WATA UWA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 26.7K words

tsaye kan maganar da kikeson yi,dan kinsan ni ba yaro bane,dole nasan ?addara da yadda kuma zan karSeta."ya faWi cikin ?osawa.

"Yarinyar nan ta kwanaki datazo alhaji ?ar tawa ce da gaske,nina haifeta,banyi zaton zuwanta awannan lokacinba,hasalima ban Wauka tana rayeba,shiyasa,Na taSa aure alhaji"ta faWi cikin matsanancin kuka ta dur?ushe aguri.

batayi zato ba,taji yasa hannu ya Wagota,kallonshi take cike mamaki,murmushi yayi yace.

"Saleema,kin Wauka girma aykin banzane,koko shi ilimin sycology shima ?aryane?,to bari kiji,abinda baki saniba,tun ranar da sajeeda tazo gidan nan ni nasan ?arkice,mamakin abinda ya hanaki karSartane,yasa zuciyata ta faWamin akwai ayar tambaya,sannan hoton datazo dashi kin mance cewa a hotunanki akwai irinsa acikinsu,tun daganan na fara binciken ?wa?waf nason gano aynihin wacece ke kuma alhmdllh nayi hakan,nasa miki idone kawai,inga iya gudun ruwanki."daga haka yakwashe tarihinta na aynihi ya faWa mata.

Saleema ta cika da mamakin faruwar lamarin kuma be taSa faWa ko nunamata yasan komai game da ita ba.

"saleema ni ke nakeso,ba zanen ?addararkiba,da kin sani kin faWamin tun farkon haWuwarmu"cewar alhaji yana marmushi.

Rungumeshi tayi tana kuka,haWi da godiya,yajata suka zauna,sannan yace"zansa anemomin sajeeda aduk inda take,namiki al?awari ?arki zata dawo gareki"

Saleeema kwashe komai tayi ta faWawa mijin nata gameda ?ar tata,tun farko,sosai ya tausaya mata dan har ?wallah,yayii.

*********

"Sajeeda bazaki kuma gwada zuwa gun mahaifiyarkiba,kiga ko zata karSeki wannan karon,baze yiwu tana raye kuma ba zakije gareta ba"cewar uncle yana duban sajeedar.

"Baba,kawai abarta tunda ta zaSi wulaantani to inaga abarta dan koda ita ko babu ita rayuwa nayimin daWi ayadda ta riskeni"cewar sajeeda cikin ladabi.

Gyara zama yayi yace"saleema bazata taSa wula?antar dakeba,dole ni nasan akwai abinda ya faru,kimata uzuri,"

"Sannan bama hakaba sajeeda,uwa uwa ce,kina son albarkarta arayuwarki komai lalacewarta"cewar aunty maryam tana dafota.

Hakade suka sata agaba da nuna mata muhimmancin uwa,tana jinsu.

******

Rayuwa taci gaba da garawa komai na tafiya akan tsari,har Allah ya nufa sajeeda ta kammala karatunta,

Naim yafi kowa farinciki da hakan,dan har can yaje ya taho da ita,bayan an gama bikin kammala karatun.

Harda uncle aka taho da aunty maryam da ?annan sajeedar,dan sun jima basu zob.

mummy tayi murna sosai da zuwan nasu,dan rasa gun ajiyesu tayi dan farin ciki.

su uncle agidan su mummy suka zauna,naim kuma ya Wauki amaryarsa suka wuce gidansu,wanda yasa aka sauya komai na ciki dan murnar dawowarta.

Ranar bacci seda gari ya waye suka fara ramashi dan jiya kwanan ibada sukayi cike daso da ?aunar juna.

*******

Tafe suke,shida ita a mota sunzo sahad store,siyan wani sweet da sajeeda takesha a america.

sun fito kenan suka ganta tsaye jikin motarsu alamun su take jira.

"Sajeeda"cewar saleema dake tsaye tana kallonsu.

sajeeda amsawa tayi da"naam, ma..."se kuma ta kasa ?arasawa.

"ki kirani mamanki sajeeda,zuciyata na kewarki"cewar saleema,tana share ?walah.

Naim kallo Waya ya mata ya fahimci mahaifiyartace,dan haka rusunawa yayi har ?asa ya gaisheta.

duban fuskarsa take cike da mamaki nason gano a wanne gurine tasan fuskar.

"mama in ba damuwa,muje gidane nan kunga kasuwace,be kyautu a tsaya anan ba"ya faWi cikin girmamawa.

Drivern ta taba umarni ya biyota da motar ita kuma naim ya buWe mata bayan tasu motar ta shiga sannan suka shiga suka bar gurin.

Naim gidan iyayenshi,ya nufa,da su,dan su uncle nacan gwanda yakaita can ayi me gaba Waya.

Sam saleema batasan gidanba dan rabonta dasu tun a kano.

parking yayi sannan yazo ya buWe mata ?ofar ta fito,sajeeda ko dama da gudunta ta fice ta shige gidan,jikin mummy ta faWa tana kukan da ita batasan ko na menene ba.

Shigowar saleema da naim ce ta katse musu tambayar da sukewa sajeeda na abinda ya sa ta kuka.

uncle jikinshi har rawa yake ganin saleema agabanshi,hawaye ne ke biyo idonshi,ya dur?usa akan ?afafunsa ya haWa hannaye biyu.

saleema wacce tsananin mamakin ganinsu guri guda yasa ta kasa mgn se kallon tsana,data bisu dashi,idanunta sun kaWa sunyi ja.

"ki gafarceni saleema,jabeer beda laifi,nice nan ummul aba isun faruwar komai,kiyi ha?uri don Allah"cewar mummyn naim hawayen takaici na bin idonta.

"Ki yafe min Allah shaida nayi iya yina in dawo gareku amma hakan yaci tura,ki yafemin"cewar uncle yana hawaye.

"Ba gurinku nazoba,?ata na biyo,dan ina tsaka da nemanta Allah ya haWamu,da nasan nan gidan zaa kawoni da bazan shigoba.sajeeda kiyi ha?uri da laifin da na miki,ni mahaifiyarkice kuma bazan taSa dena sonkiba,wannan shine adireshina anan garin,kaduna,duk sanda kika shirya kizo gareni"tana kaiwa nan ta ajiye katinta,ta juya ta fice daga gidan.ranta na mata zafi tuno abubuwan dasuka faru da ita abaya.

Uncle ne ya Wauki katin ya mi?awa sajeedar,amma seta?i karSa,tace"baba wlh bana bu?atarta arayuwata ku kaWai kun gamsar dani,tayi rayuwarta nima inyi tawa".

"baki da hankaline sajeeda,da ina kallon kin zama mutum ashe ba haka bane kenan,maman taki kike cewa bakya bu?atarta,to bari kiji ko daga haihuwarki bata kuma kulakiba ta gama miki komai tunda ta haifeki."cewar naim afusace kamar ze daki sajeedar.

Du?ar da kai ?asa tayi tace"kayi ha?uri don Allah,bazan kuma ba"ta faWi tana hawaye.

Ranar har dare suna gidan,anata tauna mgnr.da tunanin ta yadda zaa shawo kan matsalar.

********

ita ko saleema koda ta koma gida kasa sa?at tayi seda ta faWawa mijinta duk abinda ya faru,.

"Saleema zuwa yanzu ya kamata ki zubar da komai,rayuwa ba tabbas ce da ita ba,akan me zaki ta ru?o azuciyarki har haka,ita jinjirar taki da kika barta tun ranar haihuwarta in tace zata ri?e hakan kina ganin zatasan ?imarki,haba ya kamata ki dinga yafiya".cewa alhaji mijin saleemar.

Fashewa tayi da kuka tace"da ace tun farko sun karSi cikinta taya zan rabu da ita,wlh komai ya faru sune sila"ta faWi cikn kuka.

"Naji sune silar,yanzu kuma sekika gansu tare,base ki godewa Allah ba,cewa Sangaren mahaifintane suka fara ganinta saSanin ace se bayan,kin ganta zaki fara nemo mata,mahaifinta kifa godewa Allah,shawarace"ya faWi yana kallonta.

batace komai ba se kukanta dataci gaba dayi.

********

"ki shirya yau zan kaiki gun mamanki,ki mata yini,in zan dawo zan biyo in Waukeki"cewar naim dake shirin fita office.

Turo baki gaba tayi,tace"ni to ay yau ban shirya zuwa ba"

"ni na shirya zuwan naki yau,kije ki shirya,ina jiranki a mota"yana kaiwa nan ya fice yabarta tsaye.

Badan ranta nasoba ta shirya,dan har ga Allah batason zuwa gurin mahaifiyar tata,sedan gudun Sacin ran mijin nata.

shiryawa tayi ta sameshi amotar,driver yaja suka fice motocin rakashi na take musu baya.

seda sukayi shopping a hanya sannan suka nufi gidan saleemar,dabeda wahala dan unguwar rimi GRA take.

me gadine yakirata awaya yashaida mata zuwansu,bada damar shigowa tayi.

Motar da suke cikece kawai naim yasa driver yashiga,bayan yayi parking ne sunka fito,sajeeda se Wari Wari take,dan ita saleemar tsoro take bata.

Saleema cike da farin ciki ta tarbesu hannu biyu.

bayan sun gaisa da naim ne yace"mama gatanan zanje gun ayki in na taso zan dawo in Wauketa"ya faWi cikin girmamawa.

gyaWa mishi kai tayi sannan yamusu sallama ya fice agidan,yasa megadi yashigo da kayan da suka kawo tsaraba.

sajeeda raba ido kawai take agidan kamar ace ar ta ruga da gudu.

zama kusa da ita saleema tayi,tace atsanake"zaki iya yin fin abinda yafi hakama sajeeda,amma de inaso kisani,ni mahaifiyarkice,dake matu?ar ?aunarki"

gyaWa kai kawai sajeeda keyi,dan batasan abinda zatace ba.

"shi kuma wannan wayeshi,naganku tare rannan,yauma gashi naganku?"cewar saleema tana kallon sajeedar.

"Mijinane,kuma Wan mummyne y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ayar babana,we are cousines"ta faWi atsorace.

Saleema kasa cewa komai tayi,dan dukan ya sameta da kyau,jin cewa Wan mummy ke auran mata ?a.

Haka suka yini suna hira sama sama,dan ma ?annanta na tare da ita suna Webe mata kewa,har lokacin dawowar naim Win tayi.

koda ya shigo suka gaisa da saleema,lokacin sajeeda na Wakin saleemar tana sallah,

gyarawa yayi ze zauna saleema ta dakatar dashi da cewa"da ka tafi,dan tace anan zata kwana,inyaso ka dawo gobe dan ta kwanta"ta faWi fuskarta ba alamun wasa.

Naim kasa cewa komai yayi ya mi?e yay mata sallama ya fice agidan ransa na masa wasuwasi,tabbas yasan sajeeda bazatace hakanba,amma Allah ya kaimu goben.

da wannan tunanin ya isa gida,ya rasa dalilinta na faWa masa hakan.

bayan yatafine sajeeda ta fito falon,fuskarta aWan sake tace"mama kamar muryar zaki najiyo ina sallah ko?"

"Eh shine amma nace yaje yadawo ya Waukeki gobe in Allah ya kaimu"ta faWi ba tare data kalli sashin da take ba.

Shuru sajeeda tayi,ta du?ar da kanta,ko kaWan bataso kwana agidanba amma bata da yadda zatayi,da ita.

mi?ewa tayi ta nufi cikin Wakin taje ta kwanta akan gado taja fulo ta rungume,tunanin mijinta na hanata sukuni.gashi garin sauri tazo su tafi ta baro wayarta agida bare suyi koda chart ne.haka bacci ya Wauketa zuciyarta fall tausayin mijin nata.

******

Koda gari ya waye sajeedace ta shirya musu breakfast,wanda hakan sosai saleema taji daWi ta dinga sa mata albarka,sosai sajeeda taji daWin albarkar da take saka matan wani sanyi takeji yana ratsa mata zuciya.

bayan sun kammala breakfast ne,tabata wata abaya me kyau sabuwa,tace"kije ki saka zamuje kano ne gun ?an uwana,suma su ganki"

da sauri sajeeda ta dubeta tace,"mama ay mijina bece injeba,da abari se gobe inyazo yau se atambayeshi"ta faWi bakinta na rawa.

murmushi saleema tayi tace"karki damu lokacinma daze zo mu har munje mun dawo ba kwana zamuyiba,inyaso afaWa masa munje Win inyazo"

sajeeda shuru tayi batace komai ba haka taje ta kimtsa,ta dawo tasamu suma sun kimtsa,suka fice zuwa mota,

Ga mamakin sajeeda Saleem ta gani a mazaunin driver,da sauri ta juyo ta dubi saleemar,murmushi tayi mata tace"Karki damu Wan ?anin mijinane saleem,drivernmu baya nan shine nakirashi ya kaimu"

gyaWa kai kawai tayi,saleema da kanta ta buWe mata murfin motar ta shiga,suka fice daga gidan,shi kanshi saleem Win mamakin ganin sajeedar yake,duk da yanzu ta sauya ta ?ara girma amma be mancetaba.

Haka suke tafe su suna hirarsu ita sajeedako bata cewa komai har suka iso kano.

*******

Shiko naim da safe yazo gidan dan su gaisa yaga sajeedar sede ga mamakinsa basanan,se takarda da saleema taba me gadi ya basa,inyazo,ba tare da sanin sajeeda ba.

mota ya koma ya zauna ya buWe takardar yafara karantawa.

_Naim kai bakamin komai ba amma mahaifiyarka da Wan uwanta sunyimin,auranka da sajeeda ?addarace ta haWashi,amma bazan barshiba,ganin Wan wacce ta WaiWaitamin rayuwa ya auremin ?a,hakan ze dinga taSani,dan haka na nesanta sajeeda dakai,karma ka wahala gun nemanta kotu zata sa ka sakarmin ?a_

Jirine yaji yana Waukarsa,da sauri ya dafe kanshi yana karanto duk adduar data zo kan bakinshi.

ya jima yana addua kamin yasamu natsuwarshi ta dawo.mota yaja yabar ?ofar gidan,direct gidan iyayenshi yatafi,

Sunyi mamakin ganin ya dawo dan yanzu yabar gidan yace zashi Wauko sajeeda agidan mamanta.

kan kujera yaje ya zauna,duk yadda yaso ya daure ya kasa kawai seya saki kuka,wanda yayi matu?ar Wagawa iyayen nasu hankali sukayi caaa kanshi.

takardar ya basu suka karanta,atare,nanko guri ya kaure da sallallami,uncle ne yafara mgn.

"wannan ay rashin hankaline,yara ay ba ruwansu awannan mgn akan me zata yanke wannan Wanyan hukunci"ya faWi cikin faWa dan ranshi ya Saci.

"abi komai a hankali insha Allahu,zezo da sau?i,ayi ha?uri,tayi fushine wanda insha Allahu zata sauko"cewar mummy cikin sigar rarrashi.

Haka naim ya kasance agidansu kamar marar lfy,inbanda hawaye ba abinda yake,babban abinda ke cimasa rai rashin waya a hannun sajeedar.

*******

Sajeeda ko acan kano,ta cika da mamakin ganin yadda dangin maman nata kowa kesonta se nan nan suke da ita,kowa na bata kulawa.

Bata farga da lokaciba seda aka kira sallar magriba,bayan sunyi sallah ne,tacewa mamanta"mama mu tashi mu tafi nasan naim zezo gidan yasamu bama nan,kar yaga kamar baa kyauta masa ba."

"karki damu sajeeda,naim mutum ne me fahimta ze fahimceki aduk sanda kika koma,saleem ya tafi kaduna Wazu da laasar mamanshi batajin daWi,kuma shine ze dawo ya Waukemu kar ki damu"ta bata amsa cikin halin ko in kula.

"ni asani a motar haya to ta maidani gida"sajeeda ta bu?ata.

murmushi saleema tayi tace"sabida kijamin zagi gun mijinki,hanyar daba tsaro kikeso insaki kibi amotar haya to bazan iya ba,ki bari,in maidaki gida lfy,inyaso a gunsa kya shiga motar hayar ba ananba"

sajeeda shuru tayi,bata sake cewa komai ba.

Wasa wasa seda sukayi sati guda cuur a kano,zuwa lokacin sajeedar ko abincin kirki bata iya ci sabida damuwa wanda ita saleema ko tayi kamar bata san halin da take cikba.

Ticket ta siya musu zuwa abuja wanda sajeeda ta cika da farin ciki tunaninta kaduna zasuje.

Har suka sauka a abuja bata kawo komaiba,har suka iso gidan su saleemar na abuja daya gaji da haWuwa.

bayan sun shigane,salima taba masu gadi umarnin hana sajeeda fita,daga gidan batare da sajeedar tasan haka ba.

bayan sunyi wanka sun hutane,salima ta dubi sajeeda tace"sajeeda,nagode da ha?uri da juriya da biyayyar da kika nunamin,Allah miki albarka,sede inaso ki sani bana Waukeki bane daga kaduna da nufin zan maidawa mijinki ba,ko Waya,auranku zan raba dan bazan jure ganinki tare da Wan ma?iyiyataba a ?ar?ashin inuwar,aure,kamar yadda ta rabani da babanki,nima sena rabaku"ta faWi a fusace.

Kuka sajeeda tasa,ta kama ?afafunta tana faWin"komai zan Wauka mama amma banda rabani da mijina,shiWin rayuwatace mama"ta faWi cikin matsanancin kuka.

"Haka babanki yake azuciyata abaya amma sirikarki seda ta rabani dashi dan haka ki fara ?irga kwanakin zawarcinki tun yau,nagodewa Allah dayasa ba Wa ko ciki tsakaninku bare abun yadameni"cewar salima fuska ba sassauci tabar gurin.

Kwana sajeeda tayi tana kukan rabata da mijinta da mamanta zatayi.tabbas bazata taSa barin hakan ta faru da ita ba.

********

Naim ko duk wata hanya dazebi dan ganin sajeeda ya bita amma be ganta ba.

Yayi kuka,yayi adduar har ya rasa,mafitar kamawa,dan yaga abun bana ?are bane.

iyayenshi ma a wannan halin suke ciki,dan naim Win shi yake ?ara Waga musu hankali ganin yadda duk yabi ya ?are ya rame,dan tunanin awanne hali matarshi take.

Tun yana iya daurewa har dauriyarsa ta ?are ya yanke jiki ya faWi akayi asibitin aunty amina dashi.

hankalin kowa a family Win yatashi,ganin halin da yake ciki,ita kanta aunty amina kuka take in tana dubashi ganin yadda ?anin nata ya ?are ya lalace.

******

"Mama jikina na bani mijina beda lfy kiyiwa Allah kibarni in tafi gun mijina,wlh bazan iya rayuwa babu shiba."cewar sajeeda tana kuka agaban saleemar.

"Sajeeda,ni iyayena na rasa adalilin ba?in cikin uwar mijinki zanfi kowa farinciki naim Win ya mutu taji abinda naji nima"

"naim baze mutuba mama,sabida bashi ya miki laifi ba,mamanhine,meyasa kikeso ki koyawa zuciyata,tsanarki ne mama?"ta faWi tana kuka me tsuma zuciya.

Barin gurin saleema tayi dan batasan me zata kuma cewaba.

sajeeda mi?ewa tayi ta fice ta nufi get da niyyar ficewa agidan amma amma masu gadi sun hanata hakan ne yasa ta koma parking space ta zauna tana kukanta agurin.

Koda dare yayi ?in shiga ciki tayi duk ko da irin mgnr da maman tayi mata,?i tayi,komawa ciki tayi ta barta agurin ta kwana batare da tsoron komaiba.

Koda gari ya waye zuwa tayi ta sameta asume agurin duk amai ya Sata mata jiki,rai a hannun Allah.

a gigice ta kwasheta zuwa cikin gidan ta kira doctor Win gidan,yazo gida dubata.

bayan ya aunatane,yasa mata ruwa,da allurai,wanda suka farfaWo da ita,bayan ya kammala komai ne,ya shaidawa saleema,sajeedar na Wauke da ciki na sati uku sannan akwai maleria ajikinta.

Tashin hankali baa sa maka rana,haka saleema ta dinga kai gouro tana kai mari,naso samo mafita gameda hakan.

magunguna yabasu sannan ya musu sallama yatafi.

Dole ta zubar da cikin dan bazata taSa barin hakan ta faruba,sede koma meye ya faru.

zuwa dare sajeeda ta dawo hayyacinta,da ?yar tasha tea Win Win da aka haWo mata, dan yanzu Waki tasata ta rufe dan karta ?ara fita waje ta kwana.

da gari ya wayene sajeeda bayan tayi sallah ta ?uduri aniyar fita agidan kota halin ?a?a,sede koma meye ze faru ya faru.

Mi?ewa tayi ta dubi saleema dake tsaye gaban tv tace"mama ki buWemin ?ofar nan in fita"

"zan buWe miki amma da sharaWin dole ki amince da batun raba auranku da naim da zansa kotu tayi matu?ar kinaso naci gaba da amsa sunan mahaifiyarki."cewar saleema ba tare da tunanin komaiba.

Waigowa tyi da jajayen idonta da tuni suka rine dan kuka tace"mama ada na Wauka rashinki cikin rayuwatane yasa na haWu da ?alubale,ashe ba haka bane nayiwa abun bahagon kallone,dawowarki cikin rayuwatane,babban ?alubalen dazan fuskanta,daze iya sanadin rayuwata,ina son mijina mama bazan iya rabuwa dashiba!!!"takai ?arshen maganar cikin ?araji.

Tashin hankali baa sa maka rana,bakinta har harWewa yake tace"kina nufin mijinki yafini agurinki ni mahaifiyar da na haifoki?"

"Kwarai kuwa mama yafiki!!!"ta bata amsa tana kallon ?wayar idonta alamun tsoro yakau.

Da lalube saleema ta nemi kujera ta zauna ta Wora hannunta kan ?irjinta setin zuciyarta dake barazanar faso ?irjinta ta fito tsbar kaWuwa da amsar da sajeedar ta bata.

takawa tayi ta isa gaban saleemar taci gaba da cewa,"kwarai ke kika haifeni kin gama min komai,sede inaso ki sani,kin barni lokacin danafi bu?atarki yanzu ko bana bu?atar komai agurinki,Naim ya hanani kukan rashinki,na zo gareki kika koreni shi ya karSeni,be taSa barina ba kome zan masa,na fara nono,na fara period,duka ba?yanan shi yananan,mama ina zuciyar uwa take lokacin da kika iya tsallake ?arki jinjira da ko awa batayiba da haihuwa adokar daji,cikin halin ta mutu kotai rai,nace ina zuciyar uwa take mama!!!"tayi mgnr cikin Waga murya,gamida faWawa jikin maman tana kuka dake nuna Wacin abinda ya faru abaya na taso mata.

Kuka saleema ta fashe dashi,tace"kin taSa tambayata,ya akai hakan ta faru,koko ni banida abun cewa ne,taya zan haifi abinda banaso,in banasonki inkasheki mana,"ta faWi cikin kuka.

A hankali ta labartawa sajeeda tarihinta tun daga farko har ?arshe,sajeeda sosai tausayin mahaifiyarta da so da ?aunarta suka cika mata zuciyarta,duk wani haushinta da takeji abaya taji ta denaji,tabbas mummy ta cancanci fiye da hakama,amma tunda ta nemi yafiya ya kyautu ayafe mata,tunda Allah ya nuna mata ishara.
itama sajeedar nata tarihin taba saleemar,nan suka rungume juna sunata kuka na tausayin juna.

share mata hawaye tayi itama ta share nata,tace"mama na fahimceki kuma na fahimci ciwon da kikeji na mummy,kuma amatsayina na ?arki zan goyamiki baya ki hukuntata har zuwa lokacin da kikeji kin huce zanyi biyayya"

Gyara zama saleema tayi,ta kamo hannun sajeeda,tace tana murmushi"sajeeda,naim yataka rawar da kaf duniya ya kyautu ace kinfi sonshi akankowa,ciki harda ni,sajeeda,mijine da ake rabawa matan aljanna ke Allah ya zaSoki ya baki a duniya,duk girman laifin mahaifiyarshi agurina yau naim ya shafeshi azuciyata,Allah yay muku albarka sajeeda na zubar da duk wata ?iyayyata,ina muku fatan alkhairi"

Murmushi sajida takeyi me haWe da hawaye tace"mama naim yadda kika zayyanashi haka yake,ngd da janyewarki mama"ta rungume maman cikin farinciki.

"dole sajeeda na ajiye komai,in nuna miki gatan da ban nuna miki ba a baya,inaso ki kwantar da hankalinki dan kar cikin jikin ki wani abun yasameshi"cewar saleema tana shafa mata baya.

"Mama nice nake da cikin wai?"sajeeda tayi tambayar tana ware ido.

"Kece kike da ciki sajeeda ina adduar Allah ya inganta"

shuru tayi tana nazari,Wago ido tayi ta dubi maman tata tace"to amma mama taya ciki yake shiga jikin mutum ba tare daya saniba?"ta kafe mamar da ido tana jiran amsarta

Dariya saleema tayi ganin tsagwaron yarinta da gaSanci da sajeedar ta nuna mata.

"Gobe zan maidawa mijinki ke inyaso seki tambayeshi,tunda kinga atare kuke ni bazan iya

7 / 9