar nan,gara aWauki rayuwata,ni inasonta malam,"ta faWi wasu sabbin hawayen na biyo idonta.

"jameela in yadawo kuma ya nemenifa yazamuyi ni ina ganin hakan bame yiwuwa bane"cewar malam asanyaye.

"Nanfa ba garin mu bane,dan haka mu koma garinmu mana amatsayin mun haihu,tunda dama gorin haihuwa dayay yawa ne yasa mu ka baro garin"cewar inna cike da kwarin guiwa.

Ayko sosai malam yayi naam da shawararta,washe gari da safe,suka haWa kayansu sukai sallama da makwabtansu akan sun tafi garinsu.


********

TANERA

Shine ?auyan garin nasu malam,koda suka koma garin sosai mutane sukai ta tayasu murnan haihuwar da suka samu.

to yanzu inna hankalinta akwance yake,batada sauran damuwa,shiyasa ta maida hankali wajan kulawa da ?arta,datasawa suna fateema suna kiranta sajeeda.

Sajeeda taga gata agurin inna fiya da duk wani Wa dake ?auyen nasu,abinda takeso takeyi.

*******

Naim watanni shida suka kwashe a gunrin,ranar da zaa kwashesu,mashin Win wani me kawo musu cefane gurin ya ara,ya nufi ?auyen male,dan yaji yadda suka ?are,da ladan da jinjirar.

sede koda yaje,garin,ya gaza gane wanne masallacine,hanyarma duk ta sauya masa baya iya ganewa.

fatan rayuwa me tsabta yayiwa jinjirar,ya dawo sansaninsu,motoci suka kwashe su zuwa kaduna.

Koda yadawo gida seda yabawa mummynshi labarin jinjirar,da aunty amina.

"ayya dama ka kawota gidannan muyi adopting Winta"cewar amina tana murmusi.

"Bade gidan nan ba kuwa,amina,ay ku biyun kun isheni banason kowa ya raSeni bare asani damuwa"cewar mummy.

Murmushi kawai sukayi suka bar maganar.

Amma kullum Allah keda kullum,da tunaninta naim yake kwana.

*********

BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU.


Ko ina a garin ya hargitse da koke koke da ihun mutane,gamida ?arar bindiga ako ina na garin

inna da mallam cikin kaWuwa da tsoro suke,sun Soye, sajeeda wacce tayi tsit bata iya motsin kirkima.

""Jamila in muka ci gaba da zama,cikin gidannan,mutanen nan ba imani aggaresuba,zasu iya iskomu ciki su kashemu.dan haka ku tashi mu dira ta katanga mu fice ta bayan gari."

ledar bako inna ta rarrafa cikin Wakin su taWauko,sannan tazo suka Wora sajida kan katangar ta dira,inna tahau kenan,?an bindigar suka faWo gidan nasu,ayko malam dake tsaye suka buWewa wuta,take ya faWi agurin matacce.

Inna,?ara ta saki zata dawo gun malam ayko itama suka harbeta akafaWa,faWawa tayi inda sajeeda ke tsaye,Wago ido tayi taga yadda sajeedar ke kakkarwane yasa,inna yin ta maza ta mi?a mata ledar bakon,ta ri?e sannan ta kamo hannunta suka bar gurin da gudu.

ta cikin duhun shukoki suke gudun,shiyasa baa gansuba,jini na zuba ajikin inna amma burinta ta tseratar da sajeeda,

Tun daga garinsu,seda suka zo gab da titi sannan ?arfin inna ya ?are,ta faWi agurin.

sajeeda Wagata takeyi amma takasa,

"Sajeeda,wannan jakar ta hannunki,akwai kayan da aka tsintoki dasu aciki bamu muka haifekiba,amma inada tabbacin hoton cikin kayan,mahaifiyarkice ajiki,duba da kammanin da kukeyi,kije ki nemi gun da aka Wauki hoton sabida,akwai adireshi name hoton aciki,inde kikaje gurin me hoton nasan ze gane ta,akwai kuWi acikin jakar dubu hamsin ne,akwai rigar sojan daya kawoki garemu,sajeeda malam ya mutu,nima kuma tawa rayuwar tazo ?arshe,ki ruga sajeeda kar acimmiki,Allah yay miki albarka"cewar inna da ?yar numfashinta na kokawar barin jikinta.

Sajeeda faWawa tayi jikin innar tana kuka gamida ro?onta ta tashi,amma inna rai yariga dayayi halinsa.

Duk da ?arancin shekaru na sajeeda da wawtarta,tayi kuka sosai agurin sabida ta fahimci inna ta mutum.

a gaban gawar ta kwana,hasken asubane yasa ta mi?e,tayi gaba tana kuka,batare datasan inane zataje ba.tana waigen inna dake kwance a?asa,har ta dena hangota.

koda tazo titi,motocin bada agajin gaggawane na jamian tsaro cike da gurin,se kwshe mutanen dasuka tsira akeyi zaa kaisu sakateria can cikin garin na silame.

batai ?asa aguiwaba itama ta shiga,ayko aka kawosu sakateria.

Duk mutanen,ma?wabtan ?auyen sune shiyasa bata san kowaba,suma basu santaba,mi?ewa tayi ta ware kanta ta lalubo hoton da inna tace mata,tabi hoton da kallo,sosai taga kamar da sukeyi,koda ta kalli rubutun bata ganeba tunda ba boko tayiba.

wani matashi data hangane,yasa ta mi?e ta isa gurinshi ta mi?a masa hoton tace"dan Allah inane gurin dame hoton nan yake?"ta faWi tana kallonshi.

amsa yayi ya duba bayan hoton,yace"yarinya wannan gurin hoton ay a kano yake,hotoro tsamiyar boka"ya faWi yana kallonta.

ba tare da damuwa ko tunanin komaiba tace "kasani a motar kanon don Allah"

"gun wa zaki a kanon?"ya tambaya.

"Gun mamana"ta bashi amsa hawaye na biyo idonta.

Hannunta ya kama suka tsallaka titi,basuyi doguwar tafiyaba suka iso tashar,da ike safiyace,ko kowa se hadahadarshi yake.

matashin be bar gurinba seda ya tabbatar yasata amota,danshi me Wauka daga cikin ?an gudun hijira takeba,kuma da ike tana da girman jiki ko kusabe Wauka batakai sh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ekaru goma sha biyar ba.

cikin dabara ta zaro dubu guda ta fita amotar taje ta siyo kunu da ?osai tasha,sannan ta koma cikin motar.

koda akazo haWa kuWin motar shima cikin dabara ta Wauko,a kaynta ta biya,mota ta cika suka Waga zuwa kano.

Tafiyace me tsayin gaske,kamin su iso garin na kano,inda aka saukesu atashar kano line.

Tari?e sunan hotoro tsamiyar boka da taji matashin ya faWi,dan haka,abinci ta siya taci sannan ta nemi hanyar hotoro.

?an union Win tashar ne sika sata a napep,,daze kaita har can Win.

lokacin da aka sauketa,biyan kuWin tayi sannan ta fara nunawa mutane jikin hoton in sunsan inda me hoton yake.

ta wahala sosai kamim ta samu wanda ya gano gurin,inda yace mata"Kalane me hoton ?an da,yanzuma be hoto,sede yayi passport,"ya faWi zatonshi ko hoton ze Wauketa.

"dan Allah ka kaini gurinsa"ta faWi amarairaice.

"muje unguwarmu Waya dashi"cewar mutumin

godiya tai masa,suka rankaya zuwa unguwar
tasu,har bakin shagon me hoton yakaita,shi kuma ya wuce nashi waje.

sallama tayi abakin shagon,daga ciki aka amsa mata gamida bata umarnin ta shiga.

magidancine daze kai shekaru arbain,zaune kan darduma yanata yanka hotunan passport dayayi yana haWasu guri guda.

gaisheshi tayi sannan ta mi?a masa hoton tace"dan Allah ta jikin hotonnan naka biWa"

Kallon hoton yayi ya yi murmushi,yace"Saleema sarkin wanka,kenan".

Wagowa yayi ya dubeta yace"lafiya kike nemanta?"

"mama tace"ta faWi tana share hawayenta.

nazarin fuskar sajeeda yayi da kyau sannan,ya dubi hoton,sosai yaga kamanni dukda sajeeda tafita kyau da haske.

"karfa kamanni su ruWeki ki ce saleema mamankice,dan saleema da na sani, bata da ?a kamarki,?a?anta biyune mace da namiji,kuma bata garin nan yanxu,a abuja take aure"ya faWi yana kallonta.

share hawayenta tayi tace"ka kaini abujar,inta ganni nasan zata tunoni"

"abujar ayba nan garin bane tafiyace me nisa,sede inbaki adireshin gidanta,inkinje ki nemeta,sabida wayata ta lalacene ma,dana kirata"

Shuru tayi tana kallonshi,ta rasa mekuma zata kuma cewa.

Takarda ya Wauka ya rubuta mata address Win ya bata,bata musaba ta amshi hoton da takardar,tai masa sallama ta fice,ba tare datasan inda zata ba.

napep ta ?ara hawa,tace tashar abuja zata,ayko suka kawota tashar unguwa uku.

ata?aicede a office Win union ta kwana,da gari ya waye,akasata a motar farko zuwa abuja.

faWin irin wahala da bulayin da sajeeda tayi,kamin ta samu gidan me karatu zaa jima.

koda tazo bakin get Win me gadine ya tsaidata,da tambayoyin gurin wa tazo.

bashi amsa tayi da "mamana"

"akace miki agidannan akwai mamarki?"ya bata amsa da tambaya.

GyaWa mishi kai tayi,tana raurau da ido,hoton hannunta ta mi?a masa tace"wannan ce mamana"amsa yayi yana kallon hoton cike da mamaki.

Kujerar dayake kai yanunawa sajeeda,yace ta zauna,sannan shikuma yashiga cikin gidan,sede yana shiga yaga mutanen gidan amota sun nufo get zasu fita.

Da sauri yaje ya buWe get Win,zasu wuceshi kenan ya tsaidasu da sauri.

bayan sun tsayane,yaWan rusuna yace"Alhaji,dama waccan yarinyarce tazo da wannan hoton,tace wai hajiya mamartace"ya mi?a musu hoton gamida nuna inda sajeeda take.

Alhajinne ya amshi hoton ya kallah,sannan yadubi fuskar matar tashi,yasake kallon hoton yace yana zare glass Win fuskarshi.

"saleema,kecefa ajikin hoton nan, duba ki gani da kyau"ya faWi yana mi?a mata hoton.

amsa tayi awula?ance takalla sannan tace"bani bace,baby,pls mu wuce lokaci fa na tafiya"

Sajeeda idontane yasauka gun saleema dake ta taunar cingam ta toshe fuska da bakin glass,da gudu ta mi?e ta nufosu,tana faWin"mama,mama nita Wiyarki sajeeda"

saleema afusace ta sakko daga motar ta Wauketa da mari tace "ke dan ubanki kinga namiki kama da uwarki,inkika kuma kiranada mamarki sena takaki da mota."

Sajeeda zubewa tayi agabanta ta kama ?afafunta tana kuka tana faWin wlh kece mamata,kiyi ha?uri ki amsheni,Wiyarkice ni "ta faWi cikin matsanancin kuka.


hankaWeta tayi kawai ta rufeta da duka,da gudu alhaji ya zagayo ya ?waceta a hannunta,"baki da hankaline zaki rufeta da duka saleema"cewar alhajin cikin fushi.

"In ta kuma ala?anta kanta dani sena kasheta,to inba haukaba taya,zaace wai ?atace wannan mahaukaciyar,ko accent Win bakinta bakaji bane,me ya haWani da yankinsu"cewar saleema cikin matsanancin fushi.

Juyawa tayi tabar gurin ta shiga mazaunin direba,ranta na mata zafi.

Alhaji hannun sajeeda ya ri?e yace cikin rarrashi"yarinya wannan ba mamanki bace kinjiko,wannan matatace kuma nine mijinta na farko aduniya,waincan yaran guda biyu sune kawai ?a?anmu,anbaki adireshin ba daidai bane kinji,ungo wannan ki ?ara guzuri"ya mi?a mata dubu ashirin ya juya ya shiga mota,ayko figar motar tayi da ?arfi,tabar gurin,sajeeda binsu tayi da gudu tana kiran" mama mama kitaimakeni"amma ko gezau saleema batayiba,har suka Sacewa ganin sajeedar.

Du?awa tayi agurin tana kuka,ta jima tana kukan kamin ta mi?e,tayi gaba ba tare datasan inane zata ba.

wasa wasa sajeeda seda ta kwashe watanni shida tana gararanba agarin abuja,inda take bin wasu almajirai mata yawon bara,dan tuni kuWinta sun ?are,ga kayanta na sawa kala biyune duk sun koWe sun yayyage.

a jikin wani masallaci suke kwana,ita da sauran masu barar.

********

Damina ta sauka yanayi mara daWi ga mabaratan garin na abuja.

Yau antashi da marka marka,shiyasa garin ya?i bushewa,ga sanyi dake kaWawa.

akaron farko da sajeeda ta ciro rigar sojojin,cikin kayanta tasaka,dan rage sanyin da takeji.

sauran mabaratan sunyi sunyi ta cire amma ta?i,duk da irintsoratarwar da sukai mata amma batajiba.

Tsaye suke,abakin titi,suna bara ga masu ababen hawa,daga can tsallaken wasu motocine na alfarma guda biyar sejiniya suke,sakamakon go slow Win da ya haWu agurinne yasa suka tsaya sojojin dake tsaron lafiyar na cikin motar tsakiyane suka firfitodan bashi tsaro agurin,kamar ance ya waigo,hangota yayi tsaye tanata tsalle tsallenta sanye da rigar sojoji,ba tare da taji tsoron sojojin dake gurinba,sosai ta burgeshi ta bashi tausayi, ya yafito ta yayi ya mi?o mata bunch na Wari biyar,da gudunta ta tsallaka taje ta karSo,fuskarta cike da faraa,tana zubo masa addua,sanna ta juya zata dawo gun tsayuwarsu.

Ko kaWan be iya ganin komai se sunansa da numbarsa ta gidan soja dake rubuce ajikin rigar sojojin dake jikin almajirar yarinyar daya ba sadaka,har wani jiri yakeji yana Waukarsa da sauri ya buWe motar ya kwalla mata kira.

"almajira!!!"

daidai lokacin tazo tsakiyar titin da zata tsallaka,tsayawa tayi ta waiga,ayko mota tai sama da ita.

Da mahaukacin gudu,ya ?araso gurin,tuni ta faWo ?asa sumammiya.


?agota yayi yaga bata numfashi,da sauri ya Wauketa,yayi mota da ita,cikin gaggawa aka buWe hanyar,suka nufi asibitin Chalawa Hospital dake maitama.

Tun kan su ?araso tuni,antanaji abun bu?ata dan ya kira waya ya faWi.

suna zuwa aka shigar da it ICU domin ceto rayuwarta.sun kwashe sama da awa guda kanta kan susamu ta farfaWo.

allurar bacci aka mata sannan aka kaita aminity room.

office Win likitar ya shiga,tana goge hannunta da sanitizer,kan kujera yaje ya zauna,agajiye,yace "sister Amina ya condition Win yarinyar yake?"

"Alhmdllh Naim jikinta da sau?i ba wani rauni bane me yawa,ta farfaWo yanzu bacci takeyi"ta bashi amsa tana murmushi.

Shuru yayi yana kallonta,itama shi take kallo,kawar da shirun tayi da cewa"naim rigar jikin yarinyar can fa,sunankane fa ajiki tun kana sargent,gashi kuma number kace ajiki,meke faruwane a ina tasamu rigar?"cewar aunty Amina cike da kulawa.

"Aunty amina nima tambayoyin dake kaina kenan,nide kawai a bakin titi naganta suna bara,na kirata na bata sadaka nima naga rigar,na fito na kirata,mota ta bigeta"ya faWi cikin damuwa

"karka damu zuwa dare nasan zata farka cikin ?oshin lfy,zamu san koma menene"cewar aunty amina.

Mi?ewa yayi yace "Bari inga jikin nata"

Ficewa yayi ya nufi aminity Win,zuciyarshi se sa?e sa?e take masa.

a kwance take ana mata ?arin ruwa zama yayi,akan kujera yana bin ta da kallo,inbanda warin jikinta ba abinda yake tashi.

ya jima a Wakin kamin yatashi ya fita,sallama yayiwa aunty amina,ya wuce gida da nufin ze dawo da dare.

********

Sajeeda bata farkaba se washgari da safe,inda ta fara waige waigen inda take,dirowa tayi agadon ta fara neman hanyar fita amma bata samuba,turo ?ofar da akayine yasa ta zabura da gudu tayi jikin bango tana ware ido.

aunty aminace da naim sanye cikin kakin sojoji,dake ?ara masa kyau.

"Ina zaki kuma ?anmata keda baki da lafiya"Cewar aunty amina tana murmushi.

"Lafiyata lau,"Ta basu amsa a tsorace.

kamo hannunta aunty amina tayi ta zaunar da ita gefen gado zama tayi kan kujera shiko naim kusa da ita ya zauna yana ?are mata,kallo,tabbas yaso yasan fuskarta,amma ya kasa tuno ko a ina ne yasanta.

"Karku cutar dani kunji,wallahi Allah Wai bisa ga lalura naka yin bara,dan insamu abinci"Ta faWi a tsorace tana kallonsu.

"Ba abinda zamuyi miki,amma sekin faWa mana gaskiyar ke wacece daga ina kike kuma rigar jikinki waya baki ita?"Cewar naim yana kallonta.

Jikinta na rawa ta kwashe komai daya faru tun daga labarin da inna ta bata,har korar da saleema tai mata,duka seda ta faWa musu.

Da ?arfi naim yajata jikinshi ya rungume wasu siraran

2 / 9