WATA UWA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 9

12K to 15K   out of 26.7K words

abun mgn akai,tana sakin habaici.

malam tirke saleema yayi,dan yaji wanda yamata cikin,duk da zuciyarshi tafi zargin jabeer,amma yanaso yaji daga bakinta.

"wannan cikin saleema na waye?cewar malam rai a Sace yana kallonta.

kanta a?asa tace"jabeer malam,amma wlh ba zina mukayiba,"ta faWi cikin kuka,daga haka ta kwashe komai daya faru ta faWa mashi,lokacin zuwansu lagos.

Shuru malam yayi yana jinjina lamarin,tabbas ya gamsu zamani yayi nisan da besan yayiba,dubanta yayi murya na rawa yace.

"in kums ya musa cewa ya aureki kuma fa,saleema?"

da sauri ta Wago kanta tana girgizawa,tace cikin kuka",baze ceba baba,sabida yana sona da abinda ke cikina."ta faWi tana ci gaba da kuka.

"kiraminshi kice ina nemansa"cewar malam

"Yayi tafiya bana samunsa awaya,amma,nasan gidan yayarshi uwarsu Waya ubansu Waya,anan,nasarawa gra"ta faWi hawaye na ci gaba da bin idanunta..

Malam beyiwa matansa bayanin komaiba yanaso yaje gidan yayar tashi ta haWashi da iyayensu dan asan abunyi.

wasa wasa seda suka shafe fin kwana biyar basa samun damar ganinta,sede su dawo,ga mgnr ciki har inna habiba ta fasata a unguwa saleema tayi cikin shege.

akwana na shida haka malam yasake tasa saleema agaba suka koma gidan.

sun isa gidan yayar tashi lafiya,da laasar,amma basu samu damar ganawa da itaba se ?arfe tara na dare,faWin irin wula?ancin da suka gani gurin masu gadi baze faWuba.

bayan sunje garetane,ta amshesu a wula?ance,duk da ta gane salimar hakan be hanata wula?antasu ba.

"baiwar Allah"cewar malam.

"Hajiya"ta bashi amsa ranta aSace.

"to hajiya,mu ba munzo neman taimako agurinki bane,wannan ?atace,kuma ?aninki jabeeru ya yaudareta sunyi auran sirri,yanzu gashi harda ciki wata huWu,shine nazo dan asan abunyi"cewar malam atausashe.

Dariya yayartashi tayi me isarta,sannan tace,cikin izza"kunyi hauka tabbbas da kuka kwaso tsumman rayuwarku kukazo gareni da wannan tatsuniyar,jabeer ay ko mata sun ?are ba abinda zeyi da ?arka,koda can ita ta nace masa,to kuji da ?yau inkai ?arka tafi ?arfinka zata iya aure bada izininka ba,to mu namu mun isa dashi baze taSa aure bada izininmuba,to tun kan dare beyiba ku nemi uban cikin ?arka bade ?anina ba,"

"kide kirashi kiji daga gareshi,dan kar kizo kuma kiji kunya daga baya cewar salima tana kuka.

"Abinda jabeer ze iya nasanshi base na kirashiba ku tashi ku ficemin da gani"cewar yayar tashi afusace.

Mi?ewa malam yayi yafara yin gaba,salima ma mi?ewa tayi,ta kalli yayar tace"ko badaWe ko bajima,sekunyi danasani alokacin dabaze amfanekuba"tana kaiwa nan ta fice tana kuka.

Haka suka dawo gida malam yatara matansa duka yamusu bayanin halin da ake ciki,inda take yanke inna habiba ta goyi bayan su yayar jabeer Win kan cewa saleema ?arya take.

itade mahaifiyarta bata iya mgn sabida zuciyarta tacika da ba?in cikin abun.tayarda da ?arta amma tunda ba shedu aykin banzane.

*******

tun daga wannan lokaci,saleema da iyayenta suka shiga cikin tsangwama a unguwa,malam be iya gudanar da ayyukansa kamar da,hakan yasa yasallami almajiransa,kowa ya koma garinsu.

Sannu a hankali mahaifiyarta ta fara rashin lfy,inda ciwon beje koina ba,ta kwanta ta mutu,bayan ta albarkaci saleemar.

Rayuwar tayiwa saleema Waci,na rashin uwarta,haka taita wahala ita kaWai,bame tausaya mata,ga malam yanzu ko mgn bayaso tai msa,amma kullum yana ayko mata da rubutun masu ciki.

Cikin saleema na wata bakwai shima malam ya mutu,yarage se salima da ?annanta da kishiyar uwarsu da yayyansu maza.

tsabar masifa haka kullum suke taruwa su zaneta kan cewarsu ita takashe malam da ba?in ciki.

cikinta na wata takwas ta yanke shawarar barin garin,kano gaba Waya,sabida ko waje bata iya fitowa cikin salama,se yara sun bita sunyi mata ihu,gashi kullum cikin jiran jabeer take amma babu alamunsa,hakanne yasa tayi aniyar guduwa ko ta samu salama agaba,dan tun suna lavel two aka aurar da ?annanta uku mata,sabida su basu da raayin karatu me zurfi,se ?annata guda biyu maza.ayko cikin dare ta fice bayan ta sallami ?annan nata.

sokoto ta yanke shawarar zuwa,ayko mota tahau takaita can Win inda ta samu uwar Waki a silame local govt area hajiya rabi mace me mutunci da tausayi da kamun kai,,suna sanaar abincin ita salima na wanke wanke sabida ciki baze barta aykin dafa abincinba.matar na bata abinci.da ?an kuWin kashewa,jin salima bata da kowa anan Winne yasa hajiya ke tafiya da ita ?auyansu su kwana agidanta in gari ya waye,su dawo gun sanaarsu.

Matar ?ar asalin garin gande ce,zuwa take cikin garin na silame sanaa in dare yayi su koma garin gande su kwana.

bayan wata guda da zuwan saleema wani dare da misalin sha Waya na dare ,sun kammala komai suna jiran me motar hajiya rabi me abincin dayasaba kaisu gida duk dare yazone.
na?uda ta kama saleema,haka suka koma cikin rumfar da taimakon hajiya Allah ya sauketa lfy,tasamu ?arta kyakkyawa me kama da ita amma tafi kama da mahaifinta jabeer.

hajiyace ta yanke cibi sannan ta taimakawa,saleema suka shiga mota dan drivern ya ?araso,ta naWe jinjira a Wankwali.

sun yi nisa atafiyarne,da misalin sha biyu da rabi na dare,faWa ya kaure tsakanin ?an taadda da sojoji.

cikin jeji driver ya yanke,sede suna cikin tafiya ajali ya riskeshi,shida hajiya rabi inda gun musayar wutan harsashi ya iso garesu dan basu da nisa da inda abun ya faru.rashin sani da ?arar kwana yasa be juya dasuba yashigo dasu.

ga motar ta?i tsayawa,agigice saleema ta rungumo ?arta,ta buWe murfin motar,suka faWo ?asa,sabida motar dama a hankali take tafiya.

tana faWowa,agigice take,tami?e tabi hanyar da suka biyo da gudu,rungume da zani batare datasan ta jefar da jinjirar,a?asa ba,,ta fice da mahaukacin gudu.

koda tazo titi agigice take,dan mutuwar hajiya rabi ta razanata bada wasa ba,koda tazo titi yanke jiki tayi ta faWi,?asa sumammiya,sabida bata yi ko awa guda da haihuwaba,bata da wani ?arfi ajikinta.

bata farka ba se bayan kwana uku,a asibiti,acikin garin sokoto,,?arta ta fara nema,aka shaida mata baa ganta da ?aba,Warsawa tayi aranta ansacene lokacin data suma,

tayi kuka kuma taji Wacin rashin ?ar amma data tuno abinda,akayimata,setaci tadena jin haushin komai.tana gama samun sau?i ta baro asibitin,zuwa abuja,

anan ne ta ci gaba da sanaar data baro sokoto tanayi,wato seda abinci.takwashe shekaru shida tanayine ta je kotu,al?ali yasaketa bayan tamasa bayanin komai daya faru.

to bayan sakin ne,ta haWu da mijinta,Alhaji usman inda tai masa ?aryar bata taSa aureba bare haihuwa,kuma tace bata da kowa aduniya,haka yajata zuwaga ?an uwansa sukai mata gata suka aura masa ita bayan tasha haWin maida tsohuwa yarinya.

shekararsu biyu da aure ta haifa masa tagwaye mace da namiji,soyayya da gata babu ta inda bata samu,kowa sonta yake.

asalin su mijinta kanone,sjuna zuwa duk sallah amma koda wai bata zuwa gidansu,sede tana ganawa da ?annanta aSoye tai musu ihisani,su wuce.

me hotonta ma yardace tayi dashi yasa tabarshi yake zuwa har gidanta,kuma be taSa faWawa kowaba,danshi mutum ne me amana,shike zuwa ya karSowa ?annanta wasu sa?on inba na kuWi bane.

bayyanar sajeeda agareta,kallo Waya tai mata tasan cewa ?artace,duba da kama da take da jabeer,faWin irin daWin dataji na ganin ?artata baze faWuba,amma bazata bari ta rusa mata gidan auranta ba,uwa uba takaici da ba?incikin mahaifin sajeeda baze barta ta karSetaba.

uwa uba tayi imani ubangijin daya raya sajeeda har tazo gareta,cikin aminci tasan zeci gaba da kulawa da ita aduk inda take,amma bazata karSeta ba.

wannan kenan.

*********

Shiko anashi Sangaren mahaifin sajeeda,yayarshi wayar mijinta ta kira tasa yabashi,sashi tayi yatashi acikin mutane,bayanya keSene tace masa.

"Jabeer kaga abinda nake gujema ko,soyayya da ?a?an talakawa,Wazu budurwarka sukazo da babanta,wai kunyi aure da ita aSoye gatanan ma daciki,kajifa"

"Aunty duk abinda suka faWa gaskiya,wlh basumin ?aryaba,shaawace ta ruWeni da kuma son da nikewa saleema pls anty kibasu kulawar data dace don Allah jibi zan dawo"ya faWi atausashe.

"jabeer kayi haukane,bakasan yanzu duk abinda zanyi nida ?an uwana zaayi attaching Winshi da sunan mijinaba,bakasan idan ?an jareeda suka ji wannan labarin se kasuwancin mijina yasamu nakasuba,bama hakaba shi kanshi baxeji daWiba,dan bame yarda auran kukayi,dan haka,tun wuri kamance dasu ma arayuwarka dan wannan abun kunya bazan bari ya faruba wlh"

"aunty infa manta kikace nufinki in manta da matata da gudan jinina dan kawai martaba da mutuncin naki mijin,baze yiwuba dole indawo inkula dasu."ya bata amsa afusace.


"jabeer katunafa bamu da uwa bamuda uba,shine komai namu,bata haka yakamata musaka masa ba"

"seme,wlh ko baze ?ara kulani senazo gun iyalina"ya bata amsa cikin fushi.

""To Allah ya dawo dakai lfy jabeer"ta faWi sukai sallama.

a daren tasa pa Win mijinta,yasace passport Win jabeer da wayarsa,batare daya saniba,sabida wayar da itane ze kira wani a nigeria yaje yaduba masa salimar,passport ko sedashi ze dawo shi kanshi.


jabeer tun yana Waukar abun kamar wasa harde ya fahimci dawowarshi nigeria sede wani hukuncin Allah.

haka ya ha?ura ya fauwalawa Allah,gashi lokacin social media bata yawaitaba,shiyasa abubuwan suka gaza warware masa.

mijin antynshine yabashi ayki a sabon kamfanin daya buWe a?sar ya Worashi akan dukiyar

sede yayar tashi,takai masa ziyara ita da ?a?anta,ko kaWan be zargetaba,shiyasa aduk lokacin datazo yana jin daWin ganin nasu

se bayan shekaru,huWu da faruwar lamarin ne tasa aka bashi passport Win nashi ta hanyar ajiye masa shi amota batare dayasan wanda yay hakanba,ganin yasamu passport Win nashine yasa be tsaya binciken wanda yadawo dashiba,ya shirya yazo nigeria,inda yasamu labarin salimar ta shiga bariki kuma iyayenta sun rasu,yayi kuka dajin hakan,sosai,ya rasa inda ze nemota,hakanne yasa ya ha?ura ya koma america gaba Waya da zama ko marmarin zuwa nigeria bayayi.

yayi aure,da matarshi maryam,wacce suma mazauna can american ne,sannu a hankali take rage masa damuwa da tunanin salima da abinda ke cikinta.

sun haihu,yara biyu duka maza amma kullum yana adduar bayyanar salima da abinda ta haifa masa.

*********

Naim kwance kan gadonshi,wayarshi manne akunnensa,fuskarsa Wauke da niimtaccen murmushi,alamun wanda yake wayar dashi na jefashi cikin shau?i,duba da yadda yake shafa ?irjinshi.

"Dan Allah zaki kadawo haka nadena Sata maka rai,"cewar sajeeda lokacin da suke wayar cike da shagwaSa dan tana ganin yadda aunty amina ke waya da mijinta.

"ba kina tare da auntyba me yasa kika dameni in dawo?"ya faWi atausashe.

turo baki gaba tayi kamar yana kallonta tace"to kome ne auntyn zata min,wlh nide na gaji,kullumfa ni kaWai nake kwana"ta faWi ashagwaSe.

sosai yakejin daWin hirar,tasu dan yanzu ta fara zubda accent Win garinsu,sannan ta Wan natsu ba kamar daba,da ko hirarce duk shirme ne acikinta.

"sajeeda,in nadawo akwai wata tafiya da zamuyi tare da nakeso takawo sauyi me girma acikin rayuwarmu nidake"

"zaki ina zamuje?"ta tambaya.

"Sede nadawo tukunna bazan faWa miki ba surprise ne"ya faWi cikin raha.

"sumurise kuma,minana haka?"tayi tambayar cikin rashin fahimta.

"To bazata zan miki"

Murmushi tayi,sannan tace"zaki tunda ka aureni baka taSa,kawomin hatsi nayi sindil?e ba"

"meneneshi iya rigimata ko a ina yake anemoshi akawowa gimbiyata tayimin sindil?e"yafaWi cikin raha,ayko taji daWin kalaman nashi,nan ta,shiga ?yal?yala dariya yana ?ara sata.

sun jima suna wayar dan har seda tai barci sannan ya kashe shima ya kwanta yanawa Allah godiya.

*******

Zaune take tana ta kallon tiktok,wani video ne na decorating cake tagani,da yay matu?ar burgeta,haka ta lalace gun kallon video,wanda yasha ado sosai.

anan ne taga inda akewa mutum bazata na murnar birthday,tana cikin kallonne,anty amina tace.

"sajeeda mijinki yace min nanda sati biyu ze dawo,yace kema ya faWa miki ko?"ta faWi tana kallonta.

"eh ya faWamin amma aunty gani nake wasa yake seyafi haka"ta faWi tana murmushi.

dariya amina tayi batasan daliliba itade tanajin son sajeeda aranta har cikin jininta,komai tayi burgeta takeyi,uwa uba kama da takeyi da mummynsu.na ?ara sawa tajita aranta.

"daWina dake shirme,shiyasa ko kimtsawa baki fara ba,ay miji inze dawo tafiya shirin tarbarsa akeyi sajeeda,gashi ranar daya dawo washegarine murnar zagayowar ranar haihuwarsa,amma shine baki fara shiryawa ba"anty ta faWi tana dariya.

nande aunty ta mi?o mata ledar magungunan data siyo mata daga niger,ta bata gamida mata bayanin kowanne.

sajeeda bataji kunyar komai ta amshe ta fara godiya.

ayko ?udurcewa tayi itama aranta seta haWawa zaki birthday party surprise nagani na faWa,tunda taga yadda akeyi.

Ana eh gobe ze dawo tuni tayi kitso tayi lalle gwanin burgewa,anty tasa anmata dilka da halawa se she?i take,tana fitar da wani niimtaccen ?amshi,me kwantar da hankali.

da dare tasa amaidata gidanta,acewarta tafiso yadawo yasameta acan.

anty bata hanataba,dan haka ta haWata da me aykinta Waya driver ya kaisu,dan ta tayata wasu aykin dan inde girkine yanzu batajin sajeeda ko a villa zata girka.

*******

washe gari ko gidan me aykin ta gyare mata gidan fess,inbanda ?amshi ba abinda yake,sajeeda da kanta ta gyara Wakn naim kamar yadda taga aunty nayiwa mijinta.inbanda sassanyan ?amshi ba abinda ke tashi,ga wasu sabbin zannuwan gado data zubawa gadon taushi kamar jikin mage.

Duk nauin abincin datasan yanaso seda ta shiryashi adinning area.

me aykin ta gyara kitchen Win fess kamar baayi amfani dashiba.

kuWi taba me aykin tai mata godiya drivern sajeedar ya maidata gida.

jilbab Winta tasaka ta fice agidan,zuwa layin bayansu inda tai sanaar masara.

ayko nanfa sukai ta murnan ganinta bayan sun gaisane,taje shagon kusa dasu ta siyo gero,da cingam,data dawo gun ?an shaye shayen ne ta mi?a musu kwalin cingam Win taje.

"gobe da misalin ?arfe bakwai na safe ina gayyatarku,taro gidanmu,dan Allah ku faWawa kowa fa,kuma kuyi ha?uri lokacin ya ?ure,bananan ne,sejiya nadawo"

"karki damu ,uwar kyawawa,safennan garantine,muna gidanku,ba Sata lokaci hidimarki tamuce,"suka haWa baki gurin bata amsa.

sosai tai musu godiya sannan ta wuce gidanta.

tana zuwaji?a geron tayi da ruwan zafi,ta jira yaWan ji?u,tasa blender ta markaWashi,tana gamawa ta tace shi ta cire dusar,sannan ta rufeshi,ta gyara gurin sannan ta shiga wanka,ta jima tana wanke jikinta sannan ta fito tazo ta turara jikinta da turaren wuta na tsugunno.

bayan ta gamane ta haWe kanta awasu sheggun riga da sket,maroon color,masu bin jiki,da suka fitar da kyawun surarta,batasa Wankwaliba,haka tasa takalminta mekyau,ta feshe jikinta da turarukan da anty ta bata.

naim ko tunda suka sauka a airport bayan ishai yake ?age dayaga sajeedarsa,dan tun jiya ta shaida masa tana gidanta.

tana falon sama taji alamun shigowar motocin da sukaje Waukoshi.

zumbur ta mi?e tayo waje tabi hanyar step daze kaita falon ?asa dan tajiyo sallamarsa yana kiran sunanta.

Naim tunda yashiga falon kansa so iyi ya juye,dan be taSa shigowa yaji yanayin dayaji yanzun ba.

wani farincikine ya mamaye zuciyarshi lokacin daya hangota da gudunta tana sakkowa daga matakala,fuskarta Wauke da faraa dake nuna jin daWin dawowarshi da tayi.

buWe mata hannu yayi tako shige jikinshi tana faWin "zakina ya dawo"Wagata sama yayi yana juyawa,afalon yana cusa hancinshi setin haq Winta yana sha?ar ?amshin dayake fitowa daga gurin dake kwantar da hnkalinsa.

sunjima ahaka kamin ya sauketa, ya Wan ja da baya yana ?are mata kallo yana yabawa itako,sejuyi take tana kaWa jiki tana dariya.

"lalle madam Wina ta girma,iyenba"ya faWi yana rungumeta,.

"muje sama kai wanka,babyna,"ta faWi kamar yadda taji anty nacewa mijinta baby.

dariya naim yayi yace"nine babyn yau?"

Dariya tayi tace,"mijin antyma me furfura babyn take cemasa bare ni me sabon jini,"

dariya naim yake kamar cikinshi zeyi ciwo lalle zuwanta gidan aunty taimakone agareshi.

koda sukaje Wakinsa daskarewa yayi a tsaye ganin yadda ta ?awata Wakin,dakanta t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ai masa wankan,naim nata mamaki,yagaza rufe baki ganin sajeedar yake kamar anmasa customising.

koda suka fito ita ta kimtsa shi,shiyafison ahau gado yaji ya lafiyar damina uwar ruwa,amma ita sajida yau da sabon tsari tazo.

dinning takaishi,anan ne ta?urewa mamakinsa,haka yacika tumbinsa da abincin,dasukai masa daWi sosai.

bayan ya kammala ne ya dubeta yace"to yanzu kuma se me yayi saura?"

"ka taso muje kaci me abincin ka biyani ladan girkina"ta faWi tana lashe leSe gamida Wan ri?eshi da ha?ori.

ba musu ya sureta,zuwa sama,ranar har akan tiles seda naim ya dirji sajida,kan kujera,kan gado,kan mudubi,kai har abango seda ya mannata yaci abarsa.

sun jijjigu,shiyasa suka yada zango agado bacci me daWi ya Waukesu rungume da juna.

*******

Da asuba bayan sunyi sallah shi bacci ya koma,itako ina kitchen ta nufa,kullun geronta na jiya ta tsiyaye ruwan, ta yamutsa gasarar,ta juye atukunya,ta Wora akan wuta,tasa muciya ta fara juyawa.

sannu a hankali har ya dahu,yayi kauri kamar tuwo,

fan Win yin cake ta Wauko,tasa aciki,guda biyu da me 4 shape da me cycle.

sauran kuma mulmulashi tadinga yi kamar Wan sululu.

chopping bord ta Wauko ta kwakkwafe na cikin fan Win ayko suluf ya fito ta fara saka,me 4 shape Win sannan ta Wora me cycle Win akai.

?an ?ananun data mulmula ta Wora,asaman tayi decorating dasu,abun gwanin burgewa,tana gama jerasu,taje ta jajjaga tarugu da albasa,tasa manja awuta,ta soya tayi de ?ar miyar jajjage,wacce taji wadataccen manja da kayan yaji.

Wauka tayi ta she?a akan wannan tuwon Sulan nata,datayi decorating Winsa azuwan cake,(ita ala dole tayi suger icing an zuba ruwan chocolate)

dakakken yaji ta Wauka ta barbaWa asama,sannan ta zuba yankakkiyar albasa.

falo ta Wauko cake Win nata ta kawo ta Wora kan center table.duk manjan ya Sata guri.seda ta gyara komai sannan tayi sauri ta dafa taliya me rai da lafiya da taji kaji,me yawan gaske sabida ba?inta.

Wakinta ta je da sauri tayi wanka ta kimtsa,tayi kyau sosai,ta fito kenan taji alamun hayaniya awaje,ayko fitowa tayi,jamaartane suka iso,sojoji sun hanasu shigowa.

da sauri ta ?arasa gurin tace ay naim Win yasan da zuwansu,ba musu aka barsu suka shigo,wajan su hamsin,wasuma duk a?wale suke ta Wurasu falon gidan.

"sannunku da zuwa,abokaina,yanzude ku zauna,bari inje intaso zaki,dama murnar zagayowar ranar haihuwarsa nakiraku ku tayani,bazata nayi masa,dan haka ku tayani birgeshi"cewar sajeeda bayan sun zazzauna falo ya cika.

"Se kinsha uwar kyawawa,ba sauti ne"cewar tsula Waya daga cikun abokan nata.

"sauti kai tsula,gasunan ku kunna mana"ta nuna musu home theater.

Ayko kunna wa?ar ado gwanja sukayi ta safeera.

abinci da abunsha taraba musu,bayan ta ba kowa ne
ta haura da gudu Wakin naim,wanda ?arar wa?ar tasashi ya tashi abacci,ganinta ta shigo fuskarta Wauke da faraa ne,yasa ya dubeta yana murmushi yace"madam radion yayi yawa sautin ko ke be damekiba?"

wani irin tafi tayi tayi tsalle ta dire,ta girgiza kafaWarta,tayi wani juyi,tace.

"SUMURISE"ta faWi tana washe baki.

dariya yayi yace "surprise de ko"

"GAS WAT"ta sake faWi cikin shau?i dake nuna tsantsar farincikin datake ciki

dariya naim yake sosai,dan yafahimci abinda takeson faWi.

"Zakina yau ranarkace,dan haka taso muje falon ?asa kaga abun mamakin dana shiryama irin naku na ?an birni"cewar sajeeda tana janshi.

Mi?ewa yayi yana dariya tasa hannu ta rufe masa fuska,yana gaba ita abaya suka nufo falon fuskarsa Wauke da faraa.

suna shigowa,tsakiyar falon,tsula ri?e da cake Win na musamman ya tsaya agaban naim,sajeeda tana cire hannunta a idon naim Win suka fara masa wa?ar happy birthday to you"

robar kunun za?in datayi ta Wauka ta buWe murfin,sannan tasa tafin hannunta ta toshe bakin ta jijjiga da kyau ayko tayi kumfa,tazo dede setin naim Win ta cire hannunta ta Waga sama tana zazzaga masa azuwan champagne,cikin ?an?anin lokaci fuskar naim tayi farin gasara,kan ya farga ta lakuto manja me yajin jikin cake Win ta lanchaSa masa afuska setin ido,tana masa wa?ar itama.gamida ti?a rawa ta gani ta faWa mijinta na birthday.

naim wanda kusan zamu iya cewa ya suma a tsaye,lokacin dayaga irin ri?a??un ?an daban dake tsaye tsakiyar falon gidansa da matarsa atsakiyarsu,tana rawa.duk da azabar manjan daya shigar masa ido,naim ya gaza kulle idon tsabar tashin hankalin da yake ciki.

Wata uwar tsawa ya daka musu,me razanarwa,ayko cak suka,tsaya,radion ya kashe,sannan ya dubi su tsula

5 / 9